*MATAR DAMISA*
Page 11
Kwance take a saman gadon asibiti tana ta sumbatu "Uma! Uma!! Uma dan Allah karki mutu ki barni, Dan Allah Uma ki dawo gareni" tana cikin wannan yanayin hankalinta ya fara dawowa jikinta, ido ta fara bud'ewa a hankali tana ganin Dishi-dishi har idon ya washe
Wata farar Mata ta gani gefen ta tana zaune ta zuba mata ido sai kyakykyawar murmushi dake kwance a saman fuskarta
Tashi ta fara 'ka'karin yi, sai ji tayi matar tace "Sannu ko, ya jikin nakin?"
Tana shirin gyara mata zaman.
Juyowa Ayush tayi tana kallon matar daga bisani tace "Ina Mamana?"
Shafa sumar kanta matar tayi sannan tace "Am sorry my dear, ke kad'ai aka kawo asibitin nan, but mutanen da suka kawo ki sunce already sun sallace Mahaifiyarki bayan sun tabbatar da ta rasu, we lost your mom"
Fashewa tayi da wani matsanancin kuka tana fad'in "shikenam kin tafi kin barni Uma, Ina Zansa rayuwata, bazan iya rayuwa ba tare dake ba Uma, bani da kowa innalillahi wa inna'ilaihi raju'un" kuka ne yaci raanta sosai.
Rarrashinta Matar take tana bata baki, da haka har Ayush ta samu da dawo hayyacinta, ajiyar zuciya ta shiga ja.
Murya a sanyaye Matar take fad'in "Allah yana tare da ke, insha Allahu bazaki tozarta ba"
Ayush murya Ciki-ciki tace "banida kowa sai Uma na, yanzu Ina zansa kaina"
Ajiyar zuciya Matar tayi ta jawo Ayush jikinta tana shafa bayanta alamar rarrashi sannan tace "meye sunanki?"
"Sunana Ayushert" atakaice ta bada amsa!
"Shin zaki iya zama a tare da ni?" A cewar matar.
Ɗagowa Ayush tayi ta ƙurawa matar ido daga bisani ta mayar da kanta saman jikin matar, batace komai ba.
Matar ce ta sake yin magana tace " no karki damu insha Allah zan riƙeki tamkar mahaifiyarki, ni sunana *DOCTOR* *FATEEMAH* wannan asibitin da kike gani it's my own, inaso ki kwantar da hankalinki, zaki cigaba da zama dani a gidana". Kafin ta rufe baki taji wayarta tana ringing, ɗaukar wayar tayi tare da karawa a kunnenta, ji tayi ance "HAJIYA KI DAWO GIDA YANZU AKWAI MATSALA..." daga nan aka katse wayar!
"Ikon Allah meke faruwa ne, kinga Ayush ki jirani Ina zuwa yanzu" ta shafa sumar kan Ayush tare da ɗaukar hand-bag ɗinta tana tafiya cikin tsari duk da tana haɗawa da Sauri-sauri sai takun takalminta kake ji qwas qwas qwasss, danƙararren less ne a jikinta tasha ɗinkin Riga da zani sai gyalen data yafa, ko Ina sai ƙamshin turare jikin ta yake, asalin ƴar washh ce,
Ayush kallon ta take ba ƙaramin burgeta Doctor Fatima tayi ba, har sai data ƙule mata kafin da dawo da kallon ta kan ledar ruwan da aka ɗaura mata.
*****
Da gudun gaske Doctor Fatima ta shige harabar gidanta da danƙararren motor ta black colour mai taya ta baya..
Ƴan Sanda ta gani su uku sunyi cirko-cirko suna jiran isowarta already mai gadi ya basu damar shugowa cikin gidan, cikin tashin hankali ta nufi gurinsu tana faɗin "lafiya kuwa na ganku a cikin wannan yanayin?" Ta 'karasa maganar tana kallon Ogan nasu.
Ogan ne ya bada umarni cewa "a fito da shi"
Doctor Fatima ce ta maida kallon ta kan Wanda za'a fito dashi daga cikin motor,
Lokaci guda ta furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un *JUNAID* , maiya faru da shi? ya naga jini a saman kansa? mai kuka mishi? Wayyo Allah na Junaid, Allah yasa dai ba ciwon naka bane ya tashi" tana zubda hawaye haɗe da sambatu.
Wani daga cikin ƴan sanda ne yace "Hajiya waɗannan tambayoyin nakin bazasu amsu ba anam sai mun shiga daga ciki tukun"
A gigice Doctor tace "to to toh mu je mana jini yanata zuba masa"
Ayush kuwa dake kwance saman gadon asibiti ta ƙudurta a raanta cewa duk Wanda yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyarta sai ta ɗauki fansa,
Jinin mahaifiyata bazai zuba a banza ba.....
*ASMEETAH WRITER* ✍️✍️
