*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
ꨄ Ɗan...ɗano
🤫😢........Unexpected and Surprising 🔥💥
Our official trailer for the incoming ƘARSHEN ƘADDARA....
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
This Book is dedicated to you *NA'EEMERH SULAIMAN SARAUTA NIMCY LUV*
1&2
★...
The writer's of
MIKIYA
TA DABAN
DUNIYARMU
RAMIN KURA
KAREN BANA
ƘAUNA BIYU
JALAAL AREEF
SO DAN RAYUWA
DUHU na dukan DUHU
And Now ƘARSHEN ƘADDARA
★
ꨄShin ta ina ya kamata ace ma na fara muku ne?,saboda nasan kan kowa ze kulle ne da tambayar ta ina ƙaddara take da ƙarshe???. Ehhhh lallai kuwa wannan nazartaccen littafin yaci suna mu ƙira shi da suna ƘARSHEN ƘADDARA. Saboda ita kanta ƘADDARAR tana gwada zuciya ne, ba don ta karya ba, A ahh sai don ta shirya ka zuwa wani mataki mafi ƙololuwar girma da daraja, don Kalmar ƙaddara bata gama garin mutane bace. Ita kanta yawaitar ambatar kalmar ƙaddarar tana zama ne tamkar ana mana washin KWAƘWALWA neeee. Se dai da yawan mutanen da ƙaddarar ke ci sukan tambaya kansu da cewa. _Amma me yasa ita ƙaddarar take cin mutane marasa laifi?_ Sedai amsar anan itace abinda ALLAH ya rubuta zai faru da rayuwar ɗan Adam, komai ƙarfin halinsa, komai tsarinsa, komai wayonsa.
Dole akwai wani labarin dake sanja hakan kwarai, Anan ina son mu sani cewar wannan kaddara ce abin da ALLAH Ya rubuta, hakan na nufin babu wanda zai kauce masa kenan, duk kuwa iya gudunka duk iya saurin ka, sedai mu sani ba nufin ALLAH bane ya zaluncemu ba. Sedai mu sani cewar ALLAH yana da hikimarsa nayin hakan a cikin duk abinda yaga dama, Domin Ƙaddara tana koyar da mu abubuwa da dama…
★..
Ta farko- Rayuwa ba ta tafiya yadda muke so sai dai yadda ALLAH Ya so.
Ta biyu- Kowane abu da ke faruwa ko da zafi yake, to tabbas akwai alheri a cikin hakan idan akayi hakuri aka jure,
Ta uku- Mutum ya kasance mai haƙuri da godiyar ALLAH kan duk lamarin daya gindaya masa, saboda duk lokacin da kaddara ta same ka kayi hakuri kayi juriya ka kumayi gwagwarmaya karka taɓa bari ka sare don hakan yana cikin jarrabawarka shima. Mutane da yawa suna fuskantar tarin ƙalubalai a cikin rayuwa, wasu rashin lafiya ne, wasu kuwa rashin aure ne, wasunmu kuma suna fama da talauci ne me zafin gaske, saboda kar bawa yaga tarin ƙalubalai na bebeye dashi yaga kamar cewa ko duniyar tana mantawa dashi ne, to maganar gaskiya anan ita ce ba kai kaɗai bane, duk wanda ka gani me rai a cikin wannan duniyar to lallai tabbas yana fuskantar ƙalubale, sedai na wani yafi na wani tsanani... ALLAH yana gwada bayinsa da hanyoyi daban-daban ne domin ya ga wanene zai yi haƙuri, wanene zai ci gaba da yin addu’a.
ƘADDARA bata nufin ka zauna babu ƙoƙari. A’a, Ka yi ƙoƙarinka, ka nemi ilimi, ka nemi arziki, ka nemi aure, saidai sakamakon na hannun ALLAH ne. Sabo da manyan mu sukan ce damu kada mu bari rayuwa ta koya mana baƙin hali. Idan ƘADDARA ta rufe ƙofa guda, tana buɗe wata da kuka bai bari mu gani ba...
ꨄ Kada ka bari ganin wani yana samun nasara ya sa ka watsar da damar da kake da ita. Abinda ALLAH ya ƙaddara naka ne, to kuwa lallai naka ne don nasarar ka ba zata taɓa wuce ka ba. Ka nemi Albarkar iyaye, kuma ka nisanci hassada,duk ƙanƙantarta kuwa. Amma kuma kada ka taɓa barin ka gayyato bakin ciki cikin rayuwarka,
kada ka zama me aje nauyin da wani ya ɗora maka shi, kada kuma ka bari kalaman wani ya dameka, Kar ka taɓa bari kunci, baƙin ciki da damuwa su sama matsugunni su zauna a zuciyarka tamkar baƙon da yasamu gurin zama.
Me yasa zaka ɗauki nauyin kalaman wani? Me yasa zaka aje abin da ya faru da kai ka maida shi ciwo a zuciyarka?...... Idan kana cikin jinya, ko kana fuskantar ƙalubale da barazana ka ringa tuna abu ɗaya, ALLAH baya gwada bayinsa don ya hallaka su, amma Sai don ya gafarta musu, ya ɗaukaka su ya kuma koya musu ƙarfi da gwagwarmaya tamkar RAYUWAR AMEENERH SHEHU USMAN....
Tabbas akwai darussan rayuwar da ba zaka taɓa koyarsu cikin nishadi da Jin daɗi ba sai ka shiga ƙunci. To me zai sa ka bari damuwa ta fara cinye zuciyarka idan ba za ta warware komai ba? Damuwa ba ta kawo mafita sai dai ta ƙara nauyin zuciya. Ka saki zuciyarka ka bar komai a hannun ALLAH, ka kuma dage da addu’a. Domin ALLAH yana tare da kai fiye da yadda kake zata.A wannan zamanin ƙaddara idan ta same ka, kaddara ce. Amma idan ta faru ga wani namu, sau da yawa mu kan dauke ta ne a matsayin iskanci ko kuskure. A fahimtar gaskiya a duk duniya dan adam bashida na biyu ba kowa bane yake iya gane asalin zahirin mene ne ƙaddara acikin rayuwar mutum Rayuwa da kake gani a waje ba ita ce cikakkiyar rayuwar zuciya ba. Tun daga ranar da aka halicci zuciya a cikin jiki, ALLAH ya bai wa mutum ikon sarrafa tunaninsa, Daga nan ne ya zama ba kowa ne zai iya fahimtar damuwa ko farin cikin wani gaɓa daga cikin rayuwarmu ba, Saboda haka idan ka ga wani yana rayuwa cikin ƙalubale, ka sani ba lallai ka fahimci abin da yake ciki ba, Idan ba za ka iya taimaka masa ya fita daga halin da yake ciki ba, kuma ba za ka iya saka shi cikin addu’arka ba, to mafi alherin shi ne ka bar shi cikin mutunci ba tare da sukar rayuwarsa ko halin da yake ciki ba inda ZAN BA KA SHAWARA.... To shi ne ka guji zama da Mutane masu yawan janjanin magana, domin ba tare da sanin kaba suna rage maka ƙarfin zuciya ne, su kuma iya hana ka ci gaba. Hulɗa da su na iya mayar da rayuwarka wuta, domin kullum suna kallon ɓangaren mara kyau na rayuwa, suna yaɗa damuwa da rashin kwarin gwiwarka. ★Amma idan ka kusanci masu godiya da yarda da ƘADDARA, zaka ga rayuwarka ta cika da nutsuwa da farin ciki, Mutane masu zuciya mai kyau suna ƙarfafa ka, suna sa ka kaɗa baki da murmushi harma su wanzar da farin ciki cikin rayuwarka, suna kuma nuna maka cewa rayuwa tana da daraja duk da ƙalubale sun cinye ta, to waɗan nan mutanen su ne abokan tafiya na gaskiya, domin suna kallon alheri a dukkan yanayin da kake a ciki, suna kuma karfafa ka ka ci gaba da neman nasara tare da gwagwarmaya. Domin sune rayuwa ta yar dasu, mu zaɓi irin mutanen da muke hulɗa da su. waɗanda idan ka zaɓi masu kuka, zaka sha wahala. Idan ka zaɓi masu godiya, zaka sami kwanciyar hankali ne da nasara, don haka mu kusanci masu son farin ciki da nasararmu, domin su ne za su taimaka mana har zuwa lokacin da zamu gina makoma mai kyau. To amma duk hakan baya faruwa se anyi hakuri da ƙaddara, domin duhu baya dawwama, haske zai zo duk runtsi, Abin da ya same ka bai wuce rubutacciyar ƙaddara ba, sedai me???. Wata ƙaddarar da kuɗinmu muke sayenta. Ehhhh lallai tabbas da kuɗinmu muke sayenta... Saboda muna fifita addinin kiristoci fiye da namu a wannan zamanin. Shin ba kun matsu kuji ta yanda muke sayen mummunar ƙaddara da kuɗinmu ba?,mu kuma zaɓeta da kanmu da hannuwanmu ba?, To nidai AMMEY LAYLERH nace babu ruwana AMEENERH SHEHU USMAN wacce akafi sani da *DR MEENERL itane zata banbance mana me hakan ke nufi....
Kun shirya a kafta???....
_Kun shirya jin ta yadda da kanta ta zaɓa mummunar ƙaddarar?, ta hanyar kin bin dokoki da darajar dake cikin aure?, ta fuskanta tarin ƙalubalai masu tarin yawa, cikinsu kuwa har da ƙaddarar AURE AUREN mazan data dinga yi mabanbanta?, Ƙaddarar Fyaiɗen da rashin daraja AURENTA da ya hau kanta, wannan shi ne matakin farko kuma shi ne wasa farin girkin nata_. *Kun shirya jin ta yadda ƙaddarar nata zata zo ƘARSHEN kuwa?*. Dan dai idan nace *ƘARSHEN ƘADDARA* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *ƘARSHEN ƘADDARA* ba zan iya cewa an barki a baya SIS. Don It is going to be a hit, that I promise you. Saboda tafiyar *ƘARSHEN ƘADSARA* da banbanci da sauran littattafai na baya, yeah banbancin kuwa ma shi ne about 90% na littafin ƘARSHEN ƘADDARA is based on true life events ne, musamman daga farkon sa zuwa gaf da ƙaresunsa, karshen sa ne kawai zai zama fiction ta yacce zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shi ne from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share ruwan hawaye, so get ready to do both💃🤸.........
♡♡♡
ꨄ Tsaye Matashiyar matar da kai tsaye zamu iya ƙiranta da ƴar kimanin shekaru ashirin da biyu, take gaban Madaidaicin mirrorn ɗakinta me kyau da tsari, wanda yake a gyaren da kallon farko zakama ɗakin da wacce take tsaye gaban mirrorn ka tabbar da cewar me tsafta ce, tun daga yanayin yadda ɗakin nata ke a tsaftace tsaf, jikinta kuma na ɗaure da wani blue towel se faman shafe shafe take yi kyakkyawar fuskanta, wacce take ɗauke da zallar farin cikin fitanta aiki na farko yau da zata fara, wanda kai da ganin yadda take cikin farin cikin zaka tabbatar da cewar lallai wannan aikin nata me girman matsayi ne a cikin ranta, soson powdern dake hannunta take sake goggawa chocolate ɗin fatar fuskanta, wacce ta zarta mu ƙirata da baƙa sedai bata kai mu ƙirata da fara ba kuma, wannan dalilin yasa muka bata chocolote ɗin kai tsaye. Lipstick ta sake ɗauke tana gogoma lips nata wanda take suka ɗauki shining na kyau da sheƙin abinda aka goga musun, eyeliner ta sake ɗauka tana gyara eyelashes nata again kuma tana ci gaba da gyara duk abinda be mata ba, har zuwa dogon wuyanta shima da take sake gyareshi da soson powdern. Ta ɗan ɓata lokaci me nisa a nan tsaye a wurin, kafin ta miƙe ta nufa gaban wedrop nata me shida, irin me madubi da katifar nan ba laifi suma sun yi kyau babu ƙarya, kayan ta shiga bi da ita tana research da idanunta na wanda ya kamaci ace ta saka, haka har idanunta suka sauƙa akan wata lafiyayyar abayarta black, wacce take ta cikin kayan lefenta ce kuma bata taɓa sakata ba, don haka kai tsaye takai hannunta tana tare kayan dake ƙasa da sama kasancewar rigan itane a tsaƙiyan kaya, ahankali ta janyota bayanta ta ɗan gyaggyara kayanta da suka zamo wosu kuma suka yi ciki. Zame towel ɗin dake jikinta tayi bayan ta zira wata sitred riga daga jiki linor, kana ta ɗora abayar tare da komawa gaban madubi tayi Rolling kanta da vail ɗin da bai kai ya kawo ba na abayar, tsaf kuwa tayi kyau ta kuma karɓu cikin shigan daya mata wani kalan kyau na musamman. Turaren dolcy nd gabbana ta feshe ilahirin jijinta dashi, kana ta wuni nufi ƙofa tana taku ɗay ɗay kamar bata taka ƙasa ba, tin kafin takai ƙofar parlourn ta take famar kwala ƙiran.
"Baby!Baby!!Baby!!!"
Tana ci gaba da tunkarar ɗakinsa tana sake tunkaro ƙofar bedroom nashi, tana ci gaba da mitar ta "Haba Baby har yanzun baka tashi bane mun makara fa?" Tayi maganar tana wani ɗan zazzaga parlourn irin a matse ɗin nan take, "To wllh sedai ka biyo napep don Wllh nidai tafiyana zan yi....." Takai ƙarshen zancen nata tana kaiwa zaune saman kujerarta me kyau, ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjiga jiki. Babu jimawa sega takun tafiyarsa nan na tunkaro inda take zaunen, zama yayi kusa daf da ita yana ɗan kishin gida daga zaunen da yakai, fuskansa da murmushi sosai ya ce. "Kai My luv yanzun duk wannan zumuɗin fara aikin ne haka?, to yanzun dai a taimakeni da abinci don yunwa nake ji...." Fuskanta ta saki kaɗan tana miƙewa,babu jimawa se gata ta dawo hannunta riƙe da cooler na abincin data yi tin farar safiya, ajje musu tayi tana buɗe cooler'n kai tsaye ƙamshin couscous ɗin data ma lafiyayyen haɗi na dukar hancinan su. Wani ɗan lumshe idanunsa yayi yana sake jin ƙaunar matar nasa na sake bebeye shi, ta iya komai na cikin rayuwa tin daga kama kan kula da kanta, Mijinta, cikinsa, haƙƙinsa, da duk wasu al' amura nashi. Saƙƙowa yayi yana me furta. "ALLAH yama Meenoh na albarka, ya saka miki da gidan aljannarsa mafi tsada..." Wani kallo ta masa wanda ya saka shi kusan sarƙewa da yawun da ya taho kai tsaye daga cikin maƙoshinsa, don shi kaɗai yasan iriyar masifar ƙaunar da yake ma wannan baiwa tashi, gaba ɗaya jinta yake a ko ina na jikinsa, jinsa yake daga kanta ya gama aure IN SHA ALLAHU, domin duk abinda yake so yi masa take kai tsaye babu shamaki, a natse sukaci abincinsu cike da ƙaunar junansu... ruwan swan suka sha me sauƙin sanyi kasancewar ita da kanta ta saka musu dokar hana shan ruwa bame sanyi ba sosai, daga nan ya miƙe yana ce da ita _just 15 minutes_ kanta ta ɗaga mishi tana sakar masa murmushin daya kusan kashesa da ransa, da yar sassarfa ya nufi bedroom nata don babu jimawa kuwa se gashi ya dawo sanye cikin tattausan shigar shadda brown color, wacce ta masifar amsar nasa jikin, don sosai daga ita har shi suke da wani irin sahihin kyau me sanyi da nutsuwa, ba wai irin me ɗaukar hankalin nan... Kallonta yayi daga sama zuwa ƙasa ganin yacce ya tafi ya barta haka take, don haka yace "Baby ya naga ke baki shiryo bane?" Kallonsa tayi ta kuma kalla shigar dake jikinta tana miƙewa tsaye, tsadaddar wayarta me ƙirar _TECNO POP 9_ ta ɗauka tana cewa. "Kaga muje don ALLAH Ya Ahmad lokaci na ƙurewa kaga wannan shi ne karo na farko kar inji a makare...." Tayi maganar tana ƙoƙarin ficewa a parlourn, hannunta ya ɗan jawo yana dawo da ita baya, cikin komawa seriously nashi yace. "Yanzun don ALLAH Meenoh ke idan na ƙyaleki seki fita a hakan?" Cikin yanayi na ɗan fusatuwar data soma tace. "So what idan na fita a hakan Ya Ahmad?, kalla ka gani a suturce nake fa!, ko kuwa illa ka gani tattare da shigan dake cikina?, ya zaka fara abu kamar wani wanda be waye ko ya shiga class ba?" Ta ƙarasa maganar tana fita a ɗan kamar fusace, da sauri ya biya yana bama zuciyarsa hakuri akan cewar wannan ɗin ba komai bane sharrin shaidan ne. Lokacin da yake fitowar kuwa har me gadi na ƙoƙarin buɗe mata get zata fita ta tara napep, saurin dakatar dashi yayi yana isa ya kamo hannunta cikin nasa yana kallar tsaƙiyan cikin idanunta yaje... "Oya les't go!, ko in na barki kin fita ke kaɗai kinsan hospital ɗin ne?, kuma wurin wane zakije?..." Se ya ɗan shiru daidai lokacin da yake buɗe mata gefen me mazan banza a motar, shi kuma yana komawa driver sit ya zauna, Ahankali yakai hannunsa yana lakatar dimple nata da yake gefe guda yana cewa. "Bestien Besty rigima..." Daga haka yaja motar tasa me ƙirar GLK bugun 2025/2026 suna barin harabar gidan, hannunsa na cikin nata ɗaya yake driving ɗin wa'azin Marigayi *SHEIKH MUHAMMAD AUWAL NASEER ALBANY ZARIA* Na tashi a cikin motar me suna *IN KASAN WATA* Sabo da sosai yake son wa'azin Malamin, sabo da matuƙar feɗe gaskiyar sa da yake yi.... Haka har suka isa katon private Hospital ɗin da anan ne yayi duk wasu cuku cuku ya nema mata aikin nata, tin da suka shigo cikin harabar asibitin take kallar tsari da yanayin ta aka tafiyar da ginin wurin kawai na yi mata hundred percent. Ci gaba da bin komai da ido tayi a cikin zuciyarta tana ayyana lallai Ahmad na manyan mutane yana kuma da hannu da manyan, in banda hakan ta yaya ita AMEENERH SHEHU USMAN ta taɓa zata ko tsammatar cewar zata taɓa aiki a ko me kama da wannan asibiti ne, amma se gashi sanadiyyar Mijin nata yau wai ita ce da aiki a wannan tsadaddar asibitin da a da sedai ta hangeta daga nesa nesa, wanda koda a tunani bata taɓa kawo cewar zata zama ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin ba, don ta san cewar ko aikin zatayi tofa sedai ta ƙare a na gwamnati, wanda inta sama aikin ana gwamnatin ma kenan ita nata yayi kyau, amma se gashi yau ata sanadiyyar Mijin nata yau gata a matsayin ma'aikaciyar asibitin, Ikon ALLAH fa kenan, Lallai ta sake yarda cewan Ikon ALLAH shi ne gaba da komai. Wata doguwar ajiyar zuciya ta kawo lokacin da yake farkar da ita daga tunanin data ɗan shilla. Ƙafanta dake cikin wani vk shoe ta fara zirowa me laushi sosai plat me kalan jikin miski, kafin ta fito a natse tana buɗe kofofin hancinta ta shaƙi iskan cikin asibitin da kyau idanunta a lumshe, zagayowa yayi daga mazaunin nasa yana dawowa ta setin da take, tare da kama murfin motar ya zuba mata kyawawan idanunsa, wani numfashi ta ɗan shaƙa tare da buɗe idanunta tar kuwa se akan Babyn nata, wata iska me ɗan nauyi ya fesar yana sarƙe hannunsa a ƙirji tare da sakar mata da wani tsadadden murmushinsa me kyau. "Les't go idan DR. Meenerl ta gama abinda take yi...?" Taji muryan mijinta abin sonta da bata taɓa haɗa shi da kowa, wanda suke yau kimanin watanni Bakwai kenan da aure, amma idan ka kallesu zaka iya shan cewa sun kai irin fin shekarun nan ne a auren, bawai don zaka gane hakan bane ata siffar jikkunansu, A ahhh sedan ta iriyar shaƙuwar dake tsakanin nasu, amma kai idan har ta suffar jikkunan nasu ne tsaf zaka iya ƙiransu ma budurwa ne da samrayinta. Fitowa tayi suna jerewa a tare suka soma tafiya suna ƴar firarnsu suna ƙaramar dariya ƙasa ƙasa, duk wanda suka haɗu dashi a hanyar kuwa seya sake waywayensu koda ya wuce, don yanda suka matuƙar dace da juna. A gaban wani babban office suka tsaya yana zaro wayarsa ƙirar iphone ya saka ƙira a wata number, wayar second yayi yana datse ƙirar, babu jimawa sega wata nurses ta ƙaraso tana musu iso, gaba tayi suka take mata baya har zuwa babban parlourn dake cikin office ɗin, ruwa da lemu ta kawo musu tana ajjewa gabansu bayan ta sake gaidasu, fita tayi ta wata ƙofan daban can kuma babu jimawa sega wani hamdsome guy ya fito sanye cikin labcoat na likitoci sky color, wuyansa rataye da Patient screening hannunsa cikin handglov kansa da surgical cap, zama yayi kujeran dake fuskantar su fuskansa da murmushi sosai, "Barka da zuwa abokina, na ɗan ɓata muku lokaci ko?" Yayi maganar yana miƙa masa hannu tare da sake cewa yayi hakuri wata Surgery ce ya shiga ta gaggawa, "Ba komai DR BILAL" yace masa yana dawo da dubansa kan Meenal. gáidashi a mutumce tayi duk da bawai ta san shi bane ko ta taɓa ganinsa da mijin nata, bayani ya masa game da cewar ita ce Meenal ɗin. Kansa ya ɗan shafo yana cewa "Okay to Ma sha ALLAH, zamu duba mu gani duk dai takaddun nata da kyau, amma duk da aka zan sake gwada ta ko na mako guda ne. Kuma daga gobe In sha ALLAHU zata fara zuwa, yanzun kuma za'a mata interview ne..." Yay maganar yana jan landline ta parlourn ya saka ƙiran wata babbar likita, babu jimawa wata gaggaɓar mata ta iso, nuni ya mata da Meenal yana ce da ita, "Dr pooja jeki da Meenal zaki mata interview a fannin surgery...." Cikin harshen turanci ya mata bayanin kasancewarta Christian ce, fuskanta da yanayin da murmushi me kyau ta kama hannunta cewa "les't go My freind!" Murmushi ta nata tana mara mata baya suka fita, shi kuma suna yin hannu yace zai je wurin aikinsa don har kamar ma yayi late. Har parking car's ɗin DR BILAL ya raka AHMAD....
Lokacin da Dr pooja ke can tana ma Meenal interview tuni shi har ya jima ma da barin cikin hospital ɗin baki ɗaya, kuma Alhamdulillah sosai tayi ƙoƙari dan tiyatan Ɓera ne tayi, kuma cikin ikon ALLAH bayan allurar baccin da akama ɓeran ta masa tiyatan cikin taka tsantsan da kuma tsoro, amma cikin iko na Ubangiji tana kammalawa sega ɓeran nan na motsi harma yana ƙoƙarin tashi ya gudu, wata nannauyar ijiyar zuciya daga ita har Dr pooja ɗin suka saki ita tana godiya wa ALLAH,ita kuma tana cewa. "THANKS JESUS...." daga nan suka ci gaba da ƴan ababuwa har ƙarfe sha biyu da kusan rabi, kafin ta ɗebeta suna komawa office ɗin Dr BILAL, sedai tin kamin Meenal ɗin ga kawo kanta taga Dr pooja ɗin tayi hanzarin yowa baya tana dafe goshinta da zuciyarta, na irin alamar nasha da kyar ɗin nan kafin kuma taga lokacin data furta thanks jesus, ta motsawar mukwallonta, tana kama hannunta suna saurin barin wurin, suna yin ta bayan window me girma, tsaiwa tayi bayan ta saki hannun Meenal ɗin dake ganin Ikon ALLAH, "Thanks god Sir MAJEED!! be ganmu ba...." Ta furta tana sake sakin wata ijiyar zuciyan. office nata ta wuce da Meenal ɗin, suna isa ta saka ƙiran Dr BILAL. Nan take bashi labarin ai taje zata shiga office nashi ta tarar da Sir MAJEED a ciki yau dai jesus ya tseratar da ita, dariya bame yawa ba Dr Bilal ɗin dake tare da Sir MAJEED ɗin har kusan daf ya saki, can ƙasa ƙasa yana satar kallon inda MAJEED ɗin ke zaune daya wani sha mur sosai yana cike wasu takaddun da shi ne abinda ya kawo shi cikin asibitin da seya kusa shafe rabin shekara be leƙo taba,dan hakan nema yasa ba kowa ne ya masa cikakken sani a matsayin me hospital ɗin ba, mafi yawancinsu ma sukan danganta asibitin data Dr Bilal ɗin ne, idan kuwa kaga mutum ya masa farin sani a cikin asibitin to kuwa tabbas babbane me girman matsayi kamar dai Dr pooja ɗin da ta ganshin a yanzun, wanda mamakin ganin san da tayi har yaso bata mamaki, wanda ita a karan kanta sau da dama takan sha mamakin yadda aka yi Majeed ɗin ke mata kwarjini bayan kuma schoolmate nata ne, tare suka yi karatu a ƙasar Oxford amma yanzun ya wani girme mata ya zama magidancin dole, duk da dai dama magidancin ne kuwa, harda ƴar sa ƴar kimanin 7 year's. Fesar da iska daga bakinsa Dr Bilal yayi yana datse ƙirar bayan kallon da yaga Majeed ɗin na jifarsa dashi, komai kuma be ce masa ba, wanda dama yasan hakan cewa zata faru tin da hakan shi ne kusan ɗabi'arsa. Miƙewa yayi yana nufar hanyar barin office ɗin, seda yaga yakai har bakin ƙofar kana ya masa gwalo yana cewa. "Maye dai yaci kansa banza miskilin tsiya da baƙar zuciya, yanda mutum yaƙe baƙi haka ma zuciyar tirr da MAJEED DAWOUD ISHAQ...." Yana kai nan ya fice a guje daga office ɗin baki ɗaya,ɗan yasan tsaf shi idan ya tashi yaɓo tashi baƙar maganar ze kusan kashesa da ransa. Kai tsaye office na Dr pooja ya wuce saɓunta gaisuwa tsakanin su suka yi, yana amsar document ɗin da pooja ɗin ke bashi, dubawa yayi yana cewa ta kwana ma gidan sauƙi bara kawai ya bema Majeed ya shigar da file ɗin cikin jadawalin list na ma'aikatan asibitin, seda Dr pooja ta ɗan waro ido har tana gaza yin shiru tace. "You don't see any problem with that, do you Dr?" Murmushi yayi yana fita kawai dan ya fahimci tsaf pooja ɗin zata bashi ciwon kan da Majeed ɗin ke yawan cewa tana bashi. A lokacin da yaje masa da zancen duba file ɗin daya masa wani kallo yana ma turar da laptop ɗin dake gabansa gefe daban, kafin ya wani kalle sa yace. "Kai me yasa ba zaka shigar ba,halan ka haɗu da cutar kuturtace bana da masaniyar hakan, to bara kaji indai se na shigar da wannan cikin jadawalin list ɗin ne, to kuwa ko waye sedai ya mutu be sama aiki anan ba...." Daga haka yasa kansa yana ficewarsa, ko ina be kalla ba ya shige motarsa yana ma yin reverse yabar cikin asibitin.
Ƙarfe biyu daidai Ahmad ya dawo asibitin suka wuce bayan ya sake jaddada godiyansa ga abokin nasa Dr Bilal, har gaban motarsu ya sake rakasu daga ita har shi suna sake jaddada godiyar su, tana cewa ya sake miƙa mata godiyarta ga Dr pooja. Daga nan kai tsaye gidan Hajiyarsa yakai Meenal ɗin, duk kuwa da yanda gabanta ke faɗuwa da haɗuwar nata da hajiyar san, don tasan bame kyau bace, amma bata nuna masa komai ba har suka isa gidan, hong yayi get man ya buɗe musu get ɗin yana cilla hancin motar nashi cikin haraban gidan nasu, Motar Abbansa daya gani a gidan ne ya bashi tabbacin yau babu inda ya fita kenan, duk da dai dama be ganshi a Company ba, wanda da ya zata ko wani wurin yaje, ashe duk ko ina ne ma beje din ba. Ajiyar zuciya me kyau na ziran da tayi itama tayi ganin motar Abban, don tasan ko babu komai ta kuɓuta daga bakaken maganganun hajiyar Ahmad ɗin....
Da sallama ɗauke a bakunansu daga ita har shi suka shiga parlourn gidan, wanda mutane uku ke zaune a babban ƙaryataccen parlourn, magidancin jarida ce ɗauke a hannunsa yana dubawa, yayin da magidanciyar matar ke zaune tana fuskantar plasma da ake haskaka labaran Duniya, se wata matashiyar da ita kuma ke kwance saman 3siter tana lallatsa wayarta, wanda sallamar su Ahmad ɗin ya saka gaba ɗaya attention nasu dawowa kansu ciki kuwa harda hajiyar da tana kallon sa tare da Meenal take ta ɗauke kanta bata sake kallar inda suken ba. Zaune matashiyar ta miƙe tana gyara hulan dake kanta dake ƙoƙarin zamewa, fuskanta da fara'an ganin Meenal ɗin ta miƙe tana nufosu tana cewa _Oyoyo Meenally'n babban Yaya...._ ta isa gare su tana rumgume Meenal ɗin da ita ma ta rumgume Fatiman, A kunyace ta ƙaraso tsakiyan parlourn tana ɗurƙusawa gaban Abba da yake tace da ita ta koma saman sofa, gáidashi ta shiga yi a girmame tare da Hajiyar da take wani amsata a ciccure, wanda hakan ma tasan albarkacin Abba ne taci, se lokacin kuma Ahmad ɗin ke ƙarasowa cikin parlourn shima yana zama daga ƙafafun Abban nasa ya gaida shi, kafin ya juyo a natse ga mahaifiyar nasa, "Hajiyata barka da rana, fatar kin wuni lafiya...." A daƙile ta amsa may da "Lafiya Alhamdulillah" kawai tana ɗauke kanta daga garesa. Fatima ce ta Abba yace ta wuce dani ɗakinta,hakan kuwa yamin daɗi ba kaɗan ba muka wuce abin mu, babu jimawa sega Ya Ahmad ya shigo mana da abincin da na tabbata ni ya kawowa ma. Da ido na masa alamun ya ka min haka?, shima da idon yamin alamu da sabo da hakan hakkinane... Murmushi kawai nayi kuma kamar abin haɗin baki muka saki dariya a tare, be zauna ba ya fita sakamakon shigowar ƙira cikin wayarsa ya fita, dake tayi salla a can asibitin se kawai ta zauna sukaci abincin, koda suka kammala kwanciyar ta tayi a gadon Fatiman take nannauyar bacci yayi awon gaba da ita, wanda ta jima yi, don se bayar la'asar sosai ta tashi sallarn ta fara yi kuma zuwa lokacin Fatima bata nan, wanda take da tabbacin Islamiyya ne ta tafi, fita tayi zuwa parlourn Hajiyar, har lokacin Abba na zaune a parlourn amma babu Ahmad, Hajiyar kuma bata parlourn sema motsinta data fara juyowa a kitchen don haka kai tsaye ta nufa kitchen ɗin, A ɗan tsorace ta mata sannu tana ce da ita ta kawo ta mata aikin, wani banzan kallo ta wurgo mata tana jan tsaki tare da nuna mata hanya alamar ta bar mata wurin, "Don ALLAH kiyi hakuri Mami ban san abinda na miki ba wllh..." A wani irin fusace kuwa ta juye tace. "Baki san abinda kika min ba?, tun da ke muna fuka ce gadon munafurci taya ya zaki san abinda kika min kuwa, tin da kin gama mallake min ɗa babu kowa a gabansa in ba ke ba, gashi yau watanni Bakwai kenan da aurenku, ban ga alamar komai tattare dake ba, halamar sedai aci aje masai kenan ke ba matar ƙaruwa bace out....."
Ta wani ƙarashe maganar nata da tsawa tana korar ta a kitchen ɗin, wani abu me kama da ruwan hawaye ne taji sun ciko idonta, don haka babu musu ta fice, sa'an ta ɗaya Abba baya parlourn don haka ta shige ɗakin Fatima ta zauna a gefen gadon ta tana dafe kanta da hannayenta. Jin Shigowar Hajiyar har ɗakin Fatiman ne ya saka gabanta yayi wani irin faɗuwa, yawun bakinta na ƙafewa ƙaf, take taji kanta ya sara mata, don haka a cikin zuciyarta ta shiga nanata kalmar INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN... Tamkar sauƙar aradu haka taji muryan Hajiyar tana cewa. "Wllh³ bazan taɓa son ki ko na amsheki a matsayin surukuwata ba Meenal, sabo da na tsanake!, bana sonki!, bana ƙaunarki, gaba ɗaya so kawai kike ki haukatar min da yaro baya da aiki se naki,yanzun fa duba har aiki ya samo miki a asibitin *4&4 SPECIALIST HOSPITAL* wanda ni nan babu kalan roƙon da ban masa ba akan ya samowa Fatima amma yaƙi, se gashi ke dake ke kece ya samo miki tashin farko, ko shawartana beyi da maganar ba, sabo da ga makiyiyarsa se yanzun naji ya a faɗama ubansa ni ban kai ba, ban kuma isa ba...., To ki sani wllh se nayi duk me iyuwa na rabaki da Ahmad kamar yadda kike nemar rabani dashi kema....." Fuuuuu daga haka tasa kai tana ficewa har wani hucin bala'i da masifa take. Kuka tayi me rai da lafiya a wurin tana roƙon ALLAH ya ganar da Hajiyar Ahmad ta gane gaskiya, tana nan zaune har bayan sallar magrib amma hawayen be dena zubo mata ba, jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ɗin Fatima ta wanko fuskanta tana gyara yanayin ta sosai, don tasan Ahmad ne , tin da taji shigowar Fatima da kuma lokacin da Hajiya ta dakatar da ita daga shiga ɗakin ta aiketa makota. Idanunsa ya zuba mata da kallon farko ya gane cewar kuka tayi, zama tayi a sofar dake daf da gadon Fatiman kwara ɗaya, inda ya ƙaraso har wurin a natse daf da ita yana zama tare da janyo ta jikinsa. "AMEENERH?" Haka taji ya ambata sunanta da full name nata kafin ya sake jefa mata tambayar "lafiyanki kuwa? Ko wani abu akayi miki?" Tsaye ta miƙe
sannan calmly ta goge hawayen idonta da bayan hannunta daya sake zubo mata, kanta ta jinginar a jikinsa tace. "Babu abinda aka yi ya Ahmad bacci nayi, kuma kasan idan nayi bacci tsakanin sallar la'asar da magrib da ciwon kai yawanci nake tashi..." Ta faɗa da sanyin murya and I can swear I saw him relaxed. Kanta ya ɗago bawai don ya gama yarda ba wani abu Hajiyarsa ta mata ba, fuskar sa cike da concern ya furta. "Kin tabbata?" Yana saka idonsa cikin nata don sake tabbatar da hakan. Vail nata dake gefe a tashe ya ɗauko mata yana ɗora mata samar kanta yaje suje. Babu musu kuwa ta bi bayansa don dama hakan take ta jira tin ɗazun, koda suka fito babu kowa a parlourn don dama Abba be dawo ba, yasan kuma dama ba sosai ya fiye dawowa idan yayi sallar magrib ba se anyi isha'a yake dawowa gaba ɗaya. Hannunta ya kama ya nufa sashen Hajiyarsa da ita, wanda gabanta keta sake faɗuwa amma babu yacce ta iya ko tace ba zata ba, haka ta bishi tana zaune samar darduma suka isa, sallama yayi bata amsa ba taci gaba da laziminta, tsugunne yakai gabanta yana ce da ita zasu wuce. Da hannu ta masa alamar suje duk da beji daɗi ba amma haka yaja hannun Meenoh ɗin nashi suna wucewar su. Gidan gaba ya buɗe mata ɓangaren me zaman banza ta shiga ya rufe ya zaga ya shiga driver sit yana tada motar suka bar gidan. A wurin gashin wasu zabbi ya tsaya fita yayi babu jimawa se gashi ya dawo hannunsa ɗauke da ledoji biyu, ɗaya ta gashin zabbin ce, ɗayar kuma fruits ya sai musu kasancewar yaga kamar na gidan sun kusa ƙarewa. Sannu ta masa tana amsar ledojin ta miƙa ta baya, daga nan yaja suka wuce gida, be shigo gidan ba ya fita don baya son ya shigo beyi sallar isha'a ba, shima kusan irin Abban nasa ne, yafi gane idan yayi isha'a ɗin ya shigo gidan shima, ita ce ta shiga da ledojin ta ware fruits ɗin a fridge ta rage wasu zabbin ma ciki don tasan da safe ba sai ta musu girki ba, ta ware musu kuma wanda zasu ci idan ya shigo. Karfe tara saura ya dawo, wanka ta taya shi ya fara yi kafin su fito cikin shigar kayan shan iska, don itama tayi bayan tayi sallah'n isha'a. Se baza ƙamshinsu suke, a natse suka kammala cin nama da youghout ɗinsu kafin su zauna suna kallar Film na HAQ a tare a laptop nashi, don duk Film sabo daga fito yake sauke musu su kalla. Har wajajen sha biyu saura kana suka kammala suna ta mayar da yacce film ɗin yayi kyau, ya kuma tsaru, don ba ita mace ba ko shi kansa da yake namiji Film ɗin ya taɓa masa zuciya, gashi kuma akan addinin Musulunci aka yi Film ɗin, har yacce wasu mazan ke wulaƙanta matayensu na gida idan sun ƙara aure, da yacce Ƴaƴan wacce ake zalumta suke ƙin iyayensu maza, saboda kuntatama mahaifiyarsu da ake, haka dai sukayi ta maida yadda suka tsara Film ɗin. Ɗan kwantar da kansa a kan kafaɗarsa yayi, wanda ya saka Meenal ɗan juyowa ta kallesa, shima kallon nata yayi yana wani kashe mata idon daya sakata lumshe nata, matso da fuskansa daf da nata yayi zata ɗan koma baya kaɗan yakai hannunsa ya kama waist nata daya saka ta jin yirrrr, tsigan jikinta na tashi bakinta yama kissing yana cewa. "In sha ALLAHU bazan taɓa kasancewa miji irin Abbas ba, don zalumcinsa yayi yawa, ya kuma cuci Yami Ghautam da yawa tare da yaranta. Idonta ta sake lumshewa tana jin tabbaci akan duk maganganunsa akan ta, ta kuma yarda dashi samm bata da haufi akan mijin nata, daga nan ya tashi da ita suna wucewa bedroom nasu, don har ta fara bacci a jikinsa, kwantar da ita yayi shima yana kwanciyar gefen ta tare da janwota yana shigar da ita cikin jikinsa, ta buɗe baki da niyar masa magana ya haɗe bakin, dole ta tsaya da kyau tana bashi kulawan daya kamata, sune har wajajen karfe ɗaya da rabi basu yi bacci ba, seda suka tsaftace jikinsu kana suka kwanta tana lafe a jikinsa tana sakin ijiyan zuciya me ɗan zurfi. Daga nan wani daddaɗan bacci me cike da SO da ƘAUNAR da suke ma junansu ya kwashe su, washegari har kusan a makare suka tashi, don se a gida ya jasu sallar subhi. Daga nan basu komawa tayi ƴan gyare gyarenta ta sake gasa musu namansu na jiya suka karya dashi, sedai yau ɗin ma dai kalan jiya da doguwan riga ta bubu ta fito, se sani ƙaramin vail, har ze mata magana kawai ya kyaleta suka fita. Ajje ta yayi yau be shiga cikin asibitin ba ta wuce ita kaɗai.....
_Byu byu hayya hayya ya take ne?, fatar dai wannan ɗan littafi nawa ze amsu a wurin ku, kamar yacce kuka saba amsar duka littattafaina..._
_Idan naga reactions naku akan littafin zan fara sakinsa nan bada jimawa ba IN SHA ALLAHU....._
_ALLAH yasa wannan salon labarin da muka sanja ya muku, don labari ne akan irin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin gidajen rayuwar aurenmu zahiri da kuma baɗininsu, da yacce wasu mutanen su da kansu ke siyar ƙaddararsu da kansu da kuma hannayensu...._
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
