Tsantsar Kauna 16 Abokiyar Hira Novels

Page 16 Tsantsar Kauna

Tsantsan Kauna - Kashi Na 16


Na

Tahir Yusuf (Novels Elite)


Na sami Fatima har tayi bacci, na barta ban tashe ta ba, da ƙarfe 12 na rana Naman Fatima da Ƙanwar Fatima suka kawo abinci, amma sun sami Fatima Tana Bacci. Na tarbe su,


“Sannu Kamal, ya njikin na ta” Mama ce tayi Magana,


Alhamdulillah, jiki yayi Sauki sosai ba wani abu ne sosai ba Zazzabi ne kawai, likita ma yace idan wannan Ruwan ya Kare za’a sallame mu mu koma gida.


Ban fada mata asalin abinda k eke damun Fatima ba, to amma ga dukkan alamu mama ta fahimci abinda ke faruwa, saboda irin Kallon da naga tanayi ma Fatima sai wani murmushi da naga tayi tare da shafa kan Fatima.




Nan na fita don kiran Ma’aikaciyar jinya wato Nurse domin duba cire abin Karin Ruwan da aka saka ma Fatima, ko kafin na dawo na sami Fatima ta tashi daga baccin da takeyi. Ba’a jima ba nurse ta zo ta cire abin Karin Ruwan dake hannun Fatima. Dr. Salim ne ya shigo tare da nurse wacce ke rike da kudin Fatima na asibiti wato files, yayi wani rubutu sai ya tambayi Fatima “yanzu me ke damun ki?” ta amsa da “babu komai saidai kai na dake min ciwo sai kuma jiki na babu karfi sosai, wani lokacin kuma sai naji kamar zanyi amai.”


“to shikenan babu damuwa, rike wannan takardar, magani ne wanda zaka siya mata, ta rika sh, In Sha Allah zata koma daidai, amma kafin ku tafi kazo office” ya bani takardar tare da zuyawa ya koma office dinsa. Bai jima da fit aba nim ana bishi.




“Fatima sannu, ya jikin. Allah ya Kara sauki” ta amsa tana murmushi na karfin hali saboda ciwon da kan ta ke yi.




Na sami Dr. Salim cikin Office zaune yana rubutu, na sami lkujera a jefe na zauna, bayan y agama rubutun ya dago kansa yak alle ni, “Kamal dan Allah a kula kada a bari tayi aiki mai yawa ana so ta dinga samun bacci isasshe, kada tayi aikin da zai sa tayi amfani da karfi, kamar daukar abu mai nauyi” Na na amsa da in Sha Allah zan kula sosai. Har na Tashi zan fita ya kira ni “Karin wani abu ma, a ‘yan wannan watannin ba komai ne zai mata dadi ba, ko da kuwa irin abincin da ta fi so ne” na sake amsawa da to a karo na biyu, mukayi sallama na juya na fita.




Kafina Nakoma dakin da Fatima take sun gama hada kayan da suka zo dashi dukka, Mama ta rike mata hannu muka fita. A bakin kofar asibitin ne muka sami adaidaita sahu muka shiga, mun isa kofar gidan mu amma Mama tace baza ta shiga ba, nayi magiya amma taki shiga, sai n ace da mai Adaidata ya kaita gid ani da Fatima da Yar uwarta muka shiga gidan tare.




Kasancewar gidan tun safe babu kowa kuma ba’a gyara ba, Fatima ta umurci Suhaila da ta gyara gidan sannan tayi masu girki. Suhaila ta gyara gida tsaf sannan kuma tayi girki. Fatima dai bata iya cin abincin ba saidai wani abinci aka nema mata.




Tun komawar Mama Gida kuwa, tayi ta kokarin kiran Alh. Abubakar don yi masa albishir amma wayarsa bata shiga, tayi ta gwadawa amma bata samunsa sai ta hakura. Karfe biyar da rabi ne Alh. Abubakar ya shiga gida, ko hutawa bata bari yayi ba ta sanar dashi abinda ya faru. “Alhamdulillah, yanzu ya jikin Fatima?’’




Mama tace “jikin Fatima ya yi sauki sosai don yanzu haka ma suna gida, amma na hada ta da Suhaila domin ta taya yan aikace-aikacen gida kafin ta sami sauki.




Tun daga samun cikin Fatima, budi yayi ta zuwa min ta inda ban yi zato ba. Allah kenan mai yin yadda yaso, idan yaso sai ya gwada ka ta kowace hanya.




Bayan sallar Isha’i ina zaune a falo kan kujera Fatima tayi matashi da cvinyoyina muna fira, karar wayata ne ya dawo damu daga cikin kogin soyayyar da muka fada, sai naga wata lamb ace wacce ban san ta ba kamar bazan dauka ba, saidai na daure na dauka don ban san wanene ne ko menene dalilin kiran ba, “Assalamu Alaikum”


“Wa’aikumussalam” na amsa cikin girmamawa domin daga jin muryar kasan na babban mutum ne.


“da fatan ina Magana da Kamal Umar”


Eh da shi kake Magana.


“Suna na Suleiman Zakari, Admin officer na FIRS, idan ba damuwa muna so ranar Monday kazo da takardun makarantar ka office din mu dake Kaduna, mun tura maka sako ta e-mail Dinka da duk irin abinda muke bukata”


Na amsa da In Sha Allah zan zo. Mukayi sallama na kashe waya ta.


“Allah yasa dai lafiya,”


Fatima ce ta tambaye cikin kosawa taji menene, ”Ana nema na a Kaduna ranar Monday, ana bukatar na tafi da takardun karatuna”


“Alhamdulillah, gaskiya nayi murna sosai, Allah yasa a dace”


Da haka mukayi dogon fir ani da Fatima, Suhaila kuwa tuni tayi bacci.


Mu haɗu na kashi na 17


Kada a manta ayi sharing da comment domin muna son jin ra'ayoyin ku game da ko wani page idan mun saka

Post a Comment

Previous Post Next Post