https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
1 / 04 /2026
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM?mode=gi_t
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
TUNATARWA!
Rayuwa ba ta tsaya ga wanda yake jin daɗi kawai ba wani lokaci jarabawa ce ke koya mana darasi.
Rayuwa tamkar hanya ce mai lanƙwasa wanda ya yi tafiya da gaskiya, ko da ya yi jinkiri, zai isa, amma wanda ya yi tafiya da ƙarya, ko da ya yi gudu, wata rana zai fāɗi.
Kamar yadda rana ke fāɗuwa bayan ta fito, haka farin ciki da baƙin ciki ke juyawa a rayuwa.
To idan mutum ya manta da gaskiya saboda duniya, me zai amfane shi idan ranar sakamako ta zo? mu gyara ayyukanmu tun kafin lokaci ya kure.
TSOKACI
Rayuwa tamkar gona ce; abin da mutum ya shuka shi zai girba, wanda ya shuka mugunta, kada ya yi mamakin girbin nadama.
Giya da sha’awa suna ɗaukar mutum kamar iska mai ƙarfi, suna rufe masa idanu har ya manta da darajar rayuwa da mutuncin wasu. A lokacin da yake wasa da lokaci da dukiya, yana ganin duniya tamkar wasa ce. Amma wata rana sai ya farka ya tarar cewa abin da ya ɗauka wasa ne ya zama bala’i.
Sau da yawa mace marar laifi ce ke ɗaukar nauyin kuskuren namiji. Ita ce ke shan ƙunci, ita ce ke ɗaukar ciki, ita ce ke fuskantar zargin duniya, alhali laifin ba nata kaɗai ba ne.
Hakika, duk wanda ya lalata rayuwar wani saboda son zuciya, to lokaci zai zo da zai nuna masa cewa nadama ba ta dawo da abin da aka riga aka lalata.
Don haka mai hankali ya koyi darasi tun kafin lokaci ya kure, domin kuskure na ɗan lokaci kan iya zama hawaye na tsawon rayuwa.
AFNAN KINAN
PG 1
SUDAN
ATLAS KINGS vs SAHARA UNITED
Filin wasan Khartoum National Stadium ya cika ya tumbatsa kamar teku lokacin da iska ta taso mutane sun zo daga kowane lungu na duniya, tutoci suna girgiza a sama, karar bushe-bushe da ihu suna gaurayawa da kiɗa. sunan Atlas Kings FC na yawo a bakin kowa kamar wata waka da ba ta ƙarewa.
“AT-LAS! AT-LAS! AT-LAS!”
A irin wannan rana ne mutum ke gane cewa ɗaukaka ba ta zuwa a banza, duk wanda ya hau saman tauraro, dole ya taɓa duhun dare kafin hasken safiya.
A ɗaya gefen filin kuma, ‘yan Sahara United suna shirin shiga. Fuskokinsu cike da jarumta, amma kowa ya san dalilin da ya sa filin ya cika yau…
NADIR.
Lokacin da ya fito daga tunnel ɗin ‘yan wasa, sanye da jersey ja da zinariya na Atlas Kings, jikinsa mai ƙarfi ya haskaka ƙarƙashin fitilu. Fatar sa mai kama da chocolate, gashin kansa baƙi an gyara shi cikin tsari na zamani. Sajen da ya tara a jikinsa da kuma a gefen fuskarsa suna ƙara masa kwarjini.
Idanunsa masu nutsuwa amma cike da ƙarfin zuciya sun nuna cewa wannan ba sabon wuri ba ne a gare shi. Duk da shahararsa, bai haura shekaru talatin ba.
Nan take filin ya fashe da ihu.
“NADIIIRRR!!!”
“KING OF ATLAS!!!”
Ya ci gaba da tafiya a hankali, ba tare da hayaniya ba, kamar wanda ya saba da ɗaukaka. Ya ɗaure takalminsa, ya murza wuyan hannunsa kaɗan, numfashinsa a daidaitacce, agare shi, wannan wasa ba wasa ba ne.
Ƙaddara ce.
Alƙalin wasa ya busa ƙaho.
Ƙwallo ta motsa.
Nadir ya karɓi ƙwallo a tsakiyar fili. Da sauri ya juya ya wuce ɗaya… biyu… uku! masu kallo suka miƙe tsaye.
Ƙwallon tana manne da ƙafarsa kamar an ɗaure ta da sihiri. ‘Yan Sahara United suna binsa amma ba sa iya kamawa. Ya ɗaga kai ya hango raga…
BUGU!
Ƙwallon ta tashi sama ta shige kusurwar raga.
GOOOAAALLL!!!
Filin ya girgiza. Mutane suna tsalle suna ihu suna rungumar juna. Sunan NADIR ya cika sararin samaniya kamar karar guguwa.
Amma shi…
ya tsaya kawai ya ɗaga hannunsa sama. Ya kalli sama na daƙiƙa guda, kamar wanda yake tuna cewa duk ɗaukakar duniya tana da asali daga sama.
Bai san cewa a wani ɓangare na duniya ba,
akwai yarinya mai suna AFNAN…
Yarinya wacce zuciyarta ta ƙi ƙwallon ƙafa ƙin da ya fi ƙiyayya tsanani.
@@@@@@ MARROCO @@@@@@@@
Oga Salman ya fito daga ofishinsa yana rike da remote, fuskar sa cike da muhimmanci da jin daɗi Ya kunna babban TV da ke tsakiyar hall ɗin Company su ya ce da murya mai ƙarfi a duniya akwai abubuwan da suke tara mutane kamar zuma ke tara ƙudan zuma. Ƙwallon ƙafa na ɗaya daga cikinsu.
“كلكم تعالوا… شاهدوا المباراة جيداً! سأسألكم عنها بعد قليل!”
(Dukanku ku zo… ku kalli wasan nan da kyau! Zan tambaye ku daga baya!)
Nan take ma’aikatan company suka taru a gaban TV. Wasu tsaye, wasu zaune a gefe, wasu na riƙe tray na abinci amma idonsu a allo sai hayaniya ta tashi.
“نــادر! نــادر! هيااا!”
“نــادر! نــادر! لنذهب!”
Hall ɗin ya cika da ihu, tafawa, tsalle.
Wasu suna rawar murna kamar suna filin wasa da kansu.
AFNAN ta tsaya a bayan layi, tray ɗin ruwa a hannunta. Fuskar ta a dunkule ta tsani ƙwallon ƙafa charff a ganinta, wasa ne na hayaniya da ɓata lokaci , banda hauka ya zaka hurga abu kuma ka bishi da gudu, ta juyo kaɗan kamar za ta tafi sai a allo ta hango shi.
NADIR.
Yadda ya karɓi ƙwallo, yadda ya yi tsalle, yadda jikinsa ya motsa cikin sauri da ƙarfi mutane a hall suka yi ihu.
“وووففف!”
NADIR ya wuce ‘yan wasa biyu, ya ja ƙwallo da ƙafarsa, ya yi tsalle, ya bugi ƙwallon da kai—
GOOOAAALL!!!
Allon ya nuna sakamako:
ATLAS KINGS 3 — 1 SAHARA UNITED
Hall ɗin ya fashe.
Wasu suna tsalle, wasu suna dariya, wasu suna bugun tebur Oga Salman ya yi murmushi, ya ce:
“هذا هو اللاعب الحقيقي!”
(Wannan shi ne ɗan wasa na gaske!)
AFNAN kuwa ta tsaya cak, numfashi ta ya dauke na wasu daƙiƙai ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ɗan buga ba ta san dalilin da ya sa idonta bai iya barin allon ba.
Ta haɗiye yawu a hankali, ta ce a ranta:
“Ina tsanar ƙwallon ƙafa…”
“…amma wani Irrin wasa ne wanan yayi kamar tsafi ?”
ba ta sani ba a wannan lokaci cewa
NADIR, wanda duniya ke kira da suna,
shine ƙaddarar da zata shigo rayuwarta ba tare da izini ba.
Oga Salman ya rage ƙarar TV, ya tsaya a tsakiyar hall ɗin hotel kamar wanda zai faɗi babban sirri. Murmushinsa ya ƙara faɗi, ya ce:
“طيب… عندي لكم بشرى.”
(To… ina da albishir a gare ku.) hayaniya ta lafa nan take.
“تيم ATLAS KINGS سيأتي إلى المغرب…”
(Tawagar ATLAS KINGS zata shigo Morocco…)Da ya faɗi hakan, zuciyoyi suka buga.
“…للعب مع فريق PHOENIX UNITED wani irin ihu ya tashi kamar filin wasa.
“…وقد وقعوا عقداً مع شركتنا.”
(Kuma sun yi kwangila da company ɗin mu.)
Oga Salman ya ɗaga yatsansa:
“الأسبوع القادم سيدخلون الفندق، وسأخرج قائمة بالموظفين الذين سيتولون خدمتهم من بينكم.”
(Mako mai zuwa zasu shigo hotel, zan fito da jerin ma’aikatan da zasu kula da tawagar daga cikinku.) Hall ɗin ya rikide.
Wasu suna cewa: “Insha Allah sunana zai fito!”
“Wallahi wannan dama ce na yawo da kula da babban tawagar ƴan ƙwallon duniya !”ana ta murna kamar an raba zinariya.
AFNAN kuwa ta tsaya shiru ta saki tsaki a ranta, ba tare da ta motsa ba “na san sunana ma ba zai fito ba a wannan haukar nan.”
Ta kalli rigarta mai zubin Pakistan wanda yasha omo da rana yayi haske daga jaa ya dawo ruwan ƙasa takalmanta da suka ɗan tsufa, sannan ta tuna da kalaman su ..
Ta juyo a hankali, ta ɗauki tray ɗinta, ta nufi hanyar fita, ta sanya uniform nata
A wannan lokaci aka buga bell ,alamar an tashi daga taro nan take kowa ya watse, kowa da burinsa, wasu suna tattauna yadda zasu burge Oga Salman wasu suna ambaton sunayen ‘yan wasa wasu har suna cewa:
“Idan na shiga jerin nan, rayuwata zata canza.”
AFNAN ta bi ta gefen bango tana tafiya, zuciyarta cike da tunani, ba tare da sanin cewa sunanta yana dab da fitowa cikin jerin da zai girgiza rayuwarta ba.
⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️
