Tsantsar Kauna - Kashi na 18
Na Tahir Yusuf (Novels Elite)
Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.
Kada ki saka damuwa a ran ki Kamal dinki kullum zai dinga debe miki kewa sai na dan ja hancin ta na ce "wa yaga Fatima na da Jariri" hakan yasa da fashe da dariya mai karfi hakan ya nuna min cewa ta samu natsuwa sannan na sumbaci kumatun ta, ta sake rungume ni na dan wani lokaci kafin mu rabu.
Cotonou
Alhamdulliah! munyi nasarar tafiya in da muka isa cikin Cotonou Karfe Takwas na dare inda muka kira Jamilu dan asalin Nigeria ne amma yana zaune a can, ya sauke mu ya bamu abinci muka ci, sannan muka yi fira kadan sannan mukayi bacci.
Da safe karfe 9am muka fita don mu zagaya muga gari tare da Jamilu kafin mu fara maganar siyan muta, har kasuwan motocin ma ya kai mu inda muka ga abubuwa da dama. Bamu dawo ba sai karfe 2pm na rana mukayi wanka muka ci abinci.
kiran Fatima ne ya katse min dan baccin da na fara "Assalamu Alaikum, Dafatan kun sauka lafiya. Tunda baka kira ni ba"
Wa'alaikussalam, Dan Allah kiyi hakuri, Rayuwata, mun sauka a gajiye ne kuma yau mun fita zaga gari
"To amma koda sako sai ka tura min amma baka yi hakan ba."
Yanzu dai kiyi hakuri hakan bazai sake faruwa ba In Sha Allah. Da haka firan Ya koma na soyayya, mun kwashe kusan minti 40 muna waya kafin katin wayar nawa ya kare.
karfe 5 na yamma muka sake fita tare da Jamilu da wani abokinsa dan asalin Cotonou, domin zuwa uji farashin motoci kafin mu siya. Mun shiga Kasuwa kai tsaye ofishin dilallan motoci muka wuce, nan muka sami dillalai guda biyu wanda zamu duba motoci dasu. Bamu bar kasuwa ba sai karfe 9pm na dare sannan muka dawo gida.
Masha Allah mun sami damar siyan motoci guda uku, sannan kuma na siya kayan sawa na maza da mata da yawa na sauran kudin da ya rage anyi custom duty da duk wata takardar da ya kamata ayi. muka fara shirye-shiryen dawowar mu gida. Mun saba da Jamilu sosai saboda yana da kirki, kuma ya cika mutum.
Mun gama hada kayan mu da zamu dawo gida ya hada mu da wadanda zasu kawo mana motoci wanda dama aikin su kenan. Sun yanke mana kudin da zamu biya su mun biya harda abincin da zasu ci. An bamu komai da komai na motocin da muka siya. Karfe 6pm na yamma muka bar Cotonou muka dauka hanyar dawowa gida Nigeria.
Mun biyo jerin gwanon motocin da suka taso daga Cotonou zuwa Nigeria, Kwanan mu daya da yini daya muka shigo garin Jibia dake jihar katsina karfe 4 na yamma nan muka tsaya hutawa taer da cin abinci dama tuni yunwa ta gama wahalar dani.
Bayan Muna tsaya na Daga waya na Kira Fatima na shaida mata gamu a Katsina, in sha Allah yau zamu dawo gida. Tayi murna sosai. Mun ci abinci mun huta sannan muka cigaba da tafiya.
tun Bayan gama wayar ta da Kamal ta Kira Suhaila, suka shiga kitchen aka fara shirya abincin taran Kamal tare da Gyara ko ina na cikin gidan. Ko ina na cikin Gidan Kamshin Turaren wuta da na abincin da Fatima ta dafa da Kan ta.
Karfe 7pm na yamma suka shigo cikin garin Zaria birnin Ilimi, gidan Abdullahi suka wuce kai tsaye domin ajiye motocin da suka siyo. Direbobi kuwa nan gidan Abdullahi suka sauka don hutawa da cin abinci kafin a kaisu wani dan karamin hotel dake unguwar su kwana zuwa gobe sai su koma.
Ban shiga Gida ba sai 7:52pm tare da kayan da na siyo da tsarabar da nayi ma Fatima. Ina yin Sallama ta taso da sauri ta rungume ni nima na rungumeta, shiruuuuu muka tsaya, gyaran Muryar Suhaile ne ya dawo damu duniyar mutane.
Ta ce "Barka da Zuwa, Yaya Kamal"
Na amsa, amma a cikin zuciyata ina fadin meyasa kika zo a wannan lokacin.
Daki na wuce nayi wanka sannan na zauna kusa da Fatima mu ka ci abinci, ba muyi wani hira saboda gajiya da baccin da ke idona.
Tare muka koma daki na kwanta tun muna magana ina jin Fatima har bacci mai nauyi ya daukeni.
Nima zan ce mmuku saida sa fe idan mun hadu a kashi na 19 don jin yadda kasuwancin su Kamal zai Fara.
kada a manta da Share da comment domin karfafa mana gwuiyar rubuta wannan littafin'
nagode
Na Sadaukar da wanna Shafin ga Duk wata mai Suna Khadija.