Tsantsar Kauna - Kashi na 17
Na Tahir Yusuf (Novels Elite)
Wannan Littafin free ne ba na sayarwa bane.
Da safe bayan na dawo daga sallar asuba, na sami Fatima zaune kan dardua tana addu'a, ban koma na kwanta ba na zaune kusa da ita nima na daga hannu ina yin addu'ar tare da ita.
Bayan gama addu'ar ne mukayi gajeruwar fira mai dauke da soyayya da kaunar juna, daga nan na koma falo na zauna, Suhaila kuma kitchen ta shiga ta fara shirye-shiryen abin karyawa, fatima kuma a daddafe ta Gyara cikin Daki sannan itama ta fito ta zauna.
"Fatima, gaskiya da wuya idan zan tafi Kaduna Dinnan, bana jin zan iya zuwa. ni da abokina Abdullahi zamu fara kasuwanci" Fatima ta Gyada kai tace "amma meyasa baza kaje ba?"
Na dan yi murmushi na kalleta sannan nace "bana son aikin gwamnati na fison kasuwanci"
"To yanzu wani irin kasuwanci zaku fara"
ina da wasu kudade da nake tarawa a cikin banki na wanda ban taba cire ko naira ba, yanzu haka sun kai naira miliyan 3 da su nake so na fara
"Allah ya sa hakan shine abinda yafi zama alkhairi a garemu baki daya"
na Amsa da amin, kafin na gyara zama na juya da kyau na kalle ta sosai, na ce "Fatima addu'a kawai nake so a yanzu, domin mota zamu fara sayarwa tare da Abdullahi shima wajen shi akwai wasu kudaden."
"Amma kayi magana da mama tukuna kafin ka fara komai"
Eh, munyi shawara da ita, kuma ta amince.
Muna zaune da fatima Suhaila ta kawo abin karyawa, naji dadi sosai ganin yadda Fatima ke cin abincin, kamar ba ita ba ce ta kasa ci jiya.
Bayan gama cin abincin, nayi wanka na fita don haduwa da Abdullahi don tattauna ta yadda zamu fara siyan mota da inda zamu sayar da su.
Kai tsaye Majalisa na wuce, inda Abdullahi ya ce na same shi, nan kuwa na same shi zaune yana danna wayarsa. Alhamdulillah, mun tattauna sosai mun cimma matsaya, don Cotonou zamu tafi a siyo mota guda hudu don farawa, hadda inda zamu saida mun samu, ban dawo gida ba sai karfe daya na rana, bayan munyi sallah na shiga gida.
Falo na sami Fatima da Suhaila suna fira wanda shiga na yasa Suhaila ta tashi ta shiga daki ta barmu, tunda na shigo falon Fatima ke rufe hanci wai turarena yana wari, dole na cire kayan jikina kuma nayi wanka kafin na fito na fada mata yadda mukayi da abokina.
Bayan kwana biyu da maganar mu da Adullahi, yazo gida na muka hadu, muka sanya ranar tafiya Siyo mota, don an hada mu da wani mutumi a can wanda zamu same shi bayan mun siya za'a yi masu takardu wato custom duty. mun gama tattaunawa tsaf, ya koma gida nima na shiga ciki.
Dare yayi sosai ta tashi zata sha tea duk da baccin da ke idona lhaka na tashi na hada mata na kawo amma da kyar ta iya shan rabin kofin da na zuba duk da kankantar kofin.
washe gari na fada mata yadda mukayi da ranar da zamu tafi ta kalle sanna ta marairaice tace "Yanzu zaka sake tafiya ka barni"
Cikin Tausayi na kalle ta "haba Fatima ba dadewa zanyi ba kuma ai ga Suhaila nan"
"Suhaila da ban kai da ban, dan Allah kada ka dade"
In sha Allah ba zamu dade ba Fatima na. Nayi ta rarrashin ta don naga ta dan shiga damuwa, kuma ba'a so tana shiga damuwa ko kadan sakamakon cikin da take dashi, wanda zai iya cutar da ita da abinda ke cikin ta. Da kyar na iya shawo kan ta har sai da naga tana dariya sosai.
Yau Shine Ranar da zanyi nisa sosai da Fatima wanda a baya ban taba yin irin shi ba, na gama shiryawa tsaf don Abdullahi ma ya dade da kira na akan ya shiryawa. Fatima dai dan babu yadda zata yi ta hana wannan tafiyar ne amma da ta hana, rungumo ta nayi jikina ntare da rike hannunta na
"Fatima kiyi hakuri in sha Allah yadda na barki Lafiya in Sha Allah haka zan dawo na same ki lafiya, bana so kina daga hankalin ki saboda hakan zai iya zama wata matsala ta daban duba da abinda ke cikin ki, ki saka a ranki kullum Kamal yana tare dake a ko wani irin hali na wuya ko dadi"
"To amma fa sai kunyi kusan kwana biyar, gaskiya yayi yawa ga inda zaku da nisa"
Kada ki saka damuwa a ran ki Kamal dinki kullum zai dinga debe miki kewa sai na dan ja hancin ta na ce "wa yaga Fatima na da Jariri" hakan yasa da fashe da dariya mai karfi hakan ya nuna min cewa ta samu natsuwa sannan na sumbaci kumatun ta, ta sake rungume ni na dan wani lokaci kafin u rabu.............
Shin Kamal suna samun Abinda suka je nema kuwa?
sai mun hadu a kashi na 18 don jin yadda rayuwar Kamala da Fatima zai cigaba lokacin da basa tare.
Ina son jin ra'ayoyinku
Kada a Manta ayi Comment sannan ayi sharin domin wasu ma su karanta