Ragayar Dutse Page 13 Complete by Nana Haleema

Kida a Ruwa

 RAGAYAR DUTSE.

         ©️ Nana Haleema.

Book 1

Page 013.

__________

Muslim tunda Islaha ta shiga ɗakin ya kasa tsayawa, sai zagaye yake yi yana ji kamar ya zama iska ya shiga ɗakin ya ji abinda ake tattaunawa. 

Sai kallon ɗakin yake yi, yana ji zuciyarsa babu daɗi a kan hakan. 


Saleem da yake zaune ya bi sa da kallo ya ce, "ka zo ka zauna mana, sai zagaye ka ke yi kamar sabon soja." 


Ya ɗan kalle sa ya ce, "so nake ta fito kawai, ina ta addu'ar Allah ya sa ya amince." 


Saleem ya ce, "to ka zauna mana." Ya dawo ya zauna yana kallon ƙofar har lokacin bata fito ba. 


Wani iri yake ji a zuciyarsa, dan bai san me ake yi a ciki ba, ba haka yake so ba, so ya yi a buɗe iv card ɗin a gabansa, dan ya ji irin cin fuskar da za a yi mata.


Ya kalli Saleem ya ce, "kar fa mu je wani abun yake yiwa yarinyar nan."  


Saleem ya zaro ido ya ce, "me zai yi mata kuwa? Ka jira ka gani mana." 


"Ka san namiji ba abin yarda bane ba akan mace." Saleem ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. 


A lokacin Islaha ta fito duk suka miƙe suna kallon ta, ta ƙaraso wajansu ta ce, "mu je ko?." 


Saleem ya ce, "ba ki faɗa mana komai ba."


"Na yi tunanin sai mun je mota ai."


"Faɗa mana yanzu dai."


"Mun yi magana dashi, ya ce da kansa zai faɗawa baƙon na mu, kuma ya yi min alƙawarin ni ce ta farko da zan fara hira dashi." 


Saleem ya ce, "good, haka muke fata, Allah ya ba mu nasara." 


Ta ce, "Amin. Mu je ko?."


Saleem ya ce, "babu abinda ki ka manta?."


"Eh, ban bar komai ba" ta faɗa suna shiga elevetor ɗin. 


Suna sauka Reception suka ba da key ɗin ɗakin suka fita zuwa harabar hotel ɗin. 


Kamar an ce ta kalli gefenta, sai gaban ta ya faɗi, ta ɗan yi jim tana kallon wajan kafin ta juyo tana kallon su. 


Saleem ya ce, "mu je ko?." 


Ta ɗan girgiza kai ta ce, "ku je, zan biyo ku daga baya." 


Saleem ya ce, "kamar ya zaki biyo mu? Me za ki yi?."


"Akwai abinda zan yi, ku je kawai" ta faɗa tana komawa da sauri.


Mualim ya ce, "Anya ba shine ya ce ta koma ba?." Saleem ya ɗan yi shiru ya bita da kallo a lokacin har ta koma ciki.


Islaha tana shiga ta jawo mayafinta ta rufe fuska, ta saka faacemask ɗinta ta shiga eleavtor. 


A floor 7 ya buɗe waɗanda suke ciki suka fita itama sai ta fito. 


Ta yi hanyar dama su kuma suka yi haggu, kamar wacce ta manta hanya sai ta yi saurin dawowa da baya ta bi baya a lokacin suka buɗe room suka shiga. 


Ta ɗan zubawa ɗakin ido tana nazari, dan ko tantama bata yi wannan Hafsa ce, Hafsa ƙanwarta ta gidan marayu. Me ya kawo ta hotel har aka shiga da ita ɗaki?.


Dafe kai ta yi tunawa bata da inda zata zauna ta jira su, sai ta juya a inda take tsaye akwai camera, ta gyara nutuswarta ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakin gabanta yana faɗuwa. Kamar zata yi knocking sai ta fasa, ta ja da baya ta koma ta sauka ta koma reception. 


A nan ta ga Saleem yana jiran ta, yana ganin ta ya ce, "me kika koma yi ne haka?." 


Ta ɗan yi jim ta ce, "wata na gani wacce na sani tuna baya, shine na koma muka gaisa. Mu je" 


Ta faɗa tana yin gaba ya bi bayanta suka shiga mota suka tafi zuciyarta cike da tsananin tunani akan abinda ta gani.  


         Rehaan bai farka ba sai gab da sallar la'asar, ya miƙe ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya a lokacin aka yi kiran sallah. Ya yi sallah a ɗakin ya tashi ya kunna kettel ya haɗa tea yana sha. 


A lokacin Jazy ya shogo ya bi sa da kallo ganin bashi da alamun shiryawa ya ce, "Malam ka tashi mu tafi. Na gaji wallahi." 


Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ce, "baza mu bari sai dare ba?." 


Ya girgiza kai ya ce, "A'a, yanzu zamu tafi. Tashi" ya faɗa yana rufe masa box ɗinsa yana kallonsa.


Rehaan ya ajjiye mug ɗin ya ce, "ka kasa gane bana son komawa gida." 


Ya kalle sa ya ce, "wallahi dole ka koma, in ba haka ba zan yi tafiyata na ƙyale ka. Ya zaka dinga raina min hankali kamar wani yaronka, dan ka ga ina biye maka sai ka dinga yin abinda ka ga dama?."


Ya ɗan yi tsaki ya miƙe tsaye, ya ɗauki face cap ɗinsa ya saka, ya saka facemask ya ɗauki wayarsa ya ce, "mu je" ya faɗa yana yin gaba. 


Jazy ya riƙo hannunsa ya ce, "dakata malam, waye bawan ka da zai ɗaukar maka jaka? Ka san dai baka isa ba ko?."


Bai ce komai ba ga dawo da baya ya ɗauki box ɗin, har zai fita sai ya dawo ya cire charger sa ya fita daga ɗakin zuwa ƙofar ɗakin yana danna waya. 


Jafar yana fitowa ya ja ta sa box ɗin suka sauka ƙasa zuwa compound ɗin hotel ɗin. Suna ƙarasawa suka shiga mota suka ɗauki hanyar gida.


Tunda suka nufi gida yake jinsa babu daɗi ko kaɗan, sai kallon hanya yake yi yana ji kamar su koma. A haka suka ƙarasa aka buɗe musu gate suka shiga. 


Jazy zai buɗe ya fita ya riƙo hannunsa ya ce, "kar ka ce zaka wuce gida yanzu, ka zauna tare dani." 


Ya bisa da harara ya ce, "da yake ga bawan ka ko? Dallah cika min hannu, in na shiga muka gaisa da Abba da Mamy tafiyata zan yi, nima uwata tana son ganina ai" ya faɗa yana buɗe motar ya fita.


Jazy yana fita suka haɗa iso da Janan, ta saki ihu ta nufo sa a guje tana zuwa ta rungumesa tana welcoming ɗinsa. 


Jazy ya yi dariya ya ce, "Janan ya aiki?."


"Alhamdu lillah Hamma Jaafar. Ina Hammana?." 


Ya nuna mata side ɗin da Ray yake har lokacin bai fito ba. Ta buɗe ido ta ce, "da gaske tare ku ke?" ta faɗa tana zagyawa da sauri ta ƙarasa ta buɗe masa. 


Suka haɗa ido ta faɗa jikinsa a cikin motar, ya yi murmushi yana zare facsmask ɗin ya ce, "My little Jan." 


Ta ɗago daga jikinsa ta ce, "Hamma shine babu labari? Baka faɗawa kowa ka shigo ƙasar nan ba." 


Murmushi ya sake yi ya ja kunatunta kafin ya sakko daga motar. Janan ta kanƙame hannunsa ta ƙi saki, tana ta murnar ganinsa ta ce, "Kuma da yake ban ga security guard ɗinka ba, shiyasa ban yi tunanin kai bane." 


Ya kalle ta ya ce, "kina zuwa aiki?." 


Ta yi dariya har tana tsalle kamar yarinya ƙarama ta ce, "yanzu ma na dawo." 


Ya sake yin murmushi tana riƙe dashi cikin murnar ganin favorite brother ɗinta.


Ya kalli Jafar da ya yi nisa a hanyar apartment ɗin Mamy. Ya juya yana kallon Janan, kafin ya ce wani abu ma'aikatan gidan sun ƙaraso wajan ana ta gaishe sa ana yi masa barka da zuwa. 


Suka gaisa cikin sakin fuska, aka ɗauki box ɗinsa aka kai apartment ɗin Mamy. Janan dai tana riƙe da hannunsa suka nufi apartment ɗin Mamy, sai da zasu shiga sannan ta tuna ta bar abu akan gas ta sake shi ta tafi a guje.


A lokacin Riyya da Banisha suka fito a guje suka rungumesa a tare. Murmushin jin daɗin ganin ƙannen nasa ya yi, dukkansu kansu babu ɗankwali, gashinsu mai tsaho da santsi ya bayyana har gadon baya. 


Ya ce, "Riyya za ki yar da ni ba, baki san kina da girma bane?." 


Ta ɗago tana kallonsa ta ce, "Shine ko ka faɗa min."


"Saurayinki bai faɗa miki ba?." 


Cike da shagwaɓa ta ce, "bai faɗa min ba." 


Ya yi murmushi, ya shafa fuskarta suka shiga ciki har falon Mamy.


Da sallama ya shiga ya samu Mamy a zaune ita da Jazy gaisawa. Rehaan ya bita da kallon kewar mai yawa, fara'arsa ta ƙaru sosai. Ya ce "Mamy." 


Kafin ya ƙaraso ta miƙe ta cim masa, ta yi hugging ɗinsa ta ce, "sannu da zuwa My love." 


Ya ɗago daga jikinta, yana kallon fuskar ta, cikin harshen hindi ya ce, "na yi kewar ki Mamy." 


Itama cikin yaren ta ta ce, "nima na yi kewar ka Rehaan. Zauna." Bai musa ba ya zauna yana kallon kowa da yake zaune a falon. 


Riyya ta je ta kawo masa favorite drink ɗinsa, wanda ta san yana so indai ya zo gida, daman Jafar ya faɗa mata zai dawo, shiyasa ta yi masa da kanta. 


Ta ce, "kamar na san zaka dawo na yi cocunut drink, gashi ka sha” ta faɗa tana miƙa masa. 


Ya karba ya riƙe hannunsa, ta zauna a kusa dashi ya ce, "thank you. Ba ki ga saurayinki ba?."


Ta kalli Jafar da yake kallon ta, ta yi dariya tana kwanciya a kafaɗar Rehaan cike da kunya. 


Mamy ta yi dariya tana kallon Rehaan cikin murnar ganinsa ta ce, "tana murnar ganin ka, ko sannu da zuwa bata ce masa ba." 


Ta kalli Mamy ta ce, "Allah na ce masa sannu da zuwa.” Ta juya ta Jafar ta ce, "ban faɗa maka ba?." 


Shi dai murmushi kawai yake yi bai ce komai ba, yana jin daɗin ganin iyalan Mamy cikin farin ciki sosai, yana son zama a cikinsu dan kamar ba sirikin Mamy ba haka yake. Tun zamansu a Uk Mamy ta mayar dashi kamar Rehaan, komai tare suke yi, yadda take rarrashin Rehaan haka take yi masa. Zama da ita ya saka yake jin yaren ta kamar yadda Rehaan yake ji, komai in zata yiwa Rehaan zata haɗa dashi.


Ya yi tunanin da ya furta yana son Riyya, har maganar aure ta shiga tsakani zata ɗan canja saboda kunya, amma sai ya ga shine yake haukansa Mamy ko a jikinta. Yadda take yi masa ɗin nan dai bata canja ba, wani lokacin har tsokanarsa take yi. Shiyasa shima ya sake, ya daina jin kunyar ta gabaɗaya.


Jafar ya kalli Mamy ya ce, "Mamy Abba yana nan?."


"Ba ya nan Jafar, sai dai ka dawo in anjima."


"Shikenan, ni zan wuce Mamy."


"Amma zaka shiga ku gaisa da matan gidan ko?." 


Ya ɗan yi jim bai amsa ba, Mamy ta ce, "ka je Jafar, kar ka bar shaiɗan ya yi galaba a kanka." 


Ya girgiza kai ya ce, "To Mamy."


Mamy ta ce, "sai ganin ku kawai na yi, babu labari ko a waya." 


Ya yi dariya ya ce, "Rehaan ne wallahi, magiya ya dinga yi min akan kar na faɗa mu ku. Tun jiya muka dawo, a hotel muka kwana sai yanzu mu ka zo." 


Mamy ta ce, "na yi mamaki da ban ga Rehaan a gajiye ba, ashe kun jima da dawowa."


"Ai da yana nan yana faman furta ya gaji. Rago kawai." Mamy ta yi dariya kawai bata ce komai ba.


Jazy ya miƙe ya ce, "Mamy na tafi."



Mamt ta ce, "ka gaishe da Mummy, ka ce mata zan zo in sha Allah."


Ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah." 


Mamy ta kalli Riyya da take satar kallonsa tana murmushi ta ce, "baza ki raka sa ba?." 


Riyya ta miƙe tana ɗaukar hularta, ta saka ta bi bayan Jazy da sauri.


A lokacin Rehaan ya kalli Mamy da take kallonsa ta ce, "a kawo maka abincin?." 


Ya ɗan girgiza kai ya ce, "A'a Mamy, zan sha drink ɗin kawai, in anjima zan ci." 


"Me za a dafa maka?."


"Anything from my Mamy i like it." 


Ta yi murmushi tana cire hular kansa, gashinsa da ya ɓuya a ciki ya sauka har bayan wuyansa. 


Ta bi gashin da kallo tana shafawa ta ce, "Rehaan ka san jama'ar gidan nan basa son gashin nan ko?." 


Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Mamy dan ba sa so sai na ƙi yin abinda na yi niya? Ni Ina so, kuma babu haramci a ciki, saboda su sai na fasa?."


Mamy ta girgiza kai ta ce, "ka je ka huta, zamu yi maganar daga baya. Banisha ɗauki box ɗinsa ki kai masa ɗaki." 


Banisha da take jikinsa ta miƙe ta ɗauki box ɗin zuwa ɗaki. 


A lokacin Riyya ta dawo shi kuma ya miƙe tsaye, ta ƙaraso tana sake riƙe hannunsa ta ce, "Ina da labarin da zan baka." Ya sake yin murmushi ya shafa fuskarta bai ce komai ba. 


Har zai fita sai Mamy ta ce, "Rahaan." 


Ya dawo yana kallon ta, ta ce, "Ka je ku fara gaisa da mutanen gidan, in ku ka gama sai ka wuce ɗaki." 


Bai musa ba suka fita su ukun ta bisu da kallo, tana yi musu addu'ar neman tsari daga duk wani mai nemansu da sharri.


Apartment ɗin Mama suka shiga da sallama, Janan tana ganinsa ta fito daga kitchen, ta ƙaraso gare sa suka shigo falon tare. 


Ya kalli mutanen da suke zaune a falon, yayyensa maza ne, sai kuma ita Maman da take zaune. 


Ya kalle su ya ce, "Barkan ku." 


Daƙyar suka iya amsa masa, ya kalli Mama cikin harshen fulatanci ya ce, "barka da gida." 


Ta bisa da harara tana taɓe baki ta ce, "an dawo lafiya?."


"Alhamdu lillah" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Kafin su ce wani abun ya ce, "sai anjima" ya faɗa yana fita daga falon. 


Sameer ya bi sa da kallo tare da jan tsaki, sai kuma ya yi ƙwafa ya miƙe shima ya fita bai sake waiwayon kowa ba. 


Shi kuwa wajan Umma ya shiga, a nan ya tarar da Yayarsa mace da kuma ƙanwarsa wacce ta jima da aure. 


Suka gaisa sama-sama, ya fito ya shiga wajan ta ƙarshen, itama suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan ya wuce wajan Daada. Har zai shiga sai ake shaida masa bata nan ta fita, ya dawo da baya suka wuce part ɗinsa shida ƙannensa mata guda uku.


Yana saka ƙafa a apartment ɗinsa kansa ya sara, ya ɗan yatsine fuska kaɗan ya shiga falon ya zauna yana ɗan murza goshinsa. 


Janan ta ce, "Hamma ya dai?." 


Ya ɗan girgiza kai alamun babu komai kafin ya ce, "ku je ku yi sallah, nima yanzu zan fito masallaci." 


Suka amsa, Riyya ta ajjiye masa drink ɗinsa su fita. 


Ya dafe kai yana sauke numfashi, ya miƙe yana tafiya a hankali, ya shiga ciki zuwa ɗakinsa ya buɗe yana kallon ɗakin kamar ba nasa ba. 


Ya ƙarasa gaban mirror ya cire agogo ya ajjiye, ya ajjiye hula da glases ɗinsa ya ya taka a hankali zuwa banɗaki.


Alwala ya yi ya fito, bayan ya fito kansa yana juyawa sosai, ya ɗan tsaya cak kafin ya zauna a gefen gado yana ji kamar ana juyasa a cikin ɗakin. 


Kiran sallar da aka yi ya saka shi sauke numfashi, ya koma closet ɗinsa ya ɗauko jallabiyya ya saka ya fito dan zuwa sallah.


     Islaha tunda suka ɗauki hanya ta yi shiru tana tunanin abinda ta gani wanda ya ɗaga mata hankali sosai, ta ɗan sauke nunfashi a hankali. Sai kuma fuska wanda ya watsa mata tea ya zo idanunta, ta ji takaici ua mamaye mata zuciya. 


Ta yi tsaki ta ce, "shirme!." 


Saleem da yake kallon ta ya ce, "ke da wa." 


Ya ɗan lumshe ido ta buɗe ta ce, "don Allah ajjiye ni a orphanage, akwai abinda zan yi a ciki." 


Muslim ya bita da kallo ya ce, "baki gaji ba kenan?."


"Akwai wanda nake so na haɗu dasu, shiyasa nake so in shiga."


Basu jima ba suka ƙaraso, ta fita daga motar tana yi musu sallama suka tafi ita kuma ta nufi gate ɗin gidan. 


Suka gaisa da ma'aikatan wajan, ta shiga ciki kai tsaye ɗakin su Hafsa ta wuce. Zata shiga Zainab zata fito, zata yi ihu ta rungume ta ta yi saurin rufe mata baki suka shiga ɗakin. 


Islaha ta ce, "yi shiru, bana so a san na shigo gidan nan."


Zainab ta ce, "Adda Islaha sannu da zuwa."



"Yauwa Zainab. Ina Hafsa?." 


Zainab ta yi shiru bata ce komai ba. Islaha ta ce, "magana nake yi miki fa, ina Hafsa take, itama bata nan kamar sauran?." 


Zainab ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Adda Islaha Mama ta fita da Hafsa tun jiya, har yanzu bata dawo ba."


Islaha ta gyara zama ta ce, "ina ta je da ita? Meyasa ke ba a tafi dake ba?."



"Wallahi ban sani ba, tunda aka yi wasu baƙi bayan kin bar gidan nan, sai aka kira mu dani dasu Hafsa da Saliha mu ka je wajan, tun daga lokacin Mama ta kira Hafsa suka fita basu dawo ba."


"Su waye baƙin? Mata ne ko maza?."


Zainab zata yi magana cikin tsawa aka katse ta aka ce, "Ke Zainab!." 


Dukkansu sai da gabansu ya faɗi, dan tsawar ta zo musu a bazata. Suka juya suna kallon wacce ta yi musu tsawar. 


Ɗaya daga cikin wacce suka tashi tare ne, da shekaru da komai na su ɗaya ne. 


Ta ƙaraso ta janye Zainab ta ce, "me ki ke yi a nan? Ba an ta fi dining cin abinci ba?."


Zata yi magana ta daka mata tsawa ta ce, "wuce ki bar wajan nan kafin na yi ball dake." 


Islaha ta miƙe tsaye ta ce, "babu inda zata je, yadda ki ke da iko da ita nima haka nake da iko da ita" ta faɗa tana riƙo hannunta. 


Fadwa ta bi Islaha da kallo ta ce, "Islaha ba da ke nake ba, ki bari na yi abinda aka saka ni. Baki fa iko da kowa na gidan nan, ba a nan ki ke ba yanzu."


"dan ba a nan nake ba, amma ƙanwata ce."


"Zainab fita." 


Islaha ta kalli Zainab ta ce, "jeki Zeey, kar ki damu." Zainab ta fita a hankali bata sake magana ba.


Islaha ta kalli Fadwa ta ce, "kin bani mamaki, ban yi tunanin haka daga gare ki ba. Me ku ke ɓoyewa wanda ni ban san dashi ba?." 


Fadwa ta ce, "babu ruwanki da abinda mu ke ɓoyewa, nan gidanmu ne muna da ikon yin duk abinda mu ke so. Bakya cikin mutanen gidan nan, baki da file a gidan nan a yanzu, dan haka ba a gidan mu ki ke ba. Ki daina ƙoƙarin ganin sai kin nemo abinda aka ɓoye, babu ruwan ki."


Islaha ta girgiza kai ta ce, "Tabbas sai na nemo abinda aka ɓoye, kuma in zargina ya tabbata na rantse da Allah kaf gidan nan babu wanda zai sha. Wallahi sai kowa ya kwashi kashinsa a hannunsa."


"Babu abinda zaki gano balle ya tabbata, ki cigaba da tsayawa a matsayin da aka ajjiye ki. Tunda ke kin koma gidansu saurayi da zama ke ki ka sani, sai ki je ki yi rayuwarki, ki bar mu mu yi tamu rayuwar."


Islaha ta yi ƙwafa ta ce, "zamu gani Fadwa, na gode da samun information daga gare ki" tana faɗa ta fita daga ɗakin da hanzari. 


Fadwa sai ta tafi tunani, wanne irin info take zance? Wacce irin magana ta faɗa da ta zamarwa Islaha information?. Sai ta ji tsoro ya kamata, gabanta ya faɗi kar ta je ta faɗi wani abun.


Da hanzari ta fita ta nufi office ɗin Mama, ta samu tana ganawa da baƙi, an kawo gudunmawar kaya masu yawa a rabawa marayu.


Ta jima tana jira su tafi amma basu tafi ba, sai bayan sun tafi sannan ta shiga ta ce, "Mama Islaha ta zo nan." 


Mama ta juyo ta kalle ta ta ce, "me ya kawo ta?."


"Na je na same ta ita da Zainab tana tambayarta ina Hafsa take, kuma kin san Hafsa bata gidan nan." 


Mama ta ajjiye ruwan da yake hannunta ta ce, "da wa da waye a ɗakin lokacin da take tambayarta?."


"Duk an tafi wajan cin abinci, daga ita sai ita sai ni." 


Ta da ki table ta ce, "Yarinyar nan tana ƙoƙarin wuce tunanin mu fa. Amma kin hana Zainab magana da ita ko?."


"E na hana, amma already ta riga ta faɗa mata Hafsa bata nan. Wai Mama babu ta yadda za a hanata shigo gidan nan? Babu hanyar da za a bi a hanata zuwa gidan nan tunda ba a gidan take ba yanzu?." 


Mama ta girgiza kai ta ce, "na san abinda zan yi mata Fadwa, na san maganinta. Abinda nake so dake, duk bala'i kar ku faɗa mata komai, ku iya bakinku dan yarinyar nan shaiɗaniya ce, kuma ƴar jarida ce, zata iya tarwatsa mana komai."


Fadwa ta ce, "To Mama." 


Mama ta ce, "ki faɗawa sauran, ko da yake in anjima ki turo min su ina da meeting dasu" ta faɗa tana ɗaukar ruwa ta sha ita kuma Fadwa ta fita. 


Ta girgiza kai ta ce, "sai na yi maganin yarinyar nan, na daina saurara mata, lokacin da zan ɓatar da ita ya yi” ta faɗa tana ɗaukar waya da niyar yin kira.


    Islaha kuwa ko da ta fita napep ta tare kai tsaye ta koma hotel ɗin da suka baro. Ta rufe fuska da facemask ta shiga ta wuce har floor ɗin da ta ga Hafsa. 


A nesa da ɗakin ta tsaya, ta saka waya a kunne kamar tana amsa waya tana satar kallon ɗakin, ta cigaba da kallon wajan tana ɗan yin waya kamar mai yin wayar gaske.


Kamar a mafarki aka buɗe ƙofar ɗakin, da sauri ta sauke wayar daga kunnenta ta shiga camera ta cire flash light, ta mayar da wayar kunne kamar tana waya. 


A lokacin Hafsa ita da wani suka fito, Hafsa ta ɓoye fuskarta da facemask, sai wanda suke tare shima ya rufe fuskarsa da facemask. 


Islaha ta juya ta cigaba da yin video da hotuna har suka wuce, da sauri ta yi kamar zata koma ciki, har sai da suka sauka, ta tabbatar sun fita sannan ta fito ta fita daga hotel ɗin.


Napep ta sake tarewa ta shiga, ta tafi tana tunanin abinda ta gani wanda ya ɗaure mata kai ya kuma bata mamaki mai yawa. 


Me Hafsa ta zo yi hotel ita da wani? Kuma gashi a gidan an san bata nan balle ta ce zuwan kai da kai ne, har ana cewa da Mama suka fita.


Ta girgiza kai a bayyane ta ce, "Allah ka kiyaye yaran nan daga abinda nake zargi, Allah ka tsare maraicinsu.” 


Ta shafa fuskar ta ta ce, “ko iya haka na samu hujja mai ƙarfi." 


Ta cigaba da kallon titi suna tafiya, tunanin ya ƙi barin zuciyarta da idanunta, ko ya ta rufe ido Hafsa take gani ita da wanda bata san waye ba, gabaɗaya ta takura ta rasa abinda zata yi. 


Suna cikin tafiya wata dattijuwa ce ta zo tsallaka titin, ƙiris ya rage mai napep ɗin ya buge ta, dan ya ɗan taɓa ta har ta faɗi a ƙasa.


Islaha cikin kiɗima ta ce, "Subahanallahi! Malam tsaya." 


Mai napep ɗin ya tsaya, ita kuma ta sauka ta nufi wajan matar da hanzaru, dan daga ganinta ka san ta girma sosai, tana buƙatar taimako. 


Nana Haleema✍🏻❤️

09030398006.

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post