Nour Ayn Page 1 By Zainab Amza



 NOUR AYN

Hasken idaniyata 

BY ZAINAB AMZAH ✍️ 

03

*Team WOW 5 WRITERS HUB*

Paid Book.

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS?mode=gi_t

Ina mika sakon godiya ta ga shugabar kungiyar mu ta WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW) Allah ya kara lafiya da daukaka. 



Da kuma Aysha shafi’ee, Nagode maki sosai sister.


Allah ya jiƙan iyayen mu da rahma da sauran musulmai baki daya. 🙏🏻


*To whomever comes across this book, please say a prayer for my mother who now rest in peace. May Allah forgive her shortcomings. Amin* 🙏🏻


> *This is a work of fiction.* Names, characters, businesses, places, events and incidents are either the products of the author's imagination or used in a fictitious manner.  

 Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental.

*Ban yi rubutu don cin zarafin wani ko wata. Idan an samu akasin sunan ko makamancin labari irin naka/ naki, ayi haƙuri please* 🙏🏻



*PAGE 1*


Kyakkawar matashiyar budurwa ce. Akalla ba za ta wuce shekara 18 ba. Kyawawa ce sosai mai dirarren jiki. Duk da a kwance take, da alama dai bata da tsayi sosai. Sannan ba gajeriya bace. Ba zamu ce fara tas tas ce ba. Amma ba baka ba ce. Tana da matsakaicin haske mai kyau. Za mu iya cewa tsaka-tsakiya ce. Tana da dirarren jiki. Akwai mazaunai don hips dinta a cike suke MashaAllah. Tana da cikar halitta sosai, amma a sama ba ta da cikar ƙirji. Kwance take saman royal bed ɗin da ke ɗakin. Za kace ɗakin amarya ne saboda yanayin kyau da tsaruwar ɗakin. Sai juye-juye take saman gado saboda period cramps ɗin da take fama dashi. Ga wani irin nishi da take saukewa cikin wahala. Ta yi amai har ta gaji. Ba ƙaramar wahala take sha ba ko wane wata idan za tayi period. Har zullumin zagayowar wata take. Ba ga ita kadai ba, har ma da sauran yan’uwan ta.


Wata matashiyar budurwa ce wacce ba zata wuce shekara 19 ba ta shigo ɗakin a gajiye tare da yin sallama. Dawowarta kenan daga school. Tana ta mitar fita da tayi tun safe. Ta tsani saturday lectures. Shiyasa ba ƙaramin daɗi taji ba da aka yi canceling lecture 2 to 4 da za suyi. Aƙalla zata samu tayi barcin da ba tayi ba na safe. Gadon ta nufa kamar yadda ta saba, tana shouting sunan Mimi da ke kwance. Idan har ta shigo gidan bata ga Mimi a kitchen ko ɗakin Ammi ba, ta san tana nan ɗaki kwance tana game da wayar ta or chatting with her bae. Ko kuma barcin da bata gajiya da shi. Ci gaba da shouting sunan ta take yi. Jin shiru ba ta amsa ta ba. Wannan yasa ta ƙarasa ta zagaya gefen gadon. Tasan tunda taji tayi shiru definitely barci take. Hawaye ta gani kwance a fuskar ta. Cikin sauri ta ɗago ta, ta daura ta saman jikinta. Cike da damuwa tace, Mimi, kuka? What's wrong with you, and why are you crying? Duk a lokaci ɗaya ta jero mata tambayoyin. Dai-dai saitin cikinta ta nuna mata. Wanda hakan yasa tayi saurin gane period cramps ne da take fama dashi kowane wata. Ya Allahi, cike  da damuwa tace, sorry sis Kamar za ta yi kuka itama. A duk lokacin da wani abu ya samu ɗayansu, idan na farin ciki ne sukan kasance cikin farin ciki gaba ɗaya. Idan na damuwa ne sukan shiga damuwa gaba ɗayansu. Wata irin kauna da shakuwa ce mai girma a tsakaninsu. A duk lokacin da Mimi za tayi period sukan kasance cikin fargaba da damuwa gaba ɗayansu saboda yadda take shan wahala. Za mu iya cewa kusan tare suke shan jinya, sai dai idan Nadiya tana school. Amma duk wata wahala da zafin ciwon da Mimi take ji itama tanaji. Ciwon ne kaɗai ba’a jikinta ba, amma tana jin kwatankwacin zafin a zuciyarta. Sannan tana mugun tausaya mata. A hankali tace, did you take your drugs? Girgiza mata kai tayi. Cikin sauri ta sake ta, ta nufi bedside drawer in da suke ajiye magungunansu ta fara searching maganin da take sha. Ba ta samu magani ko ɗaya a ciki ba. Hakan na nufin ya ƙare kenan. Cikin sauri ta nufi ɗakin Ammi da yar damuwa kwance a fuskar ta. Zaune ta same ta a kan prayer mat ta idar da sallar zuhr tana addu'a. Shigowa tayi da sallama dauke a bakinta. Bayan sun gaisa Ammi tace har kin dawo Nadiya? Eh, na dawo Ammi, ta bata amsa a sanyaye. Tace tun yaushe? Just now. Ai na shigo na ga kina sallah sai na wuce ɗaki. Ok, Amma yau kin dawo da wuri, ke da idan ki ka fita sai yamma kike dawowa. Eh lecturer ne bai zo ba. So morning lecture kaɗai mukayi shiyasa. Cike da damuwa tace Ammy, Mimi tana ɗaki kwance, cikinta ya fara yi mata ciwo. Wallahi baki ganta ba sai kuka take yi. Da mamaki Ammi ta Kalli Nadiya, tace Subhanallah. Kuma ban daɗe da barin ɗakin naku ba. Saboda naji shirun yayi yawa tun safe da muka yi breakfast ban ƙara ganinta ba. Allah sarki, shiyasa yau bata shigo kitchen ba gaba daya, haba nidai nasan ba hakan nan ba. Kuma ban daɗe da dawowa daga ɗakin ku ba, nadai ganta a kwance nayi tunanin barci take yi. Nace bari in barta in yi sallah. Idan na idar sai na koma na tashe ta. Ashe ba ta jin daɗi?

Eh wallahi. Nima ban sani ba, nasan Lafiya lau na barta da safe da zan wuce school, ina shiga na ganta kwance tana kuka. Kin san ciwon bai mata da sauki. Ta karasa fada muryarta na rawa kamar za ta yi kuka. Ammi tace haka ne Nadiya. Ni ma abin yana damu na sosai wallahi. Allah ya bata lafiya, ya yaye mata wannan ciwon. Amin Nadiya ta Amsa.


Miƙewa Ammi tayi ta ɗauki wayarta. Ta fara dialing number ɗin Faruk. At the same time ta nufi dakin su. Kwance ta same ta har zuwa lokacin kamar yadda Nadiya ta bartata. Duk wani ƙarfinta ya ƙare saboda uban amai da tayi.  Duk ta galabaita.  Ƙarasa wa wurinta tayi. Ta zauna kusa da ita. Ta ɗago ta ta kwantar da ita a saman kafarta tana patting bayanta a hankali. Tace sannu Mimi. Baki da lafiya shine ba za ki faɗa mini ba? Har sai da Nadiya ta shigo ta ganki kwance ta zo ta faɗa mani. Yanzu da ba ta dawo ba, haka zaki ta zama da ciwo ba zan san ba ki lafiya ba? Haba Mimi, mi yasa kike haka? Idan ba zaki iya zuwa ki faɗa mini ba, ko a waya ya kamata ki kira ki sanar da ni. Ita dai mimi kuka kawai take tana riƙe da cikinta da ke yi mata wani irin ciwo. Kuma har zuwa lokacin ba ta iya yin magana da Ammi. Kin sha maganinki kuwa? Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba. Nadiya tace Ammi, maganin ta ya ƙare gaba ɗaya. Kafin nazo wurin ki saida na duba mata amma ban samu ba. Miƙewa Mimi tayi daga jikin Ammi, cikin wani irin sauri ta nufi bandaki. Ko kafin ta ƙarasa har ta fara amai a ɗakin. Da sauri Nadiya ta bi bayanta suka ƙarasa toilet ɗin tare. Ta dafa bayan ta tana mata sannu. bayan ta gama, ta taimaka mata ta gyara jikinta, sannan ta kama ta suka dawo cikin ɗakin. Ko da suka fito, Amina da Ammi ta kira ta a waya suka taras tana gyara wurin da ta bata. Ta sake kwanciya. Bayan ta kwanta, cikin kulawa Ammi ke ƙara yi mata sannu. A lokaci guda tana sake dialing number ɗin Faruk. Ganin har zuwa lokacin bai picking call ɗin ba, ya sa ta yanke shawarar kai Mimi hospital. Kar ta barta gida kuma ciwon yafi haka. Maida duban ta ga Nadiya tayi tace, please get her hijab. We need to rush her to the hospital now. Cikin sauri Nadiya ta buɗe press ɗinsu, ta ciro mata hijab dinta ta saka mata. Sannan ta kama ta suka fito.


Malam TK, driver nasu dake zaune tare da Shafi'u gateman suna ta hira. Tun dawowarsa daga ɗaukar Nadiya school suke zaune a wurin suna hirarsu kamar yadda suka saba. 

Da sauri ya tashi ganin su Ammi sun fito riƙe da Mimi dake a gakabaice. Cikin hanzari ya buɗe musu back seat, yana gaishe da Ammi tare da yi wa Mimi sannu. Suka kama ta ta shiga mota. Sannan Nadiya ta zagaya front seat ta zauna, ta kwanta a jikin Ammi don ko zama ba ta iya yi saboda yadda cikinta ke mata ciwo da bayanta. Suna gama shiga ba tare da bata lokaci ba yaja mota suka bar gida. Kai tsaye ALYSHA PREMIERE HOSPITAL da ke garin Abuja ya nufa da su. Kasancewar daman ya san nan ne wurin zuwansu. Sannan ba su da wata hospital da suke zuwa da ta wuce wannan. Kuma a nan Dr. Faruk yake aiki. Ammi’s first born.



Ina mai farin cikin sanar daku muna siyar da Kaya Kala Kala masu kyau da quality direct from Egypt Abaya, jalbabs,  boubou, scarfs, jersey hijabs, jersey veils, comfy gowns, tie back caps,crinkle turban caps,nightwear’s and lots more. Muna yin adashe na kome kake so  ga wanda bashida halin siya lokaci daya..

Masu son fara business su ma muna maraba dasu 

For more info +201508856397

WhatsApp only.


+201508856397 

My WhatsApp number 

Tiktok @amzaah

Instagram @zainabuh_Amzah

Snapchat @Zainabuh Amzah 

Arewa pen @Zainab Amzah.


*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*



*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*



1- Ummulkhairi Sani Panisau  (Khairatup)

GABA TAZO BAYA


2-Harira Salihu Isah 

 Uwar Batoorl 

YARIMA BAHJAT


3-Zainab  yahaya Amzah 

NOUR AYN


4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)

KUSKURENA NE


5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) 

WAHEEDA



Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.


Guda ɗaya  1k

Biyu  1500

Uku  2k

Huɗu  2500

Biyar 3k



Account Number  9126022777

Bank: Opay

Suna: Ummulkhair Sani Panisauu


Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇


09023907030


09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post