Matar Taj Page 1&2 Complete - Abokiyar Hira Novels

Matar Taj

MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍) 

❤️‍🔥Romantic love story❤️‍🔥

     Written by QueenMarh  

Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai.

Alhamdulillah Alhamdulillah….my previous book was a great journey to endeavor… Ina godiya ga Allah daya bani ikon dawowa da sabon littafina mai suna MATAR TAJ, ina mai rokon Allah ya bani ikon kammalawa Ameen.

Special appreciation to my loyal AKK fans, and my supporters i can’t be bold enough without you guys😘

Boss bature

M shakur

Thank you guys for your endless help and support❤️

Special thanks to My arewa book readers, thank you for sticking around (Halima arewabook)😆 i’m sorry for saving your contact as halima arewabook but this lady right here is a great person, (my Siyam, aisha , susu, my nanasko, my ruks and aysha) and my vvips thank you for supporting me and the words of encouragement guys, mummy ammi na❤️❤️❤️ ban manta dake ba I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.

The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃

 

Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba. 

Enjoy!!!!!

 

 

Free page

Chapter 1-2

 

Wata katuwar bus ce mai dauke da mutane ta shigo harabar jirgin sama dake garin abuja.

Matuqin motar ne ya taka burki da karfi wanda yasa mutanen cikin bus din doka salati. ‘’haba malam ka dunga bi ahankali mana, rayuka fa ka kwaso ba dabbobi ba, wannan tukin gangancin bashi da wani amfani’’ daya daga cinkin matan dake zaune tayi Magana.

 

A zafafe matuqin ya juyo, bakinshi har yana kunfar masifa ya soma Magana ‘’malama dan allah ku min uzuri haka nake tukina, in badan nayi sauri ba ay da kun rasa jirgin naku’’

Shuru matar tayi don da gani drivern bazaiyi mutunci ba, shiko yana bata amsa ya juya wajen wanda ya shawo gabanshi.

Cikin masifa irin tasu ta yan tasha ya soma zagin matuqin motar kafin ya juya ya soma neman wajen parking.

 

 

‘’wash allah na’’  budurwa dake zaune chan saqon acikin bus din ta dago kanta data chusa tsakanin gwiwoyinta saboda burkin da drivern bus din ya taka, wanda yayi daidai da buga kanta datayi da karfen bayan kujerar dake gabanta, sanye take da koren hijab kamar kowa dake cikin bus din sai face mask data saka a fuskan nata..

 

Bazan iya tatance tsarin hallittar fuskarta ba saboda mask din saidai kwayar idanunta data bude su da sukayi jaa sosai suna da masifar daukan hankali don kwayar cikin idanun nata yana da haske kamar gajimare, irin su ne ake kira da hazel eyes.

 

Tana da cikar gira wanda ya tabbatar min zata yi suman kai sosai, matar dake gefenta sai kallonta takeyi tana mamakin kukan data dunga yi tun shugowarsu cikin bus din.

Allah kadai yasan meke cikin zuciyar yarinyar saboda yanda take kukan kasa kasa kamar ranta zai fita.

 

Zuciyarta ta zama kamar dutse tayi mata nauyi, rayuwarta ta kara dusashewa, emotions dinta baya responding komai saboda yanda takeji a cikin zuciyarta.

Idan ta tuna da wasu abubuwa saitaji hawayen dake saukowa daga idanunta sun kasa tsagaitawa, babu abunda takeyi ayanxu sai tausayin kanta, karfin imanin da take dashi ne kawai ke sata hadiye duk wani kunci dake danqare a bangon zuciyarta.

Ku Karanta Wannan littafin

  1. Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 89 Complete
  2. Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 90 Complete
  3. Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 91 Complete

 

Tambayoyin da take ma kanta tsakanin jiya da yau suna da yawa sosai gashi kuma babu wanda zai bata amsa, abunda yafi tsaya mata arai shine kodai tana da wani aibu ne? to kodai ita yar tsintuwa ce? haka ta dunga tambayar kanta countless of times, saidai sanin cewa bata san menene enci ba yasa ta zama confuse akan abubuwan da suke faruwa a rayuwarta ayanxu da shekarun baya ma lokacin data fara mallakar hankalinta.

 

 

Driver nayin parking ya fito tare da bude kofofin bus din, daya bayan daya, mazan cikin bus din suka fara sauko kafin matan, kowannensu tana sanye da koren hijabi kamar uniform, da jakar goyo a bayansu, yanda suke futowa ajere kamar bazasu kare ba don sunkai su kusan goma sha biyar.

 

Layi sukayi a jere kowacce idanunta zuru zuru, yan matan duk sunfi yawa don zasu kai wajen su goma sannan kana ganin wasun su zaka san daga kauye aka kwaso su, sai wasu manyan mata da bazasu wuce su uku ba sai maza biyar.

 

Yanda sukayi layi ya bama daya daga cikin mazan damar soma Magana kamar haka ‘’yauwa masha allahu, zan baku passport dinku yanxu, kamar yanda nasha fada maku, wannan passport din shine ticket dinku a ko’ina, idan har kuka batar kuyi kuka da kanku ba wannan agency din ba, sannan jirginku zai sauka a jidda, duk wadda ta gudu daga nan idan aka kamata kartayi tunanin agency zata dauki nauyin consequences din laifukanta don komai a rubuce yake,’’

 

Yana kaiwa karshe ya fiddo da passport dinsu kowacce da ticket dinta, daya bayan daya ya soma kiran sunayen su yana basu.

 

‘’sabeeha dalhatu, wacece sabeeha dalhatu’’ jin shuru ya sashi doka tsaki har zai wuce sunan yarinyar ta daga hannunta ‘muryarta na seizing tace

‘’ni.. ce’’

Kallonta yayi daga sama har qasa kana ganinta kasan a tsorace take da al’amarin, ‘’malama kinaji ina kiran sunanki kinyi shuru baki san sauri muke ba’’

Saurin sauke kanta tayi tana rarraba idanuwa saboda tsoro, kafin ta nufi inda yake ta karba passport din, kallon hannunta yayi da yake kyarma zufa ta gama wanke hannun, ganin hakan ya sashi cewa ‘’wannan kuma ko daga wani kauyen aka dauko ta oho kibi a hankali dai kar ki jawo ma kanki a kamaki’’

 

Jin abunda yace yasa cikin ta yin wani irin qugi har saida gabanta ya fadi da furucin shi, ayanxun ne ta kara tabbatar da rayuwar kuma bata da wani sauran amfani.

Yau ga mahaifiyarta wadda ta tsugunna ta haifeta wadda duk duniya bata da kowa sama da ita ta saidata,don kwata kwata batasan dalilin hado ta da mutanen nan da mahaifiyarta tayi ba, ta tashi ne kawai da asuba tana shirin hada masu abunci Karin kumallo wanda kawu zaikai  asibiti don duk suna asibiti saboda kwantar da inna da akayi, ita ke zaune a gida don ko zuren gidan bata futa, wata uku kenan rabonta data taka kofar gidan saboda wani dalilin mamanta da bata sani ba, innalillahi ta soma furtawa idanunta na kawo ruwa.

*

Mutumin ne ya jagorancesu zuwa cikin airport din, suna biye dashi, saida akayi checking dinsu daya bayan daya kafin su shiga wajen waiting room don jirgin nasu na gab da tashi.

 

Yarinyar nan dai tana biye da kungiyar tasu da suka taho tare, bata yarda sun daukema ganinta ba har suka zazzauna a waiting room na lower economy.

Gefenta kuwa matar nan ce wadda suka zauna kusa da juna a cikin bus.

Miqewa matar tayi ta sayo meat pie da ruwa kafin ta dawo, gaba daya mutanen wajen binta suke da kallo musamman yan matan nan, don kana ganinta kasan ta san yanda yanayin wajen yake don hidimarta take hankali kwance, ita kuwa daman ba wannan ne zuwan ta na farko ba, tasha zuwa saudiyya aikatau, tun tana kamar su .

 

Matar tasha adan bula a fuskanta inda tayi bular hanci har guda biyu ga hakoran Makkah data saka a hakoranta har kusan guda hudu.

 

Kana ganinta kaga asalin takarin saudiyya wanda idanunsu ya bude sosai.

 

Zama tayi kusa da yarinyar nan inda yarinyar ta hade jikinta waje guda saboda fargaba, gashi bata iya communicating da mutane ba don kwata kwata tun tasowarta ba a bata damar mu’amala da mutane ba, daga mamanta sai innarta da kawu shikenan, gaba daya rayuwar ta is just around them su uku.

 

Meat pie dinta ta fara ci hankali kwance ta kora da ruwa, saida ta cinye tas ta ajiye dayan daman guda biyu ta sayo, kallon gefen yarinyar tayi, haka kawai taji yarinyar ta bata tausayi, don itama lokacin da aka tura ta aiki lokacin bata wuce shekarunta ba, ita tundaga kauyen gezawa dake garin kano aka daukota aka kawota saboda talauci.

 

Kallon meat pie din da matar ke miqo mata yarinyar tayi kafin

‘’karbi mana’’ matar ta fada tana mai sake miqa mata.

Hannu biyu yarinyar ta saka ta karba, har lokacin hannunta karkarwa yake saboda tsoro, sai alokacin ta bude baki tace ‘’nago..de’’

 

Murmushi matar tayi mata tana mai kokarin tura sauran yan chanji ta cikin Jakarta ‘’sunanki sabeeha ko? Kema aiki zakije yi?’’

 

Dago da jajayen idanunta tayi ta kalli matar don bata ma san taqamaiman dalilin kawo ta nan da akayi ba, kawai dai ta amsa ta da ‘’eh’’,  

Wata tambayar ta sake jefo mata ‘’wannan agency dinne suka dauke ki?’’

 

A tsorace dai yarinyar take amsa matar, da eh, gaba daya ma she’s confuse ita kuwa matar babu abunda take mata sai murmushi kafin tace ‘’ki cire tsoro kinji, wannan tsoron zai iya jawo maki matsala, don mutanen kasar basu da yarda musamman idan sukaga mutun baki ne,’’

‘’toh nagode’’ yarinyar ta amsata sai alokcin ta danji dama dama datayi Magana da matar.

 

Meat pie din ta soma turawa a bakinta badan dadi take ci ba sai don yunwar dake nuqurqusarta daman bataci komai ba don bata gama sauke tukunyar dumamen data daura masu ba mama ta tasota gaba tun da asuba, babu ko tausayawa.

Suna nan zaune aka kira jirginsu, gaba daya suka mike suka shiga cikin jirgi,jirgin nasu dan karami ne bashi da wani girma sosai, daga gani dai irin kananun jiragen nan ne waenda kudadensu ke da sauqi.

 

Koda suka shiga da taimakon matar nan ta samu wajen zamanta, cikinta ya gama durar ruwa sosai, sai a lokacin ta tabbatar wata duniyar za a kaita, inda bata san kowa ba batasan me zata tarar achan ba, karshen zance ma bata san me zai kaita chan ba.

 

 

*

**Saudi Arabia Tahlia street**

Tahlia district na cikin garin jedda a kasar saudia, wannan anguwa ta kasance anguwace ta wane da wane manya manya masu kudin dake kasar saudia masu mulki da masu mukami, yawanci da kaji an anbaci tahlia street to ana nufin zuciyar jedda don shine top wealthiest district a kasar saudi arabia.

Duk wani mazaunin wajen yana ji da kudi da arziki tun lokacin da aka kafa ma anguwar tambarin zuciyar jedda don ba kowa ke iya zama anan ba, gashi gaba daya anguwar ansan juna don yawanci manyan masu kudi da suka zauna a anguwar bayan sun mutu yayansu ne suke gadar wajen don zama a anguwar babban assets ne.

 

Tahlia district kamar gari guda take don babu abunda babu a cikin district din, daga kan manya manyan branded shopping malls zuwa ga manyan companys da top class hotels da restaurant wanda yawanci na mazauna wajen ne, don kamar competition sukeyi tsakanin junan su.

 

TAHEEL Groups.

Taheel groups yana daya daga cikin manyan companies dake cikin tahlia district, an kafa taheel group tun shekaru da suka shude wanda ayanxu yayan masu shares din company din ne suke running companyn.

Major holders na group din taheel group sune the taheel family,don mahaifinsu (Taheel Abdullah Tajuddeen) shine founder na TG wato taheel group,kuma suke da 75% share na company din.

 

Taheel groups suke providing gaba daya malls dake cikin tahlia district harma da wasu garuruwan daban a cikin kasar saudi kamar su riyadh da Dammam, suna da collaboration da manyan manyan shop irinsu Gucci, dolce gabbana, ralph lauren, Giorgio Amani da dai sauransu inda suke sayan product dinsu harda tag dinsu su kuma saisu saka masu a shopping mall market dinsu, bayan wannan sune masu babban bankin da ya zamanto yana cikin top 5 best banking service (TG BANKS).

 

The Taheels Residence…….

Wani tamfatsetsen modern gida ne a cikin tahlia street, gidan ya gaji da haduwa gashi da dan banzan girma sosai don zaikai gidaje biyu da suke jere a street din don kamarma yafi sauran gidajen kyau da haduwa, daga wajen gate din farko ma abun kallo ne don an qawatashi da karafuna mai adon royal gold dogaye duk sun zagaye da gidan.

Street din,kwata kwata babu hayaniya kamar babu mutane, ko’ina tsaf tsaf so organised, babu karikicen gidaje masu hayani, kowane gida is bulid with luxury and class don dole arziki yayi kuka a wajen nan don an kashe kudi sosai.

Tsirarrun jigaggun motoci ne ke shige da fuce a street din inda Wata mota mai nunfashi kirar audi r8 baka wuluk ta shigo street din, bata tsaya ko’ina ba sai gaban taheel residence, motar ta dan dauki minti biyu kafin electric gate din ya fara sliding ba tare da an taba shi ba, gate din na wangalewa motar ta kutsa cikin gidan, haka motar ta mike babban compound din dayasha duwatsu farare tass sai bishiyoyi daga gefe koraye tarr, matuqin bai tsaya ko’ina ba wajen parking lots inda motoci ke jere kusan guda goma, brands daban daban abun dai ba a cewa komai, wajen parking dinma abun kallo ne.

 

An dauka kusan minti biyar kafin a bude kofar motar, kafarsa ya fara fiddowa wandda ke cikin wani loafters cover shoe baki kafin ya fito gaba daya, kyakyawan magidanci ne fari tass, yana da farin saje wanda ya fidda girmansa da haibarsa, sanye yake da suit baki wanda tayi mashi kyau sosai, idanunshi na cikin wani farin glass.

 

Rufe motar yayi kafin ya nufi hanyar shiga cikin gidan, anatse yake tafiya har yazo gaban wata katuwar security door mai kalar gold, kamar an kerata da gold.

 

Door bell ya danna anatse kafin ya dan jinkirta for a second.

Karar door creak dayaji ne yasa ya sanya hannu ya tura kofar…

Maids din dake ta faman shige da fuce suna hidima a sitting room dinne suka soma gaishesa sanin koshi waye, hannu kawai ya iya daga masu kafin ya wuce sitting room din baqi inda shine face of the house don nan ne babban parlorn gidan, gida dai ya tsaru karshe haduwa basai na tsaya baku rahoto ba, abunda zan iya cewa kawai shine gidan nan aljannar duniya ne, komai na daban ne a cikin gidan don an narkar da kudade masu daraja anan..

 

 

*

Bude kofar dakinta da akayi ne yasa ta dagowa don ganin wanda zai shigo mata daki kai tsaye haka.

Wani irin kallo ta watsa ma wadda ta shugo bedroom din tayi kafin ta danyi tsuka ta maida hankalinta kan wayarta kirar latest Samsung ultra,kwance take kan wani makeken gado na alfarma dayasha beddings mai kyan gaske cikin wani kayataccen daki daya sha kayan alatu, hannayenta duka biyu data rike wayar tata yasha manya manyan zobunan daham da awarwaro gefenta kuwa surface laptop ne kalar wayar nata black color, farace saidai ba tass dinnan ba sannan siririya ce don bata da qiba kwata kwata amma akwai kyau masha allah, sanye take da wata baqar riga ta zaman gida.

 

For the second time ta sake dagowa ta kalli wadda ta shugo ganin ta tsaya bakin kofar kuma tayi shuru tana kallonta ‘’babu salam?’’

 

Rufo kofar wadda ta shigo tayi, itama kyakyawa ce ajin farko saidai ita tafi wanda ke kwance kan gadon haske sosai kuma suna kama sosai, hannunta na rike da hand dryer da alamu gyaran gashinta tayi daya sauko har wajen mazaunen ta yana sheki, gaba dayansu kana kallonsu kasan larabawa ne kuma jinin larabawan asali, ga hancin ga idanu kamar sun qera kansu.

 

Wadda ta shugo sai kamshin bakoor take,ita kuma tana sanye da riga da wando wanda suka dan kamata sai yar jellabiya data daura akai baqa kuma transparent, fuskanta adan hade ta karaso inda yar uwar tata take zaune kafin ta zauna gefen gado ta soma Magana cikin harshen larabci da turanci ‘’kedai wallahi idan kika maqale a daki bakyasa futowa kamar wadda ke boye boyen wani abu, marasa gaskia ne ke kulle kansu waje daya, ni bama wannan ba kinsan waye yazo kuwa fadwa?Guess who?’’

 

Wadda ta kira da fadwa bata dago ba hankalinta nakan wayar dake hannunta tace ‘’who?’’

‘’khaal’’( meaning uncle) yar uwar ta bata amsa

Cikin hanzari ta ajiye wayar tata ta zauna tana mai kallon ta tace ‘’khaal kuma afiya? meyazo yi kuma na dauka ay ya daina zuwa gidan nan tun bayan abunda ya faru last zuwan nashi?’’ fadwa ta tambayi yar uwar tata tana mai sauraronta don tasan ba haka kawai zaizo ba don it’s been a while rabonshi da yazo don kwata kwata zuwanshi rikici yake kawowa.

Kallonta wadda ta kira da afiya tayi kafin tace ‘’its obvious mana yazo duba wannan mara hankalin ne gashi ukty bata nan, hmm I don’t even know what’s going to happen today’’

Fadwa ce tayi saurin cewa ‘’uktyn bata dawo daga office din bane? Naga yanxu it’s almost 5?’’

‘’nop not yet but I’m sure zaman jiranta zaiyi,saita dawo tukunna ni karma ya fara min maganar aure cause….’’ Dan jinkirtawa tayi da Magana kafin ta tabe baki ta cigaba da cewa ‘’anyways muje dai kasan mu gaisa dashi muji dame yazo yau kuma, I don’t understand why he’s wasting his energy akan wanda baima san ina kanshi yake ba’’ tana kai aya ta mike tsaye ta nufi wajen dresser ta ajiye handryer din.

Afiya ce ta fara fita kafin fadwa tabiyo bayanta.


 *

Atare suka sauko daga stairs din mai shegen tsayi dayasha floor carpet, saida suka fito ne na masu kallo tass, gaskia suna da kyau, masha allah ga gashi tabarakallah,bazasu wuce shekaru from 31, 33 ba, kamannin su daya kana ganinsu kasan siblings ne, hannayensu dasuke rike da manya manyan wayoyi sanye da zobunan gold haka zalika kana ganinsu kasan kudi ya zauna a jikinsu saboda yanda skin dinsu ke sheqi, saidai kuma jikin ne dan kiff dan sirara ne basuda girman jiki.

Kwata kwata babu alamun girma na shekaru a tattare dasu saboda arziki ya danne tsufan sai ya zamana kamar yan 20s.

  

Yanda suke saukowa cikin aji kamar bazasu sauko ba, sama sama suke hira suna dariya, Wato gidan ma ya gama gajiya da haduwa, daga waje ma ba komai bane ba don saika shugo daga ciki zaka tabbatar da haka don yasha kayan alatu na zamani, duk inda suka gifta ma’aikata ne suna ta hidima kowannen su sanye da uniform daban daban, gidan dai kamar gidan sarauta don yana da girma sosai ga kofofi da yawa alamun parts parts ne.

Ko’wanne lungu da sako shaqe yake da kayan zamani, ga luxurious interiors ta ko’ina.

Hanyar second sitting dake cikin gidan suka fara wucewa kafin su karasa first sitting room wanda shine face of the house.

 

Da sallama suka shiga parlorn afiya na gaba fadwa na biye da ita abaya saboda tana receiving call din daya shugo mata saida suka zauna tayi sallama da wanda take wayan dashi inda tace ‘’bye qalb’’ kafin ta sauke wayan daga kunnenta.

 

Azaune suka taddashi idanunshi nakan news saidai kwata kwata hankalin shi ba’akan news din yake ba,babu abunda yake mashi yawo akai sai tunanin last zuwanshi da yayi cikin gidan, ba da karamin bacin rai yabar gidan ba saboda y’ay’an dan uwan nashi musamman hidaya, kwata kwata bata ganin girmashi, tafi karfinshi ma, don sai abunda tace za ayi, darajar alqawari da kuma mahaifinsu ne kawai ke sashi zuwa gidan badan haka ba da bazai sake saka kafafunshi cikin gidan ba, bayan wannan akoda yaushe idan ya zauna babu abunda yake dana sani akai sai tilasta dawowar taj da yayi, dukda ya yarda komai muqaddari ne daga allah saidai deep down yana regretting dawowarshi don shine ya tsaya tsayin daka akan dole saiya dawo, sai yake jin kamar ta dalilin nan ne abunda ya faru wata uku da suka wuce ya faru.’……

 

Muryoyin su da ya soma jiyowa ne ya sashi fargawa daga tunanin daya fada, duban tafkeken wall clock din da akayi ado dashi a parlon yayi, karfe 5 da rabi Kenan na yamma,

sallamarsu ya sanya shi dagowa ya kallesu daya bayan daya, zaman half an hour yayi a wajen sai aynxu suke saukowa, shidai yana mamaki hali irin nasu koda yake baa abun mamaki bane don yanxu kam ya saba da halayensu, .

 

kauda kanshi gefe yayi daga garesu ya maida kan tv, kowannen su sanye take da kayan zaman gida gashin nan a bude don ko rufewa basuyi ba,bayan wannan yasan su da practicing rayuwar turawa so su hakan ba komai ne a wajen su ba dukda shi dai hakan a wajenshi ba wayewa bace da girmansu kuma da shekarunsu, shigar fadwa ne ma yafi tsaya mashi arai don ita tana da aure ba kamar afiya ba amma idan ka gansu zaka dauka gaba dayan su basu da auren

.

Karasowa sukayi inda yake zaune dan nesa dashi, kan kujerun single chairs dake facing nashikafin su zauna, fadwa ne tayi saurin cewa ‘’marhaban khaal’’

Ba tare da ya kalleta ba fuskanshi adan hade yace ‘’shukran fadwa,’’

Afiya ce ta dan tabe baki don daman itace tafi rashin kunya kuma yawanci yafi sa ido akan ta musamman rashin auren da bata dashi.

‘’Marhaban khaal’’

‘’shukran’’ ya amsata kai tsaye ba tare da ya sake kallon inda suke ba.

 

Takun sahun kafafun da sukaji ne yasa duk suka dago, wani dan yaro ne ya shugo kyakyawan gaske bul bul dashi, bazai wuce 12years ba, yana sanye da kayan paw patrol sai wata yar cute jaka a bayanshi, hannunshi rike da pack of doritos chips da nintendo switch gaming pad, sai faman cin doritos din yake.

Cikin sitting room din ya karaso aguje yana washe hakora ‘’Jadd’’ (meaning grandpa)

Inda dattijon yake zaune yaron ya nufa cikin farin ciki da jin dadi, farin ciki ya gama lullubeshi,

 

Hannu dattijon ya bude mashi ya taho a guje ya shige jikinsa kafin ya rungumeshi shima dadi duk ya gama lullube shi sosai, ‘’Barad’’

Dattijon ya kira sunan yaron bayan ya fiddoshi daga kirjinshi, murmushi yaron ya soma mashi kafin ya soma gaishesa, kumatun shi dattijon ya kama irin yanda ya saba yi mashi koda yaushe‘’I missed this cute baby face’’

Turo baki yaron yayi kamar zaiyi kuka yace ‘’jadd I’m not a baby anymore, I’m turning 13 next month’’

Shafa kanshi dattijon yayi kafin ya sumbaci kumatunsa yace ‘’kaje school yau?’’

‘’yes jadd’’ yaron ya amsa dattijon.

 

 

Wani irin kamshi ne ya danno cikin parlorn mai tsada don lokaci guda ya bade parlor kamar anyi ruwan turare, takun tafiyar ta ne ya biyo baya ‘’qwas qwas qwas’’wanda yasa duk suka juyo suna kallonta banda dattijon da yayi mata kallo daya ya dauke fuska sai yanayin fuskanshi ya chanza gaba daya kamar bashine ya gama yima yaron nan dariya ba.

 

Nima dai kallota na soma yi, kasa dauke idanuna nayi akanta, wato wata irin classy matace a tsaye, daganin fuskanta kasan ta soma manyanta saidai tsufan ya boye sosai don kwata kwata bazaka iya tantance shekarunta ba dukda tana early 40s, farace tass kamar a bula fatarta jini ya futo,ya allahu, tana da kyau sosai don doguwace, sanye take da wata azababbiyar abaya baqa wadda ta haskata sosai tayi mata kyau don ta haska fuskanta data dan hade girar sama da kasa, gaba daya zubinta irin na matan nan ne da basa daukan nonsense, ga jii da kai da kudi da aji, waya ce kawai a hannunta kirar iphone 15 pro max latest, gefenta kuwa wata maid ce rike da Jakarta da wasu document tana biye da ita a baya don kusan taku uku ne tsakaninsu saboda ita ba a jerawa da ita.

Idanun matar sunsha kohl baki wuluk tayi lining idanun nata sai bakinta dayasha jan matte lips stain.

Kamaninta sun fito sosai da su fadwa saidai kamannin nata yafi zama visible da afiya don tama fi yanayi da afiya akan fadwa dukda kamanninsu ta jini itama ta fito.

 

Saida ta gitto parlorn ta hango dattijon sai kuma maganganunsa da barad data jiyo.

Chak ta tsaya tana kallonshi kafin ta tako cikin kasaita ta karaso parlorn, fadwa ce tayi saurin miqewa tana mata sannu da zuwa kafin ta bata inda ta zauna ta koma gefe.

 

Kamar an mata dole haka ta dago ta kalli maid din kafin ta bata umarnin wucewa da Jakarta zuwa sama, kallon barad tayi kafin ta mashi nuni da hanyar stairs ba tare da tace uppan ba, miqewa yayi yana ma dattijon murmushi kafin ya fuce daga parlor.

 

Gyaran murya tayi kafin tayi relaxing bayanta akan kujerar ta daura kafa daya kan daya duk akan idanun dattijon yana kallon ikon allah, saida ta dan dauka yan few seconds kafin ta soma Magana anatse with class

‘’marhaban khaal’’

‘’shukran Hidaya fatan na sameku lafiya’’

A gatsale ta yatsine fuska tace ‘’alhamdulillah’’

Shuru ne ya biyo baya, su fadwa dai kallonsu suke daga shi har ita, yanda kasan maqiya sun hadu.

A duniyar nan hidaya bata kaunar ganin mutumin nan agidannan,a yanu tana mashi kallon kamar maqiyinta dukda yana matsayin qanin mahaifinta marigayi Taheel, duk yanda taso akan ganin ya raba hanya da gidan abun yaci tura don ita gani take yana son ya shiga tsakaninta da big baby dinta ne to wama ya isa? Babu shi a doran kasa.

Bata qaunar kowa ya rabe shi kwata kwata,wannan yasa duk yanda zatayi saitayi don ganin tayi pushing uncle away.

 

Ganin shurun yayi yawa ne yasa hidaya cewa ‘’ko zan iya sanin dame kake tafe?’’

Mamakin jin tambayarta yayi da yanda tayi mashi tambayar saidai saninta da halinta yasashi dannewa kawai ya gyara zama don idan har zai bi abunda zuciyarshi ke raya mashi akan yayan dan uwan nashi marigayi Taheel to fah bazai kara waiwayar su ba, gyara zama kawai yayi ya danyi relaxing bayanshi kafin ya soma magana.

 

‘’ba komai ne ke tafe dani ba sai maganar Tajudeen,’’

Saurin rintse idanu tayi kafin ta budesu ta sauke akanshi,

Ganin haka yasa shi cigaba da cewa ‘’yanxu wata uku Kenan babu wani progress akan condition dinshi, shine nace ko zamuyi trying wasu expert health organization da suka kware sosai ta wannan fannin na wasu kasashen daban ko za a samu dacewa’’

  Tsagaitawa yayi kafin ya nunfasa ya cigaba da Magana cikin kamala ‘’ ni ina ganin idan muka dage sosai akanshi za a samu cigaba akan matsalar tashi’’

 

Wani irin kallo take mashi mai wuyar fassara wanda yana hango tsantsar bacin rai a cikin idanunta saidai fuskanta bai nuna hakan ba shima hakan bai sashi ya tsagaita ba don hakan bazaisa yayi shuru ba.

 

Cikin muryarta mai tafe da wani irin salo mai jan hankali ta soma Magana ‘’so yanxu kana ganin babu abunda nakeyi akai ne?well likitocin nan kasar ma top notch doctors ne kuma there are one of the best in the whole world and I trust them, khaal I know what is best for him, babu wanda zai nunamin damuwa akan matsalar big baby, so please idan kazoo ne akan wannan maganar ka ajiyeta don I know what is best for him baka fini sanin abunda zai taimakeshi ba don nice komai nashi, so please..’’ta karashe tana mai kallon cikin idanunshi babu ta kunya balle ganin girmansa

 

Fadin irin bacin ran da dattijon da suke kira da khal yake ciki ma bata lokaci ne, yau yaga karshe rashin mutunci wajen yar dan uwansa, yarda aka haifa a gaban idanunsa.

 

Wani irin heavy abu yaji a kirjinsa kamar an buga mashi dutse, haka yayi saurin runtse idanu yana danne abunda yake ji.

 

Mikewa yayi tsaye ba tareda ya kalleta ba yace ‘’shikenan na barku kuyi abunda kuka ga yayi dace, saidai ina tunasar dake, ba’a wasa da amana duk qanqantarta zan samu ganinshi yanxu?’’

Cikin sauri ta dago ta maida dubanta gareshi da jajayen idanunta kafin ta maida dubanta ga agogon rolex dake maqale a hannunta ‘’I’m sure he’s asleep by now, don…’’

Kasa daukan wulaqancin yayi don haka yayi saurin katseta ta hanyar cewa

‘’ ba damuwa na barku lafiya’’

 

Yana kaiwa nan ya masu sallama ya nufi hanyar futa, harya fuce hidaya bata bar kallon hanyar dayabi ya fuce ba, tafarfasar da zuciyarta keyi kamar an zuba tafashen ruwan zafi, su fadwa kuwa kasa cewa uppan sukayi sai zuba mata idanu da sukayi suna kokarin karantar reaction dinta,

‘’tirkashi ana wata ga wata,interesting’’ fadwa ta fada a zuciyarta tana mai tunanin wani abu.

Ganin ta mike tsaye yasa suka bita da idanu harta wuce hanyar stairs anatse kamar wata dawisu.

 

Kallon juna sukayi atare kowannen su da irin tunanin dake yawo a zuciyarshi

Post a Comment

Previous Post Next Post