Wata irin daji ne mai cike da manyan bishiyoyi, waɗanda suka miƙe har zuwa inda ido zai iya hangowa, tare da sautin tsuntsaye suna rera waƙoƙinsu. Ko da kuwa halin da jikina yake ciki, ina ta gudu duk inda ƙafata ta taka, abin da ake ji kawai shi ne ƙarar ganyaye da rassan da nake taka wa. Gumi kuwa ya lulluɓe ni tas. Na ɗaga ƙafata sama da ƙarfi lokacin da na hango ƙarshen dajin, inda wani faffadan fili ya buɗe. Na isa wurin ba tare da na dakatar da guduna ba, ina jin wani zafi mai tsanani a tafin ƙafafuna, duk da cewa babu rana. Ban tsaya ba, na ci gaba da gudu har na fara hango wasu bukkokin Fulani. Cike da bege, na yi hanzarin nufar wurin, sai na hango wata tsohuwa a tsaye a bakin wata bukka, tana kallona sosai ba tare da ta kawar da idanunta daga kaina ba.
Da wani gajeren ƙara, ina dab da isa gare ta, sai na faɗi ƙasa. A dai-dai lokacin ne na farka daga barcin da nake yi, inda na ga kaina a cikin wannan mafarki. Na murɗe zanin gadona gaba ɗaya, jikina kuwa ya jiƙe sharkaf da gumi. Na miƙe zaune ina riƙe da kaina kafin daga bisani na tashi tsaye. Abin da nake so kawai shi ne in bar gidan, in nufi wurin da na gani a mafarkin. Ba ni da wani sutura a jikina sai doguwar riga baƙa, da kuma hular baƙi a kaina.
Ba tare da na tsaya neman takalmi ba, na fita daga ɗakina. Ban haɗu da kowa ba har na bar ɓangaren gidan da nake zaune, na isa harabar gidan. A cikin ma’aikatan gida da suke ta kai-komo suna gudanar da ayyukansu, babu wanda ya kula da ni, har na buɗe ƙofar fita ta masu tafiya a ƙasa. Mai gadi da abokansa guda biyu da suke ta hira ba su ma kalli inda nake ba.
Na nufi gabas, ina tafiya da ƙafata cikin wahala da ƙoƙari sosai, har na ci karo da dajin da na gani a mafarkin. Amma abin da ya faru a zahiri ya bambanta da mafarkin, domin a wannan karon ba gudu nake yi ba. Daga ƙarshe, na sami tsohuwar a bakin bukkar. Da zarar na faɗi ƙasa, ban sake sanin abin da ya faru da ni ba, sai da na farfaɗo na tsinci kaina a kwance a kan tabarma ƙarƙashin wata bishiya.
Wani matashi mai ƙarfi, dogo, mai hasken fata, wanda shekarunsa za su kai kusan talatin, yana durƙushe a gabana tare da wata budurwa da na yi tsammanin matarsa ce.
“Ta farka, Amina. Je ki ɗebo mata ruwa.”
Ya umarce ta, nan take ta yi saurin miƙewa ta tafi.
Ta dawo da ƙwarya a hannunta, ta miƙa masa. Ya kalle ni sannan ya ce, “Tashi, baiwar Allah.”
Na yi ƙoƙarin tashi zaune, amma na ji dukkan jikina yana min ciwo. Da na daidaita zamana, sai ya miƙa mini ƙwaryar. Ruwan da ke cikinta kuwa fari fat yake, kamar an tace shi sosai. Na sha ruwan, sannan ya ce in ɗan watsa a fuskata.
Na yi yadda ya ce, daga nan sai ya fara tambayata sunana da kuma garin da na fito. Na buɗe baki da niyyar yin magana, amma na kasa. Na riƙe maƙogwarona, amma magana ta ƙi fitowa daga bakina. Ƙoƙarina ya zama kamar aikin banza, tamkar mutum ya ɗauki sabulu yana ƙoƙarin wanke kuturu da shi.
Ya kalli matar, ita ma ta kalle shi. Sai ya ce, “To, ki kai ta ɗakin Inna.”
Nan take ta zaro idanu cikin mamaki, ta zuba wa jikina ido, sannan ta yi masa magana da harshen Fulfulde. Shi kuma ya amsa mata da Hausa, daga nan sai ta miƙe ta tafi.
Sauke Littafin Kishiya Tara Complete Hausa Novel PDF
Danna maballin da ke ƙasa domin sauke littafin daga Google Drive:
📥 DOWNLOAD
Tags
Hausa Novel
