H I Y A A M Page 9: The Secret

 *H I Y A A M*

 

Page 9: The Secret 

Bright pens 

Yota/001

I can repeat it again, this book dedicated to Nazeefah Sabo Nashe.

AUTAR MANYA: Thank you so much na gode da ƙoƙarinki Allah Ya saka da alheri Ubangiji Ya bar zumunci.

Ta cikin motar ya ɗan sake ware idanunsa kaɗan ya kalli yadda take tsaye a waje tana rarraba idanu. Kamar zai yi mata shiru sai ya ɗan duba agogon dake hannunsa sai yaga lokaci yaja yana kuma da abin da zai yi. A nutse yana kame fuskarsa ya dube ta ya ce "Are you getting into the car, or will you keep standing outside, looking around like someone who has something to hide?"


Yadda take kallon nasa sai yaga kamar bata fahimci me yake cewa ba, ya danna mata horn da ƙarfi sai ta yi saurin sakin ajjiyar zuciya saboda ɗan firgitar da ta yi duk ta kasa samun sukuni da nutsuwar zuciya. Ta ɓata fuska ta ce "Me kace ne?" Ya yi mata ƙuri da ido sai kuma ya ce "cewa na yi za ki shigo motar ne ko za ki tsaya a waje kina rarraba ido kamar mara gaskiya?" Sai ta tura bakinta gaba kaɗan itama ɗin ta makara ƙwarai da gaske, amma a yau ɗin sai ta ji bata samu ƙwarin gwiwar shiga motar ba, ta kuma rasa dalili, ba zata yadda saboda auren da yake kanta bane bata jin hakan. Kai bama shi ɗin bane, aure ai ba zai iya shata mata layi da abin da ta zaɓa kuma take so ba. Sai ta taka sannu a hankali ta buɗe murfin motar ta shiga kanta a ƙasa, bayan ta shiga da sallama ta zauna taja murfin ta rufe. A kunne motar take sai ya fara driving da hannu guda ɗaya hannun kuma yana shafa gemun fuskarsa yana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci yake juyawa yana kallon ta. Sai ta ɓata fuska tace


"Allah ban shirya mutuwa yanzu ba, ka kalli gabanka ka yi driving a nutse please"


A kasalance ya ce "Nima hakan take baby"


"Shine kake ta kallo na?"


Ya ɗan ɗaga shoulders alamar rashin damuwa da furucinta ya ce "Wataƙila da bana kallon naki shine zai yasar damu a titi, but trust me baby, ki yarda dani baby kallon fuskarki ke bani energy a jikina kin ji ko?"


Ta yi masa shiru saboda faɗuwar gaban da take ji ta yi kaɗan ta kwanta a jikin kujerar. Shiru ne ya ratsa cikin motar lokacin da ya ɗauki titin da zai kai shi Bright Fm ɗin tasu.


"Ahlam.....


"...Tell me something please!"


"Kamar me kenan a something ɗin?"


Ya sake shafo sajensa ya ce 


"Me kike ji yau?"


Ya ɗora da "Ina nufin wanne irin farinciki kike ciki yau ɗin nan, domin na san a jerin shekarun da kika ruska a rayuwarki yau ɗin zata iya zama ta musamman a gare ki kamar dai nima haka nake ji yau ɗin" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa alamar nuna kan shi. Ta yi shiru alamar nazari da tunani, tunani ta fara saboda kamar wani aiki ya sata wanda ba ta yi niyya ba ko kuma bata san dashi ba, ta fara processing da ƙwaƙwalwarta wajan haƙaito anahin abin da zai iya zama na musamman a yau ɗin a kuma rayuwarta. "Aure?" Sai ta yi saurin girgiza kai a ranta ta ce "No, impossible" Wannan aure ba zai zama na musamman a wajanta ba, wannan auren dai ba zai zama abin da zata rubuta shi a history na rayuwarta ba, auren da Engineer da Anty Jiddah ne kawai suka san dashi, suka san waye mijin ma? Sune suke ɗoki da zumuɗin yau ta zama matar aure, matar wanin da bata waye shi mene halinsa da ɗabi'unsa. Ita fa ko sunan shi ma bata buƙatar ji ɗin, tana son ta ƙarfin dole ta fuskanci matsalarta kuma ta yi maganinta. Ƙaddarar cimma burinta bata san ina zata tsaya ba, bata kuma san ina zata kaita ba. A fusge taja numfashi bayan ta lumshe idanunta tace. "Bani da wata rana ta musamman"


"Bana jin akwai wani abu special....


"Really.... Da gaske kike?"


Ta dude shi kawai ba tare da tace komai ba.


Ya murmusa "Ni ina da, ina jin akwai ta" Ya sake jan gemunsa "Ina jin ƙamshin zama ango, ina kusantar rayuwar aure da amarci"


Dam! Gabanta ya faɗi ta yi saurin cewa "Anees!" Yadda ta kira sunansa da ƙarfi ya saka shi juyawa ya kalle ta suka haɗa ido sai ta yi saurin ɗauke fuska ganin ya kashe mata ido ɗaya. "Yes baby, soon zan tare da matata in sha Allah. Aure zan yi ko na ce...,"


"Stop.....


Ta yi saurin dakatar dashi tana taro ƙirjinta da take jin kamar zuciyarta ce zata yanko ƙirjin ta fito, bata fatan ace abin da take hasashe ya zama gaskiya. Sarai ta san mahaukacin son da Anees yake yi mata amma babu haka a lissafinta ya shi ya sa ma bata bashi fuska ba, kar ta wahalar da zuciyar ɗan mutane a banza. "Ahlam"


Ya kira sunanta a tausashe ya ɗora da faɗin "wannan satin za'ayi Annual Media Excellence 2025. Shagalin karrama ma'aikatan kafafen yaɗa labarai na shekara ta 2025. Kina expecting karramawa ne a wannan shekarar ne kikai da za'a iya baki wani award, wanne kalar award kika hasashe za ki samu a taron?" Jikin Ahlam har rawa yake yi ita gabaɗaya ta mance da taron da ake yi duk ƙarshen shekara wajan bada karramawa ga ƴan jaridun da suka fi kowa hazaƙa. A wannan shekarar ne kuma take son nunawa Yussy cewa za ta iya, zata nuna mata nakasa ba zai zama kasawa ba.


"Allah Ya bawa me rabo sa'a Anees"


"Amin. Allah Ya sa ki samu Outstanding Journalist Award a ɓangaren mata baby"


Maganar award da taron da Anees ya yi ya sake saka Ahlam cikin damuwa, a hankali ta ciro wayarta saboda wani program da zata fara gabatar tana buƙatar bincike sosai. Data ta kunna, ta shiga Chatgbt ta fara bincike a hankali take dubawa, sai idanunta ya sauka akan wata kalma da bata taɓa gani ba, kuma ta kasa fassara ma'anar ta. "Kwagh" shine kalmar sai ta sake tambaya, mene fassararta wanne yare ne wannan?


Nan take ya bata amsa da "Tana nufin Almara a harshen Tiv, wanda yana cikin harsunan Bantu/Congo"


A hankali ta furta "TIV?" Anees ya juya ya kalle ta, sai ya yi murmushi ya cigaba da driving domin shima bai san mene Tiv ɗin ba. Ta samu kanta da buƙatar son sanin mene Tiv.


Chatgbt ta sake tambaya ta ce "Mene Tiv?"


"Tiv wata kaɓila ce a Nigeria, sun fito daga yankin da yake kusa da Kamaru"


Taɓe bakinta ta yi, a hankali kuma ya fice daga cikin application ɗin bayan ta karanta, haka kawai kuma kalmar Tiv da son sanin su waye su ya shiga yi mata yawo a cikin kanta.


Har suka ƙarasa Bright Fm bata sake cewa komai ba, saboda abubuwan da take ji sun fi ƙarfin ta faɗe su. Parking Anees ya yi a harabar gidan rediyon ganin Ahlam ta fito tana ƙoƙarin amsa kira ya ɗan yi gaba saboda akwai aikin da zai yi a ciki. Da murmushi ta amsa kiran ta ce


"Zainab Alƙali"


Ta cikin wayar Zainab Alƙali ta ce "Golden voice, ya naga har yanzu ba ki shigo ba ko ba ki da duty ne yau?" Cikin jin daɗi ya ce  "Kin ganni a haraba yanzu zan shigo reception. Shegiya ki ce yau akwai labari, wanne littafi kika samo za ki fara karanta mana Besty?" 


Zainab Alƙali ta yi dariya.


"Ke dalla ki shigo ciki tukunna"


"Please bama ƴar haka"


"Ban wani duba littafin ba, amma naga sunan wai ko INUWAR GIGINYA. Akwai labari ki ƙarasu ciki"


"Ok....." Cewar Ahlam.


Kashe wayar ta yi tana ƙoƙarin juyawa taga mutum tsaye a gabanta yana ɗan zazzare idanu "Malam lafiya ya  zaka tsaya mini a gaba kamar ka haɗiye taɓarya?" Ya ƙura mata jajayen idanunsa yana watsa mata wani irin malalacin kallo zata tafi ya ce 


"Kece Ahlam Abdallah Kurmi?" Ta ɗan dube shi kaɗan "Yeah, ni ce ya aka yi?"


Ya jinjina kai ya ce "Ƴar jarida fa Golden voice?" Siririn tsaki taja saboda ta fara gajiya da rainin da wayon da yake yi mata. Duk ni ce. Malam ka faɗi mene matsalar aiki ne dani a ciki kuma ka tsayar dani waje guda" ya yi baya yana murmushi da ɗaga kai. "Relex..... Relex.... Relex"


"Ina nufin wacce ta saka labarin matar da aka ƙonawa jariri fa?" Ya tambaya.


"Ni ce, kana da matsala ne?"


"Eh babba ma" ya bata amsa.


Kafin ta ce komai ya ciro wata lafiyayyiyar wuƙa a ƙugunsa tana wani irin sheƙi ya yanki Ahlam da ita a hannunta ta fasa wani gigitaccen ihu ta yi baya ya sake yi mata wani lafiyayyen yanka a wuyanta ya ce 


"Hukuncin ɓatawa mahafinmu suna" Yana faɗin hakan ya juya a guje ya fice daga cikin wajan. Wani gigitaccen ihu Ahlam ta kurma tana dafe wajan da hannunta, jini tuni ya wanke mata wuya da rigarta har jiri ya fara ɗaukanta, ta kasa motsi ta ƙanƙame wajan da hannunta tana jin kamar ranta ne zai fita idan jininta ya ƙare, kai tsaye rayuwarta aka nema, rabata da duniya aka so yi ta ƙarfin gaske akan case ɗin da bata da laifi a kan shi. "Wayyo wuyana, don Allah taimaka mini zai kashe ni, Anty Jiddah, yayana, wuyana" da ƙarfin gaske take kiran sunayen nasu.


Sannu a hankali yake murza ɗan Bluetooth ɗin hannunsa daga inda yake tsayen, waya yake yi don haka dukkan attention ɗinsa yana ga wayar da yake yi ne. A hankali ya ce 


"Ki fita daga maganar nan, kin san bana shiga sabgar kowa bana son raini at all"


Ya yi shiru alamar saurare can ya nisa ya ce "Zan sake faɗar the same abin da na ce, babu ruwana ok?" Wanda yake wayar dashi zai sake magana MD ya yi saurin dakatar dashi da faɗin. 


"Hold on....."


Ya kashe wayar tare da saurare na ihun da yake ji tun ɗazo, ya juya idanunsa sai kuma ya ɗan taɓe bakinsa tabbacin bashi da ruwa da tsaki akan me ihun da dalilin ihun. Addu'arsa ɗaya ce, kar hargagin ya saukar masa da ciwon kai mara tushe. Amma me? Takalmi macen daya gani da jaka a yashe sune abu na farko daya ja hankalin nasa. "Wace wannan?"


"Ta kuma rasa wajan yin taɓararta sai a nan? A gidan rediyonsu? Ta ɓata musu suna?" Gently ya fara tafiya hannunsa ɗaya cikin aljihu, idanunsa cikin glasses wanda ya amshe shi ya yi daidai da faɗin fuskanta me ɗauke da zagayayyen sajen daya kwanta. Yana isa idanunsa ya sauka akan ta tana durƙushe jini na zuba daga wuyanta gashin kanta ya tarwatse a bayanta kamar zautaciyya. MD yaja numfashi ya sauke sbd bai yi tsammanin ganin jini ba, ya kuma fahimci wacece tunda ga Id card ɗinta nan a yashe. Bayan ya ƙarasa ya ɗan miƙa ƙafarsa kaɗan yana zungurinta. A gigice Ahlam tace  "Don Allah kar ka kashe ni, nifa matar aure ce, ko tarewa ban yi ba. Kar ka cutar dani"


Idanunta ya faɗa a kan shi, sai ta miƙe tsaye da ƙyar tana layi idanunta na shanyewa, a firgice ta ƙarasa kusa da MD ta miƙa hannunta ta damƙi nasa ta ce "Na san ni da kai bama shiri, amma kar ka bari na mutu saboda jin haushina da kake, bana son na mutu banga ƴaƴana ba, yau aka yi mini aure ko mijin ban sani ba, wayyo yaya za su kashe ni" Ta sake damƙo MD ta ce "ka taimaka mini ka kira mini yayana, wallahi bana son na mutu, ina da buri akan aikina, ina da burin ganin na ɗaukaka ina da burin naga na haihu na tara zuri'a masu yawa" da ƙyar take yin maganar saboda fitar hayyaci.


"Help me.....


"Please!" 


Ta ce cike da raunin murya.


Taɓe bakinsa kawai ya yi ganin ta sulale zata faɗi a wajan ba numfashi ya saka hannunta ya riƙo nata, ɗaukarta ya yi gabaɗaya ya sakata a cikin motarsa, daidai nan Baba driver yazo wajan ya ce "Yallaɓai ina zaka?"


Hannu MD ya ɗaga masa alamar babu buƙata. Baba driver har ya juya ya ji MD ya ce "baka ji ba?" Sai Baba driver yaja ya tsaya


"Na'am, ka ce wani abu ne?"


A nutse MD bayan ya shiga mota ya ɗan murza key ya ce "Ka faɗawa officer muna buƙatar police a cikin Bright Fm right now"


"Police? Ƴan sanda fa Yallaɓai?"


"In sha Allah" cewar MD.


Yana faɗin hakan yaja motar a guje ya bar cikin gidan rediyon.


***

"Mita 119 bright Fm kuke so sauraro. Au yau ne hukumar ma'aikatar ilimi ta jiya ta sanar da sabon tallafi da gwamnati ta fitar ta ƙarƙashin hukumar, inda za'a ɗauki adadi ɗaliban jami' kimanin mutane dubu ɗaya aikin Gwamnati, tare da bada tallafi ga wasu. Za'a fara tantance ɗaliban a ranar Litinin me zuwa, ɗaliban zasu taho da takardun makaranta wanda dama ta iya wanda suka fita daga first class ne" sai aka ɗan dakata da maganar aka sako taken gidan rediyo. "Labaran Duniya" muryar na namiji ya fito.


"Daga gefe guda, wasu da ba'a san ko su waye ba, suna shiga rugar Fulani tare da yi musu kisan gilla, bayan kisan suna tattare kan jama'ar su yi gaba dasu, an fasa Fulani adadin da ya kai 75. Duka ina jami'an tsaro da gwamnati suke ake wannan abin? Aka ce, kowa ya ji daɗin gemu bai ka maƙoro ba. Ahlam Abdallah Kurmi ke tare daku"


A hankali ya kashe radiyon tare da yin baya ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa na bugawa sosai, tun rahotanni da ta yi jiya da daddare ne sai yau aka saka. Ya numfasa ya ce.


"Ba wani bayani akan yarinyar ne?"


Wanda aka tambaya ya ce "Akwai, Ahlam Abdallah Kurmi sunanta, amma asalin sunan shine Haleemah, iyayenta sun rasu tare zaune a wajen yayanta Engineer Abdallahi. Shine ya tsaya mata tun daga primary har zuwa secondary da jami'a, karatu me kyau ta yi a makaranta me tsada a ɓangaren aikin jarida. Tana da ƙoƙari da jajircewa a aikinta, amma a nutse take, bata da hayaniya tana da kamun kai, ba irin sauran da suke mata aikin jarida bane. Sir i wonder why kake son ganinta, is there any problem da ba zaka iya sharing ɗinsa dani ba?"


Ya ware idanunsa, kallon yaron kawai ya yi ta cikin glasses ɗin idanunsa ba tare da ya ce masa komai ba.


A ɓangaren Maryama a wannan dare a tasha ta kwana, mutane sai kallonta suke yi, wanda tana da tabbacin kallon mahaukaciya suke yi mata, ƙudaje suna ta binta saboda jinin haihuwar daya ɓata mata jiki, zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi a ƙirjinta, ko kuka ta kasa idanunta ya bushe sai yawo take yi da gawa a hannunta wacce ta ɗan fara wari. Mutane na ganinta suke matsawa zuwa gefe.


A hankali taja jaririn ta ƙanƙame a ƙirjinta sai a lokacin ta samu damar sakin wani irin raunataccen kuka me cin zuciya, ta yi ta gama ta lallashi kanta ta faki idanun jama'a ta ajjiye gawar a gefen kwata dake tashar ta tashi da sauri ta bar wajan tana dafe ƙirjinta.


***

Ana ce kwance a gadon asibitin da take, ta yi shiru idanunta a rufe tana sauraran bugun zuciyarta daya ruɓaya fiye da yadda take ji a lokutan baya, a hankali ta miƙa hannunta zuwa saitin zuciyar da nufin ta danne ta da tafin hannun, sai ta ji haƙarta bata cimma ruwa ba, tamƙar tana saƙa ne zaran baya data tufke yana warware kan shi. A dalilin bugun dake ratso ƙirjin yana haɗawa da hannun da take ganin ta ɗora da nufin bata kariya. A kowacce daƙiƙa ta shigewar lokaci ƙara nisanta zuciyarta da Daada take yi, nisan da take murna dashi domin da gaske bata buƙatarsa a rayuwarta, ace da uba ake gado, ita kam bata yarda da wannan gurɓatacciyar kalmar ba, bata yi believing da ita ba, kuma bata jin ko nan gaba da abada zata yarda cewa da uba ake ado har ta bawa jimilar muhalli nada ban a zuciyarta. Da Innti take yin ado, ita ce sahibarta abar adonta, abar ta ɗauki abu ta yi shelan irin tarin soyayyar da take yi mata, sau tari ta kan rasa sanin adadin soyayyar da take yi wa Innti da Mahaɗinta, soyayyar kunnen doki ce, kowanne ba zata iya shaƙar wadataccen numfashi ba idan babu shi.... Bayan su sai waye next? Yaa Jadid, da Yaa Jaheed jaruman yayyinta a ɓangaren uba kuma Babban yaya shi ne ubanta shine abu mafi ƙauna a ranta a ɓangaren maza. Shine duniyar Ana.


Bayan su sai wa zata saka a lissafin nata?"


“Haysaam"


"Yaa Sam.....


Ta faɗa a fili tana sakin lallausan murmushi.


Motsin da ta ji ya saka ta buɗe gajiyayyun idanunta wanda sukai laushi saboda ciwo da galabaitar da zuciyarta ta yi saboda tunanin 'future life' ɗinsu ita da Iftihal. "Abbaa" ta kira sunan a tausashe tana faɗaɗa murmushinta. Kallon ta ya yi na wani lokaci, jikinsa sanye da sabbin kaya wanda sukai masa kyau sosai, ya ɗan sake yin fresh, lallausan sumar kansa da take har baya ta dinga ɗaukan idanu a nutse ya ƙarasa ya zauna daidai kanta ya zuba mata ido, ita ɗinma kallon shi take yi da manyan ƙwayar idanunta jin shiru ya saka ta miƙa hannunta ta riƙo nasa ta ce 


"Abbaa...


"Abbaana"


Ya ɗan buɗe ido bai magana ba. "Ina ka je? Tun jiya baka dawo ba in ji Yaa Sam" bai bata amsa ya juya idanunsa alamar


"Kina jin ciwo?"


Ta ji ya  furta da silent voice ɗinsa me sanyi a cikin shurunsa da maganarsa ta body language.


Ta jinjina kai lokaci ɗaya ta ce 


"Eh"


Ya zauna kusa da ita ya damƙe hannunta dake cikin nasa ya shafa gefen kanta ya zuba mata ido alamar saurare. Ana ta ce "Abbaa ka yi mini alƙawarin ba zaka zama irin mijin Innti ba, ba zaka dinga cutar da matarka ba, da yaran da Allah zai baka, ka yi mini alƙawarin zaka dinga sakawa yaranka albarka daga cikin yaran na zama ɗaya daga ciki, ka zama babana ni na riga na zama ƴarka Abbaa. Zan yi addu'a Ubangijin Ya yi mini yalwar arziƙi na siya maka gida babba mu koma can ka yi aure ka buɗe babban shago a Farm center. Ina son ka Abbaa kaina hope ɗina, kai na nake gani na ji ka cike mini gurbin uba, ina ƙaunarka Abbaa"


Ya shafa goshinta alamar "Idan ba Ubangiji ba, waye zai maka kyautar ɗa babu aure?"


Ta washe masa jerarrun fararen haƙoranta. Ya shafa hannunta tabbacin "Idan Ubangijin Ya ara mini rai da kuma dama, zan cike miki duka gurbin da kika rasa, In sha Allah"


"Da gaske kake Abbaa?"


Ya jinjina kai alamar 


"Me kike buri a rayuwa?"


"Na yi rayuwa daku ta har abada, naga na zama cikakkiyar marubuciya idan na kammalawa karatuna, idan Allah ya yi mini arziƙi na kai ku hajji da umara na siya muku gida, na dinga ajjiye kayan abinci akai akai"


"Kayan abinci?"


Ta matse hannunsa a nata tana jin relief yana sauka a gangar jikinta yana samar mata da nutsuwar zuciya. "E. Saboda kada mu ji yunwar da muka rayu a cikinta, kada mu sha wahalar rayuwa My Abbaa" Ya ce "Na fahimta"


Ƙuri ya yi mata da nasa idanun dake nuna maganar 

"Ba ki yi maganar aure ba?" In seconds yaga mood ɗinta ya sauya, damuwa ta maye gurbin walwalar wani abu ya tukare ƙirjinta ya tsaya mata tana jin ya yi mata nauyi. 


"Kodayake you're still my baby"


Ta yi murmushi "I'm always been your baby"


"Your favourite daughter"


Sai ya sumbaci goshinta yana faɗin "In sha Allah!"


hanyar fita daga ɗakin ya nufa da ƙarfi ya ji ta ce "Abbaa" jikinsa na rawa ya juya yana tambayar mene sai ta ce "Ina son ka Abbaa"


Girgiza kai ya yi ya fita cike da karyewar zuciya da tunani kala-kala a ransa ya nufi titi neman me napep ya ɗauke su zuwa gida.


Haysaam.

Yana zaune a cikin ofis ɗin likitan ya zuba masa ido tare da sauraran abin da yake cewa cike da zallar nutsuwa da fahimta. Dr ya gyara zama ya ce "Wannan yarinyar Allah ne ya yi tana da sauran kwana Sam, ga binciken da muka yi abin da ya nuna" ya tura files ɗin gaban Sam ya ɗora da faɗin. "Bincike ya nuna ta samu tabo a mahaifarta dalilin dukan da akai mata, wanda a turance muke kiran matsalar da SCAR wani gurɓataccen nama ne da jiki ke ƙirƙira bayan rauni ya warke. Idan aka samu duka, ita kuma ta samu Scar a MAHAIFA (uterus) wanda zai haifar mata da miscarriage, ko ta samu wahala wajan samun ciki, wahala wajan saduwa. Zubar jini mai yawa (internal ko external bleeding) don haka disvirging nata zai wahala, kamar yadda ɗaukan ciki zai mata wahala. Wannan serious issue ne Haysaam, yana da kyau duk wanda zai nemi aurenta ya san da wannan matsalar Please" 


 Wata zufa ce ta shiga tsastafowa Haysaam ta tsakiyar goshinsa, ya yi shiru bayan ɗora kan shi da ya yi a saman table ɗin dake gaban likitan, jikinsa duka rawa yake yi kamar an watsa masa ruwan ƙarƙara wanda ya yi daidai da lokacin hunturu ƙofofin da suke lulluɓe gargasar jikinsa, ya yi shiru.


"Haysaam....


Likitan ya kira shi da kulawa. "Naga ka damu da Chocolate girl ɗin nan, ka yi haƙuri kowa da ƙaddararsa, ka dai ja mata kunne akan wasan banza ko don lafiyar jikinta"


Haysaam ya kasa magana, dr ya dafa ƙafaɗarsa "A kula sosai da jikinta, a faɗawa wanda zai aure ta" a hankali Sam ya ɗago kan shi ya watsa rinannun idanunsa a fuskar Dr a kasalance ya ce "Ina son maganar nan ta zama sirri, kar yarinyar ta ji haka mahaifin yarinyar ka bar ta daga ni sai kai" Dr ya buɗe ido da mamaki "Amma ta ya ya wannan matsalar zata zama sirri, bayan dole ta yi aure ta zauna a gidan mijinta?" Haysaam ya ce


"Dole ta zama sirri Dr "


"Ok tell me how? Tayaya......


"Saboda ni ne mijin, ni zan aureta" ya nuna kan shi da yatsa 


"What!" Dr ya furta da sauti na zallar mamaki.


"Haysaam baka yi mini kala da wanda hankalinsa ya bar jikinsa ba, kana son sadaukar da lafiyarka saboda ita ne?"


A ɗan harzuƙe Sam ya ce "Ok Kamal, Ka faɗa mini ya kake so ayi, ya kake so yarinyar ta fahimci rayuwarta zuwa nan gaba? Wannan ba zai zama hujja kaɗai ba, bai zama hujjar da zaka gina na cewa na yi Sacrifices ba, idan sadaukarwa zan yi mata nawa ke buƙatar hakan, na je gidan gyaran hali, ko gidan karuwai, ko gidan marayu zan iya ruskar matan da zan iya zaɓa na yi Sacrifices akan su" sai ya yi baya kaɗan ya taka a hankali zuwa gaban Dr Kamal ya ce "Wannan daban yake, dalilin ma daban na, is difference Kamal ina fatan zaka fahimta" Dr Kamal ya ce


"Matsalar soyayya?"


"I did say it.....


"You don't need to say it ai dama, baka buƙatar ka ce ma, your action shows. Soyayya kaɗan ke rufe idanunta mutum ya gaza gane gaskiya, ta ya zaka auri yarinyar da zaka iya ƙare rayuwarka babu haihuwar ko kuma ka ƙare rayuwar ba tare daka taɓa saninta a matsayin mace ba?' ƙuri Sam ya yi da jajayen idanunsa akan fuskar Kamal. "Ai ya zame maka dole ka kalle ni, ba zan ɗauki wannan rubbish ɗin ba, akan wannan yarinyar ko farcen da zaka sosa jikinka wallahi sai ka neme shi ka rasa, ka ɗauki responsibilities ɗin daba naka ba, ka ɗora wa  kanka kazar tsaba haka za ta yi ta binka. Kai ne suttura, kai ne kayan abinci, kai ne kayan ƙyale ƙyale na mata. Babban takaicin ma, yadda ta fito daga maragurbin gida, kallon turɓaya nake mata, gidan da basu da tarbiyya ko ta misƙala zarratan........,"


"Kau.... Kau!" Haysaam ya ɗauke Dr Kamal da wasu maruka lokaci guda, wanda ƙarfinsu ya bada wani irin sauti. Ya dafe kunci yana kallon Haysaam ya ce "Mari?"


"Marina ka yi akan yarinyar can fa Haysaam?"


"Zan iya yi maka fiye da mari akanta. Sai dai wannan marin ya sha bambam da tunaninka. Rayuwarta kake kallo kawai, mahaifinta kake dubawa kawai, baka san wacece ita da irin tarbiyyar data samu ba"


A zafafe Kamal ya ce "Tarbiyya banza da wofi, tarbiyya idan irin ta gidansu ce Allah Ya tsine mata, ko kyauta za'a bani auren mace a gidan nan banga uwar da zan yi da ita ba. Har shine kake da zafin zuciyar marina akan ta?" Da wata irin zafin zuciya shima Sam ya yunƙuro kan Kamal ya ce "Kasan zafi da raɗaɗin da yake cikin muzanta ɗiya mace? Idan maganar tarbiyya kake akaso ɗari na tarbiyyar yarinyar nan kaso talatin nawa ne, kashi hamsin na babarta kashi ashirin na Yaa Marwaan"


"Matse muku ta yi kai dasu, amma alamu yana nuna shaiɗaniyya ce alaƙarka kai da ita babu alheri tunda har ka iya marina akan ta" wani irin huci su biyun suke fitarwa kamar masu ganin hanjin juna, fuuuu kuma Sam ya juya. "Kazo ka bani kuɗin treatment ɗin da na yi mata don ubanka ni ba bawa bane" cewar Dr Kamal yana ɗaga murya amma ko ta kan shi Sam bai bi. Ko da ya fito daga ofis ɗin sai daya tsaya ya samawa kan shi nutsuwa ya saita fushinsa kafin ya ƙarasa room ɗin da take ciki a nutse abin shi


Bacci ne ya ɗauke ta tana rungume da hannunta a ƙirji kanta a tsakiyar katifar gadon gashin ya barbaje numfashinta na sauka a ƙirjinta a hankali tana sakin ajjiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun tsira da rai. Haysaam ya jima tsaye a kanta ya zuba mata idanunsa a cikin jinya take amma sosai ta yi masa kyawun gani a cikin idanunsa. Yaja nasa idanun ya lumshe yana haƙaito lokacin, da ranar daya fara sanyata a cikin idanunsa, ranar daya fara ganinta.


Wata ranar talata ce, da farar safiya ya fito sanye da fararan kaya wanda suka kasance uniform, ranar da zai rubuta jarrabawar ƙarshe a Rumfa College lokacin yana Sakandire. Yana tsaye ya zubawa gefe guda ido yana lissafin yadda zai taka a ƙafa daga nan Kankarofi zuwa Rumfa College ɗin. Murmushinta ya ji, murmushinta ya fara ji ya sauka a cikin kunnensa, idan ba zai mata ba abu biyu daya gani a tattare da ita bayan murmushinta shine yatsun hannunta, wanda ta yi amfani dasu wajan riƙe tsinke tana yin zane na haƙa rami za ta yi ƴar carafke ake cewa, bai ba gama sanin sunansa ba. Kasancewar ɗaukewar ruwan sama kenan, wanda yana daga cikin abin da ya saka shi yin latti a makaranta. Bayan yatsun hannunta sai sumar kanta wacce aka rabata gida biyu aka tufke. Babu takalmi aƙafar kamar yadda ya lura da koɗewar kayan jikinta. Bai mata magana ba, ya nufi shigewa ta ƙofar gidansu a sama ya ji ta ce 


"Ramina... Wayyo ka rufe mini ramina"


Ya ji wannan karaɗin, ya ji slow voice ɗinta.


"Ƴaƴana na wasa suna ciki, wayyo ni" Cak ya tsaya a wancan lokacin ya juya ya kalle ta, bashi take kallo ba, hankalinta yana kan abin da take ƙorafin ya yi mata ɗin.


"Ƙazama" abin da ya furta kenan. "Ba ƙazama bace ni, mahaɗita nake jira ta fito mu yi wasa shine ka cike mini ramina"


Sai ya dakata gabaɗaya fuska a tsuke ya ce 


"Tashi a nan wajan"


Sanda ya fara ganin ƙwayar idanunta sai da ya yi tasbihi a cikin ransa, ba ƙwayar ido ce bai saba gani ba, hasken daya fito daga cikin nata ya shiga nasa shine abin da bai taɓa fuskanta  ba a rayuwarsa, bayan hasken shine manyan da ƙwayar idanun nata suka kasance dashi, sai kuma shuɗiyar kala madadin baƙa. "Idan ba ƙazami ba, wake wasa a turɓaya?" Ita dai kallonsa take yi, kallon da bata taɓa tsayawa ta yi wa wani ba, idan aka ɗauke ƴan gidansu.


"Kana da kyau"


"You're very handsome"


Ya ji kyau ɗin, ya kuma yi mamakin fitar turanci daga cikin bakinta. Miƙewa ta yi tsaye sai ya lura jikinta ya girme wa shekarunta, ya kuma lura da yadda take ƙyanƙyamin turɓaya kamar ma akwai abin da ya fito da ita daga cikin gidan. Ya nisa yace "Ina takalmanki? Kallabinki?"


"Suna gida" bata bari ya sake yin wata maganar ba ta shige cikin gidansu a nutse.


Motsin da ta yi a saman gadon ya tilatsa Haysaam dawowa daga tunanin abin da ya shuɗe, gani ya yi tana jujjuya kanta zufa na yanko mata a goshinta sai ya ranƙwafa kaɗan ya kalle ta, har numfashinta na sauka a saman fuskarsa. "Nanaah.... Nanaah..."


"Kai na....


"Kaina Yaa Sam zai cire"


Da farko ya rasa abin yi, domin yana avoiding duk abin da zai haɗa shi da ita wanda yake a haramce. Amma alaƙar shi da Ana tafi ƙarfin haka, mu shi da kan shi shaiɗan zai ji kunyar kunno kan shi cikin su. Hannunsa biyu ya ɗauka ya ɗauki kanta ya ɗora a cinyarsa ya ɗora tafin hannunsa yana murza kan nata. Babu jimawa ta sauke numfashi tare da buɗe idanun. "Nagode"


Ta ce a sanyaye. Ya yi mata ƙuri da ido.


"Ya jikin naki?"


"Allahamdulilah"


Ya jinjina kai ya ce "Sakko muje"


"Lagos?"


Harara ya watsa mata ya ce "Ba za ki raba kan ki da zuwa Lagos ba?" Sai ta ɓata fuska taƙi cewa komai. Rufaida fura ya ɗakko ya saka cokalin ya nufi bakinta ya ce "Sha tukunna sai mu yi magana" ƙin kula shi ta yi.


"Niko?" Ta yi shiru.


Sai ya mayar da furar cikin rubar, ta ƙasan ido take kallon shi sai ta ce "Zan sha fa" Yana jinta ya share sai daya kammala tura saƙo da keyboard ɗin wayarsa ya sake ɗebo furar ya nufi bakinta, ta buɗe ƙaramin bakin ya shiga bata, idanunta a cikin nasa, kamar yadda shima yake kallon ta. Murmushi ta yi masa, shima ya sakar mata murmushin, ta lumshe idanunta shima yaja idanun ya lumshe. Idanu ɗaya ta kashe masa, a hankali yaja idanunsa na dama ya kashe mata. "Yaa Sam ɗina" ya murmusa ya ce 


"Nanaata"


"Na ƙoshi" 


Tissue ya ɗakko ya ɗora hannunsa a kanta ya ɗan matso da ita ya shiga goge mata bakin, bayan ya kammala ya ɗauki hijab ɗinta da Babban yaya ya kawo ya saka mata. Sauran furar ya fara sha shima yana cikin sha Babba yaya ya shigo. Kallonsu ya yi su biyun babu wanda ya yi wa magana ya kwashi kayansu zuwa waje. Sakkowa ya yi ya miƙa mata hannunsa ta saka nata a ciki suka nufi fita daga asibitin suna zuwa waje Yaa Sam ya yi saurin sakin hannun Ana. Napep suka shiga Ana da Yaa Sam na baya, Babban yaya a gaba suka nufi Kankarofi.


***

Ta shafe awanni huɗu a bakin ruwan, tun tana saka rana zata sake ganinsa har ya fitar da rai. Hannunta ta miƙa kaɗan ta share hawayen da yake bin fuskarta a sanyaye ta ce "Yau ma kaɗo bai zo ba, ina kaɗona? Yana ina?"


Taja idanunta ta lumshe a raunace ta ce "Innata.....


"Su waye suka kashe mini Innata?" Ta fashe da kukan halin maraican da take ciki.

***

YARI.

Yau tunda Gana ta tashi, sai ta tashi da wata kalar maita kamar ta ci babu ga ranar rugar yau a buɗe take ta rasa inda zata saka kanta ta ji daɗi, idan ta juya nan sai ta yi karta da haƙori idan ta sake juya sai ta karta haƙori idanunta ya yi jajur har barkono ta watsa a bakinta ɗanye jawaur dashi amma ƙanƙarar maitar bata lafa ba. Burin da ta ci na samu kuɗi ya rushe ta shiga ɗakinta can uwar ɗaka taja ƙofa ta rufe, inda take ajjiye kayan tsafinta ta sunkuya ta ɗakko ta zaro wani baƙin ƙyalle ta ciro wata ƴar ƙaramar aba, mai kama da tsokar nama ta dunƙule a hannunta ta shiga surutai yana yafa jan yadi, nan take sai ga kurwar jaririn Kulu ta koma ɗanshila wanda ba'a jima da ƙinƙishewa ba. Ta kwantar dashi ta murɗe kan ta yi cilli dashi kamar idanunta za su faɗo waje, ta cilla shi cikin ruwan zafi ta fiffige gashi ta ɗora sulale da jini-jini a jikinsa ta dinga ɗauka tana ci tsabar masifar da ta yi mata yawa. "Wayyo.... Wayyo daɗi, naman jariri akwai Musulmin daɗi wallahi"


Soyawa ta yi tana gamawa ta juye a ƙaramin filast ta tsiyaye man soyar a ƙaramar roba. "Naman jariri yafi kowanne daɗi, dashi da tayin da ba'a haifa ba. Inama Kulu ta sake haihuwar wani. Oh ni Gana ina zanga wani jinjirin yanzu da zan ci? Waye ke da ciki?"


"Gafaranku dai"


"Allah yai mana" ta amsa sallamar tana buɗe ƙofa ta fito waje. Washe baki ta yi ta ce  "A'a wa nake gani kamar Hindatu"


"Ni ce rana tsaka Gana"


Gana ta ce "Lale maraba da Hindatu" Ta shimfiɗa assabari a gefen inuwa ta ce "Yada zango mana Hindatu, jiyan nan kika faɗo mini a rai nace muna maƙwabta amma ba zumunci walle kunya ta yi mana yawa"


Hindatu ta ce "Bari ke dai Gana, surfe da casa ne ya azo ni gaba. Yanzu ma ina zaune ina taɗin zuci na ji ƙamshi ta saman kanta shine na leƙo nima ayi dani, ko me gidan ya yi miki tsaraba" Gana ta zubawa Hindatu ido na wani lokaci kafin ta ce "kayya, Ƙamshin man ƙuli dana soya da albasa kika ji. Bari na kawo miki ruwa da abinci ko?" Miƙewa ta yi ta zuba mata wake da gero da ƙuli ta ɗauki man data soya jaririn Kulu dashi ta kelaya saman abincin ta ajjiye mata ta kawo ruwan tulo me sanyi a kofi ta ajjiye. 


"Bisimillah Hindatu"


"Hadda wahala haka Gana?" Bakinta har dalalar da yawo yake tsabar kwaɗayi ta fara cin abincin. "Gana wai ni kowa ina Batty ana ta raɗe-raɗin yaro hura mata iskar balo a ciki shi ne kika ɗauke ta, wasu ma sun ce saboda uwarta bata raye kin kasa riƙe marainiyyar Allah" Gana ta fashe da kuka tana kunce bakin zani ta ce 


"Na shiga uku kuma ni Gana, duk ɗawainiyyar da nake da Batty babu wanda ya yaba sai yanzu da jarrabawa ta same ni? Yadda naga Saleh yana turmushe Batty a zaure da murje ƴan ƙirjinta Allah Ya nuna mini Annabi. Ki faɗa mini da ban ɗauki matakin ɗauke Batty ba ai da tuni ya hura mata iska a ciki mun shiga uku. Da uwar uwar Batty dani nono ɗaya muka sha fa?" Hindatu ta ce "Sai haƙuri, mutane akwai su da gadon zancen wasu. Gana kin ji abincin nan inda ya yi daɗi? Ban taɓa jin man ƙuli da daɗi irin wannan ba, ko nama aka bani ba lalle ya yi daɗin wannan man ba" Gana ta yi murmushi ta fara tunanin yadda zata sawa Hindatu ƙanƙarar maita ta yi maganin shegen kwaɗayinta. Ta ce "Naman ma ina dashi, kuma idan kikai biyayya ma irin wannan kullum dashi za ki ci abinci na rantse" Hindatu ta waro ido waje ta ce 


"Don Manzo?"


"Taso muje na ba ki nama da wani man" cewar Gana tana miƙewa tsaye ta yi cikin ɗakinta zumbur  Hindatu ta miƙe tare da bin bayan Gana tana tafe tana riƙe zani da suɗe yatsun hannunta tana tunanin kakarta ta yanke saƙa daman ta biyu ta shigo gidan....



Littafin HIYAAM na kuɗi ne akan 1500. Muna tsarin discount akan mutanen farko da suka fara payment, daga book 1 2 3 za su biya 1k kacal. Wannan Discount ɗin ana kammala free pages an rufe.


Mutanen farko da suka fara payment na HIYAAM za su biya 1k kacal ne.


Idan mukai limit da yawa za mu yi Hiyaam a WhatsApp ne, idan ba'a samu limit ba, za'ayi a Telegram da ArewaPen. Kana da ikon siyawa ƙawayenka, ko ka yi sponsoring wa jama'a domin Allah ko kuma a tallata maka business ɗinka.


Wannan tafiyar sabuwa ce, baku taɓa cin karo da ita ba.


0116886423

Union Bank

Na'ima Sulaiman S


Shaidar biya.

08164069385 ko 

08082101373


A yi weekend lafiya.

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post