Tsantsar Ƙauna – Kashi na 13
Na
Tahir Yusuf(Novels Elite)
A rana ta biyu da safe Fatima ta kira Ni domin tambaya ta tana so ta tafi gidan mu ta gaida Mama daga nan zata wuce gidan su. Na bata daman yin hakan nan ma dai Mukayi waya sosai.
Bayan Mun gama waya da Fatima Na shirya Ni da abokina dan Nassarawa domin komawa wajen ranta cewa, Alhamdulillah, munyi duk abin da ake buƙata. Sai dai mu jira sakamako.
Da yamma ina kwance a ɗakin hotel ɗin da muka sauka, Ina hutawa kiran Fatima ne ya shigo wayata, da sauri na ɗauka, cikin murya mai cike da soyayya ta ce " Assalamu alaikum Farin cikin Rayuwata"
Na mayar mata da wa'alakumussalam. Bugun Zuciyata.
"Na yi kewar ka sosai, na kosa ka dawo"
Koyi haƙuri in Sha Allah gobe zan dawo, na zauna tare da Fatima na.
Nan dai muka cigaba da wayar mai cike da soyayya har lokacin da aka kira Magriba daga nan ne kuma ajiye wayar don yin Sallah.
Wasu ranaku sukan zo da nutsuwa mai ƙayatarwa. Bayan kwanaki na biyu a Abuja, na fara shan sabuwar rayuwa cikin jinkirin karɓa, amma zuciyata na bugawa bisa tunanin Fatima. Kamar ba ni ba, duk wata rana sai na duba wayata fiye da yadda na saba, ko don ganin wani saƙon nata ko kuma don kawai jin muryarta a cikin saƙon murya.
Washe gari da safe ina shirye-shiryen dawo wa gida, ina zauna a bakin gado, na danna kiran bidiyo. Daga ɗayan ɓangaren, Fatima ta amsa, tana sanye da hijabinta mai ruwan ruwan zuma, fuskarta cike da annuri.
“Kamal,” ta ce cikin ƙasa da murya, “Na shiga dakinmu, na zauna a kan kujerar da kake yawan kwanciya akai. Sai kawai na fara jin kamar kana kusa. Na tuna da lokacin da kake min dariya, ko lokacin da zaka rike hannuna baka ce komai ba, amma sai nake jin kalamanka suna dawowa.”
Na ɗan saki murmushi, ina kallon kyakykyawar fuskarta.
“Fatima,” na ce, “Zan iya jure komai a duniya amma ban da rashin wannan murmushin baki , ban san yadda zan iya jure rayuwa ba tare da ke ba.”
Shiru ya ɗan ɗebe mana lokaci, amma irin shiru mai daɗi, wanda yake ɗauke da tunanin da alhini.
“Ina jin kamar soyayyar mu yanzu ba kamar ta da ba ce,” ta ce a ƙarshe. “Ta girma, Kamal. Ta zama kamar wani abu da ya wuce jin dadi kawai, ta zama rayuwa kanta.”
“Eh, Fatima. Ta zama numfashi.”
Muka ci gaba da kallon juna, kowanne na jin zuciyarsa cike da ƙauna, da fatan gamuwa, da fatan cika burin zama tare har abada.
Bayan gama wayar mu, na tashi nayi wanka na shiga tsaf, Kaduna na fita na sake kiran Fatima. Kiran na shiga nan da nan Fatima da ɗauka.
"Ya naji kamar Muryar ka ta canja ne" Fatima ce ke tambaya ta Muryar ta cike da tsoro. "Fatima, ina ji kamar bani d lafiya jikina duk babu ƙarfi kamar wani abu zai faru...... "Kamal ɗan Allah ka daina irin wannan maganar, kada k sa na ƙasa natsuwa" da haka dai muka gama wayar cikin fargaba na fita, bayan minti Sallama da abokina dan Nassarawa.
Na hau mota daga Abuja zuwa Kaduna. Mun fara tafiya na dauko wayata na saka karatun Alqur'ani na Sheikh Afif Taj na saka abin sauraro na kunne saboda wurin da ake yi a motar.
Munyi nisa sosai don bana jin abinda mutanen motar ke faɗa sosai saboda karatun da nake ji. Wani ƙara naji wanda ya tsorata Ni har sai da na cire karatun da nake ji jikina babu inda baya rawa, kowa salati kawai yake yi shi kuwa direban motar yana ta ƙoƙarin komawa da motar kan hanyar da Yakamata yabi Saboda kaucewar da tayi sakamakon fashewar da tayar mota tayi, gaban mu kuma ga wata babbar mota nan tana zuwa abinda ya ƙara firgita mu kenan.........
Sai mun haɗu a kashi na sha uku
Kada a manta ayi sharing sannan ayi comment. Nagode.
Domin ƙarin Bayani ko tambaya kuna koya yin magana da i da wannan lambar, amma Whatsapp kawai, pls. 08027058704