Ragayar Dutse Page 9 Complete by Nana Haleema

RAGAYAR DUTSE.

         ©️ Nana Haleema.

Book 1

Page 009.

   A tsaye yake ya juya baya yana waya, idar da sallar asuba kenan ya dawo daga masallaci ya tsaya yana amsa waya. 

Ya sauke nunfashi ya ce, "ta faɗa min ta zo, amma bata faɗa min dalilinta na zuwan ba. Kuma ni ban ga dalilin da za a ce akwai aibu dan ta zo ba. Meye rashin dacewa dan ta zo nan ɗin?."

Ya ɗan yi shiru yana magana sannan ya ce, "babu damuwa, zan kula da komai. Amma baza ta fasa zuwa gidan nan ba, dan a nan ta girma babu abinda zai saka ace kar ta zo. Ni bazan hanata alaƙa da waɗanda ta tashi tare dashi ba, ban ga dalilin kirana da asubar nan ana yi min wata magana ba" Daga nan ya sauke wayar yana ajiyar zuciya.

Islaha da ta fito ɗaukar doguwar rigar Safeera da ta wanke mata ta ji yana waya, sai ta tsaya tana jin me yake faɗa, yana juyowa suka haɗa ido. 

Saheer ya ɗan buɗe ido ya ce, "me ki ke yi a nan?." 

Ta nuna masa kayan ta ce, "rigar Safeera ce ta jiya, shine nazo in ɗauka in goge mata kafin a ɗauke wuta." 

Ya matso kusa da ita yana kallon dogon cikakken gashinta, wanda ya sauka har gadon bayanta, gashin a cike yake sosai, ba irin na fulani da aka saba gani mara cika sosai ba. 

Saheer ya ce, "shine ki ka fito ko ɗankwali babu? Asuba ce fa Islaha."

Ta shafa gashin kanta ta ce, "ina idar da sallah na zare hijjab ɗin, sauri nake ina na goge mata shiyasa." 

Ya gyaɗa kai ya ce, "ki je ki goge." 

Har zata juya sai ta kalle sa ta ce, "Hamma da wa ka ke yin waya a wannan lokacin?." 

Ya kalle ta ya ce, "ƴan gidan ku ne, suna yi min magana akan kin je kina yin wani abu kamar mai zargi a gidan, shine suka kawo min ƙarar ki."

"Kuma su rasa lokacin kiranka sai yanzu?."

"Ni na kira su, missed call na gani." 

"da asuba?."

"A'a, tun jiya suka kira."

"To meye na faɗa maka naje ɗin?."

"Nima yadda suke yawan kirana akan zuwan ki yana bani mamaki. Kamar ba gidanku ba, meyasa basa so ki je?."

"Ka san da yawan yaran da ake adopting ba a cika bari suna mu'amala da inda suka baro ba. Maybe shiyasa suke yin haka."

"Laifi ne hakan?."

"Oho musu."

Ya girgiza kai ya ce, "jeki ki gama abinda zaki yi, in za ki tafi aiki sai mu yi magana da ke." 


Ta girgiza kai ta juya ta nufi ciki ya bita da kallo. Godon gashinta yake bi da kallo, ganinsa har ƙugunta a kwance, gashi baƙi mai ɗaukar hankali.  Kuma bata wasa da gyaran gashi, shiyasa ko yake a kwance da ɗaukar hankali. Ya sauke numfashi ya shiga ɓangarensa.


Tana shiga ɗaki ta ajjiye rigar hannunta tana tunani, ta ɗan yi shiru tana tuna abinda ta ji yana cewa, ta ɗan ɗaga kai kaɗan ta ce, "Ni ban san meyasa suke faɗawa Hamma in na je ba, ana yiwa mutum iyaka da gidansu ne?" ta faɗa tana shinfiɗa doguwar rigar ta goge mata ita tasss. 


Ta miƙe ta saka hula ta fito kitchen ta ɗora abinda za a karya, bayan ta gama ta koma ta yi wanka ta shirya tafiya aiki.


Lokacin da ta fito falon da Baffa suka haɗu, ta gaishe shi ya amsa sannan ta ce, "Baffa na gama abinci, na dama maka kunun da ka ke so." 


Ya yi murmushi ya ce, "Allah ya yi albarka Islaha." 


Ta amsa da amin ya ce, "ki cigaba da riƙe maraicinki, kar ki aikata wani abun mara kyau, ki cigaba da riƙo da addini, za ki ga amfanin hakan yanzu ko nan gaba. Ta ɗaga kai ta ce, "in sha Allah zan yi Baffa." Ya yi murmushi ya fita, yana jin alfahari da ita fiye da ƴaƴansa.


Yana fita Mama ta fito tana waya, Islaha ta bari ta gama ta sake gaisheta duk da sun gaisa da asuba. Ta amsa tana binta da kallon ɗai ɗai, tana yi mata kallon sama da ƙasa.


A lokacin aka yi sallama aka shigo, Islaha ta kalli wacce ta shigo gabanta ya faɗi ganin aminiyar Mama. Itama bata ƙaunarta kamar ƙawarta, da wahala ta zo gidan bata haɗa su da Mama ba, shiyasa bata so ta ganta kwata-kwata. 


Islaha ta duƙusa ta gaishe ta, ta amsa mata mata sama-sama. Hajiya Karima ta kalli Mama ta ce, "ashe wannan ragowar marayun tana nan har yanzu?."


Da sauri Islaha ta bar wajan ta shiga kitchen dan yanzu zasu fara ci mata mutunci kala-kala. 


Kasa shan kunun ta yi, duk da sha'awarsa da take ji amma sai ta kasa, ta fito daga kitchen ɗin ta ce, "Mama zan ta fi aiki, na gama komai yana kitchen." 


Mama ta ce, "to ya yi." 


Ishala da hanzari ta shiga ɗaki ta ɗauki abinda zata ɗauka, har lokacin ƴaƴan gidan bacci suke yi, ta fito ta nufi gidansu Safera.


Tana fita ƙawar Mama Karima ta ce, "Zulai kina bani mamaki wallahi, har yanzu kin kasa maganin yarinyar nan?." 


Mama ta ce, "To ya zan yi mata Karima? Saheer sonta yake yi kamar ya busa mata rai, alfarmarsa take ci take zaune a gidan nan har yanzu." 


Karima ta ce, "za ki bari ya aure ta ɗin ne?."


Mama ta ce, "wannan bazai yu ba wallahi, babu abinda zai saka na bari ɗan da nake ji dashi ya auri wannan yarinyar." 


Karima ta ce, "dah ki ka ce kin amince, saboda a hannunki ta ke."


"Ina jin tsoron sirikan zamani shiyasa nake so ya aure ta wani lokacin, dan ita bata isa ta kawo min iskaci ba, daidai nake da ita. Ta sanni na santaa, ta san me zan yi da wanda bazan yi ba. Dan wallahi ko gida bazan bari ya canja mata ba, a gidan nan zasu zauna, yadda duk abinda za a yi a kan idona za a yi. Bazai yu na haifi yaro shekara da shekaru wata ta zo ta fini morarsa ba."


Karima ta ce, "ta wani fannin hakan yana da amfani, amma idanun yarinyar nan a buɗe yake wallahi, babu kalar iskanci da bata gani ba. Amma tunda ya ji ya gani sai mu ƙyalesu, ko babu komai amfanin mu ne."


"Ina faɗa miki, shekaran jiya iskanci ta zo min dashi, bata san nasan labarinta kaf tun na gidan marayu har na wajan aiki. Wai kuɗin da ake bani duk sati, ni zata kalla ta ce mata da kuɗi...." 


Kafin Mama ta kai ƙarshe ta katse ta ta ce, "Amma kin yi maganin ƴar iska? Bayan mun san asalin ungulu, wannan yarinyar meye bata samu a wajan maza?."


"Kin san tana da wani ciwo kamar asthama, bata san sanyi da ƙura da zafi. Kin san shekaran jiya anyi sanyi sosai, na tura ta waje nace ta je sai na nema ta. Kin san wanne bariki ta yi min?." 


Karima ta ce, "Sai kin faɗa."


"Ɗakin Saheer ta je ta kwana." 


Karima ta zaro ido  ta ce, "Saheer ɗin ta saka a ɗaki suka kwana tare? Amma da safe kin duba shi ko? Dan na tabbatar ta lalala mana shi."


Mama ta ce, "bari kawai, kuma wai ina magana yarinyar tana magana. Har da cewa Hanan ba da ita take magana ba ta daina saka mata baki, shi kuma yazo, yana cewa wai wallahi ba a gidan nan ya kwana ba fita ya yi. Ƙarfe bakwai yarinyar nan ta tashi ta fita sai dare ta dawo. Wani lokacin shiyasa zancen auren nan yake fita daga raina, bana son sirikar da zata yi sa'insa dani."


Karima ta ce, "ubanta zamu ci, wallahi bata isa ta auri Saheer ta ce zata mallake sa ba. Ita ɗin banza, a hanun mu take, me biye mata ma mahaifin Saheer ɗin a hannun mu yake balle ita. Ki kwantar da hankalin ki, baza ta auresa ba, ni so nake mu ƙaru da ita."


Mama ta ce, "kamar ya kenan."


"Aikatau mana, mu turata wata ƙasar ta je tana kawo mana kuɗi. Yarinyar nan tana da kyau, irin fatarta larabawa suke so. Gashi tana jin turanci, babu inda baza ta yi aiki ba."


Mama ta yi dariya ta ce, "ba ki fi ni son hakan ba, amma duk inda ki ke tunanin wannan shaɗaniyar yarinyar ta wuce haka, tsaf zata saka camera ta yaɗa mu a labarai."


"Duk da haka dole mu san hanyar da zamu bi. Gida aka samu a Jedda, matar tana neman ƴar aiki ido rufe. Tana neman ƴar aiki kamar zubin Islaha, mai jin turanci kuma mai ilimi. Kin san nawa zasu bayar albashi?."


"Sai kin faɗa."


"riyar dubu da ɗari biyar zasu bayar duk wata."


Mama ta buɗe ido cike da mamaki jin kuɗin ta ce, "kusan dubu ɗari shida fa kenan a naira...." 


Karima ta ce, "cass kuwa, ban da alkhairin larabawa." 


Mama ta girgiza kai ta ce, "tashin hankali, ga bikin zuwa babu zanin ɗauwara."



"Akwai zani fa, akwai zani mai kyau gata nan ta fita. Meye amfaninta da zama mu turata ba? Yanzu ko rabi muka raba kuɗin, muka ɗauki rabi muka bata rabi bamu ci riba ba? Kawai tana zaune damu bamu san kowa nata ba, ba dangin uwa babu na uba, sai dai mu ciyar da ƙatuwar budurwa dan kawai zata auri ɗanmu? Ya kamata mu sake nazari da tunani wallahi."


Mama ta ce, "baki san Islaha ba, shegiyar kanta ce, bata da kunya. Wallahi baza ta amince ba, Saheer ma bazai taɓa bari ba." 


Karima ta ce, "Haka zamu zuba ido kenan? Haka zamu bari wannan abin alkhairin ya wuce mu Zulai? Riyar dubu ɗaya da ɗari biyar fa, kuma in mu ka matsa tsaf zasu cike riyal dubu biyu."


Mama ta gyara zsm jin ruwan kuɗi ta ce, "kin san maƙociyata Maimuna? Babar Safeera ƙawar Islaha?."


"Na santa."


"Mun yi magana da ita tana son zuwa ita da kanta, me zai saka baza mu ɗora ta ba?." 



Ta girgiza kai ta ce, "ta yi girma da yawa, ƴan mata take so, kuma wacce take jin turanci. Mu tura Maimuna mu ce mun turawa don Allah?. Kin san larabawan nan basa son manya, kuma Maimuna ko larabci bata ji, gidajen aikin nan sun fi son mai jin larabci. In tana son akwai na riyal ɗari bakwai, sai mu tura ta. Wannan gidan da Islaha ya dace wallahi. Kawai ki shiga ki fita a samu ta je."


Mama ta yi shiru tana tunanin mafita, ta kalli Karima ta ce, "baza ta yarda ba wallahi, Saheer ma bazai taɓa amincewa ba." 


Ta gyaɗa kai ta ce, "shikenan ai, sai mu kai bare muna ji muna gani arzuƙi ya tsallake mu. In kuwa itace ba sai abinda muka ga dama zamu bata ba? Sai abinda muka yi niya zamu manna mata mu riƙe sauran."


Mama ta yi shiru ta ce, "Zan san abinda zan yi akan hakan, amma ba abu ne wanda zai yu ba gaskiya, na san halin Saheer, na san halin Islaha, duk baza su amince ba."


Labiba da ta fito tana jinsu ta ce, "To gani, a tura ni mana." 


Duk suka juya suna kallon ta, Mama ga ja dogon tsaki ta ce, "baki da hankali ai, ke zan tura aikatau ɗin?." 


Labiba ta ce, "da arzuƙi a gidan wasu gwara a gidan ku, ni ba sai in je na samo ba." 


Mama ta kalli Karima suka tafa, Karima ta ce, "ku cigaba da zama a nigeria, kuna yin ƴan dabaru kuna kawo mana kuɗi, amma zuwa wata ƙasa ba na ku bane. Ita dai da take ba jinin mu ba ta je, amma ku kam kuna gida, sai aure ne zai raba mu."


Labiba ta ce, "meyasa? Ni ina so in je ba, sai a kaini ba?." 


Mama ta ce, "babu inda za ki je, tafiyar nan da Islaha ta dace, kuma da ita za a yi. Ɗaya gidan kuma zan yiwa babar Safeera magana in tana so." 


Labiba ta ce, "Mama da gaske ina son zuwa, in na je sai na fi sakin hannu, ina na turo da kuɗi akan Islaha, ni ta ku ce, ita kuma ba ta ku bace. Ku yi tunani."


Bayan barin Labiba wajan Karima ta kalli Mama ta ce, "kuma fa abinda ta faɗa haka ne Zulai, Labiba tana da wayo, tsaf zata iya tara mana abinda mu ke da buƙata." 


Mama ta bita da kallo ta ce, "ke kin san Baffa bazai yarda ba, nima kuma bana son tura su, saboda yawancin masu tarbiyya in suka je suna komawa fanko ne."


"Ki bar batun mahaifinta, indai zata je ɗin ba komai bane, zamu iya maganinsa. Batun tarbiyya kuma mun yarda da wacce mu ka bawa ƴarmu, baza ta watsar da ita ba. Mu turata kuma mu bita da addu'a. Ni ba dan yaran sun yi aure ba da mai zai hana ban tura ɗaya ba? Mahaifin nan nasu ba wata tsiyar yake yi musu ba, in suka je ko kuɗin aurensu suka tara basu rage mana wahala ba?."


Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne wannan, amma nafi buƙatar zuwan Islaha akan zuwan Labiba gaskiya."


"Sai mu haɗa su duka biyun su tafi. Amma yadda ki ka gani fa, ban ce dole hakan za a yi ba. In kina ganin zaki amince sai ayi, in baza ki amimce ba sai a bar sa." 


Mmaa ta gyaɗa kai ta ce, "Zan yi tunani a kan hakan, amma kafin nan wannan gidan Islaha ce zata je aiki cikinsa. Shi kuma ɗaya gidan zan yiwa Maimuna magana, in zata je a shirya mata komai ta ɗaga."


Karima ta ce, "Ya dai kamata, ayi a tura musu kin san basa son ɓatan lokaci. Daman shi gidan ba su ce ga wacce suke so ba, kin ga babar Safeeran zata iya tafiya." 


Mama ta ce, "zan yi mata magana, na tabbatar zata je." Suka cigaba da hirar yadda abin zai kasance.


      Islaha da ta fita gidan su Safeera ta shiga da sallama, fitowar Umma tsakar gida kenan ta zare sakata Islaha ta shigo. 


Ta amsa tana binta da kallo, Islaha ta duƙa ta gaishe ta. Umma ta ce, "lafiya haka da sassafiya?." 


Islaha ta ce, "wajan Safeera nazo Umma."


"wajan Safeera da safe haka kamar kina binta bashi?." 


Islaha ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba. Ummansu Safeera ce, baza ta iya yi mata komai ba. 


A lokacin Safeera ta leƙo ta ce, "Bestie shigo mana." Islaha ta kalli Umma, kafin ta miƙe ta shiga jiki a sanyaye. 


Safeera ta ce, "Ki yi haƙuri da abinda Umma take yi miki, wallahi Mama ce take zugata." 


Islaha ta murmusa ta ce, "ke kar ki damu, Umma ai uwata ce. Ga rigarki ta jiya, undies kuma na riƙe bazan bayar ba."


Safeera ta karɓa tana dariya ta ce, "daman kin riga kin buɗa min ya za a yi ki dawo min dasu? Ya na gan ki da safe haka?." 


"Bari kawai, gidan ne gabaɗaya ya fita daga raina. Ƙawar Mama ce tazo, wannan Kariman mai zubin ƴan bariki. Yanzu in suka saka faifan zagina sai na yi hawaye, shiyasa na baro gidan kawai."


Safeera ta ce, "Shegiya, na tsani wanan matar wallahi." 


Islaha ta ce, "ki ka tsane ta ko na tsane ta?." 


Safeers ta ce, "Jiya Saleem ya ce min kin je gidan ku, shine baki faɗa min mun je tare ba?."


"Wallahi kawai na ji ina son zuwa ne shiyasa kawai na tafi. Kuma na je duk basa nan wallahi, Hafsa da Zeey kawai na samu."


Safeera ta ce, "ina suka tafi?." 


Ta ɗan gyaɗa kai ta ce, "akan wannan case ɗin da na muka yi magana dake, ni jikina yana bani hakan ne gaskiya." 


Safeera ta ce, "hakan zai iya faruwa fa Bestie, komai na duniyar nan yanzu ya ɓaci wallahi, abinda baka yi zaton zai zama gaskiya ba sai ya zama, abubuwa sai a hankali."


"Hmmm! In na tabbatar da maganar nan gaskiya ce zan yi ɓarna Betie, babu wanda zan bari ya sha wallahi. Sai na saka gwamnati a maganar nan wallahi."


"Da gaskiyar ki wallahi, in dai hakan ya kasance zai iya faruwa kar ki bar maganar, ina bayan ki."


Sai kuma ta ce, "Ya maganar Mr Rehaan? Ya dawo ƙasar kuwa?." 


Ta girgiza kai ta ce, "bai dawo ba, amma ana tunanin gobe zai dawo." 


Ta girgiza kai ta ce, "Allah ya dawo dashi lafiya. Bara in je na kawo mana abinci mu ci sai mu wuce. Jiya na bar aiki da yawa, gwara na je da wuri na ƙarasa" daga haka ta fita daga ɗakin Islaha ta yi ajiyar zuciya, ta ɗauko waya tana dubawa ganin saƙon Hafsa..


_Book 1 free ne, Book 2&3 paid ne akan naira 1k kacal. Pay into Sadiya Nuhu Mukaddas 5903999117 Moniepoint MFB. A tura shaidar biya a wannan number 09030398006 ko 0701 809 8175._

Nana Haleema✍🏻❤️

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post