Karshen Kaddara Page 3&4 Complete by Ammey Laylerh - Abokiyar Hira Novels


*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢  𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

 _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥 

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 

_My NAINERH TARH, My Ƙaunar ƙaunata My aminiyar kwarai mutuniyar kirki  Uwar yaro na Mubeen kuma this Book for you, gashi ya iso gareki da zafi zafinsa fa💃🤸_ 

Page 3&4

♡ ♡ ♡ ♡     

ꨄ  Tana isa cikin asibitin kai tsaye office na Dr pooja  ta wuce, wasu ayyuka ta ɗan bata ita kuma tana yin ɗakin wata me haihuwa da aka kawo, tun cikin dare ta  kasa haihuwar da kanta shine ma  abinda yasa take tunanin ko C/S ma kawai za'a mata, don tana matakin ƙarshe ne don tana 1/cm  haihuwa a koda yaushe, amma gashi abu ɗaya ake fama tin wajajen karfe 7 gashi kuma yanzun har goma na nemar wucewa ma, labcoat nata ta zira da handglov a hannunsa ta sake nufar  delivery room ɗin da matar ke ciki, tin kafin ta kai ga ƙarasa shiga room ɗin take jin ihu da salatin matar na tashi, goshinta ta dafe tana ƙarasa shiga da ɗan hanzarin ta, handglov ɗin dake hannunta ta sake gyara zamansa tana kai hannunta ƙasan matar dake kwance saman gadon masu haihuwar nan, ganan dai kan jaririn ya ɗoso sedai  daga uwar har yaron ko yarinyar dake cikin cikin kowa fafatuwar tsira da rayuwarsa yake, ita tana son taga tayi duk me iyuwa ta yunƙura koda ta numfashi ne abinda ke cikin cikin nata ya sama damar fitowa, shi kuma dake cikin shima yunƙurin yaga ya fito ɗin yake, wata nurses ta ƙora Damaga kan ta haɗo mata allurar naƙuda kawai tama matar, kanta matar ke jijjigawa gafa ɗaya gumi ya gama jiƙeta sharkaf, da kyar ta iya samun bakin furta. "Karku daura min ruwan naƙuda ina da sugar da hawan jiniiiiii...... San...sa...sa....san...nan...ina da raunin zuciya....." Duk wannan abin da take yi cikin fusgar numfashi take da haki.. gaba ɗaya ta gama saddakarma rayuwar ta gama sallama cewar shikenan ita nata ajalin yazo, don haka ta shiga adda'a 'o'i masu kyau da girma idanunta na ƙoƙarin lumshewa, su kuma gaba ɗaya ma ɗakin sun rasa abinda ya kamata su mata, don haka kawai Dr pooja ta fita babu jimawa se gata hankali a matukar tashe da file na saka hannun mijin matar dake can haraban asibitin yana ta safa da marwa yawa me dawafi. Abinda ze baka ma dariya ƙafansa ɗaya da takalmi ɗayan kuma babu faɗi yake. "Don ALLAH NA'EEMERHTOU karki tafi ki barmu!, ki taimaki rayuwar yaran mu dake dani Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" haka yake ta famar ambata gaba ɗaya shima ya gama jiƙewa se kace shi ne me haihuwar, gefe can kuma dashi wasu mata ne biyu kowannensu ya buga uban tagumi kowa da abinda ke damunsa. A can ɓangaren Meenal shigar Dr pooja office ɗin ta hankali tashe da kuma fitar ta ne itama ya tashi hankalin ta, don haka ta mara mata baya, bayan ta ɗora labcoat da handglov a hannunta koda ALLAH yasa zata iya musu da wani temako ne haka, gaba ɗaya zuwa lokacin kuwa har Dr pooja ta kammala duk wani shiri nata na fara surgical ɗin, harma an nufi surgery  room da matar. Lokacin da take kaiwa ainihin room na Surgery room  ɗin har pooja ta ɗora Scissors  nata saman cikin matar da numfashin da take shaƙa ma na Oxygen ne, don tuni rauninta yayi ƙasa sosai dole se da taimakon oxygen zataci gaba da numfashin.  "Wait a minute, ma'ame..." Haka Dr pooja ta tsinkayi muryan Meenal, dakatarwar kuwa tayi tana isowa ita kuma. Cewa tayi pooja ɗin ta taimaka mata da sabuwar rezor, seda ta sake risinar da kanta tana juye baki cikin yaren Ingilishi tace da ita tayi haƙuri ta shiga cikin hurumin da ba nata ba, ba komai tace da ita, don haka kai tsaye ta saka sabuwan rezor ɗin tana ɗan yankar ƙasan matar, da komai bata ji ba sakamakon allurar kashe jikin da aka mata, oxygen ɗin dake hancin matar Meenal ta zare kaɗan tare da ɗan ɗago kan matar kamar zata zaunar da ita ta kuwa takarkare ta saki wani zazzafan numfashin dake kumshe cikin bakinta ya fashe, wanda dama ita Meenal ɗin hakan take son samu daga matar, daga ƙirji zuwa cikinta ta ɗan danna tare da sake mata irin ta ɗazun bayan ta mayar da ita ta sake ɗago ta, aikuwa a wannan karon ma ta sake yin irin na ɗazun, haka har suka yi karo uku, ana huɗun kuwa tayi wani kyakkyawan nishin da kai tsaye ya taho da yaron dake cikin, hannunta ta saka duka biyun tana ƙarasa janyo yaron ya fito kuwa da assalatunsa, wato kuka irin na jarirai sabuwan haihuwa, suluf haka matar taji jikinta ya koma kamar wacce aka sauƙe mata cutar shekara da shekaru, tana meda wasu numfarfashi, kafin ta tafi zuwa duniyar sumewa... Dama tasan za'a yi hakan duk da cewan bata taɓa amsar haihuwa ba amma kuma Alhamdulillah tana da kyawawan da bata mantuwa, don wannan ɗin duk cikin interview ɗin da aka musu ne na irin dabarun haihuwar da tayi gaddama, kuma Alhamdulillah tayi nasara wanda dama se irin kamar ana daf da yima mutum operation ɗin ake son yin hakan, wanda ita da classmate nata sun sha gwada hakan akan kansu da numfashin da suke gumtsa su fesar idan an zame oxygen ɗin, kamar yadda tayi tama matar. Dr pooja ce ta rumgume ta tana furta "Ohhh jesus Today I saw a young lady who was thoughtful and knew her job well.Thank you Jesus.... Thanks u Maanol....." Dake haka tin jiyan take ƙiran ta dashi wato Maanol ɗin. Ko kafin kace mene se gashi tuni har an gama shelanta wa duka sauran Dactor's ɗin dake cikin hospital ɗin cewa ga wata ƴar baiwar likita sun samu me matsakaicin year's. Cikin ƙanƙanin lokaci se gashi sunan Dr Meenerl Shehu Usman na nema yin shura tun a matakin farko, da kansa Dr Bilal ya ziyarci wurin ya kuma zauna da sauran Dactor's tare da Meenal kan fikirar da tazo musu da ita, nan kuwa ta tashi ta ringa musu bayanai daki daki, wanda daga ƙarshe suka gane cewar lallai ashe ba se iyaka private school's bane suke jajircewa wajen koyar da ɗalibansu ba, nan mijin matar ma ya bada wasu kuɗi masu ɗan gwaɓi yace na likitar data ceci rayuwar matarsa ne da kuma abinda ke cikin ta,duk da kuwa kasancewar tana  a Cold room ne.  Wato ɗakin sanyi amma kuma ai tana ci gaba da shaƙar numfashin daba na oxygen ɗin bane, ga kariyar da aka haifa ɗin tazo cikin ƙoshin lafiya abinta,  dake dama tun a lokacin ta gama wa matar ɗinki,don haka yaci gaba da kulawa da marasa lafiya a fannin haihuwa, kowa se kaji yana don ALLAH a ƙirawo masa Dr Meenerl shima tazo ta taimake shi, wanda ita abin ma yake ɗan bata dariya, wato ma ita ne zata temakesu ba ALLAH, ko dan ance me ciwon haihuwa tamkar zautacce haka yake komawa, duk abinda yazo bakinsa faɗa yake. Ba itane ta koma gida ba yau se wajejen ƙarfe 7:30pm, tin kuma 7:15am data fito. Dake dama tayi waya da Ya Ahmad ɗinta cewar yau kar ya biyo da wuri se after magrib ze biyo ya ɗauketa, SO shi kuma lokacin Hajiyarsa ce tayi ƙiransa dole haka ya tafi yace ta biyo napep amma karta yarda ta hau machine... Koda ta dawo ta tarar ya dafa musu farar shinkafa da yaji, ta wani cunkule ƙaramin bakinta kuwa don ita ba Sosai take son farar zallar shinkafa da may da yaji haka ba, har ƙara ya musu couscous ko noodles da egg, haka bayan tayi wanka tana ƙananun ƙunƙunai tana komai ta tuttura abincin...  Wayarta ta ɗauka bayan sallarn isha'a ganin be shigo ba ta shiga WhatsaAp nata da duk wunin yau bata hau ba, da test messages na Shareefah ƙanwarta kuma babbar aminiyarta ta fara cin karo, don haka ta shiga, voice note ne don haka ta kunna tare da kaiwa kunnenta ta saurara. Wata ijiyan zuciya ta sauƙe lokacin data kammala sauraran voice note ɗin, kafin itama ta fara mata nata voice ɗin.  _Look Shareefah ina son ki kwantar min da hankalinki kinji, ki kuma ci gaba da haƙuri bana son kika sanya wata damuwa daban a cikin ranki, kinsan koda ace da ran Ummanmu ba zata so ganinki cikin damuwar hakan ba, kuma Baffa yana daidai gwargwadonsa a kanmu tsakanin mu da gwaggo Sadiya, kuma ke ba karatun ki ma kike ba, don ta hana ki abinci kuma se yaya ina ce kusan duk bayan 2 weeks nake saka miki kuɗi a account naki?_  daga nan ta tsaida voice ɗin, babu jimawa kamar da 5 minutes sega wani voice ɗin na Shareefah'n ya sake faɗo mata. _Aunty Ameenatou ba wai rashin hakuri ko rashin kaiwa zuciya nesa bane, kin san ni ina son naga anyi komai cikin tsakani da ALLAH,  bana son cuta ko zanba da zagon kasa irin na gwaggo Sadiya, matar nan makirace wllh, bayan rashin bani abincin da bata yi ina jinta ranar tana cema Baffanmu wai na dena cin abincin gidan, haka ta ɗebo kwanukan abinci kusan na kwanaki biyar ta dire a gabansa wai bana cin abincin ya tuhumeni wai a ina nake samar kuɗi?, kin ji fa, karki ga yadda baffan kuma ya wani rutsani wai in faɗa masa inda nake samar kuɗin, alhalin gidansu Yaya Jafaru nake shiga inci wajen mamarsu......_  wata doguwar ajiyar zuciyan dai again ta sake sauƙewa a cikin zuciyarta tana ayyana wai se yaushe gwaggo Sadiyan zata san cewa Annabi ya faku ne?, se kuma zuwa yaushe zata gane gaskiyar dake bayan ƙarya?. Wani voice ɗin ta mata tana ce da ita taci gaba da haƙuri zata ma Yaya Sadeeq babban ƴaƴansu kenen maganar, kuma itama yanzun ganan wasu ƴan kuɗaɗe zata turo mata daga wanda mijin matar nan ya bayar a bata, shi ne ta raba uku ta ɗauki kaso ɗaya biyun ta ce su Dr pooja ɗin su kasa suma, gashi alert nata na wata har ya shigo mata wajen dubu ɗari huɗu da arba'in da biyar. Dake su haka al'adansu yake a ranar da kaje aiki a washe garin ranar alert naka ke faɗo maka. 100k ta turo mata take aiko sega saƙon godiya nan daga ƙanwar nata harda kukanta, da cewar lallai ita ce uwa mahaifiyar da suka rasa itace kuma bangonsu se kuwa Yaya Sadeeq da shima ba'a barinsa a baya, duk da kasancewar ba wata gwaggwaɓar sana'a ke gare shi ba, amma kuma kusan kullum cikin rufin asirin ALLAH suke,don kusan shi ne ke ɗauke da gidan mahaifin nasu, kai tsaye suna kammala maganarsu da Shareefah ɗin ta laluba No na Yaya Sadeeq ɗin buga ɗaya ana biyu kuwa ya katse shi ya ƙirata, ɗan murmushi kawai tayi,don tasan dama ba wai ɗagawar ze yiba, amma kuma ze biyu tunda kamar hakan na masa nuni ne da tana son yin magana dashi kai tsaye, tana cikin wannan tunanin ƙirar nasa ya shigo mata, answering call in tayi tana kai woyar kunnenta. Gaidasa tayi yana tambayar lafiyanta, komai normal tace masa kana tace ta saka masa ɗari biyar a opay nasa ya sake data jarinsa, tif yaji wata wuta ta ɗauke masa duk da dai ba wannan ba ne karo na farko da take tura masa kuɗin ba, duk da kuwa kasancewar baso yake ba yace ta bari alhakin kulawa dasu na a hannunsa ne, wata numfashi me ɗan zafi ya furzar yana ce da ita a ina ta samu kuɗi har haka?, da har tashin farko ta saka masa dubu ɗari biyar?. Wata ƴar ƙaramar dariya tayi tana cewa. "Laaa Ya Sadeeq kana manta cewa yanzun na fara aiki ne halan?"  "Kuma daga fara aikin naki shi ne har kina sama uban wannan kuɗin haka?" Fuska ta ɓata tana cewa. "Amma ai na faɗa maka cewar babbar asibiti ce, kuma tashin farko su suke fara biyar ma'aikatansu sabbi,kuma ƙarshen watar ma Dr pooja tace zasu sake sakamin 200k...." Wata yar gubtuwar murmushi yayi yana cewa. " Su kuwa wannan waɗan da irin masu kuɗi ne haka, da tashin farko su hankaɗo miki uban kuɗaɗe haka?, kana kuma ƙarshen wata ma su sake biyar ki har 200k?...., kuma halan ALLAH dai ma yasa kin shawarci Mijin naki, don a wannan fannin na sanki farin sani ba shawara kikayi da kowa ba, duk abinda ya miki kawai kike aiwatarwa..." Tsaye ta miƙe daga zaunen da take tana wani tura micil ɗin bakinta gaba tare da cewa. "To shi in na bashi ma me zeyi da kuɗi?, nasan ko da ace na bashin ma ba amsa ze yiba ai...." Sosai daga ta can ɓangaren Ya Sadeeq ɗin ya haɗe ransa yana cewa ze dawo mata da kuɗin nan lallai ta tabbatar ta fara shawartan mijinta kafin kowa, tin kafin ta ce komai ya datse ƙirar sega alert nan na kuɗinta na dawo mata har da ƙarin dubu ɗarin da take da tabbacin Shareefah ta faɗa masa shi ne ya haɗa ya dawo mata dashi, duk da tasan cewar bawai ze amsa na wurin Shareefah ɗin bane yayi ta aljihun sane, wanda tasan yanzun haka ya gama budget na abinda zeyi da kuɗin sa... 


 Ɗakinta ta nufa tana wani huhhura hanci sama,ita ala dole yayan nata ya ɓata ranta, kwanciya tayi saman lafiyayyen bed nata idanunta lumshe, tana son yaƙar zuciyarta akan ta ringa bijirema duk abinda take raya mata, ta sani sarai cewar ita bame sauki bace, ba kuma me ƙyaliya bace ga duk wanda ya shiga gonar ta, sedai in mutum yaga bata tankashi to lallai ya kai ya kawo girmansa take gani,mutumcinsa take gani ko na wani nasa, kamar dai Hajiyar Ahmad da ita ma nashi mutumci da albarkacin take ci da har take yaɓa mata duk maganar data gadama kuma ta kyaleta. Duk zuciyarta take jin a cunkushe badon an mata komai ba sai don kawai dawo mata da kuɗin da Ya Sadeeq yayi. Tana nan a haka har bata san Ahmad ɗin ya shigo har nan bedroom ɗin ba, sedai taji hannunsa a shoulder nata kana ta ankare, zaune ta tashi tana ɗora kanta akan kafaɗarsa bakin nan a tinzire kamar wata ƙaramar yarinya, "Meke faruwa da Rayuwar Ahmad Junaida Haris haka?, wanda me gangancin ne yayi ƙoƙarin taɓa farin cikinsa kuma?" Seda ta haɗiye abinta ke son ɓallo mata ruwa don se da Ya Sadeeq ɗin yace da ita, _Saura kuma in yazo kice masa ga abinda ya faru wacce bata iya kalmasa zance ko kalamanta ba...._. Makut ta sake haɗiye maganar tana tauneta da ƙarfin tsiya kana tace. "Ba kai bane kaki dawowa da wuri ba!, kuma ka dafa min shinkafa farar da kason ban fiye sonta hakan ba...." Jikinsa ya shigar da ita yana cewa. "Wannan shi ne dalilin?, shi ne kuma musabbabin fushin naki Bestie?" Se ya dakata tare da ɗan janye ta daga jikinsa yana kama kunnensa da kokarin sauƙa yayi kneel down, tayi saurin tarosa tana wani famar zazzare fararen idanuwanta. Kana ta kai hannunta samar bakinta tana me furta. "A ah Babyn Baby kayi haƙuri ka kuma rufamin asiri maza su kaini ba mata ba, in ma hukuncin ne ai ba irin wannan ya kamaci ace ka amsa ba, irin haka...." Tayi maganar tana ɗagosa ta kama gefen kuncinsa ta ɗan ciza kaɗan ba da yawa ba. Fuskanta ya ɗan tallafo ya mara marin wasa yana jijjiga fuskan suna sakin dariya kusan a tare. Bayansa ta juya tana ɗurƙusan dashi ta haye bayan wani shauƙin ta hau bayan mijin nata na kamata. "Ohhh Bea bayan yayan naki kikeson ɓallewa ya dena samar na moro ko?, ke baki san  kin ƙara lukucewa bane halan...."  Tam fa an taɓo ta, don ta tsani taji yace ta fara lukucewa tace masa yaka cewa ta fara zama ƴar duma duma kawai, amma ita ina take son wani girma. Dariya yayi yana cewa "Tuba nake wane ni inji kare da yaga kura maza hau bayan kine, da ma don inyi ta goyaki ALLAH ya min shi ne auki haka...." Gefen kunnensa ta kama ta ɗan ciza tana cewa, "ALLAH Ya Ahmad ɗin nan ka fiye tsokana, za kayi ta zaga gidan nan dani har nayi bacci a bayanka wannan shine hukun cin naka. Dan waro idonsa yayi da riƙe haɓa yace, "Nie kuma in kikayi baccin waye ze kula dani har inyi nawa baccin cikin salamar?" Seda ta cakulkuli wuyarsa kana tace. "ALLAH mana..." Ɗan sakin ta yayi kamar ze kayar ya ce "Naki wayon ban isa ba wllh, kin gama saƙƙo nayi missing ɗumin jikinki duk wunin yau... Se kuma ya wani haɗe rai kamar ba shi ba yana sake furta. "Gaskiya wannan aikin na son shiga haƙki nafa Baby, iyaka jiya da yau har kulawanki ya fara raguwa daga gareni anya zamu seta kuwa da wannan aikin?...."  Yayi maganar yana fara tafiya da ita a jikinsa  zuwa nasa ɗakin tana cakulkulinsa tana cewa babu abinda ya isa ya shiga ƙarkashin kulawan da suke bama junansu, har suka kai bedroom ɗin nasa, kafin su kai kuwa gaba ɗaya ta gama susuta jikinsa da ababuwan data ringa masa, ga hannunta ɗaya na cikin rigarsa data ziro bayan ɓalle boturan gaban rigan da tayi, don haka suna isa bedroom ɗin suka zube yana fara kunnata itama, duk dai dama a kunnen take, indai zata jita a jikinsa to kuwa lallai babu zaman lafiya a gangar jiki da ruhinta, har se sun ziyarci juna.  Amma se ta fara masa rakin ita ya kyaleta ta gaji da yawa ƙafafunta sun yi tsami, ko ta kanta be bi ba yaci gaba da abinda yake har se da yaji shi ontop kana ya sarara mata yana janyota jikinsa ya shigar yana sauƙe mata numfashinsa me ɗumi a gefen wuyarta, ita kuma ganan shatin kwanciyar hawayen da suna dinga gangaro mata. Sedai suka jima sosai kafin su tashi su tsaftato jikinsu kana suka dawo suka kwanta, bayan sun san gyaggara gadon. Can gabanin asuba ya sake nemarta inda taso zamewa ta gudu amma ya sake nuna mata bata isa ba, haka ya sake biyar buƙatansa da ko Sallah yau ɗin ma wuce su tayi, karfe shida saura kana ya ja su Sallah'n. Aikuwa tayi kwanciyar ta taƙi fita musu dinner murmushi kawai yayi yana fita yaje ya soya musu bread da kwai. Da ruwan bunu, koda ya dawo seda ya fara yo wanka kana ya tadata yace ta fito suyi dinner karta makara. Wankan tayi itama sama sama kana ta fito cikin wata ash jallabiya ta mata, wacce ta amshi surar jikinta kwarai, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ta zauna sukayi dinnerh ɗin, seda suka kammala tsaf kana ya fuskanceta yace. "Yanzun yauma fisabilillahi Meenal yau ɗin ma haka zaki fita?, anya kuwa kina son ci gaba da fita wannan aikin naki?" Tsaye ta miƙe tana dubar shigar nata kana tace. "Haba Ya Ahmad mana, kar ka neda kanka wani ɗan kauye mana, yanzun miye laifin shigana don ALLAH? Se dai in kaine ba ka son zaman lafiyan...." Daga haka ta suri jakarta tayi waje fuuuuu.... Da wani kalan daskararren kallon mamaki al'ajabi rudu ya bita. Kafin yayi ƙarfin halin miƙewa tsayen shima ya bi bayanta, sedai me wayam babu ita har ma ta fice kenan?...  Duk yacce zuciyarsa taso ingizo hasalarsa fili kin yadda da hakan yayi, yana ajje ta a matakin mata uziri ne kawai. Don haka yama motarsa key ya tashe ta yana fita daga haraban gidan. Sedai kome kama da ita a hanyar be gani ba don haka yayi wucewarsa gun nasa aikin tin da yasan ita ba yarinya bace, ta kuma san inda ta nufa, haka ya tafi yana ta tunanin sabbin halayenta daga ranar fara aikin nata zuwa wayewar yau da yake na uku a fara fitan nata, a cikin zuciyarsa yake ayyana lallai da akwai matsala kenan indai har tace a haka zasu ci gaba da tafiya. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauƙe yana karanto Hasbinallu wani'imal wakeen...


Meenerl kuwa yau se aikinta yafi na jiya yawa don har sun sau mata ragamar fara aikinta gadan gadan, harma sun gama tsara mata time table na lokutan aikin nata, a sati tana aikin tin daga safe har zuwa yamma sau uku, daga yamma zuwa safe sau biyu. Koda ta koma gida take bashi labarin be ce mata komai ba,  har ya fara gudanar da aikin nata, a memakon shigar da take ya sanja sema sake ɓauɗewa da take,  amma se ya tattarata duk gefe guda yaga iyaka nata gudun ruwan, itama kuma bata damu ba haka har suka cinye tsawon wata guda kenan a hakan,  idan tayi bacci yakan ɗauka wayanta time to time bawai don yana zargin tana sedan kawai tsaro da kariya, baya shiga duk abinda ya danganta family issue nata, be kuma taɓa kamata da aikata ba daidai ba, sedai yakan tsinci video's nata  tsilli tsilli duk ranar da take da kwanan asibiti tana yar rawa abinta, wanda take yi a tiktok seta yi sev nashi akan wayan,seta goge daga tiktok ɗin da dama a private account nata yake. Amma na yau ɗin se yafi na koda yaushe daga masa hankali don kuwa daga ita se wata sky ɗin rigan baccinta iyaka gwiwwa kanta babu kitso a tubke ƙasar ƙeyarta, ga hannun bra nata nan ɗaya ya fito koda saninta kodai akasin hakan, se ya shigawa WhatsaAp nata ze tura a wayanshi amma se wani abu ya ɗauki hankalin sa a cikin wayar nashi, wato kamar sabbin status da sunan _BESTIEN BESTY_ ke ɗauke dashi, don haka kai tsaye ya shiga status ɗin ya kalla, video'n daya gama kalla yanzun ne tayi status dashi, duk da kasancewar ta saka hoton love ta kare jikinta amma kuma ai be dace ba, inta kare ƙasan saman kuma fa?, nan ya shiga na biyun yaga ol de same da wancan ɗin, shi wannan da tana yi har kamar wulgawar  wani namiji ya gani da kayan likitoci sanye a cikinsa. Guda uku ne don haka na ƙarshen tana tafiyane tanayi tana sanye da kayan ta na aiki ta a video ɗin,  view na mutanen da suka kalla ya duba, yaga sama da mutum goma sha biyar har sun kalla, cikin kuwa harda classmate nata,  fitowa daga wurin status ɗin yayi yana duba na farko farkon da suka fara mata message, nan ya kalla na Yayanta Sadeeq da shi kai tsaye cewa yayi Lallai lallai maza maza ta sauƙe status ɗin,  bata bashi amsa ba duk da ganan taga message nashin, daga nan yaga group 

na school mate nasu saƙonni nata shigowa, don haka se hankalin sa yafi karkata wurin kawai ya shiga, shi dai wannan video ɗin da tayi status dashi ne wata daga cikin freind nata da suka kalla ta tura musu, a ƙasan video ɗin ta rubuta. _Gafa mutuniyar an fara ɗaukan haske...._  Mutum na farko kuma daya fara magana akan video ɗin na miji ne, me suna Hasheem Al'asan, shi ne yace. _Ohhh ALLAH Yarinyar nan wai dama zata waye haka?, kodan No wonder daga yanayin tsiwa da rashin kunyar tama, idan kuma aka haɗe da kalan mijin data samu lallai dole ne ta numfasa itama...._   Se na biyu shima dai namijin ne inda shi kuma yace. _Wooo Malam yarinya ta gama timbatsa ba, ta zama wata se kace renon madara da A/C....._ se ta ukun kuma macece ita kuma tace. _Shegiya nera wato dai shi kuɗi da jin daɗi babu abinda baya saka mutum aikatawa ci gaba dayi da kyau hakan ma India'n girl...._  namiji ne ya sake tag na hoton yace. _Je kaya alaji, gaskiya sa hijjab ma duniya, da yarinya kullum a cikin manyan kanya,amma da dukkan alamu mijin nan nata na shagwaɓata da yawa..._ _Yo ba dole ya shagwaɓata ba ya sama wanga ganima haka, dole ai yayi ta bata tana kwashewa ita kuma...._  Wani kalan rumtse idonsa yayi ganin duk cikin maganganun babu na kirki, babu kuma wanda aka samu ya ce tayi ba daidai ba, se dai masu yabon tama. Dubawa yayi yaga itama group admin ce a group ɗin, don  haka kai tsaye ya goge video ɗin, tare da exit kanta daga cikin group ɗin gaba ɗaya,  yana fitowa ga mamakinsa duk da kasancewar lokacin wajen karfe ɗayan dare ne se yaga wani guy har ya biyota private yace. _Haba India'n girl ya zaki mana haka uyhmmmm?, bafa mu riga munyi saving video ɗin nan a wayoyinmu ba kika goge?, kana kinyi left daga cikin group ɗin, halan Mijin kine yasa ki fita ko???, Hhhhhhh yayimin dai-dai ta wani fannin kuma be kyauta min tin da duk mun sakan kance bamu yi sev na video ɗin cikin wayoyin muba, ita kuma waccen Yar Is ɗin data ɗora na mata magana naga bata online, dama ita kowa yasan kasa ce uwar yan bacci, amma zuwa safe na mata magana ta turomin, in kuma zaki bani zan yi farin ciki da hakan, daga Jinior Ahlam kd_  take wani mummunar ɓacin rai ya sake kume zuciyarsa,  kai tsaye ya rubuta masa.


_Come to your senses and calm down, otherwise I may mislead you or end your life in prison, be careful..._


Daga haka yayi block nashi yabi yarinyar data ɗora video ɗin, yace mata.


_ The biggest mistake you will ever make is to forward this video to someone else, because I will look at every possible connection between the two of you and I will have you arrested, an arrest like forever, so be careful, From Meenal's husband Shehu Usman_


Daga haka ya kashe wayan yana fita a ɗakin zuciyarsa na tururi da kuna akan wannan abin data masa, don haka cikin ransa yake raya dole ya nuna mata kuskurenta a wannan karon. Da safe ta farka ta ganta ita kaɗai babu ma alaman ya kwana a ɗakin, se kawai ta taɓe baki ai dai ko babu komai ta tsira daga takurawansa da ba sosai yake barin tayi wani baccin kirki ba. Don haka wanka tayi tayi sallan subhi ta shirya cikin shigar wasu riga da wando palazzo's cubeb. Se ta kawo wani himar irin robo robo ɗin nan ta ɗora kan palazzo's ɗin ta fito, bayan ta dudduba wayanta bata kalla ba, baya parlour ko kitchen don haka kai tsaye ta bishi zuwa dakinsa sedai nan ɗin ba baya nan, gaba ɗaya baya gidan don haka cikin hanzarin karta yi let wurin aikinta ta ɗiba cake da biscuit ta zira a handbang nata ta fita, yau ma ba aikin dare bane da ita don haka tana isa ta kama aiki. Amma time to time tunanin wayartan da bata gani ba kan fado mata, bayan sallar zuhr dai ta gasa samar nutsuwa ta amshi wayar pooja ta ƙira No nashi, amma yana ta ring be amsa ba, short message ta aika masa cewar ita ce yayi answering call nata, kamar da 2 minutes ta sake kira amma No answer. Dole ta haƙura ta kyaleshi tana ayyana baƙar zuciyar ta motsa kenan. Se wajajen 8 na dare take komawa gida lokacin harya jina da shiga gidan shi, yana zaune a parlour yana kallo ta shigo a gajiye sosai, a gabansa ta zube dama takarmi da guntun shimar nata a hannu ta shigo dasu. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana kuma ƙoƙarin zame kanta daga jikinsa data ɗora, kanta ta ɗago ta kalleshi tana furta... "Besty yau duk me ya faru ne?, banga woyana ba na ƙira ka data Dr pooja har test messages na ma amma No answer lafiya kuwa?..." Hummmm ya kawo wani gauren numfashi yana ƙarasa zamar da ita daga jikinsa yace. "Yanzun kin kyautama kanki kenan meenor?, duba kalan shigar da kika fita dashi, ina ma laifin kici gaba da saka bubu ɗin kina fita dasu kiyi rolling vail na kayan, bayan haka yanzun ke abin birgewa ne a gareki kiyi video da karamar riga har kiyi status dashi, wasu can su ɗauka su ɗora a group naku da kuke haɗe maza da mata uyhmmmm?. Duk sabbin halayen da kike ta bijiromin dasu inata ƙoƙarin shanye wa sabo da ina SONKI Meenal, amma duk na miye waɗan nan ababuwan?...." Kanta ta dafe tana furta "Ohhh shit dama nayi tunanin hakan wllh" se kuma ta taso gaba ɗayanta tana shigewa jikinsa tace "I'm so sorry Dear, Amma ai naga na kare jikin nawa, kuma ma ai nake kallar hakan ba laifi bane, ni wllh ma sabo da kai ne nayi video's ɗin, idan kana wasu ababuwan se kace wanda be gama wayewa kodai yake da ƙarantar wayewar kan.... Tin da  ta fara maganar yake kallonta da kaifafan idanunsa ko fiftawa bayayi, wato ma ita hakan ba komai bane a wurinta, har yana faɗa mata abinda tayin ba daidai bane amma take ƙiran sa me ƙarancin wayewa?, Lallai ya riga yayi saken da Meenal ɗin ta gama rainasa. Amma duk da hakan se ya danni zuciyarsa  yana ɗago fuskanta ya riƙe a cikin tafin hannuwansa ya furta. "Ki gyara!, ki sake halaye da ɗabi'unki Meenor!, ina SONKI ba zan iya ɗaukar waɗan nan sabbin halayen naki ba, Pls ki taimaki wannan zuciyar dame zuciyar...."  Yayi maganar deep down na bugun zuciyarsa na sake ƙaruwa, daga yanda take lafe a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke beating very fast akai akai.  Tashi tayi ta nufa ɓangarenta wanka ta fara kafin tayi sallan magrib da isha'a da batayi ba duk ta haɗe su a lokacin, wasu riga da wando masu taushi ya saka tana baje jikinta ta turare ta nufa ɓangarensa, zuwa lokacin har ya bar parlourn,yana kwance idonsa bisa p.o.p na ɗakin yana kalla kamar me nazartan wani abu daga cikin sa, be ji shigowarta ba sejinta kawai yayi a jikinsa ta wani faɗo masa, ƙanƙameta yayi da hannunsa yana cusa  kansa cikin wuyarta ya wani shaƙi numfashin daya tafi may da mayen ƙamshin ta me bala'in rikitasa. Anan wurin ya zubar da duk wasu makaman yaƙinsa yayi yaƙin gaskiya da gaskiyar da babu saussauci ko sauƙi na ragwanta tattare da shi, amma kuma akwai sanya nutsuwa da nishaɗin hakan tattare da lamarin. Washe gari babu aiki weekend ne, don haka daga shi har ita suka mora wunin ranar da ƙaunar junansu, tuni harya mayar mata da wayarta bayan ya sake roƙon ta da karta sake don ALLAH. Washegari daya kasance Lahadi  kuma ta tambayi gidansu,don kawai kewar Shareefah da tayi da kuma Yaya Sadeeq ɗin ta, sha biyu daidai ya sauƙeta a gidan yace after isha'a ze dawo ɗaukanta.  Wata leda ya bata yace ta shiga musu da ita, godiya ta masa yana shirin komawa motarsa sega Yaya Sadeeq ɗin ma ya fito tare da Baffansu, fasa shigar yayi yana dawowa ya tsugunna ya gaida Baffan dake tai masa godiya, kafin ya bama ya Sadeeq hannu su gaisu yana jan sa cikin motar shi kuma Baffan suna komawa ciki shida Meenal ɗin, babu jimawa sega Ya Sadeeq ɗin shima ya shigo kafin Gwaggo Sadiyan data matsu da a buɗe ledan ta muskuto tana cewa a buɗe ledan mana.... Komai babu wanda yace mata taja ledar daidai damin kuɗi sabbin ƴan ɗari biyar biyar na faɗowa, daidai kuma da shigowar Shareefah tare da Bilkisu wacce take ƴa ga gwaggo Sadiya, duk su biyun a guje suka taho suna rungumeta da faɗin..... "Oyoyo  Yayarmu🫂...." Suka faɗi kowa na sake rungumeta da murna, a cikin ledan kuwa kayan fruits ne da nama me uban yawa, kuɗin kuma pakege ne da 100k dake da Yaya Sadeeq a wurin shi yasa gwaggo Sadiyan ta tura kuɗin ga Baffa tana cewa. "Kai Ma sha ALLAHU babu abinda zamu ce da wannan yaro se godiyar ALLAH, ALLAH dai ya saka masa da alkhairinsa ya bashi masu masa shima, Malam kawo dubu biyar se Bilkisu ta sawo lemu muci da naman...."  Ya Sadeeq ne ya buɗe aljihun gaban rigansa ya zaro 2k ya bama Bilkisun yace ta amso na hakan ai ze isa, duk da bata so hakan fa amma haka ta kyale bayan yasha wata uban harara a fakaice. Daga nan ya Sadeeq ɗin da Baffan suka fita don ƙirar sallar karfe ɗayan da ake ta kira,  suna fita gwaggo Sadiya taja wata tsuka tana tashi ta bar musu wurin, wajajen ƙarfe uku shiru shiru Meenal taga ba'a ɗora sanwar dare ba, don haka ta fito bayan ta yi shara a gidan ta sake tarar da gwaggon nayi...

"Sannu da gida gwaggo amma ai nayi sharar ɗazun babu jimawa." In wurin ya tankata to ita ma ta tanka, yi tayi kamar ta juya se kuma dai ta danni zuciyarta ta sake cewa.

  "Gwaggo me za'a ɗaro a gidan ne?" 

Meenerl ɗin ta faɗa tana me sunkuyar da kanta kasa, saboda sanin halin mebi yanzun ma ba wai ya zama lallai bane ta tanka mata. Gwaggo Sadiyan kuwa data wani ɗan ya nutsa fuska kafin cikin halin ko in kula ta ce....

 "Dake da can ma ai kene kike min aikin ko?..." 

Da idanu kawai Meenal ta bita kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, kafin ta dawo daga duniyar tunanin daya faɗa, ta tsinkayi muryan gwaggon nasu na cewa....

"Sumumu kasau, rasa kunya ɓeran tanka...."

 Tasan da ita take amma se komai bata sake ce mata ba ta nufa Dakin Shareefah bayan ta sauƙe wata ƙaƙkafar ajiyar zuciya, kafin a hankali 

 kuma wasu abu me kana da siraran hawaye masu sanyi taji suna zubowa daga cikin idanunta, tana tunowa da Mahaifiyarsu, Ammeyn su mutum me nagarta da sanin ya kamata, da haka ta koma ɗakin nasu  ta kwanta wani abu me kama da kewa na taso mata irin na uwar da aka rasa mahaifiya kuma jigon rayuwarsu.....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215 

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post