Tsantsar Kauna Page 12 - Abokiyar Hira Novels

 

Soyayyar Fatima da Affan

Tsantsar Ƙauna Kashi na 12


Bayan wannan daren, rayuwa ta ɗauki sabon salo. Soyayyar ta da Fatima ta kai wani matsayi na ɗaukaka da fahimta. Yanzu ba wai kawai muna soyayya ba ne, muna zama tamkar rai da jiki. Duk wani motsin daya ke ji, ɗayan zai fahimta ba tare da an furta ba.


Wata safiya, Fatima ta tashi da ciwon kai. Na lura da hakan, Ban tsaya tambaya ba, na shirya mata shayi mai kauri na ɗora a kan teburin cin abinci. Ina sanye ƙananan kaya, ina kallonta da murmushi. Fatima kuwa na sanye da doguwar riga, tana ƙoƙarin murmushi duk da tsananin ciwon kan dake damunta.


“Allah ya baki lafiya,” na ce a hankali, ina matsa ɗan matsa yatsun hannunta. “Bari ni na ɗauki nauyin komai.”


Ta kalle nii da ido mai cike da ƙauna. “Ka yi kamar ni ba matar ka bace, Kamal.”

“Fatima,” na ce da lallami, “ke wata ni’imar Allah ce da ya bani. Kuma zan riƙe da kulawa sosai.”


Yayin da lokaci ke wucewa, wata sabuwar dama da zo min cikin ƙankanin lokaci, An kira ni domin wani aiki da na nema lokacin da BBC ta bude neman ma'aikata sakamakon ba a Abuja ne za'ayi Interview da buƙatar nayi wasu kwanaki. Fatima taji ɗadi sosai amma idan ta tuna zai yi nisa da ita Sai wani bakin ciki ya turniƙeta. "Kamal bani daɗi sosai amma bana so kayi nisa sani"


Tausayi ta ya kamfani sosai, "Fatima koyi haƙuri, kwana uku kawai sanyi in Sha Allah.."


Fatima ta zauna da shi suka tattauna, cikin ƙarfin hali ta ce“Allah ya tsare, ya kuma bada sa'ar tafiya, Kada ka manta da addu’a a duk in da zaka, kariƙe amana, ka zama mai gaskiya, Zan taya addu'a Nima anan in sha Allah zaka yi nasara.”


Na rike rike hannunta. “kada ki damu Fatima zanyi duk abinda kikace in sha Allah. Amma ko menene zai faru, zuciyata tana tare da ke.”


Ranar da zan tafi, na tsaya a bakin ƙofa ina kallonta, tana sanye da hijabi mai launin shudi. Ta dube ni tana murmushi da hawaye a idanunta. Ba sai ta ce komai ba, amma na gane duk abinda take nufi. Wannan shine tafiya ta farko tun da Mukayi aure, ban tafi ko ina ba sai wannan lokaci, ko da yaushe ina tare da Fatima in ba wajen aiki na tafi ba, hakan ya ƙara danƙon ƙaunar da ke tsakaninsu da Fatima.


Kwana na ɗaya a garin Abuja inda na haɗu da wani bawan Allah mai suna Sunusi wanda shine interview ɗin ya kawo shi, amma shi ɗan jihar Nassarawa ne. A nan na fara fahimtar girman lokacin da banatare da Fatima, Amma duk rana, muna waya juna, muna aika saƙonni, muna tuna da wani abu da zai sa dariya a cikin zuciyoyin mu. Har cikin dare, Fatima zata zauna a dakin, ta karanta saƙona tana murmushi.


Soyayyarmu ta canza. Ta girma. Ta yadda babu abinda zai raba sai dai mutuwa.




Kamal dai yana Abuja Fatima tana Zaria, Ko Kamal zai dawo gida ko ba zai dawo a, sai mun haɗu a kashi na sha uku.

Domin ƙarin Bayani ko tambaya kuna koya yin magana da i da wannan lambar, amma Whatsapp kawai, pls. 08027058704

Post a Comment

Previous Post Next Post