Tsantsar Ƙauna kashi na 14
Na
Tahir Yusuf (Novels Elite)
Munyi nisa sosai don bana jin abinda mutanen motar ke faɗa sosai saboda karatun da nake ji. Wani ƙara naji wanda ya tsorata Ni har sai da na cire karatun da nake ji jikina babu inda baya rawa, kowa salati kawai yake yi shi kuwa direban motar yana ta ƙoƙarin komawa da motar kan hanyar da Yakamata yabi Saboda kaucewar da tayi sakamakon fashewar da tayar mota tayi, gaban mu kuma ga wata babbar mota nan tana zuwa abinda ya ƙara firgita mu kenan. "Innalillahi wa'inna Ilahirraji'un" abinda kawai kake iya ji a cikin motar kenan. Direba kuwa ya natsu yana ƙoƙarin dawo da motar kan hanya, da ƙyar ya kauce ma wannan babbar motar ya koma hanya daidai inda a hankali ya cigaba da tafiya da ita har ta tsaya da kanta. Nan da nan muka fito saukowa ya jiƙe da zuwa masu haɗaka nayi masu yin fitsari nayi, haka masu kiran yan uwansu da kira.
Alhamdulillah! Mun tsira dai babu wanda ya ji ciwo saidai firgici ya cika zuciyar kowa dake cikin motar, babu abinda nake tunawa sai waya na ƙarshe da Mukayi da Fatima, ashe wannan abin ne zai faru naji jikina babu daɗi.
Allah yasa ma direban mu na da wata tayar, ya ɗauko sannan ya ɗauko abin ɗaga mota wato (Jack) a turance, muka taya shi ya canja taya, kowa ya koma mota. Tunda aka cigaba da tafiya motar tsit kamar anyi mutuwa, kowa yayi shiru saɓanin yadda muka taso daga Abuja.
Bayan abinda bai wuce awa 1 da rabi ba muka shigo cikin garin Kaduna inda aka wuce damu tashar motar kawo in da zan hau motar da zan koma Zaria. Ban jima ba a cikin tasha mota ta cika inda muka ɗauki hanyar Zazzau.
Tun bayan gama wayar Kamal da Fatima, bata zauna ba aikace-aikace da gyaran gida kawai takeyi, bayan ta gama aikin, ta girka abincin da tasan Kamal ya fi so ta jera su a kan teburin cin abinci, sannan ta yi wanka ta shirya cikin atamfa ɗinkin doguwar riga, tana jiran dawowar Mijinta.
"Allah ka sauke mu lafiya" abinda nake faɗa kenan a cikin Zuciyarsa Sai kuwa addu'o'in da nake yi na neman tsari. Duk jikina yayi sanyi daga ka lalle Ni kasan akwai abinda ke damina, amma bana so nake gida da wannan samuwar bana so Fatima ta san abinda ya faru.
Tafiyar da bai wuce awa 1 ba muka isa garin Zaria, ƙofar doka aka ajiye mu, na tare mai tashin na fada masa inda zai kai Ni, baiyi wata-wata ba ya kai i har ƙofar gida. Kafin na shiga gida na daure na boye damuwarta. Sallamar da nayi shine ya dawo da hankalin Fatima daga tagumin da tayi kallo ɗaya zaka mata kasan akwai abinda ke damunta. "Amin wa'alakumussalam" Fatima ce ta amsa tare da tasowa da gudu da rungume Ni, ta sauri na ɗaga ta sama sannan na sauke ta na sumba i kumatunta. "Ya gajiyan hanya"
Na amsa da Alhamdulillah
"Muje ga ruwa can kayi wanka sai kazo ka ci abinci"
Ban yi musu ba na shige ciki nayi wanka na saka ƙaramar riga da wando marasa nauyi.
Na fito na samu ta zuba abinci, Ni kawai take jira, dama ina jin yunwa amma ban iya cin abincin sosai ba, bayan gama cin abincin ne Mukayi dogon fira.
Ki shirya bayan Magriba zamu je Unguwa. Ba tare da tambayar inda zamu ba ta amsa da "to ba matsala, Allah ya kai mu."
Fatima, naga kin ƙara kyau ne menene sirrin?
Rufe ido tayi tare da kwantar da kan ta a kafadar na tace "duk wacce tayi sa'ar samun miji irin ka dole tayi kyau, kai ba miji bane kawai, kai garkuwa ne a gare Ni, bana neman komai na rasa a wajen ka."
Na riƙe hannunta tare da kallon fuskar nace, "duk namijin da yawa sami mace mai hankali, tarbiyya, girmama
manya, gaskiya yayi dace"