Tsantsar Kauna Page 11 - Abokiyar Hira Novels

Kamal, Fatima da Affan a littafin Tsantsar Kauna

 Tsantsar Ƙauna ka na 11

Na 

Tahir Yusuf (Novels Elite)


Rayuwa ta fara sauyawa a gidan Kamal da Fatima. Bayan shauƙi da annashuwa na yan watanni, a hankali suka fara fuskantar gaskiyar rayuwar aure. Kamal ya fara samun cinkoso a wajen aiki, albashi ya makara, sai dai buƙatun gida suna ƙaruwa. Fatima kuwa ta ci gaba da zama cikin ladabi da ƙwazo, tana kokarin gyara gida da ɗaukar nauyin wasu bukatu da ƙaramin kasuwancinta na dinki.


Wata rana da safe, Kamal ya dawo gida daga ofishin da ya tafi domin neman bayani akan kudaden su, fuskarsa cike da gajiya. Ya tarar da Fatima tana shirya abincin rana, sanye doguwar rigarta, tana humming wata waka na soyayya. Lokacin da ta kalle shi, sai ta fahimci akwai damuwa. Ta zauna kusa da shi, ta dafa kafadarsa tana cewa:

"Kamal, komai yana da lokaci, menene abin fushi ina tare da kai, zanyi maka duk abinda kakeso, in sha Allah in numfashi, ba zan bari wani abu ya bata maka rai ba."


Na kalli Fatima, idanu na cike da jin daɗi, amma cikin Zuciyata a kwai damuwa. Ban iya cewa komai ba sai kawai na kama hannunta yana murzawa a hankali. A wannan lokacin, zuciyarta ta kara tabbatar da cewa ƙaunarmu ba ta gushewa, kullum ƙaruwa takeyi, Fatima ce ce hasakena a cikin duhu.


Bayan kwana biyu, zazzaɓi ya kama Fatima. Sai dai rashin lafiyar tayi zafi sosai ba kamar yadda na zata ba, na dage sosai wajen kula da ita, Ni ke girki, nayi share-sharen gida, komai dai yakasance Ni nake yi saboda ana buƙatar ta sami hutu, Wannan ƙoƙarin nawa ya ƙara ɗaga darajarta a idon Fatima.


Wata rana da dare, Fatima tana kwance tana satar kallonna, Cikin wata murya mai cike da ƙauna tace 

"Kamal... da haka duk maza suke da babu wani aure da zai dinga mutuwa, Ka na da tausayi da gaskiya. Na yi sa'ar samun ka a matsayin miji, kuma abokin rayuwa."


Murmushi kawai nayi. Na ce, "Kina da zuciya mai kyau, nine nayi sa'ar samun ki matsayin mata, Kin kasance uwar gida tun kafin ki haifi 'ya'ya."

Sannu a sannu jikin Fatima yayi sauki sosai don a yanzu tana iya yin komai, hatta girki da sauran aikace aikace gida.


Yayin da kwanaki ke ja, muna ci gaba da fuskantar ƙalubale, daga ƙarancin kuɗi, da wasu abubuwan, amma kullum ƙaunarmu na ƙara ƙarfi. Sau da yawa mukan zauna mu muna shan shayi da safe, muna tattauna rayuwa, sannan muyi godiya ga Allah, daga nan sai muyi ta fira muna dariya a kan labaran baya. Wannan haɗin kai ya sa duk wata matsala da take zuwa ta zama darasi, ba ƙalubale ba.


A cikin wata hirar dare, Fatima ta ce, “Kamal, idan rayuwa tana da hanya mai duhu, zan zama fitila gare ka. Amma kai kuma... kai ne matattarar zuciyata.”


Na rike hannunta ina cewa, “Mu tafi tare, ko da wane irin hanya ce in har bazata saɓa ma adɗini ba, bazata kuma raba soyayyar mu ba, ban san ya sanyi ba duk lokacin da ba kya nan, ina tsoron ace wani abu ya faru dake ko kuma mutuwa, ban san ya sanyi ba.”




Nan zamu tsaya sai mun haɗu a kashi na sha biyu.

POV: A duk wani rayuwar aure Akwai kalubale sosai, ma'aurata ya kamata su yi ta haƙuri da yadda rayuwa ta zo musu. Allah ya rufa ma kowa asiri.


Domin ƙarin Bayani ko tambaya kuna koya yin magana da i da wannan lambar, amma Whatsapp kawai, pls. 08027058704

Post a Comment

Previous Post Next Post