Tsantsar Kauna Page 20 - Abokiyar Hira Novels

 

Haihuwar Fatima

Tsantsar Kauna - Kashi na 20

Na Tahir Yusuf (Novels Elite)


Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.


Abinda bai wuce mintuna 15 ba Suhaila ta karaso asibiti ta same mu a reception, na karba kayan na mika ma wata ma'aikaciyar jinya da ke inda Fatima take, Masha Allah, Ba'a dade ba Nurse ta Fito da Jariri kato kyakkyawa, ma'ana Fatima ta haifi da namiji. Nayi hamdala na gode ma Allah da irin wannan kyauta kta Allah ya bani wanda ba kowa ke samun irin sa ba. "alhamdulillah" abinda na fada kenan bakina kuwa kasa rufe shi nayi. 

Wani Daki aka kaimu kafin a fito da Fatima, Suhaila ce ta kira Maman su Fatima ta sanar dasu.


Kiran Mamana na yi a waya don sanar da ita "Assalamu Alaikum Mama, Albishirin ki" 

tace "goro"

"kinyi miji, Fatima ta haihu"


Mama cikin Murna tace "Alhamdulillah, Allah ya raya"


Nan da nan haihuwar Fatima ya gama zagaya dangi, kafin wani lokaci yan uwa na kusa da yawa sun zo asibitin daidai lokacin an fito da Fatima daga dakin haihuwa wato (Labour Room). Anyi ta yi min Barka Yan uwa da abokai. Sakamakon ta haihu babu wata matsala basu dade ba a asibitin aka sallame mu, muka koma gida.


Nayi ma yaro khuduba da suna Abubakar wanda hakan yayi matukar faranta ran Fatima. Bayan gama khuduban muna zaune nake tambayar ta wani suna zamu dinga kiransa dashi? Cikin d'oki ta kalleni tace "Gaskiya ban san ta yadda zan gode maka ba, nayi Farin ciki sosai, Zamu kira da Affan , amma kai me ka gani?"

duk abinda kike so Fatima ina so Allah ya raya shi bis sunnah. Na kada kaina nayi waje sakamakon mutane da suka fara zuwa. Zan fita ita kuma matar Abdullahi zata shiga gidan. muka gaisa ta wuce ni kuma na fita.


Kwana biyar da Haihuwar Fatima daidai lokacin na gama komai na gidana komawa kawai ya rage wanda dama nace a can za'ayi suna zamu koma. Bayan da dare yayi babu kowa sai kanwar Mamana da ta zo zama da Fatima saboda haihuwar farko ne wasu abubuwan sai an koya mata, na gaida ta kafin ta koma falo.


"Fatima in sha Allag Gobe Ina so zamu Koma gidan da na gina, acan nake so ayi suna"

Murna ya cika zuciyar Fatima ta dan kalle ni ta ce "duk abinda ka yanke babu wani abu da zance, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sa mu koma lafiya"

Dama kayan mu wadanta zamu koma dasu can gidan a hade suke, sai wadanda zamu kyautar da su. Bayan na gama maganar da zamuyi da fatima na wuce gidan mu wanda dama acan zan kwana, Mama na iske a daki na sanar da ita, nake tuna mata idan Allah ya kaimu gobe zan koma gidan da na gina, bayan haka kuma zan gyara muku naku in sha Allah. "Gaskiya na yi farin ciki Kamal, Allah yasa a koma lafiya, Dan Allah ka kula da Fatima, kaga tana son ka sosai" na dan shafa keya ta nace "in sha Allah zan kula da Fatima sosai Mama.


washe gari kuwa muka kwashe kaya tare da yan uwa da abokan arziki da suka zo aiki kafin suna muka rankaya sabon gida.


"Alhamdulillah wannan irin gida haka, gasiya gidan nan yayi kyau sosai" Aunty Salma ce ke fadin haka yayin da take zagaya bangaren fatima, 

"Gaskiya Kamal yayi kokari sosai Allah ya saka masa da Alkhairi."


An saka ma yaro suna Abubakar, Raguna biyu Kamal ya yanka, abinci kuwa saidai idan baki je gidan suna ba, Kamal ya tanadar da abinci kala-kala sakamakon gudun mawar da yayi ta samu wajen mutanen da abokan kasuwancinsa.

cikin Gida kuwa mata ne yan uwa da abokan arziki ke ta hada-hada. Fatima kuwa Kamal yayi mata dinkuna kala-kala wanda zata saka ranar suna, rayo kuwa ba'a maganar irin kayan da ya samu, idan kaga Fatima bazaki dauka itace maijegon ba don tayi kyau sosai, kewaye take da kawayen ta a cikin dakin ta, ko ina na cikin gidan mata ne kawai.


Mu haɗu a kashi na 21 


#tsantsarkauna #novelselite #tahir_yusuf

Post a Comment

Previous Post Next Post