༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
Unexpected and Surprising 🔥💥
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
Page 5&6
♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ Shigowan Ya Sadeeq ne ya cilasta mata tashi zaune, tana sake goge idananunta, tambayar ta yayi ko wani abu ne aka nata, se ta ce A ahhh don Shareefah bata nan tana Islamiyya, shi yasa ta kwanciya se kuma ta tashi da ciwon kai, dake duk wanda yake tare da ita yasan hakan, yasa sau da tari idan ire-iren waɗannan ababuwan suka faru take ɓuya a bayan hakan, Sosai ya fuskanceta yace. "Wato ke babu me faɗa miki ki yarda ko Meenal?, waɗan nan sabbin ababuwan kenan da kika zaɓarma kanki kuma ko?, ki sani ita kanta shiga ta mutumci kima da daraja take ƙarama mutum a idon duniya, amma in dai burinka ka burge mutanen to ki sani bawai zaki taɓa burgesu bane, se dai ƴan uwanka dabbobi, kuma ko babu komai ai kin kare daraja da kuma martabar auren Ahmad dake kanki, ke yanzun baki kai munzilin da zaki zauna kima kanki da kanki faɗan ta nutsu ba?, to ki sani wllh³ duk sanda Ahmad ya sake samuna da magana me irin haka sena sassaɓa miki wllh, idan kika yi woni abun yanda kika san goyon jakai haka kike, shin ina addi da karatu da nutsuwarki suke je?,ina Sanin yakamanta yake?, ina wannan kunya da kamun kan naki suke?, ina hasalin wannan AMEENEERH SHEHU USMAN ɗin take? Wannan me kunyar, me kare mutumci da martaba da kimar jikinta?, Ko kuwa kina manta cewar...
_A hijab is a traditional head covering, usually a scarf, worn by many Muslim women to cover the hair, neck, and sometimes chest in accordance with Islamic principles of modesty. Derived from the Arabic word hajaba ("to conceal"), it serves as a sign of faith, piety, and privacy. While often worn voluntarily, it is legally mandated in some places and restricted in others?....... kina manta cewar The Muslim hijab is a head covering worn by many Muslim women as an expression of modesty, faith, and identity, typically covering the hair, neck, and shoulders while leaving the face visible. It serves as a, voluntary or, for some, involuntary, daily practice derived from Quranic principles of modesty ne Meenal?....Ko kuwa shima kina mancewane da cewar Shi Hijjabinki mutumcinkine? Ki sani kalmar *HIJJABINKI MUTUMCINKI* wata magana ce ta hikima a harshen Hausa da ke nuna cewa sanya hijabi ba kawai umarni na addini ba ne, yana ɗaya daga cikin ginshiƙan mutunci, daraja, da kamun kai na ko wacce mace musulma. Ta inda har wasu fassarori na wannan jigon saka hijab ALLAH ya bamu kamar... Kariya da Daraja, Hijabi yana kare mutuncin mace da kiyaye ta daga kallon banza, wanda hakan ke ƙara mata daraja a idon al'umma da kuma duniya. Ita kuma kanta alamar Kunya, Yana nuna mana cewar mace tana da kunya da kuma kiyaye dokokin ALLAH ne. Kana kamun kai!, Sanya shi yana nuna cewa mace ta girmama kanta, don haka wasu ma za su girmama ta inji Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, sannan Mutunci!!!. Mutuncin mace yana tattare da yadda take suturce jikinta da kuma ɗabi'unta ne inji ALLAH (S.W.T.) A takaice, ma'anar ita ce: *Hijabinki shi ne mutuncinki da darajarki* shi ne ke kuma kike son ɓarar da naki mutumcin ameenatou?, kike son kamar kinyi jayayya ne da hukuncin Alqur'ani da hadisi ne tabbatacce tun daga Rabbil Izzati?, Ki gyara don ALLAH ki gane ameenatou idan kuma saɓanin hakan ya kasance to kiyi kuka da kanki baga kowa ba, ki kare haƙƙin ALLAH da auren dake kanki se ALLAH ya kare ki da kariyarsa shi ma...." Tun da ya fara mata Maganar zuciyarta ke wani kalan tafasa da ƙuna, wato ashe dama shi yasa Ahmad ya dage se ya kawo ta gidan da kansa?, ashe dama don ya haɗa ta yayan ta ne?, aikuwa wllh ze san ita yama haka, wllh seya gane kuskuren daya tabka na haɗata da yayan nata, fita kuma da duk shigar data ga dama yanzun ta fara. Ko kafin ya dawo tuni har ta hau napep ta tafi, ba tare data tsaya tayi sallama da kowa dake gidan ba, kai tsaye asibiti ta wuce se wajajen taran dare kana ta koma gidan, duk kuwa wunin ranar daya jima yana mata a waya, amma ko sau ɗaya bata ɗaga ba, domin taga idan ta tsaya wasa se Ahmad ya kaita ƙasa warwas. Ita kuwa ta rantse daya kaita ƙasa kara tayi duk me iyuwa ta nuna masa cewar ɗin *Kainuwace dashen ALLAH* bana *Mutum ba*, koda ta dawo lokacin yana parlour amma haka ta tsallake shi ta wuce ɓangarenta, tana kuma shiga ta kulle ta yadda bema isa shigowa inda take ba. Washe gari koda ta tashi iyaka cikinta ta dafa abinci, nan ma be tanka taba, ya rabu da ita, don yaga yau ba shirin fitar ma tattare da ita duk da kasancewar Monday ce, don riga da wando ne a jikinta trouser se vail da tayi Rolling dashi, ga wani eye glasses data maka a ido, ci kanka bata ce dashi ba kamar yacce shima be ce mata ba, amma ga mamakinsa se yaga ta fito ɗauke da handbang nata da wayarta, sokoko ya tsaya kallonta don ganin yau kuma da abinda ta fito, ganin dai tabbas da gasken gaske fitar ne zatayi ya saka shi saurin shan gabanta, yana me furta. "Meenal ina zakije da wannan shigar dake jikinki?...." Cak ta dakata tana me furta. "Wurin aikina mana ko kana da matsala da hakan ne?, ko kuwa yau ɗin ma gidan zaka je ka sake haɗa ni da yayana???..." Tayi maganar ranta ɓace zuciyarta na sake fusatuwa sosai akan abinda ya matan. Numfasawa yayi ya ce....
★..
"Ke yanzun saboda nace ki ringa suturta jikinki shi ne kikace bara ki nuna min ƙarshe na kenan ko?, to shikenan Meenal kiyi duk abinda kikaga ya dace da rayuwarki, nikam na gama nawa na kuma fita haƙƙin ki,kije rayuwarki ce, kiyu duk yacce kikaga dama da ita fine. Tun da hakan kika zaɓarma kanki rashin daraja da kimarki....." Aikuwa dama kamar jiransa take tace. "Nayi na kuma zaɓa hakan Ahmad!!!, na ji na kuma gani wannan ɗin rayuwar tawace ba ta wani ba, don haka a barni inyi duk yacce naga damar yi da ita, kai a jakin tunaninka don kaje ka haɗani da yayana shikenan ka gama ne?, to ka sani fita da duk kayan dana ga dama wannan rayuwata ce, kuna yanzun na fara..." Da kallo na hasalin mamaki al' ajabi yake kallarta kafin ya sama zarrar cewa... "Kiji tsoron ALLAH ameenatou!, AMEENERH kiji tsoron haɗuwarki da Ubangiji ya zata kasance?, ki guji haɗuwarki da UBANGIJINKI wllh... Nie dai ALLAH ya gani nayi iya yin da nai, amma abin ya gagara kin kasa sanjawa har yanzun...."
Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu tace. "Kaga dakata Ahmad!, wai Don ALLAH wannan mummunar alkaba'in da kake ta yi a kaina kana tunanin kai uwata ne ko kuwa ubana?, nace da zai kamani koya bani tsoro?......" Ɗan ja da baya yayi don se ya kalla wannan ɗin kamar ma Meenoh ɗin sa bace? Yana me furta. "Subhanallahi ameenatou Ni ina matsayin mijinki shi ne kike gaya min wannan maganar???" Wani mugun tsuka taja tana fisge car key na motar dake hannunsa ta yi compound na gidan nasu, ja da baya da baya ya fara yana dafe kansa yana rasa kalmar daya kamaci ace ya fara ambata a matsayin wacce zata bashi nutsuwar da yake nema kai tsaye... A lokacin da take barinsa nan da mutuwar tsayen da yayi ita tuni har tama motar key dake dama ta iya tayi reverse tama bar gidan baki ɗaya, cikin wannan dai shigar da bai dace ba samm ace matar Aure ne ta fita dashi, kai ko budurwarma indai tasan daraja da kuma kima da mutumcin kanta ba zata fita da shigan ba. Tana ɗaukar titin ta saki waƙar *SOJA BOY* Ta _ƘAUNA NA BAKI_ . Yacce kukasan itane tayi wakar haka take binta har wani rausaya da sakin kan motar take. Idan wakar ta ƙare ta sake dawo da ita on repeat. Tayi nisa sosai motar ya tsaya cak, taki gaba da kuma ki baya, don haka dolen dole bata da yacce zata yi dole ta saka ƙiran numbern sa, sedai baya ɗagawa saboda baya ma kusa da wayar ne, ga wani ƙara da motar ta ɗauka yi taje ɗuuuu ɗuuuu ɗuuuuu. Dole ta fito ga wayar da Dr pooja ke famar mata akan cewar tayi maza ta ƙaraso wata tiyata ce ta sauri zata shiga. Gaba ɗaya ta rasa yacce zata yi don haka ta saka ƙiran Dr pooja ɗin tace mata wllh motar tane ta sama matsala, amma INSHA ALLAHU tana gaf, tana nan tsaye kamar anyi tofin ala tsine a wurin babu motar data wulga, can sega wata mota nan ta ɓullo kiɗa se famar tashi yake a cikin motar kan gari, irin ta arnan nan. Har motar ta wuce ta ɗan yo baya kaɗan tana dawowa da baya daya har inda take tsayen, mutane huɗun dake cikin motar duk suka firfito suna tambayar "Ƴan mata lafiya kuwa?, kamar temako kike nema ko?" Ɗaya daga cikin su ya tambayeta, wayarta dake hannunta da car key na motar ta ɗan gyara riƙon su tana me furta. "Ehh motar ce ta ɗan sama matsala wllh..."
"Ok to mu gani ko zamu iya temaka miki mana..." Wannan na farkon again ya sake faɗi, gaba tayi tana buɗe musu gabar motar su kuma suna isowa suka fara kamar alamar dudduba mata. Kafin cikin su wani yayi hanzarin fakarta ya shaƙo wuyanta, wani kuma ya riƙe hannayenta suna kaita ƙasa. Ihu ta saki tana me furta..."INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN ³ ku cika ni mana me zaku min, kuji tsoron ALLAH Matar aure ce ni,wllh nie Matar aure ce ku rufa min asiri ku ƙyaleni....." Haka take faɗi sedai babu me jinta, se ALLAH'n data riga ta take dokoki da ƙa'idojinsa. Don haka se ya barta da iyawarta ya gani ko zata iya yaƙar kanta daga miyagun mazan da dama kamar tana tallata jikin nata wa su ne. Firkici da tsoron abinda taga suna shirin aikata mata ne ya sumar da ita.....
Yana zaune duk a parlourn ya gaza tabuka komai, ko ta kan ƙiranta be bi ba duk da cewar yaga miss call nata wajen uku, amma se bi ba, ga zuciyarsa dake bugawa time to time da tsananin karfi. Yana nan a zaunen wayar ya sake shigo masa, lokacin ma an ɗan ja lokaci sosai akan baya, don haka ya rarrashi zuciyarsa ya ɗaga din tana daga zaunen, sedai jin muryan wani da daban saɓanin Meenal ɗin ne ya saka shi furta "Lafiya kuwa?" Daga ta can ɓangaren aka ce "Kai ne Mijin me wannan wayar ne?" Cike da tsantsan tashin hankali ya ke cewa... "Ehhh ni ne wllh ni ne wani abu ya faru da ita ne?, accident ta samu ne....?" Daga ta can aka sake ce dashi dama mun kwaci matar kane hannun wasa yara a gefen titi sunyi mata fyaiɗe...... Yanzun haka tana kwance a asibitin da take aiki...." Wani kalan zabura yayi yana ja da baya ya miƙe ya na cewa.... "Eyeeee Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ fyaiɗe???...." Kafin ɗif ɗif ya datse ƙirar wata juwa da jiri na kwasar shi da Hajijiya....
*Around 4:20 Pm*
Ahankali slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta da dawowa cikin sense nata, ga wani nauyin da taji kanta da idanunta nayi na bala'i, gaza ƙarasa buɗe idanun nata tayi, sakamakon ahankali ahankalin da ababuwa suka soma yowa zeroying brain nata. Highlighting abinda ya faru da ita ta shiga yi tana ƙiran _Hasbinallu wani'imal wakeel_ adai cikin zuciyar nata taci ga da cewa _ba gaskiya bane wannan mafarkine baze taɓa yiwuwa ba na sani?, tabbas ba gaskiya bane hakan bazai taɓa faruwa dani ba...., Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Kalaman da take ta famar nanatawa kenan da muryarta wacce ke rawa ba kuma ta fita sosai, wanda ya saka hankalin Shareefah dawowa gare ta dake zaune se famar ɗauke kwalla take, don ita kaɗai ce a wurinta, Yaya Sadeeq yace babu ruwansa da duk abinda ya faru da ita. Ganin yacce take ne ya saka ta saurin miƙewa ta nufa fita don ƙirar Dr pooja da tace data farka ta ƙirata, se dai suna shigowa bata ko numfashi alamun ta sake somewar kenan, don haka kai tsaye wasu nurses ta kira suna turata a gadonmarassa lafiya....Direct emergency room aka wuce da ita domin abin nata na nemar fin ƙarfin tunaninsu suma, daga ta farfaɗo seta kuma suma tun kafin wani lokaci.
After 20mn.
Gaba ɗaya hankalin Shareefah ya sake tashi tun da aka shiga da Yayar tata take ta famar safa da marwa a bakin ƙofar emergency room ɗin, daga can gefe kuma Ya Ahmad ɗin ne da shi ɗin ma yake tsayen ya gaza tafiya, sedai baya kusantar inda take amma kuma ya gaza tafiya ya barta. Inda kowannensu da irin abunda yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.saidai banda ita da tunani da kuma nutsuwar zuciyarta suka kau, don sun jima da barin jikinta suna tafiya wani wuri na daban, wanda take cike da tarin fargaba acikin ranta dangane da makomar auren yayar nata, wanda indai zata tuna hakan ne ke sanadiyyar saka hawayen dake cikin idanunta kasa tsayuwa.
Around 6:30 pm.
Har zuwa wannan lokaci suna tsaye bakin emagency room ɗin, sunƙi matsawa ko ina bayan sallarn da shi yaje masallaci yayi ita kuma tayi anan dandanin wurin. Haka kuma har zuwa wannan lokacin doctors ɗin dake cikin emergency room ɗin, suma basu fito ba suna can suna kokarin saita tunani da natsuwarta da se sun samu kamar zata dawo daidai seta sake birkice musu,
duk yanda suka so control matsalan amma abun yaci tura, Ganin abun na ƙoƙarin fin ƙarfinsu ne kuma ya saka su yanke hukuncin wucewa ita ICU kaitsaye, saboda acanne zata fi samar kulawa fiye da nan ɗin ma, gashi daɗi da ƙari ko babu komai yau Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ na cikin asibitin, wanda a da ita ce wacce zata yi aikin, rashin ta ya saka dolen dole Dr pooja ma Dr Bilal waya ta sanar duk abinda ake ciki, shi kuma baya gari lokacin yaje wata interview ta manyan Dactor's, don haka kai tsaye ya ƙira gida ya sanarma Abban MAJEED ɗin ana son ganinsa maza maza a cikin asibitin, wanda kai tsaye yasan in ba hakan ya masa ba bazai taɓa zuwa ta sauƙi ba, kuma har lokacin yana cikin ICU ɗin.
Acan ɓangaren Shareefah kuwa har zuwa lokacin tana wajen emergency room ɗin a zaune tayi jigum ta manna
kanta da jikin bangon ginin, daga ta can kasar raunatacciyar zuciyarta kuwa sunayen ALLAH kawai take ta famar ambatowa, cike da saka duk wani fata da kuma burin ta akan Yayar nata,
Kan zuwa yanzun kuwa kan kuma zuwa lokacin da abin ya faru ta zubar da hawaye masu yawan gasken da basa da adadi, har saida cikin idanunta sukayi jajur suna mata wata kalan zogi da kuma zafi, fyaiɗe ba?, fyaiɗen ma wa Matar aure?, shin tayaya mutane zasu ringa tunanin duniyarmu zata zauna ƙalau, alhalin kuma ɓarna a ban ƙasa tayi yawar da bata da adadi ko iyaka?...... Tana nan zaune har bata san iyaka adadin da ta sake ɗauke ba taji kamar motsin buɗe kofa, wanda ya saka ta ɗagowa hakanan taji zuciyarta na bugawa, wannan dalilin yasa ta tsurama ƙofar fitowan rinannun idanuwanta, wanda kai tsaye ganinta na sauƙa akan *Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ*, dake ta famar wani kalan bala'i yana yima Dr pooja tsawa ran nan a matuƙar ɓace, fuskarnan da dama take ɓaka ta sake rinewa, amma fa bawai baƙi irin na muni ba, irin na hasalin masu jin daɗi da kuma kwanciyar hankalin da suka gama ratsawa, haka ya wuce wanda ya saka Dr pooja ɗin jan burki a gaban Shareefah ɗin. Tana me ƙoƙarin zare handgloves ɗin dake hannunta... "Dr yaya jikinta ?, ta farfaɗo?bata dai sake somewar ba ko???" Haka Shareefah'n keta famar jeroma Dr ɗin tambaya, cike da fargaban kada agaya mata cewar har yanzun bata a daidai nata bata cikin sense nata. Ajiyar zuciya me ɗan zurfi Dr pooja ɗin ta sauƙe, kana cikin son kwantar mata da hankali tace....
"Jikinta yayi worst sosai ne, wanda firgicin abinda aka mata ne ya sakata sumewar da tayi, har hakan ke ƙoƙarin taɓa brain nata amma In sha ALLAHU zata sama sauƙi da izinin Ubangiji....
Ta kai ƙarshen maganan tana me kallon Shareefah'n dake ɗibar kamanni sosai da Meenal da ta tsare ta da idanunta sosai tana kallonta, dukansu shiru sukayi gaba ɗayansu, yayin da itama gefen Dr pooja ɗin tsananin tausayi da ƙaunarta ke mugun kamata.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake gangaroma Shareefah'n daga cikin idanunta, zuwa kan ƙuncinta, cike da raunanta haɗi da rashin ƙwarin zuciya ta koma ta sake jingina jikinta da bango... Rashin Ammeynsu na dawo mata sabo fil, ta tabbata da ace tana raye da tuni tana nan rungume da kan Meenal ɗin suna raba ciwon tare...
Da sauri tayi hanzarin ɗago kanta jin kamar an sake buɗe ƙofar da aka shiga da Yayar nata, wasu nurses mata ne guda biyu suka fito da yayar nata a gadon marasa lafiya.Ganinsu da tayi ne kuma yasa har kamar a ɗan zabure tayi kansu, saidai kasancewar kuma suna sauri sosai ne, yasa ta kasa cimmusu saboda dakatar da ita da ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, bisa dole haka ta tsaya akan ƙafafunta dake rawa, daga can nesa tana zubawa fuskar Mijin Yayar nata ido, da har lokacin ya gaza tafiya shima,sedai dishi dishi take kallonsa saboda ruwan hawayen da suka cika mata idanu. A cikin zuciyarta take sake jin tsananin tausayin Yayar nata acikin zuciyarta, sai takejin cewa tamkar Yayar tata zata rasa damar ci gaba da kasancewa a karkashin inuwar Mijin nata, tana jin ya zatayi da irin wannan rayuwar da take shirin fuskantar ta a cikin rayuwar auren ta?,
Haƙiƙa ta sani cewar Yayar nata mutum ce wacce take kamar tinzirarriya, wacce idan aka hanata abu to ita kuma kamar a lokacin ne ma ake ingiza ta gashi wannan abin ɗin, Hakan kawai da take hasasowa ne ke saka karya mata zuciya, hakan yasa ta sake damƙe hannunta ɗaya dake cikin ɗaya a bayyane cikin raunin murya tace....
"Allahumma La sahala illama ja’altuhu sahala, wa’anta taj alul hazna iza shiyta hasla, Yah ALLAH ka taimake mu!, Ya ALLAH ka kawo mana ɗauki da agajinka ka kawo mana mafita a cikin wannan halin da muke ciki, ka dubemu da idon rahama ya Rahman ya Arrahaman Rahimin!!!......" Ta ƙare maganan tana kuka hadi kuma da ware idanunta, cikin wani kalan damuwar dake sake shigarta take cewa....
"Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Tana kamar zata shiɗe daidai da isowar Ya Sadeeq daya biyo bayanta, don bai zata abin ze kai haka ba, kuma dama shima yana da zafin zuciya da kuma riƙe abu a zuciya.
"Shareefah!"
Ya ƙirayi sunan ƙanwar nasa cike da damuwa da tashin hankali, yana tallafo fuskarta dake ɗauke da tsananin damuwan halin da yayar nata take a ciki, yanda yaga hawaye caɓa caɓa akan fuskarta ne ya sake tashin hankalin sa. Kafin a sanyaye ta ɗago cikin muryan kukan dake ƙoƙarin sake kufce mata ta kamo hannun yayan nata, kafin cikin sigan bayyana tsananin rauni da damuwarta tace.
"Ya Sadeeq ka taimakeni banason in rasa Yaya Ameenatou......"
Daga yanayin yanda tayi maganan cikin muryar kuka ne yasa idanun Yayan nasu cikowa da nashi hawayen shima, Saboda yafi kowa sanin iriyar tsananin SO da ƘAUNAR dake tsakanin Shareefah ɗin da kuma ameenatou ɗin.
Hannunsa yasa ya ɗan dafa kafaɗanta cike dason kwantar mata da hankali yace. "IN SHA ALLAHU babu abinda ze faru da Meenal, wannan ɗin ma kamar kuskuren tane ta amsa daga Ubangijin ta, idan tana da rabon shiriya daga wasu daga cikin halayenta shikenan ta rabauta ranar gobe kiyama..... Jiya jiyar nan na gama magana akan ire-iren shigar da take yi wanda be dace, amma haka ta kaɗa kunnenta maganganun nawa suka wuce ta bayan kunnenta, ita rudin sauran Dactor's na ɗibarta, da yin duk abinda suka ga dama, wanda a yanzun mafi yawancin abinda Dactor's sukafi yi kenan, duk shigar da suka ga dama daga Matan Aurensu har ƴan matan cikinsu, suna ɗaukar hakan a matsayin wata waye wace ta zamani da tazo musu, se dai suna aikata kuskure ne ba tare da sanin suba, lokaci suka nema kuma ALLAH ya basu sedai su sani. Daga lokacin da shi wannan lokacin ya gama kare musu daga nan na ALLAH ke farawa, don faɗin sane hakan domin shi da kansa yace....Yaku bayin ALLAH, ku ji tsoron ALLAH, tsoro na gaskiya domin tsoron ALLAH shi ne ginshiƙin rayuwa mai albarka, shi ne hasken da ke shiryar da zuciya a cikin duhun duniya, Ku kusanta kanku gareni ku nisanci duniya, domin duniya tana wucewa ne kamar mafarki. Abin da muke gani yau gobe zai zama labari tabbas, duk wata ɗaukaka zata barmu, dukiya za ta bar mu!, mukami zai gushe mana, kamar yadda in mun mutu mutane za su manta da mu. Amma aikin da muka yi domin ALLAH shi kaɗai ne zai tsaya tare da mu a kabari, ya kuma ci gaba da ribanya bayan koda ta hanyar kwatance da halaye na gari ne, yana cewa kada mu yaudari kanmu da buri, alhalin mutuwa ko ƙaddara basa taɓa tambayar shekaru ko matsayi da girman ikon mutum , aikinsu kawai suke gudanar akan duk wanda ya bari son zuciya da duniya suka gama rinjayarsa. Inda yake mana nuni da kamar yanda da yawan wasu mutanen sun fita daga gidajensu da safe lafiya lafiya ne, amma ba su dawowa da yamma sabo da amshi abinsa. Ko anan ya kamaci ace duk bawa me tunani me kyau ya tsaya nazartan shin, me na tanadar ma kaina wa ranar da za mu haɗu da ALLAH?, se dai kash bamu tunanin hakan sabo da duniyar kaɗai muka sa gaba, inda yake cewa da zaku gyara zukatanku kafin tsayuwa ranar hisabi, Ku kuma yawaita istigfari, ku kuma koma ga mahaliccinku da tuba na gaskiya, ku darajanta jikkunanku da kun sama babban sakamako a ranar gobe kiyama, kuyi gaggawar tuba a gareni domin ni me gafara ne, ku dena koyi da shigar arna, koyi koyi da abinda addininku ya baku ba na wasu ba, dana azartaku da manyan hijjaban da zasu kare duk haufi naku a ranar gobe kiyama.... Amma Meenal taki ganewa Shareefah, ra'ayin nasara sun rinjayi nata ra'ayin, tabbas wannan aikin nata be jawo mata komai ba face taɓewa da lalacewa mara ƙarshe da kuma tushe...
Ashe don ALLAH yace ka suturce jikinka ba ni'ima bace, yanzun ni nan dake dake nan wurin,duk mun tsaida hujja a kanmu, ita Rayuwar duniyar da muke kallo tamkar zubin dashi ne, iyaka kirki ko zunubin da muka aikata su zamu samu, domin kuwa dama ALLAH (S.W.T) cewa yay mana damu, rayuwar mu ta nan gidan duniya kamar mun zo munyi shuka ne, can kuma shi ne ranar abinda zamu girba , amma duk da zuciyoyinmu sukan rinjayi ra'ayoyin mune daga tafarki na gaskiya zuwa tafarkin ƙarya da burge wasu dabbobin mutanen da sune ALLAH ya ware ya mana misali dasu...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ yake nanatawa tare da Baffa dake tsaye daga bayansu tin farkon fara maganar nasu, se Dr pooja dake tsayen itama gaba ɗaya tsigar jiki da jikinta na wani kalan rawa, a duk lokacin da zata ji ana wa'azi, ko tunasarwa me irin haka. Gyaran muryan Baffansu su ne ya saka kukan Shareefah dakatawa, nuni ya mata da Dr pooja take kuwa itama ta fuskanta halin da take ciki, kai tsaye ta fara ƙoƙarin tallafa mata duk da itama tallafin take. Suna haka sega wata nurses mace nan ta iso wurin tana amsar pooja ɗin suka fara tafiya. Kai tsaye kuma Shareefah'n ta miƙe tana ma su Baffa jagoranci zuwa ɗakin da Meenal ɗin ke kwance amma ta cikin glas, don babu damar shiga ko waye kuwa in aka ɗauke ma'aikatansu. Wata guntuwar kwalla Baffa da Ya Sadeeq suka ɗauke kusan tare, har dama Ya Ahmad da tin isowar Baffan yake biye dashi, sedai baya da bakin da ze iya buɗewa balle har yayi magana, ganin hakan ya saka Baffan kyaleshi ya hutayye ma zuciyarsa, duk da kasancewar bawai ma sanin takamaiman makomar auren Meenal ɗin suka yiba......
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
