Kallon Kitse Complete Hausa Novel

Kallon Kitse Complete Hausa Novel

Cikin kuka take, ta cire gilashin idonta, ta kalle shi kai tsaye ta ce,

“Abban Bilal, me na yi maka? Wane laifi na aikata har za ka hukunta ni da kawo min kishiya? Abban Bilal, ni dai ina sonka ne kawai, ko ba haka ba? Me nake bukatar yi har ka sake aure a wannan lokaci? Shekaru goma sha uku ina tare da kai… me ya sa yanzu? Me ya sa za ka sake aure?..”

Ya riga ya fahimci abin da za ta ce, sai ya hanzarta rufe mata baki, ya rungume ta ya jingina kanta a kirjinsa, yana shafa bayanta cikin sanyin murya ya ce,

“Ke Momyn Bilal, me ya sa kika bar kanki haka? Shin kin riga kin yanke hukunci a zuciyarki ne ba tare da kin ji ta bakin nawa ba? Shin na taba gaya miki cewa na daina sonki ne? Ko na taba ce miki zan sake aure? Don Allah ki kwantar da hankalinki ki saurare ni, ta haka ne kawai za ki gane gaskiyar da ke zuciyata.”

Ta zame jikinta daga jikinsa, ta ce da murya mai cike da takaici,

“Na gane? Wace irin fahimta kake nufi? Wacce fahimta zan sake yi bayan ka riga ka rusa wacce na yi maka tsawon lokaci? Abban Bilal, wallahi ba zan sake sauraron ka ba. Ka cutar da ni, ka yaudare ni. Tsawon shekaru ina rayuwa cikin yaudararka… kullum kana gaya min cewa ni kadai kake so, ba ka da burin sake aure a rayuwarka, ba ka da wani dalili na yin hakan. Amma yau kai ne kake gaya min za ka sake aure!

Hakika yau na gaskata cewa namiji ba abin jingina ba ne. Duk macen da ta dogara da namiji tamkar ginshiƙi, to lallai za ta tashi a rana ta ga kanta cikin rashin gata. Yanzu na ga gaskiya da idona.”

Sauke Labule Complete Hausa Novel PDF

Danna maballin da ke ƙasa domin sauke littafin kai tsaye daga Google Drive:

Read Now

Audio by Abokiyar Hira

Download Now

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post