Karshen Kaddara Page 21&22 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*


𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ


 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_


Unexpected and Surprising 🔥💥 


𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 


ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....


Page 21&22


*End of  Last free Page's end🤗*

# SingleAndThriving

♡ ♡ ♡ ♡     

ꨄ Wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu laushi. Kafin ta shiga fesa turare mai sanyi, bayan ta shafe jikinta da humra, tana cikin saka  hula ya shigo yana sanye da pyjamasa blue colour sunyi matuƙar masa kyau, kallonsa tayi ta tarar da shima ɗin ita ya zuba ma ido. Sosai ya tsare ta da ido yana wani haɗiye yawun da yake neman sarƙe maƙoshinsa, ita kuwa gabanta se faɗuwa yake, don dama tunanin zuwa tirakarsa take don abin da kunya, wata numfashi ya ajje yana isa gabanta ya kamo hannunta ya tsotsi yatsarta ƙaramar, kafin ya rungumeta yana sakin ajiyan zuciyan kewanta da yayi. Wayarsa da yay ring ne ya saka shi rabata da jikinsa yana hanyar fita da hannu ya nuna mata ta biyo shi. Hijab kawai ta ɗora dogo akan kayan baccin dake jikinta ta nufi part ɗin nasa, baya palourn nasa  hakan yasa direct ta nufi bedroom nasa, a zaune ta same sa a gefen gado yana danna waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta  gabanta yana tsanan ta bugawa, a farkon gadon taja ta  tsaya kanta a ƙasa tana wasa da hijab ɗin ta, sam bataji tahowar saba kawai sai hucin numfashinsa  taji a fuskanta, hakan yasa da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa. Wani murmushi me kyau  yai yana lasar lips ɗinsa, kafin yakai hannu ya zare mata himar ɗin dake jikinta, Ajiyar zuciya ya sauƙe yana kanainayeta gaba ɗaya a jikinsa.  

  Sosai ya wani sake lafewa a jikinta   wani daddaɗan ƙamshi na bugar masa hanci, ga wani kalan laushin da fatar jikin nata ke da, haba ai dole ne yake neman zaucewa akan wannan ƴar shila ɗin. Kai tsaye a gadonsa ya mata masauƙi shima ya kwanta bayan ya kashe musu fitila...... Washe gari ya rigata tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta, Hijab ɗin ta kawai ta ɗauka ganin ya fita don haka ta nufi hanyar fita, sai dai har takai ƙofa ta dawo a gurguje ta gyara masa gadon dakin ta fita. Sallah tai ta  shige kitchen ta musu  breakfast don yace kowa ta ringa girkinta kuma duk wacce take dashi itane zata ka abinci dashi, lokacin daya haɗe su ya musu nasiha...Breakfast ɗin ta ɗiba takai masa parlourn sa, sedai tana shiga ta tarar da Matarsa ta biyu me suna Raƙabiya ta wani hakimce a parlourn ita da yaranta uku, da ɗan murmushin yaƙen data ƙaƙaro ta iso tsakiyar parlourn tana ajje breakfast ta gaida ta a mutumce, wani tsuka tayi tace ta riƙe aunty'nta bata so zata iya ƙiranta da Raƙabiyanta ma fine, bata  ce komai ba ta shige bedroom nasa don masa magana, a gaggauce ta gansa yana shiryawa tace lafiya ko wani wurin zashi?, yace mata wllh Mima ce bata da lafiya ze miƙa su hospital. ALLAH ya bata lafiya tace masa suna fitowa a tare se dai abinda ta tarar ne ya bata mamaki, da uwar da ƴaƴan ne gaba ɗayansu suke biki akan breakfast ɗin data kawo masa, shi ma sai da ya ɗan yi turus kana ya isa gabanta yana tambayarta ko miyeye dalilinta na cinye musu abinci, tana wani kwarkwasa tace... "Kasan jiya nace maka kwana mukai bamuyi bacci ba, shi yasa ko abincin na kasa tsayawa na mana..."

  A ɗan tsawace yace da ita kuma duk masu aikin gidan basu mata ba har se tazo ta nemi fitina?, wani ƙututun baƙin ciki ne taji ya ƙume don haka ta miƙe a fusace fuuuu taja hannun yaranta tana cewa tama fasa zuwa asibitin...


Kwanci tashi aka ce hasarar me rai se gashi har sunyi wata huɗu da aure suna daf da shiga na biyar ma, kuma Alhamdulillah  zuwa yanzun sosai take sakin jiki da Alƙali Yahaya,sedai har zuwa yanzu tsakaninta da tsaki yarunsa Indai sun haɗu su gaisa sama sama ta wuce itama ta  wuce. Don ba  ƙaramin kishi ne da ita da sam bata iya sarrafa shi, tsakanin ta kuwa da Uwar gidansa  Hajiya Asma'u se son barka. Don tamkar ƙanwa haka ta ɗauke ta, duk da dai itama tana kishi da Meenal ɗin, ko dan sabo da yadda Mijin nasu hankalinsa yafi karkata akan Meenal ɗin, komai yace ita duk randa zai koma ɗakin ta uban kowa se yaga kalar rawan ƙafan da yake, amma duk sanda ze bar ɗakin nata kuwa kusan kowa se yasan yadda baya son ya baro ɗakin nata, in me girkin ma batai wasa ba ranar ko kallo bata ishe shi ba, amma fa idan ta tanka masa, don duk da hakan yana ƙoƙari sosai don abinda yake zasu daga yarinyar shi kadai yasan kayansa. To amma sedai takan danne hakan itama ta kuma yi adda'a,  amma banda shugaba Raƙabiya da ake kwasar yan kallo da ita... Tin wajen ƙarfe tara saura yake zamar jiran shigowarta har gashi yanzun wajajen goma saura, don haka ya miƙe ya nufi Part ɗinta ya shiga ba kowa palourn kuma palourn a share yake sai dai ba wani ƙamshin da kullum baka raba parlourn dashi, bedroom nata ya nufa kai tsaye kwance ya same ta ta dugungune a cikin bargo, da sauri ya isa gaban gadon yana kaiwa zaune, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta Jin zafi rau ne yasa shi faɗin "Baki da lafiya  Meenal amma shi ne  baki fada min ba?" Rintse idonta tai hawaye suka silalo tace "Daddy  na ƙira ka ai  amma bai shiga ba kuma wayar tawa ta mutu ban sa a charge ba" takai ƙarshen maganar a mugun wahalce. Ɗan shiru yayi na wani lokaci kafin ya miƙe yace "Bara na dauko mukullin mota muje hospital, ai zama da jinya babu daɗi...."  Yay maganar yana fita, babu ɓata lokaci kuma se gashi ya dawo hannunsa riƙe da car key, da kansa ya taimaka mata 

ta saka kaya ya tallafota suka fice zuwa compound na gidan, da ko ina hasken solar da bata jima ba aka gyara, suna gaf da isa gaban motar se ga Raƙabiya kamar wacce aka cillo daga sama, kallo ɗaya ya mata don haukarta tayi yawan da ko tanka ta baya son yi, gaba ɗaya yanzun kaff gidan itace me basa ciwon kai. Be kula ta ba sema kwantar da Meenal da yayi  akan kujerar motar, kana ya zaga ɓangaren me zaman banza yaja motar suka fita, kai tsaye wani private Hospital ɗin dake nan kusa da su ya kaita, sai da ya buɗe mata file sannan suka shiga gurin doctor ɗin. 

 Ƴan tambayoyi tai mata dake Dr ɗin macece kafin ta kira nurse tace suje ayi  mata test, nan suka je aka mata shi dai Alƙali Yahaya yana ta adda'ar ALLAH yasa ciki ne da ita, sedai saɓanin hakan ya samu don cewa sukai maleria ne ya mata yawa. Magunguna aka basu suka koma gida, anan ɓangaren nata ya kwana yana kulawa da ita, washe gari bayan ya dawo daga sallar subhi ya dawo se ya ɗan janwota jikinsa bayan ta gaida shi yace.... "Wai yaushe zaki bani baby?, ina son inga kin haifa min baby kyakkyawa me kama dake..." Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsun hannunta tace "ALLAH ne be kawo ba amma nima ina so ai..."  "ALLAH ya kawo mana masu albarka" yace yana fita kai tsaye don shiryawa ya tafi wurin aikinsa.


Sannu a hankali ababuwa suka fara cakuɗema ma Meenal a gidan, ga yara da kamar ma turo su ake takanas su mata rashin kunya, in abu ya sayo irin duk gidan nan se an ga dama za'a raba da ita, gashi yanzun kamar sun haɗe mata kai ne, bata da wata kyakkyawar sukuni a gidan, tin bata kai masa kara har ta fara don ababuwan sun fara fin ƙarfin, ga wata shegiyar rama da tayi ita ba wacce tasan jinyar laulayi take ba, tin a wasu ababuwan yana bin bayanta yana bata kariya harta kai ta kawo yanzun se dai ma ya hauta da faɗa da masifar cewa da shi duk be san wasu ababuwan nan ba se da auro ta, shifa yanzun wani bin har dana sanin aurenta yake, gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacinta gashi tin da aka yi auren zuwanta gida befi uku ba, don matsin lamba ce dashi wajen fita, kuma baya taɓa barin ta wuni sedai taje da magribar fadi isha'a yaje ya ɗauko ta, wai a hakan ma ada ɗin kenan yanzun wani bin ma girkinta yakan shiga har ya fita bata saka Alƙali a idon taba, kafin taje ya rufe ɓangarensa wanda tin abun baya mata ciwo har shi ma ya shiga sahun daya sake figar da ita, idan kaga yadda ta tsige ta rame zaka ɗauka DEEPIKA PUDAKUNE ce farkon shigarta BOLLYWWOD dan rama, ko ina se ƙasusuwa da ƴan hakwara likely  dai tamkar deepika ɗin ga duk wanda ya mata farin sani farkon fara film nata lolz🤩. A lokacin da Shareefah ta mata zuwan ƙarshe da kuka suka rabu ita kuka itama kuka, amma tace karta faɗama Baffansu ko yaya Sadeeq su tashi hankalinsu, gashi shirye shiryen bikin Shareefah ɗin da Bilkisu ake lokacin, dan dama kusan fikon turakane tsakaninsu. Ko da ta koma gida adda'a ta dukufa yima Sister ɗin nata kan ALLAH ya yaye mata dukkan abinda ke damunta, in kuma rabuwar su ce alkhairi Ubangiji ya bama kowa hakuri don idan wata ukubar tayi yawa rabuwan shi yafi alkhairi...  Ita kuma Meenal a nata ɓangaren ba taji zata sare ba, za taci gaba da juriya da hakuri In Sha ALLAH, don bata son aurenta ya sama matsala se adda'ar itama data riƙe da nafilfilu kuma har lokacin ko ɓatan wata bata taɓa yi ba a gidan. Komai take cikin ƙarfin hali da ƙarfin zuciya take, wanda hakan har bama Shareefah mamaki take, don ta sha tambayarta ita kuwa wanne kalan ƙarfin hali ke gare ta, takan yi murmushi a lokacin tace mata. _Wani lokacin muna murmushi ne domin kar duniya tasan ciwon dake cikin zukatanmu.._


Akwai mutanen dake kewaye dani amma babu wanda ke fahimtar irin kaɗaicin dake cikin zuciyata, ina murmushi ne kawai don kar a tambayeni amma har cikin zuciya hawayene ke kwarara ba tare da tsayawa ba. Na koyi zama ni kaɗai na kuma sake yarda da wasu ke cewa, wasu mutanen daga nesa suke burgeka saika haɗa hulɗa dasu zaka yi nadama. Wasa wasa se gashi har gashi har mun shiga wata na huɗu cikin wannan matsalar, wanda ya kama watanmu tara da aure kenan,  tuni kuwa har wasu ƙananun maganganu sun fara fita waje har zuwa can cikin anguwarmu, wai Miji da kishiyoyi nacin ubana suna soya min aya a hannu, duk lokacin da zanji makamantan zantukan kalan hakan nakan yi murmushi ne kawai kamar yadda na saba, murmushin na lulluɓe duk wani miƙin dake cikin zuciyar tawa... Yau dake girkin tane da wuri ta kammala shirinta, don yau itama ta tanaji kalaman fara dawo dashi kan daidai ɗinsa, da huri ta isa lokacin ɓangaren nasa tin kafin ya shigo, amma se da ta tabbatar me girkin ta fita kuma Maman Abeed ce wato Raƙabiya. Ɗakinsa ta fara gyara masa tsaf kana ta fito parlour ta kunna kallo, tana zaune sega Maman Abeed ɗin ta shigo  kamar wacce tayi mantuwa, bata ko kalla inda take ba har ta gama juye juye da aune aunenta ta kama hanya ta fice bayan ta mata tsaki, amma in ta tankatama ai ta sama arziƙi... Babu jimawa kuwa se gashi ya shigo ɓangaren nasa, sedai turus yaja ya tsaya yana kallarta da take cikin shigar kayan bacci masu kyau. Zaune ta tashi fuskarta ba yabo ba fallasa, sannu da zuwa ta masa lokacin da yake kaiwa zaune saman kujera. Gaidasa tayi a natse ya amsa yana jin duk babu daɗi da abinda yake mata, Se dai babu yacce ya iya ne dole ne saboda ya na son bata kariya.... Se dai be san da wanne bakin ze mata magana ba, be kuma san da wanne idon ze dube taba, wata ajiyar zuciya ya sauƙe yana kamo tafin hannunta cikin nasa, lumshe idonsa yayi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da tsananin ƙaunarta da tausayinta.  Ahankali ta zame hannunta daga cikin nashi tana kaiwa ƙasa cikin rawan murya tace... "Daddy'n Nusaimah don ALLAH ka yi hakuri idan na baka wani abu ne ba tare da sani naba,kasan duk inda ɗan Adam yake azijine wllh ban san kome na maka ba, na kuma duk iyaka yi na amma ban gano daga inda matsalar take ba... Daddy'n Nusaimah

Me ya sa kake ƙoƙarin sanjawa daga yadda na sanka?, Me ya sa kake ƙoƙarin daina bani kulawanka?,  Me ya sa ka daina jin tausayina?, Me ya sa a yanzu bana gabanka?, ka dena lallashina. Me ya sa ka sanja min cikin ƙanƙanin lokaci haka?, Me ya sa?, Me na maka?....." Tayi maganar muryanta na rawa sosai... Hannunta ya kamo tare da ɗago ga yana share mata hawayen fuskarta cikin taushin murya yace. "Baki min komai ba Ameenatou!,babu abinda kika min wllh, kawai ina jin kamar ba daidai nake ba, ina kuma jin kamar ban chanchanta inci gaba da zama dake irin haka ba, sedai na rasa akan me akan kuma wane ne..... Wani kuka ta fashe dashi tana me furta. "Tabbas na fara zargin kaina da cewar ko ababuwan dana aikata ne ALLAH be gama yafe min, amma nima a cikin raina inajin kamar cewa tabbas wata rana zaka rasani, sannan zakai kewata ba don nafi kowa ba, ba kuma don na zarta sauran matan kaba,  A ahhh se dan kawai na san ranar zata zo maka wata rana, kuma idan wannan ranar tazo, kada ka kira shi da ƙaddara, ka ƙira shi da sakamakon abinda ka aikata!!!, tun da na tambayeka laifi na kace ban maka komai ba, haka kawai zuciyarka ta tsara maka fara tsanata sabo da binciko tsoffin laifukana na baya shi ne ka fara ɗora alamar tambaya akai na ka kuma dena SO da TAUSAYINA, wanda dama nasan su suka huce maka gaba wajen auren na...." Daga nan ta kwace jikinta a nashi ta fice daga ɗakin a guje tana riƙe bakinta da kuka ke son kwace mata...Ahankali kuma taɗan buɗe idanunta wanda cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu sukai ga sauƙa akan fuskar 


  _MAJEED DAWOUD_


zaune yake saman sofar dake gaban gadonsa,  system na shi ajiye saman desk se wasu ƙananun glass cup yana opreting wasu files na asibitin daya ziyarta na  Young pharmacy and private clinic...tshirt ce mai gajeran hannu a jikinsa  sai dogon wandon ta masu taushi. Idanunshi a sakaye cikin farin glass ya zuba su akan system  ɗin da yake ta famar aikinshi akai. Daga gefen sa  kuwa Ayla ce kwance ta dora kanta saman jikinsa,kanta babu scaf anyi saima  space buns ɗin da aka mata irin na Babyn nan, wanda suka mata kyau sosai  gwanin birgewa... Duk da kasancewar aikinsa yake gudanarwa amma kuma ƙasan zuciyarsa mamakin abinda ya gani yake, amma duk da haka cikin ƙarfin halin danne abu  a zuciya da kuma yanayin sa na rashin bama abu mahimmanci da basarwa ya ture tunaninta a ransa, se kuma yayi saurin istighfari a ƙasan zuciyarsa yana sakin wata ajiyan zuciya, abinda ya danne ƙirjin nasa  na ɗan lafa masa yana jin ɗan  sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru kawai  yay yana lumshe idonsa tare da jingina bayansa da jikin gadon, kafin ya sauƙe idonsa ahankali akan Ayla dake lafe a jikinsa tana bacci hankalinta kwance, sake lumshe lumsassun fararen idanuwansa yayi  yana ɗan tafiya wata duniya... Wani gauron numfashi ya kawo kuma  jin numfashinsa na shirin fiffizgewa , alaman tunanin daya tafi me ɗan zurfi ne. Da Ayla ya tashi a jikinsa kai tsaye Part na Ummiensa ya nufa, kai tsaye ya kwantar da ita a gadon ummie bata ɗakin, peck ya bata a goshi kana ya fice yana komawa room nashi. Zaune yake dafe da kansa ya ɗan jima a hakan kafin yayi kundin balar miƙewa adda'a ɗauke a bakinsa,  zare kayan dake jikinsa ya shiga yi  wannan asalin lafiyayyar chocolote skin ɗin nashi na bayyana tana ɗaukan ido, saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. Kai tsaye bathroom ya faɗa tare da sa karma kansa shower yana lumshe  idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna sanyaya jikinsa a hankali.

 Ya jima sosai  sosai  a ruwan yana wankan,  kafin ya fito ɗaure  da babban towel me ɗan kauri white har wani miski miskin blue yake, jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Hannun sa ɗaya na riƙe da wani mini  clean blue towel ɗin daban  yana  tsane jikinsa a natse. Pyjamas farare ya zira  yana kallar agogon bangon dake ɗakin nasa. Ganin se yanzu ne ma sha biyu  ke bugawa  ya sanya sake ɗaukan system nashi,  akan wata arniyar ɗunƙulalliyar kujera ya zauna  yana fesar da hucin numfashi,  

Ci gaba da  ayyukansa yayi har zuwa wajen ɗaya,  iska ya zuƙa ya kuma fesar yana jan idanunsa ya lumshe ganin ya kammala aikin nashi, Goran ruwan dake a Centre table ɗin dake gaban gadonsa ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin, yana ambatar ALHAMDULILLA a bayyane.......


 

Zaune takai  akan gefen gadonta tana  haɗe kanta da gwiwwarta ababuwa na nemar fasa kanta ,idanunta sunyi wani irin jajir ɗin kaiwa maƙura a ɓacin rai da tashin hankali, daga inda take cakuyen take  me roƙon ALLAH inama ya bata damar fashewa da gursheshen kuka. Se dai tayi duk yacce za ta yi amma ina kukan nan yaƙi iyuwa ya, tabbas se a yau take sake yarda wani kukan ma rahama ne, lallai kuma ta sake yarda da zancen nan na mutane da suke cewa idan baƙin ciki yay baƙin ciki kukan ma baya taɓa  yiwuwa, Shin me rayuwa take nufi da ita ne wai har haka?, hannunta na dafe da kanta  ta buɗe idonta, se kuma ta ware duka hannuwanta guda biyun tana me furta.....


  "YA ALLAH!, kai ne  ka ƙaddara min wannan daddaɗar jarabawar taka kuma na amsa da hannu bibbiyu, haka  kuma kai ne ka ƙaddara min duk kan  abinda zai faru dani a yau ɗina har dama gobena!. Haka kuma komai a cikin ikon ka da yardarka suke ci gaba da tafiya,  Ya ALLAH kaci gaba da zama  gatana!,  YA ALLAH a koda yaushe cikin gode maka nake akan duk abinda ka jarabceni dashi a cikin duniyar, ka kuma  bani juriya da hakurin ibadarka,  domin kuwa UBANGIJINA ka fini sanin daidai, Komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurarka, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddarar sane, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas nan dake takan iya sanjawa. Ya ALLAH ka fini sanin daidai na, ka mini maganin dukkan matsalolin da suke kewaye da wannan rayuwar tawa!, ka Zama gatan Mara gata...  Ya ALLAH na amshi wannan rayuwar data zo min a wani irin  hagunce,  Hakan da ka tsara min na gode Ya Rabb,  Tabbas wata rayuwar ba tamu ba, kamar yadda wata wata  ƙaddarar ba sakacinmu ba ne, domin kuwa ƙaddara ba canki in canka bace bare kace zaka zaɓarma kanka kalar rayuwar da kake so ba, Ya ALLAH bana da iko ko halin da hukuncin ka,  amma ka yanke min duk abinda yake ba alkhairi na bane..... Mafita ALLAH!, mafita ya ALLAH...."  Tayi maganar jikinta na wani kalan tsuma, ji tayi kamar ana fuskarta zuwa baya don haka  idanunta suka fara ganin xbibbiyu numfashinta kuma na gwamewa.... Se dai be kai ga rabuwa da gangar jikin nata ba wannan dai hayaniyar data gudonmawa na sake iskota har zuwa nan sashen nata, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un take ambata tana jin inama a yanzun ba sai anjima ta mutu tabar duniyar, wannan wanne kalan ƙalubale da jarabawa ce haka, me ta tare ma Hajiya Ana surukuwarta kuma Uwar Mijinta?, me ta mata da zafi haka, don kawai ta auri ɗan ne?, ko kuwa kawai don akan wannan ƙaddarar ta taɓa faɗa mata ne?  Ta na tsaka da wannan tunanin ne kuma burum taji an bugo mata ƙofar bedroom ɗin nata....  


"Kina ina shegiya baƙar munafuka!, to wllh na gaji da zama dake a haka, gaba ɗaya tun da kika auri Yahaya na dena gane mishi, gashi zama yayi zama ace zama har shekara na ƙoƙarin wucewa amma ace ko ɓatan wata baki taɓa yi ba, to wllh da sake, A yau ba sai yanzun ba indai ni uwace ga Alƙali Yahaya Shehu Usmanu seya sake ki Aminan...."


Jikintane ya tsananta rawa sosai fiye da farko, amma babu ɗigon hawaye ko ɗaya a ƙwayar Idonta, shigowar Alƙalin kamar wanda aka kifo ne ya saka Meenerl ɗin saurin miƙewa tana nufarsa, don gani take a cikin wannan yanayin shi kaɗai ne Garkuwa da madogararta, hannunsa ta koma cikin kamar ta fice a hayyacinta tana jan shi gaban Hajiyar tasa suka zube, "Don ALLAH Hajiya kiji tausayina, ki tausayama maraicina kiyi hakuri ki janye kalamanki akan mu, wllh ba laifi na bane, Daddy'nsu kace wa Hajiyarmu nima zan haihu, kai nake ta jira wllh a shirye nake indai zaka bani cikin!!!, Nima ina son yaran Hajiya...." Cafe zancen yayi shima ta hanyar sake furta. 


 "Hajiya dan girman ALLAH, don Annabin Rahama Annabi Sallallahu alaihi Wasallam kiyi hakuri Hajiya, don wanda akai duniya dominsa lahira dominsa, aka yi wuta don maƙiyansa, aljannah kuma don masoyansa ki gafartamana ki mana sassauci wllh ina son Jaririyata, ina jin tsananin tausayinta, wllh ban san wanda ya haɗani dake ba cikinsu, amma kamar yanda kika shariɗanta min wllh tin daga wannan ranar ban sake kusantar ƴar shila ba gata nan ki tambayeta koba haka ma Meenal?..." 


Wanda ita kuwa Meenal ɗin jin kalamansa na ƙarshe ne suka sake nemar gigita ƙwanyarta, me hakan ke nufi?, Hajiyar ce ta hana masa dena kusa tarta kenan da yayi tsayin watanni kusan har ukku kenan?, wanne laifin tama ALLAH ita kam da yake jarrabarta da ƙaddarori masu kwamanceceniya da juna?,  ita kuwa Hajiyar se wani sake huhhura hanci sama take tana wani karkada ƙafafunta. "Ta yaya kake son inci gaba da yarda dakai Yahaya?, A gabana fa yanzun gashi nan kake ƙiranta da sunaye na fitsara da rashin mutumci har da wata ƴar shilarka, dan ubanka yau she ka fara farauta ban sani ba da har kake da wata ƴar shila?, kuma ni dai iyaka sani na baka taɓa sunkuyawa da kanka ka haihu ba bare na sake tabbar da cewar kana da jaririyar, ka sani idan har kaji bakina ya sake buɗuwa da nufin kowacce kalan magana to ka sani ta tsinuwace gare ka Yahaya....."



"Hajiya don alfarmarki da Sayyiduna Muhammadun Sallallahu alaihi Wasallama kuyi.....h......."


_ALHAMDULILLAH!,ALHAMDULILLAH!!, ALHAMDULILLAH ala kulli halin🙏 🙏!!!, Anan na kawo ƙarshen book One  na  KARSHEN ƘADDARA, sai kuma ALLAH ya haɗa mu da masu rabo a BOOK TWO nashi_


_Tofa masu karatu yaya take ne?, mike shirin faruwa?..._


_Shin ya kuke ganin za a kare tsakanin Alƙali Yahaya Shehu Ɗan Batta da kuma mata da mahaifiyarsa?...._


_Ku a naku gani da tunanin wannan sakin ze iyu kuwa?, Me kuma kalaman Hajiyar suke nufi da gasken kenan itace da kanta ta dakatar dashi ci gaba da mu'amulantar matarsa?, kai wannan cajin kai dai da yawa yake...._


~A tunaninku shike nan wasan zezo ƙarshe ne?, La la la..... Yanzu ne ma zamu ɗauki wani salon shima me zafi, kuma shima kakan nashi ƙalubalen daban shima~



_Domin kuwa a gobe ma da wani labarin, Kwarai kuwa haka Nie AMMEY  LAYLERH'NKU ɗin ku naceeee...._


_Wai hausawa suka ce ɓukatar maji hajji Sallah, karfa ku manta  da hasashen Ahmad kar dai ya zame mana gaskiya jama'a, domin fa ance sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA karku manta, me bi kuwa akwai yiyuwar  wasu aure auren bayan na Alƙalin dake kanta, wanda yake daf da rugujewa shima....🤸🤸🤸🤸_  


_Amma fa kar FAN'S su ce na fiye zaƙewa nima a zaƙen nake da jin yadda zata kaya ɗin ne ai🤩_


_Tofa wata daban kuma wata sabuwa, wai ma waye wannan MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ne?, Baban AYLA kuma lawyer ɗin daya tsaye ma AMEENERH SHEHU USMAN, har se da Shari'a ta bata gaskiya....?_ 


_Wai kuwa 👍 🙂 duk kun shirya bin AMMEY LAYLERH'NKU, don warwarar wannan ƙaddarar da daku?, kun shirya ayi tafiyar daku  cikin labarin littafinta me SUNA KARSHEN ƘADDARA???_


_Hhhhh Hajiya ke dai nace bara nai shiru kar na cika masu karatu da tarin jawabai, domin kuwa tafe labarin yake da tarin gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon da ban taɓa yin irin saba na sani_ 


_HUMMM Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff  domin warware muku zare da abawar dake cakuɗe cikin wannan littafin_


_Duk zamu samu amsoshin waɗannan tarin tambayoyi namu ne  idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo ƙarshen BOOK 1 NA  ƘARSHEN ƘADDARA Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin ƘARSHEN ƘADDARA 500 Hundred ne  kacal babu yawa..._


_Ga duk mai son biya kai tsaye zai tuntuɓeni   a wannan number_


👇

08104493215


Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin


👇

8104493215

 Maryam Nasiru

 Opay


Or


3206656358

Maryam Nasiru

First Bank 


A turo shedar biya ta wannan number 


08104493215



_Masoya na amana a nuna min kauna sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na KARSHEN ƘADDARA, daga AMMEY LAYLERH'NKU me ƘAUNARKU FAKA FAKA_🤸🤸🤸_


_Byee my FAN'S sai mun sake HAƊUWA a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗin ka saida rabonka littafin ƘARSHEN ƘADDARA ba  hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo?...... To ai shikenan kawai A gimtse  ɗinnn🤸🔏 🫰✊_


_MASU TAMBAYANA JERIN SUNAYEN LITTATTAFAINA TO GASU KAMAR YACCE NA MUKU ALƘAWARI ZAN LISSAFO MUKU...._


*KAREN BANA FREE*

*JALAAL AREEF FREE*

*ƘAUNA BIYU FREE*

*MIKIYA PAID ONLY 500 HUNDRED*

*TA DABAN ONLY 500 HUNDRED*

*DUNIYARMU ME CIKE DA TARIN ƘALUBALE ONLY 1K*

*SO DAN RAYUWA ONLY 500 HUNDRED*

*RAMIN KURA ONLY 1K*

*DUHU na DUKAN duhu ONLY 1K*

*SE KUMA SHI WANNAN ƘARSHEN ƘADDARAR shima 500 HUNDRED yazo muku*


Ku sani waɗan nan litattafan suna jerin sunayen littattafan nawa ngd👏👏👏....


*BY AMMEY LAYLERH ✍️*


ᴬᴹᴹᴱʸ ᴸᴬʸᴸᴱᴿᴴ🤫😶🤐😥😢😩👌✍️🙏👩👁️🤦🙅‍♂️🙋‍♂️🙆‍♀️.......



08104493215


Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post