🔥 HARGITSI Page 1 by Talatu Zaki - Abokiyar Hira Novels


🔥 HARGITSI

Writer ✍️ Talatu zaki

Phone number 📱📞 +20 103 1621512

https://chat.whatsapp.com/FByzaXABiRLEuU8KIyMJmq?mode=gi_t

Babi Na Daya (Page 1) 📚📖✨

"Afsal!"

Muryar mahaifiyarsa ce ta daki dodon kunnensa, cike da bacin rai da fushin da ta dade tana dannewa. Ta juyo tana kallonsa, idanunta cike da baccin rai:

"Lafiyar ka kuwa? HaÆ™urina ya riga ya Æ™are a kan wannan al'amarin! Wannan karon ma abin ya wuce yadda muke tunani. Yarinyar nan ba ta da uba balle asali, ga ta kurma, bugu da Æ™ari kuma tana fama da tabin hankali—amma duk da haka ka nace sai ka aure ta? Ba irin tashin hankalin da ba mu shiga ba domin mu hana ka. Daga Æ™arshe ka yi amfani da rauninmu na cewa kai kaÉ—ai ne É—a namiji tilo da Allah ya albarkace mu da shi a duniyar nan, har ka kai ga nasarar shawo kanmu muka amince ka aure ta."

Ta dakata tana sauke numfashi mai zafi, kafin ta ci gaba da magana kamar tana shirin shakarsa: "Yanzu kuma gashi ta zo haihuwa, Likita ya tabbatar mana cewa ta taɓa haihuwa har sau biyu ta hanyar fida (CS)! Wato kenan tana cikin halin haukan nata wani ya yi lalata da ita har ta yi ciki sau biyu ta haihu aka ɓoye mana? Da ba a ce tiyata za a mata yanzu ba, ta yaya za mu taɓa sanin wannan baƙar maganar?"

Hawaye ne suka fara wanke mata fuska, ta kalli danta cikin tsananin takaici tace: "Kai kuma na ga dukkan alamun abun ma ko a jikinka! Lallai kai sakarai ne marar cikakken hankali. Wannan ai ba so ba ne Afsal, hauka ne da rashin sanin ciwon kai! To ni dai babban burina a ciro min jikana da ke jikinta a ba ni, amma ko ita kaɗai ce mace a doron ƙasan nan, dole ka haƙura da ita bayan yau. Wannan wane irin bala'i ne!" Tana gama fadin haka ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta fada jikin mahaifinsa da ke tsaye gefenta.

Dattijon ya sanya hannu cikin sanyin jiki ya rungume ta, yana shafa bayanta a hankali domin rarrashinta, yayin da shima idanuwansa ke cike da damuwa.

Afsal da ke tsaye kusa da su, idanuwansa sun riga sun yi jawur kamar garwashin wuta. Yana matukar tausayin iyayensa, amma ya fi tausayin kansa; domin kuwa Eshal ita ce ruhinsa, ba zai taba iya rayuwa babu ita ba.

A karkashin zuciyarsa, shima tambayoyi ne suke ta yawo: Ta yaya hakan zata kasance? Eshal dinsa mai kama da tauraruwa ta taba haihuwa har sau biyu a baya? Ya sani ba a bola aka tsince ta ba balle ace 'yan iskan gari sun keta mata haddi kamar yadda ake yi wa wasu masu tabin hankali. Zuciyarsa ta rabe gida biyu.

Gashi suna cikin dakin gaggawa (Emergency), tana buƙatar kulawa ta musamman balle ya yi tunanin canza asibiti domin tantance gaskiyar maganar. Amma kuma ta yaya Dr. Raim zai masa ƙarya? Ɗan'uwansa ne na kusa kuma amininshi na gaskiya, wanda har ma zai auri ƙanwarsa Hiyaam. Babu wani likita a fadin asibitin nan da zai fada masa gaskiya tsakaninsa da Allah kamar Dr. Raim.

Tsawar da Gwogwgo Zainab ta daka masa ce ta katse masa dogon tunanin da ya tafi. Ta dube shi ranta a bace tace: "Afsal! Ko kai ma ka koma kurma ne kamar matartaka? Kana ji mahaifiyarka tana magana amma kayi mata banza?"

A hankali ya ɗago kumburarrun idanuwansa ya kalli mahaifiyarsa, cikin sanyin murya yace, "Kiyi haƙuri don Allah Mum, komai zai zo da sauƙi In sha Allah. Ubangiji dai ya sauke ta lafiya."

Gwogwgo Zainab tana shirin sake magana ke nan, sai ga kofa ta bude, Dr. Raim ya fito yana takawa cikin sassarfa. Afsal ya tare shi cikin tsananin fargaba yana fadin: "Raim, ina ruhina? Ya take? Hope ba ta ci gaba da shan wata wahalar ba ko? Ka fada min halin da take ciki don Allah!"

Dr. Raim ya dade da sanin irin mahaukacin son da Afsal yake yi wa Eshal, don haka bai yi mamakin jin kiran ta da yake yi da "ruhi" ba. Iyayensa ne kawai ba su san iyakaci da zurfin wannan soyayyar ba. Dr. Raim ya sani sarai cewa koda ace duka shegun duniya Eshal ta Haifa a baya, hakan ba zai taba rage digon kauna a zuciyar Afsal ba. Shi majanunin Eshal ne; ba ya ji, ba ya gani!

Dr. Raim ya ƙyaƙyalo murmushin kwantar da hankali yace, "Ina taya ka murna Dr. Afsal! Mun yi nasarar ciro kyakkyawar jaririyarku mace, kuma tana cikin ƙoshin lafiya..."

Tun kafin ma ya karasa bayanin, Afsal ya katse shi cikin sauri: "To ita ruhin tawa fa? Raim ka fada min halin da take ciki 

Dr. Raim yayi murmushi yace: "Alhamdulillah! Ita ma Allah ya ba mu nasarar aikin, an yi lafiya an ƙare lafiya. Yanzu haka ana kokarin karkare gyara jaririyar ne kafin a fito dasu gaba ɗaya."

Wani katon dutse ne ya fadi daga kirjin Afsal, wani sanyayyen farin ciki ya cika masa zuciya. Take ya kalli gabas, ya zube a kasa yana mai ruku'u da sujjada domin nuna tsantsar godiyarsa ga Ubangiji. Mahaifiyarsa da Gwogwgwo kuwa mamaki ne ya cika su. Ta yaya za a ce matar taka tana da tarihin yin cikin shege har sau biyu kafin ku hadu, amma kai ko a jikinka sai ma godiyar Allah kake yi?

Dattijon dake rike da mahaifiyarsa tun dazu, a hankali ya maida dubansa ga Dr. Raim cikin girmamawa yace: "Godiya muke yi Raim. Na baka kyautar mota, duk lokacin da ka samu sarari kaje kamfanina ka zabi duk wacce kake so. Ka yi kokari yarona."

Dr. Raim ya san cewa Daddy yana fadin haka ne kawai domin danne bacin ransa, amma dole su yi murna da zuwan jinin su duniya tunda Afsal shine farin cikin gidan. Likitan yayi godiya sosai sannan ya juya ya koma ciki.

Jim kadan, sai ga wata Nurse ta fito dauke da jaririya a nannade cikin kyalle mai laushi. Ta karaso kusa da su tace, "Dr. Afsal, ga Baby din ku."

Afsal ya mika hannu tare da karbar abin alfarmarsa. Yana kallon fuskar jaririyar, hawayen dadi suka fara zubar masa. Kaf kamanninta irin na mamanta ne; kyakkyawar fuska mai dauke da kwarjini. Gashin kanta ne kawai bai yi jawur (blonde) ba kamar na uwar, launin sa ruwan kasa ne (brown). Amma idanuwanta da fatarta duka sun tafi ne a kan na baturiya uwar tata!

Ya matse ta a kirjinsa yana kuka yace: "Barka da zuwa duniya raina! Daddy zai soki har numfashinsa na karshe. Wannan alkawari ne na har abada."

Ganin haka, sai jikin Daddy yayi sanyi domin ya fahimci cewa dansa ya riga ya zurfafa a soyayya. Ya bude baki a hankali yace: "Afsal, ka ba mu jaririyar mu gani man. Muna farin ciki da zuwanta. My love, zo kiga jinin mu kema. Yaya Zainab ku zo."

Cikin sauri suka matsa kusa da Daddy. Afsal ya mika masa jaririyar, Daddy ya karba yana murmushi yace: "Masha Allah dana! Eshal ta fimu karfin jini, komai na yarinyar nan nata ne. Allah ya mata albarka." Sannan ya mika ta ga mahaifiyar Afsal.

Mahaifiyar ta karba tana karkarwa. Ta so a ce yarinyar tana kama da danta Afsal, amma tana sanya mata ido, sai taji wata muguwar kauna ta kamata, irin wacce take yi wa Afsal dinta.

Gwogwgwo Zainab ta mika hannu tana dariya tace, "Kawo min ita inga jinin mu Hajia Aisha." Tana karba tana duddubawa tare da murnar da ta sanya ta manta da kicin-kicin din da tayi dazu. "Masha Allah! Alh. Ibrahim kalli fa, komai na uwar ta dauko, bata biyo jinin Fulanin mu ba ko kadan. Amma komai dai muna son abun mu. Allah ya raya ta."

Afsal yana gefe yana kallonsu kawai. Duk da bacin ran da suke nuna wa uwar, amma hakan bai hana su nuna kauna ga jinin su ba. Ya san dole su sota, domin danginsu basa wasa da jini.

Uwar ce dai suke da matsala da ita, kuma ya fahimce su. Mahaifinsa mai hakuri ne, amma mahaifiyarsa da Gwogwgwo sune masu zafi. Amma duk da haka, ya rantse a ransa cewa babu mai iya raba shi da Eshal dinsa sai Allah. Yana da burin sanin ko wacece ita a can baya, amma ko ma meye tarihin nata, ba zai taba canza masa alkibla ba. Domin a wurinta ne kadai ya san meye ma'anar so, kuma itace ta bashi kyautar babban burinsa a rayuwa!

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post