Tsantsar Kauna Page 19 - Abokiyar Hira Novels

 

Sanadin kudin Kamal

Tsantsar Kauna - Kashi na 19

Na Tahir Yusuf (Novels Elite)


Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.


Tare muka koma daki na kwanta tun muna magana ina jin Fatima har bacci mai nauyi ya daukeni.


Ban iya tashi da wuri kamar yadda na saba ba, duk da nayi bacci da wuri, da kyar nayi sallar asuba itama a makare nayi kafin na koma bacci. Suhaila kuwa tun karfe dakwas ta gama gyaran falo ta tafa ruwa ta saka a cikin flask ta hada kayan karyawa. Bamu tashi ba sai tara saura, wanka nayi kafin itama fatima tayi wanda yau ta tashi ran ta a bace ban san menene dalilin hakan ba, ko wankan a bata sami yi ba brush kawai tayi ta fito falo kan teburin cin abincin ko da ta zauna ruwan shayi kawai tasha sannan ta koma cikin daki ko alamun fara'a babu a fuskarta.

hankalina ya tashi sosai gain yadda naga Fatima ba yadda na saba ganinta ba lokaci daya ta canja daga Fatima da na sani a baya.


Ban bita ba sai da na gama cin abinci sannan na tashi na shiga ciki na same ta kwance a gado, nayi magana amma ko kallo na batayi ba, raina ya baci sosai don na rasa yadda zanyi, daidai karfe goma na safe na fita zuwa gidan Abdullahi domin tattaunawa kan yadda zammu fara gudanar da kasuwanci.

 Gidan mu na fara zuwa saboda na gaida su Mama domin kwana biyu bana nan, a cikin gida na same ta tana sauraron radio Baba kuwa wanda tuni ya fita daga gida zuwa kasuwa. Na gaisheta sai muka shiga cikin dakin ta in da na bata labarin yadda tafiyar mu ta kasance da abinda zamuyi nan gaba. Mama tayi matukar murna tare da saka ma kasuwancin da zamu fara albarka. Sanna ta Kalle ni ta ce "Kamal ka zama mutum na gari mai kirki sannan ka rike gaskiya a dukkan al'amuran ka, kuma ka zama mai dogaro da Allah samu da rashi Allah ne ke badawa a duk lokacin da yaso. Zai iya kasancewa yau ka samu gobe ka rasa ko kuma ka rasa, don haka kada ka zargi kowa wannan jarabawa ce daga Allah.

Nayi murna sosai da irin shawarar da Mama ta bani da kuma aduu'o'in da tay min, na Mata sallama nace zan tafi Gidan Abdullahi ne yanzu. tace "Allah ya kiyaye hanya" na ce Amin, na tashi na fita.


Tare na same shi da matar sa a falo sun gama karyawa suna zaune, Ahmad kuwa na wasa a gefe guda. Tashi tayi tare da daukar Ahmad suka shiga ciki domin mu sami daman magana a natse. Abdullahi ya kalle ni cikin farin ciki ya ce "Nayi Magana da wani Alhaji Sadi wanda ke sayar da motoci a Sabon Gari, na tura masa motocin ya gani kuma ya bani taccin motocin suna da kyau kuma yana so, zamu kai masa motocin inda ya ke sayar da motoci yau da yamma ko gobe idan Allah ya kaimu." nayi murshi sannan na godema Allah. Shima nan mukayi Sallama na koma gida. 


Assalamu Alaikum, da Mamakina na ji ta amsa da "Amin Wa'alaikassalam"

kamar ba itace take fushi ba dazu sannan na shigo na zauna kusa da ita.

"Kamal dan Allah kayi hakuri dazu na rasa me ke min dadi ne zuciyata naji tana ta tafarfasa da jin haushi shiyasa ma ko maganar kaban amsa. Dan Alla idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri"

Haba Fatima babu komai koda raina ya baci ganin ki yanzu yasa komai ya wuce Allah ya kara mana zaman lafiya.


Tun daga samun cikin Fatima Mama ke ta yan saye-sayen kaya na yara tana ajiyewa, kuma tana yawan kiranta don jin lafiyar ta, tare da aikamata da dan abinda baza'a rasa ba wanda tasan zata bukata lokaci zuwa lokaci.


Masha Allah an sayar da mota mun ci riba sosai, mun fara kasuwanci da sa'a, hakan ya samo asali ne na biyayya da addu'ar iyaye. babu abin da zamu ce sai da hamdala da godiya ga Allah.


Daidai Lokacin da cikin Fatima ya kai wata biyar lokacin kuma kasuwancin mu sai habaka yakeyi, ya kai ga yanzu ba sai mun je Cotonou ba Magana da Jamilu kawai mukeyi mu tura kudi sanna a kawo mana motoci. Ganin yadda kasuwar ke ci ne ma yasa ukayi shawarar bude namu wajen sayar da motar. Alhamdulillah mu samu nasarar yin rijistan Kamfanin mu da zamu rika amfani dashi wajen saye da sayar da motoci tare da Taimakon wani Lauya mai suna Barrister Najib.

Mun sakama kamfanin mu suna "A&K Motors Ltd" masha Allah Kamfanin mu ya sami karbuwa wajen mutane sosai saboda muna kawo motoci na yayi masu kyau.


Tafiya Tayi tafiya kamfanin mu ya wadata da motoci iri-iri sababbi da wadanda ba sababbi ba.


Sannu a Sannu Cikin Fatima ya kai wata 7, ni kuma na maida hankali kan ginin da na fara wanda an gama kashi 90 cikin 100 kuma ina jira ne idan Fatima ta haihu sai mu koma a can za'ayi suna. Gida ne flat guda biyu ko wanne yana dauke da dakuna uku sai boys quarters a gefe guda da dan tsakar gida amma ba wani babba bane sosai ba bai wuce a ajiye motoci guda uku ba a ciki.


Tun Fatima na zuwa awo duk sati yanzu ta koma zuwa bayan sati uku ko wata ya taganta da yadda lafiyarta yake. Tana bin duk wasu dokoki da ake gindaya mata a asibiti. 


lokacin da cikin ya kai wata 8 an shawarce ta ta kada ta dinga yawan zama ita kadai kuma kada ta dinga zama waje daya ana so ta rika motsa jiki wanda hakan yasa lokaci zuwa lokaci idan na dawo da daddare zan dauke ta mu fita a kafa.


Duk abinda nasan ana bukata na haihuwa na siya an ajiye. Ina cigaba da Kasuwanci kuma hankalina na wajen Fatima domin yanzu ne take neman kulawa ta hakan yasa na nemi hutu na sati uku na bar Abdullahi da jan ragamar kasuwancin mu wanda a da tare mukeyin komai.


Tun da cikin Fatima ya shiga wata na 9 yanayinta ya canja sosai da kyar take wasu abubuwan. Bayan na dawo daga gida gaida Mama, Na same ta zaune cikin falo tana cin tuffa din da na siyo mata, nan ne take ce "Kamal ina jin wani iri a jikina marata na min ciwo sosai" da sauri na tashi nace mata ta tashi mu tafi asibiti, bata wani bata lokaci ba ta kira Suhaila ta sanar da ita "zamu je asibiti mu dawo yanzu kada ki ji ba kowa a gidan" 

Suhaila ta ce "To Aunty Fati, Amma lafiya kuwa"


"Bakomai zamu je ganin likita ne kawai"


"To Allah ya kiyaye hanya, Allah ya baki lafiya"


Ni da Fatima muka tafi asibiti da niyyar a duba Fatima, muna Zuwa suke ce ai haihuwa zatayi, suka fadi duk abinda suke bukata na haihuwa. Ni na Kira Suhaila da ta dauko kayan wanda dama tuni Fatima ta hadasu a waje daya.


Abinda bai wuce mintuna 15 ba Suhaila ta karaso asibiti ta same mu a reception, na karba kayan na mika ma wata ma'aikaciyar jinya da ke inda Fatima take...........



Shin me Fatima Zata haifa, mace ko namiji, Da kanta zata haihu ko kuma aiki za'ayi mata? sai kun biyo mu a kashi na 20 don jin amsoshin wadannan tambayoyi.


Dan Allah idan kun ga kuskure a gyara min domin wannan shine littafi na na farko.


kada a manta ayi comment sannan ayi sharing wannan post din domin wasu ma su sami nishadin dake cikin wannan littafin

Post a Comment

Previous Post Next Post