*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
05…“Abdulhameed!”
Gyaran murya yayi daga cikin ban ɗakin, sai ta ɗaga murya tana faɗin “I'm going to make dinner, what do you want to eat?”
Ya sake gyaran murya ta fahimci a inda yake, a ranshi yana ayyana koma menene ba za'a jira ya fito ba tunda ba'a kwana a toilet?.
“You said?” Ta sake tambaya tare da ƙara sautin muryarta, sabila da haka bayi da zaɓin da ya wuce ya bata amsa da “Rice.” yana ɗaga murya yanda zata jiyo shi.
“Kifi ko nama?” Ta tambaya cikin hausarta mai rauni.
“Nne kowanne fah!” Ya amsa a ɗan hasale.
Sauƙe numfashi yayi lokacin da yaji ta amsa da “okay” ya goga sabulu a hannun shi yana shirin kunna famfon sink ya sake jiyo muryarta tana tambayan. “Jollof or stew?”
Da sabulun a hannun shi haka ya murɗa ƙofar ban ɗakin ya buɗe ya fito. Idanun shi suka sauƙa a kanta sanye da apron riƙe da muciya da kuma ludayi a hannayenta, wato cikin shirinta take.
Ya sake mata murmushin da bata ɓata lokaci wajen maido mishi da martanin shi ba.
“Nnem” ya kirata cikin taushin murya kana ya ɗaura da “duk abinda kika bani zan ci”
Sai ta jinjina kai, cikin harshen Igbo tace “Na ɗauka baka da appetite ne saboda baka da lafiya, amma bari na yi mana stew da kifi toh”
Gyaɗa kai yayi cikin nuna amincewa, shi ya manta yayi mata ƙaryan ciwo da safe ma.
Har ta juya zata fita ya kira sunanta.
Bai tantance ba a lokacin, na niman biyan buƙatar da yake shirin gabatarwa a gareta ne, ko kuwa abinda yake ji a zuciyar shi ne yake shirin bayyana mata…
Amma da ta juya ta dube shi sai ya samu kanshi da furta “I love you”
Lokaci ɗaya fuskarta ta haska da annurin murmushin da ya taho tun daga ƙasan zuciyarta sannan ta amsa da “I love you too Nwam” tare da huro masa kiss.
Yana da tabbacin da a kusa da ita yake saidai ta janyo wuyan shi ya ranƙwafo ya daidaita da tsayinta sannan ta manna mishi sumbar a kuncinsa.
Bayan ya gabatar da sallan Isha a ɗakinshi kaman yanda ya saba baya fita yin asuba da Isha a masallaci, sai ya fita zuwa kitchen ɗinsu a inda ya sameta gaban table gas tana juya tumatirin dake zaɓalɓaka a kan wuta tana yi tana waƙoƙin yare da ɗan girgizawa.
Rayuwan da take yi a yanzu ita da ɗanta kawai yafi mata ƴanci da farinciki fiye da wanda tayi da ƴan uwanta na jini balle a sako zancen dangin mijinta, wanda take tuna rayuwar da tayi dasu kamar mummunan mafarkin da idan ta tashi ba zata bari ta sake komawa barci cikin sauƙi ba. Shiyasa duk son da take yiwa Muhammad tunda suka rabu bata sake waiwayan shi ba bayan ɗanta da taje ta ɗauko, kuma bata fatan bayan Abdulhameed a samu abinda zai sake shiga tsakaninsu har abada domin Zaman su bai yi daɗi ba sam, ƴan uwan shi ranta ne kawai basu rabata da shi ba.
“Nnem.” ya kirata cikin taushin murya.
Juyowa tayi ta dube shi, sai ya karya kai tare da kwaɓe fuska “can we talk? Please..”
Ganin damuwa shimfiɗe a kan fuskar shi ya sanya babu ɓata lokaci ta kashe wutan miyan kada ya ƙone sannan ta ruƙo hannun shi. “Menene?”
Da hannunta da ta riƙe shi, da shi yayi amfani ya janyota suka fice daga kitchen ɗin zuwa dining table ɗinsu mai kujera huɗu, yaja mata ɗaya ta zauna. Idanunta a kanshi, hannunta riƙe da nashi har shima ya samu matsuguni a gafenta sannan ya dubeta.
“Nne I don't know where to start, amma kin san a duniyar nan bani da kamar ki right?”
Jinjina kai tayi cikin tabbatarwa, tana ƙara bashi dukkan nutsuwa da hankalinta wanda bata raba da komai ba.
Ya cigaba da cewa “that's why Duk abinda nake so da abinda zan yi ba zan taɓa samun nasara a kai ba saida amincewa da kuma taimakon ki. Nne ina son waƙa, ina son nayi waƙa, ina son in shahara Nnem. Ina son a lokacin da ɗaukaka yazo mun a dubeni ace ni ɗanki ne, kuma a sanadin ki ne na zama Abinda na zama.”
Ɗan dakatawa yayi yana nazartan yanayinta, jikinta yayi sanyi kam amma babu alamun ta amshi zancen shi a kan fuskarta. Ba kuma ya zauna a nan don ya miƙe ba tare da amincewarta bane, idan yayi haka bai cika ɗa a wurin rai biyu masu masifan nacin da suka tsallake duk wasu iyaka suka rufe idanuwan su ga duk wani banbanci dake tsakanin su don kasancewa tare ba.
“Mamana.”
ɗagowa tayi ta dube shi da mamakinta ƙwalla ne ya taru a kwarmin idanun shi.
“bayan gani a hoto ban san yaya kamannin Babana yake a zahiri ba. Bai tako yazo inda muke ya duba lafiyata ba, bani tunanin ko lambar wayata yana dashi, ya manta damu saboda ya samu wasu iyalan ya cigaba da rayuwa, toh meyasa ni zai datse mun rayuwata? Me ya bashi daman jayayya da Abinda nake so bayan kece kika sha wahalar ɗawainiya dani Nnem? Kece ya kamata ace kina da wannan zaɓin, kuma ina laifi a cikin waƙa?”
Shirun da ya ratsa tsakanin su shiru ne wanda idan da Abdulhameed ya san abinda zai je ya dawo bayan shi toh da a tsakanin wannan shirun zai girgiza kan shi ne ya karkaɗe duk wani lissafi da yake ciki sannan ya dubi mahaifiyar shi ya shaida mata ya fasa shirin shi gaba ɗaya.
Ya tabbatar da burin shi ya cika ne a lokacin da ta zaro wayarta daga aljihun dogon riga ƴar kanti dake jikinta, tun kafin ta latsa layin mahaifin shi yasan cewa duk wani rikicin da za'ayi abinda yake so ya riga ya samu.
Kuma yana jin a lokacin da ta shiga jero masa kuɗurin ɗanta kaman itace daman ta tsara hakan tun farko bayan mahaifin nashi ya ɗaga kiran daga ta ɗaya ɓangaren.
Tayi shiru tana sauraron yanda yake ɗaga murya yana tada jijiyoyin wuya da tabbatuwan kafuwar shi a kan hukuncin sa.
“...Idan kuma ba haka ba, zan zo har inda kike in karɓi ɗana. Ba gazawa bane ya sanya na bar miki shi kuma ba don ina tsoron ki bane Amina Nkiru Eze.”
“I dare you Muhammad Kagarko! I dare you please!. Wallahi a kan Abdulhameed zan baka mamaki tunda ai ba tare da kai muka yi naƙudan shi ba, ni kaɗai na san zafin kayana so don't try this nonsense with me Abeg.”
Dogon tsakin da taja tana janye wayan daga kunnenta har saida ta latsa madannin katse kiran sannan yazo karshe.
Ta ɗago ta dubi Abdulhameed “promise me ba zai taɓa karatun ka ba, idan har kayi ƙoƙari sakamakon jamb, waec da neco dinka suka yi kyau ni nayi alƙawarin tsaya maka a kan abinda kake so, Saboda kai ɗana ne!”
Sai kawai ya ɗaga hannu yayi mata jinjinan ban girma kana ya fara kiɗa a kan teburin gaban shi yana mata waƙa da inyamuranci, cikin muryar shi dake kan ƙara zurfi yake mata kirari, ita kuwa ganin rawan ba zai yi mata a zaune ba sai ta miƙe tsaye tana rausayawa da faffaɗan murmushi a kan fuskarta, farin cikin ɗanta shine farin cikinta.
….
“Miƙo mun dorinan nan Filiyan”
Daman Ihsan Jira take yi saboda Taa ya tilasta musu jiranta su tafi tare gashi zata jawo musu dukan latti don haka harda ɗan haɗawa da gudunta ta koma ɗakin maama ta ciro zabgegiyar bulalan da take ratayewa a bango ta kawo.
Ilham da ta baje a kan tabarman da suka karya tana matsar ƙwalla tayi saurin tashi zaune lokacin da Maama ta karɓi bulalan.
“Kin tashi ko kuma?”
“Wallahi Maama ba zan iya takawa idan na saka safa ba”
“Sai ki saka ƙafa ɗaya tunda ɗaya ne mai ciwon”
Tana hawaye da komai suka fita daga gidan sai gashi tana haduwa da ƙawayenta ƴan hanyar su ta share hawayenta suka cigaba da hira, tafiyanta take yi normal kuma don ta manta da zancen ɗingisawa.
Maama bata tunanin ko rabin hanya sunyi lokacin da Hashimu babban ɗan goggo Fatu ya shigo gidan yana hargagi harda bulalan shi na jibgan Ilham wai tayi ma mahaifiyar shi rashin ɗa’a.
.
.
.
“kice Wallahi”
Har wani kashe idanu take yi lokacin da ta amsa da “Wallahi tallahi, kunga a jikin wancan dutsen ne ma, hala har yanzu da jini na a jiki. kuma shima ɗan shaye-shayen a…”
Maganarta ya katse lokacin da idanunta suka sauƙa a kan sigarin dake tsakanin yatsun shi biyu, yana fitar da hayaƙin da suke iya shaƙar warin shi daga inda suke.
Kamar jiya, yauma sanye yake da uniform ɗin da ba zata iya tantance na wani makaranta bane, domin bata taɓa ganin mai irin shi ba a unguwar tasu.
Idanun shi yana kan kuɗin da wani a gefen shi yake ƙirgawa, mikaƙƙun ƴan dari biyar-biyar da suka ƙara ma tsoronta tasiri lokacin da ya mayar da sigarin tsakanin leɓen shi ya karɓi kuɗin ya tusa a aljihun gaban wandon shi kana ya miƙe tsaye.
Mantawa tayi da yanda ake numfashi yayinda idanun shi suka shiga cikin nata saboda tsaban kaɗuwa. Saidai ko sakwan guda bai gifta a tsakani ba ya juya ya rataya jakar shi ya ɗauki hanyar da zai fitar dashi daga lungun, ɗayan ya mara mishi baya.
Duk tambayar da suka yi mata bayan nan basu samu wani amsa daga bakinta ba harda Ihsan mai son taji kanun labarai idan ta koma ta shaida ma Maama da ta bata aikin sakawa Ilham ɗin ido. Har suka isa gate ɗin makarantar bata sake ko tari ba, gani take yi kaman tana faɗan wani abu a kan shi dawowa zai yi ya sameta.
A ɗarare ta biyo lungun a hanyar su na dawowa saidai bayi nan, har zuwan su da dawowan su daga islamiyya bata gan shi ba don haka ta saki ranta washegari. gashi ciwon ƙafanta har ya fara warkewa ta ɗaye bandejin abunta tunda bai yi nasarar hana zuwanta makaranta kaman yanda taso ba.
A rana ta uku suna dawowa daga Islamiyya tare da ƙawayenta sai gashi nan zaune a wurinda ta saba ganinsa amma yau sanye yake da kayan gida blue din T shirt mai ratsin fari da baƙi da kuma wandon jeans.
Babu sigari a hannun shi sai waya da yake latsawa ga kwalban limca da yasha kusan rabi a gefe da laidan biscuit dake a ɓare.
Tana tafiya a tsakiyar su ne don ita take basu labarin aljanun wata da ya tashi ɗazu a gaban idonta lokacin da ake dukan latti, har mai aljanun ta cukumi wuyan ustaz ɗin dake dukan kuma itama tana cikin ƴan lattin amma hatsaniyar yasa ita da sauran ƴan baya suka tsira daga duka.
Shewa da maganar da suke yi cikin ɗaga murya ya sanya ya ɗago kanshi daga screen ɗin blackberry ɗin da yake game a ciki ya ɗaura idanun shi a kansu lokacin da Ilham take ƙoƙarin komawa ta ɗaya ɓangaren, tana amfani da jakarta dake ɗauke da Al-ƙur’ani mai girma da sauran littattafan hadisai wurin kare fuskarta amma ya rigada ya ganta.
Abinda bai tantance ba shine ma shine take ɓuya ko kuma hakan wani abun su ne na daban.
Lokacin da ya mayar da idanunsa kan wayan shi “game over” ya gani rubuce, hakan ya saka yaja tsakin da ya sanya Ilham ƙara sauri ba waiwaye kada ace biyo ta yake yi.
A washegarin ranan Abdulhameed suka yi nasaran zuwa studio suka yi recording ɗin waƙar su na farko shida Fire. ya rage saura ayi editing a naɗe musu shi a tape ya ɗauko ya kawo ma Nnem ta ji irin baiwar da Allah yayi mishi yanda zata ƙara samun ƙaimin tallafa mishi har yayi nasara a abinda ya saka a gaba.
Bayan sun gama suka dawo lungun da suka saba zama saboda yana kusa da studio ɗin, Abdulhameed ya baiwa Fire kuɗi, ya siya ma kanshi awara a wani gida a lungun shi kuma ya siyo mishi cake da 7up a shagon malam Sama'ila saboda shi bai iya cin awara ba har yau.
Suna ci suna hiran yanda abubuwa zai kasance ya fara ganin masu irin uniform ɗin islamiyyar su suna wucewa don haka ya baza idanu ko zai ganta, ko zai tabbatar da abinda ya gani jiya.
Babu daɗewa sai gata nan a tsakiyan jama'a kamar ko yaushe tana tafe tana zuba choi-choi kaman kurna.
Wannan karon da ya zuba mata idanu bai ɗauke ba har saida itama nata suka daidaita a cikin nashi. Lokaci ɗaya ta firgice ta fara ƙoƙarin ɓuya, kuma shi akwai abinda yake son tabbatar ma idanun shi don haka bai ɓata lokaci ba wurin saka yatsu biyu a tsakanin laɓɓan shi yayi fiiton da taji ƙaran shi har tsakar kanta.
“Hey!”
Ta sake jin muryar kaman na kwanaki huɗu da suka wuce. Bata san ta juya ta dube shi ba duk da zuciyarta dake mata kashedin ta gudu ko ta ɓuya. Saidai ba ita kaɗai ba, duk wa'inda suke tare ma abinda tayi shi suka yi, ciki harda ihsan kuwa.
Sai ya nuna ta da yatsa ganin sauran ma sunyi zaton hankalin su yake buƙata.
“You in the middle. What's your name?”
Ita ya tambaya amma amsar ta fito daga bakin kowa banda ita saboda yanda cikinta yake hautsinawa.
“Ilham” sauran suka bashi amsa a tare.
“Zo”
Bata taɓa sanin kalma guda ɗaya tilo yana da ikon jan linzaminta ba saida ta samu ƙafafuwanta suna kaita zuwa gare shi babu wani jayayya.
Fire ya zuba mishi idanun mamaki yayinda shi kuma yake yiwa saman haɓarta kallon ƙurilla har tazo kusa ya samu yaga abun da kyau.
Birth mark ne, abinda ake kira da tawadan Allah a hausance shine a ƙasan bakinta ta ɗan gefe kaɗan, amma ta saka wani baƙin abu ta zagaye shi ya kara turuwa da bayyana kuma kaman tasan yana yi mata kyau ne shiyasa tayi hakan da gan-gan.
“Gani” ta maimaita cikin sanyin murya, hakan yasa ya dawo da idanun shi cikin nata.
Gyara zama yayi yana gyaran murya sannan yace “ina Aliyyu?”
Ta bashi amsa da “yana gidan su baban mu a Jakara”
“Yayan ki ne shi?”
“A hankali ta gyaɗa kai”
“Idan kin je gida kice gobe ina niman shi”
Sai ta amsa da “toh”
“Jeki” ya sallameta tunda ya tabbatar da abinda yake ganin kaman idanun shi ne yake nuna mishi haka.
Ya tsaya a kan hukuncin rabin fuskar Ilham ta ƙasa yafi kyau, domin ba yarinya bace da haka kawai idan ka kalleta zaka buƙaci ƙara wani. Amma idan tana magana ko dariya ga birth mark ɗinnan da take yiwa kwalliya ba zaka so idan ka ɗaura idanunka a kanta wani abu ya sanya ko ƙyaftawa kayi ba, saboda yanda fuskar tata take rikidewa baki ɗaya.
Bata ɓata lokaci a wurin juyawa ta tafi ba kaman yanda yace. kuma hankalinta bai kwanta ba har saida ta saka kafarta a cikin gidansu.
Ƙaran keken ɗinkin da ya cika tsakar gidan shi ya sanyata dakatawa ta furzar da numfashin ta tsira sannan ta dubi matar dake kan keken tana rage tsayinta kaɗan “A fa fiyan maman baba” ta gaidata.
Idan ma shafa ta amsa gaisuwar toh bata jiba, saboda hankalinta ya tafi kan Ikram wanda ta shigo da gudu ta faɗa ɗakin maama. Ba sai an faɗa mata ba tasan zuwa zata yi ta shaida mata abinda ya faru tsakaninta da ɗan shaye-shayen nan bayan duk roƙonta da tayi har kaman zata durƙusa mata kafin su iso. Don haka ta rufa mata baya da sauri amma bata san yaya akayi bakinta ya furta sallama kafin ta shiga ba sai domin sabo da yinshi hala.
“Maama wallahi…”
“Koma kije ki gaisheta da gida mara kunya, kuma kika sake shigo mun ɗaki babu sallama sai na karya kafanki.” gargaɗin Maama da ya ceci Ilham kenan don Ihsan bata da zaɓin da ya wuce ta kame bakinta har sai tayi abinda aka ce.
“Wa’alaikumussalam” ta amsa sallamar Iham tana miƙewa tsaye daga kujeran da take zaune tana kallon draman hausa a Tv don akwai wuta.
Sai Ilham ta sake rusunawa, itama ta gaidata “ina wuni Maama nah, sannu da gida”
Ta amsa da “lafiya Alhamdulillah Fidela. Ga abincin ki a kwanon filiyan na haɗa muku saboda an kai abinci maƙwafta a naki. Idan kun cire uniform ɗinku kuma kada ku fasa watsar mun a tsakar ɗaki, bari naje na kwaso shanya Almuru ta gabato.”
da kalmar “toh” ta amsa hankalinta a kan ƙofar da Ihsan tayi sallama tana shirin sake shigowa ciki, saidai Maama bata saurareta ba tayi wucewarta hakan ya bawa Ilham daman ƙarasowa wurinta tana murmushi.
“Ƴar ƙanwata, my Filiyan ƴar kyakkyawa.” tace tana riƙo hannunta.
Ƙoƙarin ƙwace hannun tayi amma ilham taƙi sakewa “babu waninnan ai sanda tace idan baki ji gargaɗin da tayi miki ba in faɗa mata ta sanarwa Taa.”
“Wallahi tambaya na yaya Aliyyu kawai yayi kuma ai kina gani ina bashi amsa na juyo, wallahi babu ruwana dashi, ɗan shaye-shaye ne fah!”
“Toh sai idan kin yarda yau ke zaki wanke mana uniform sai ba zan bawa Maama Labari ba”
Da sauri Ilham ta amsa da “na yarda!”
“shikkenan, ki ɗauko plate ki zuba mana abinci toh.” shima ba musu ta amsa da toh tayi kaman yanda ƙanwarta da ta bawa shekaru kusan 4 tace.
````````
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
JODA by Sadi-sakhna
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
