Tsantsar Kauna Page 15 - Abokiyar Hira Novels

TK labarin Soyayyar mai nishadi

Tsantsar Ƙauna kashi na 15


Na

Tahir Yusuf (Novels Elite)


Sai da muka ɗan yi shiru na ɗan lokaci, muna jin zuciyoyinmu na bugawa a daidai sauti, kamar su na fahimtar juna, Daga nan nace, "Fatima, duk inda nake, ko menene nake yi, bana jin cikakken mutum sai idan kin kasance kusa da ni."


Tayi murmushi, idanuwanta na ɗauke da hawaye marasa nauyi, tace, "Kamal, wallahi kai kadai ne wanda zuciyata ta taɓa amincewa dashi gaba ɗaya. Da kai nake jin amincewa, lafiya, da soyayya maras iyaka."


Muna wannan fira ne har Lokacin sallar Magriba ta, nan na barta na tafi masallaci, ita kuma ta shiga kicin don ɗumama abincin da zamu ci, na yau sallah na dawo, na sake ta cikin falo zaune tana jira na dawo mu ci abinci. "Kai wannan irin abinci haka, kamar ba a kasar nan aka dafa wannan abincin ba." Ni ne na faɗi hakan cikin zukata. Ita kuwa Fatima Murmushi kawai ta saki min tana kallo na, da haka muka gama cin abincin ina tsokanar ta itama tana Tsokana ta.


Bayan na dawo daga Sallar Isha, Nace mata ta tashi mu tafi, ba mu tsaya ko'ina ba sai gidan Abdullahi, babban abokin Kamal, Ya riga Kamal ɗin yin aure don kuwa har yana da yaro guda ɗaya, nan muka same su zaune suna kallo Ahmad kuma yana bacci a kan kujera. 


"Yau dai ga Kamal da Fatima" Abdullahi ne ya faɗa haka tare ta rike hannuna, ita kuwa Khadija ta rungume Fatima suka gaisa cikin mutunta juna, nan sukayi doguwar hira. Duba agogon wayata nayi naga ashe har ƙarfe 10pm na dare muna can muna fira. Sallama kawai Mukayi Ni da Fatima muka koma gida.



Washe gari kuwa Fatima ta tashi da wani matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, wanda dole sai da muka tafi asibiti. Minti Sa'a muna zuwa muka ga likita nan aka ba Fatima gado, wata nurse ta saka mata ruwa. 


"Menene tsakaninka da ita?" Likita ne ke tambayar Kamal da ke zaune kusa da Fatima, "Mijin ta ne Ni."

"Ka same Ni a office." ya faɗa ma Kamal tare da juyawa ya fita zuwa office ɗin sa, na Kalli Fatima nace "jira ina zuwa" Nima na fita zuwa office ɗin Dr. Salim.


"Assalamu alaikum" na tsaya jira ya bani umarnin shiga.

"Wa'alakumussalam, Shigo."

Na shiga ya nuna min kujera na zauna.

"Bayan duk wasu gwaje-gwaje da muka yi wa Matarka. Ya nuna tana ɗauke da ciki har na tsawon sati biyar" na ɗaga hannu nace Alhamdulillah Dr. Salim ne ya katse min wani dan guntun tunanin da na fara "yanzu tana buƙatar hutu, ba'a son tayi aiki mai yawa, ba komai zata riƙayi ba har nan da cikin yayi ƙwari.

Dr. Salim ya rubuta min wasu magunguna da zan siya nayi sallama da shi na fita.


Na sami Fatima har tayi bacci, na barta ban tashe ta ba, da ƙarfe 12 na rana Naman Fatima da Ƙanwar Fatima suka kawo abinci.........


Mu haɗu a kashi na sha shida.

Post a Comment

Previous Post Next Post