A CIKIN RAYUWA Page 16 Complete By ZAINAB BATURE - Abokiyar Hira Novels


 _Bossladieswriters_

_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun littafin daga farko, da kuma  abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q

WhatsApp Group

https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

   _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ 

_ZAINAB BATURE_

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 16

Bayan sun isa part ɗin Fahad a falo suka zauna wanda madaidaicin falo ne mai ɗauke da kujeru leathers da kayan sauti da su hotunan family ɗin shi, yar hira suka ta6a kafin Fahad ya miƙe ya ce mashi bari ya je ya watsa ruwa ya rage kayan jikinsa, maida hankali Deen ya yi akan tv bayan ya kamo sport channel wato tashar dake haska wasanni, yana cikin kallon ya ji wayar shi na sanar da shi sweetheart na kira, ɗan jimm ya yi tare da lumshe idanunsa, ya san ko ya ɗaga ba lalle su kwashe ta ta daɗi ba shi da mahaifiyar tashi, sai bayan da kiran ya yanke sannan ya kai hannu ya ɗauki wayan a gefensa ya fara kokarin kiran ta, kamar jira ta ke wayan na fara yin ringing ta yi picking, 

   "Ai da baka neme ni ba Deen a sannan zan san ka cika ɗa, wato rainin da ka yi mani har ya kai haka! Ka tsallake ka tafi ba tare da ka sanar mana ba a matsayin mu na iyayenka, da izinin wa ka tsallake ka bar garin nan? Wai yaushe ka canja ne haka Deen? Gaba ɗaya ka daina ganin girman mu, wani ya fi mu matsayi a gun ka da zai saka ka yi abun da kasan zai 6ata mana rai, alhalin shi ko da wasa ba zai ta6a aikata abu makamancin wannan ba ga na shi iyayen. Ina wayonka da tunaninka suka tafi Nuraddeen!" Shiru ya yi tare da ɗan cize leben shi na ƙasa, daga yadda ta kira ainihin sunan shi ya fahimci ba ƙaramin harzuƙa ta yi ba don ba zai iya tuna when last da ta kira sunan shi haka ba. Sigh ya yi calmly ya ce, "I am sorry mom, ni ban yi haka don in 6ata maku rai ba, ki daina tunanin wai na canza ko na raina ku bana fatan hakan ya kasance, kuma ki daina zargin yaya Fahad ne ya sa na zo nan ba ruwansa ra'ayin kai na ne..."


   "Ka ce ra'ayin kan ka ne Deen? Ra'ayin ka ne ka 6ata mana sannan ka ce wai in daina cewa ka canza?" Ta faɗa bayan ta katse shi, 


   "Ki yi hakuri idan haka da na ce baki ji daɗi ba, ina so ne in fahimtar da ke yaya Fahad bashi da hannu a tahowana nan, shi bai ma goyi baya ba da na ce zan zo nan, a tunaninsa zan bari sai na huta, ni ne na ga is better in taho nan..." Shiru ta ɗan yi da alama nazarin abun da ya faɗa take, kafin ta ce, "Har nan ya fi maka ke nan a kan gidan iyayen ka, haka kake nufi Deen?" Juyar da kan shi ya ɗan yi yana riƙe da wayan a kunnan shi, 


    "Mom I won't hide it from you, bana jin daɗin yadda abubuwa suke faruwa, na daɗe ban zo ba I thought zan samu complete happiness amman sai na ga ba haka ba. Yaya Fahad brother nane, yadda kuke farin cikin zuwa na shima haka ne, shiyasa ya zo wuri na ba wani abu ba amman hakan ya zama abun tashin hankali.." Shiru ya yi bai ƙarasa ba, daga yanayin voice ɗin shi ta tabbatar da gaske ne abun da ya faɗa, yar ajiyar zuciya ta sauke cikin ƙoƙarin daidaita natsuwarta tare da kwantar da murya ta ce mashi shike nan ya yi haƙuri ba zata ƙara yin abun da zai 6ata mashi rai ba. ta ce, "Yanzu yaushe zaka dawo nan don muna son ka a kusa da mu saboda mun yi missing naka sosai." Ɗan murmushi ya yi ya ji daɗin yadda ta yi mashi magana, amsa ya bata da zai ɗan kwana biyu anan saboda yana shirin buɗe club ɗin shi. "To yaushe zaka je can Kano wurin su Ammin suma?" Shiru ya ɗan yi, ba wai bai son zuwa wurin na su ba, kawai akwai abubuwan da suke mashi da baya jin daɗin su bama a zahiri ba ta waya ma, yasan idan ya ce ba zai je ba hakan zai zama wani issue hakan yasa shi ce mata zai je kafin ya koma tun da zai yi 2 weeks kafin ya tafi gaba ɗaya, ta amsa mashi da ok.


    "Have u called Basma?" Ta tambaya, ɗan jimm ya yi yana shakkar amsar da zai bata don shi yama manta da Basmar balle ya neme ta, sai ɗazun da yamma a gidan hajiya da ya ga missed calls nata bayan ya fito daga wanka kuma bai bi kiran ba. "Nah, I wanted to be well settled sai mu yi magana da ita sosai." Amsa mashi ta yi da ok kafin ta ce mashi yanzu sai yaushe za su yi expecting nashi, ya bata amsa da zai yi kaman kwana biyar sai ya dawo, ta ce mashi to ko kawai ya wuce Kano daga nan ma, ya ce mata dole sai ya dawo nan tun da bada mota ya taho ba kuma yana son zai bi jirgi ne zuwa Kanon, saida ta jaddada mashi game da ya kira Basma sannan suka yi sallama. Bayan sun gama wayan shiru ya yi tare da ɗan lumshe idonsa, yana haka Fahad ya fito ya shirya da brown din jallabiya mai gajeran hannu, a kusa da Deen ya zauna yana kallon shi ya kira sunan shi, slowly ya buɗe idon shi tare da kallon shi, gyara zaman shi ya yi ya ce ya fito Fahad ya amsa mashi da eh yana bin fuskarsa da kallo, 


     "Is everything alright?" Cike da kulawa Fahad ya tambaya, ɗan yamutsa fuska Deen ya yi ya ce, "Mun gama magana da mom ne ta yi faɗa akan na taho ban sanar masu ba, amman ba wani abu." Ya ƙarasa with a smile on his face,  shiru Fahad ya ɗan yi yana kallon shi kaman yana nazarin wani abu, sigh ya yi ya furta, "I guess ta yi maka magana akan yarinyan da zaka aura?" Juyowa Deen ya yi ya kalle shi tare da yin dariyarsa mai tsada ya furta, "You guess right. Amman ya akai kasan ta yi mani maganan?" Dan ta6e baki Fahad ya yi yana gyara zaman shi ya ce, "Yakamata ta yi maka maganan ne, ina lura da kai tun a Abuja baka yi waya da ita ba, ɗazun a gidan hajiya ta kira ka lokacin kana bathroom and I thought you will call her back da ka fito sai baka yi hakan ba, nasan dole ta kai ƙarar ka." Dan murmushin gefe Deen ya yi ya kai hannu ya shafi sumar shi. "Na kasa in saba da ita ne a matsayin wadda nike dating, still ina mata kallon sis dina ne." Gyara zama Fahad ya yi tare da cewa yakamata ya saba da hakan, remote Deen ya ɗauko ya sake canza wata sport channel kuma cikin sa'a ɗaya daga cikin wasannin su ne da suka buga a kakar wasanni da ta wuce ake sake nunawa, bayan wani lokaci Deen ya duba agogon hannunsa ya ce ma Fahad bari ya zo ya tafi yana son ya kwanta da wuri don ya huta sosai, kallon shi Fahad ya yi ya ce mashi ya kwana a nan mana, "Ba zaka je aiki gobe ba?" Deen ya tambaya, amsa ya bashi da zai je amman ai gidan ba baƙon shi bane da zai ce sai yana nan zai zauna, murmushi kawai ya yi Fahad ya kai hannu ya ɗauki wayan shi da ya ajiye a gefe ya ce bari ya sanar ma hajiya anan zai kwana kada ta yi ta jira Deen ya furta ok, bayan Fahad ya gama yin wayan ya ce ma Deen ya je ya yi wanka don ya kwanta ya huta, miƙewa ya yi ya nufi bedroom Fahad ya ɗan ɗaga murya yana ce mashi idan ya gama sai ya ɗauki kayan bacci cikin closet ya ɗaga mashi kai. Wayar Fahad ce ta fara yin ringing ya kai duban shi kan screen ɗin ta, mom dinsa ce ya ga tana kira ya ɗauka, tambayar shi ta yi amman anan Deen zai kwana ko ya amsa mata da eh, ta ce ya tambaye shi ko yana buƙatar tea ko coffee ta san turawa da sabo da shan su da dare, murmushi ya yi ya sanar mata ya shiga wanka sai ya fito zai tambaye shi ta amsa da ok. After some minutes Deen ya fito jikinsa sanye da bathrobe, shiryawa ya yi ya saka kayan bacci riga mara hannuwa da wandonta iya gwiwa, yana cikin gyara sumar shi ya ji wayar shi na sanar mashi da ana kira tare da sunan mai kiran wato Basma, sai bayan da ya gama abun da yake yi sannan ya nufi inda wayan take, zama ya yi a bakin gadon ya ɗauki wayan lokacin tuni kiran ma ya tsinke, ya san ko ya kira ta cewa za ta yi su yi vedio call don ta fi son hakan duk za su yi waya, komawa ya yi ɗayan 6angaren gadon ya ɗan kishingiɗa tare da jingina bayansa da kan gadon, vedio call ya shiga kiran ta  yana shiga ta ɗauka, lokacin da ya yi arba da ita har sai da ya ɗan kauda idonsa gefe, ita dai tana son saka fingilallun kaya, har magana sai da ya ta6a yi mata can baya kan irin shigan da take yi idan yana a gida, lokacin sai ta nuna wai miye ai shi yayanta ne, ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita duk da haka bai kamata tana saka kowane irin kaya ba saboda shi ba muharraminta bane amman ta ƙi ta bari. Bayan da maganar aure ta shiga tsakanin su sai ma abun da ya ci gaba, bata jin komai ta saka kowani irin kaya, wani lokacin idan ya je gidansu har sai ya nuna mata 6acin ran shi sannan take canza kaya, duk da wasu kayan ko ta canza duk uwar ɗarin ce amman dai wasu da ɗan dama. 


Itama a kishingiɗe take tana sanye da wata vest kalar ruwan ƙasa da ko rufe mata mara bata ƙarasa yi ba, da wando casual short, irin ɗan guntun wandon jeans da iyakarsa tsakiyar cinyoyi, a kunnanta ta saka manyan zagayayyun ƴan'kunne dake da stones masu sakin ƙyalli, ɗayan hujen kunnan da take da ta saka ɗan kunne barima. Shiru ta yi tana kallon shi tare da ɗan kikkafta idanunta dake ɗauke da dogon gashin ido masu gazar-gazar,

 

  Ɗan murmushi ne akan fuskar Deen ganin kallon da take bin shi da shi irin na kana tuhumar mutum da laifi, 


   "Basma, How are you doing?" 


Ɗan kauda ido ta yi, sam bata jin daɗin yadda ya ƙi daina kiranta da sunanta ya rinƙa kiran ta da sunan da ke nuna akwai soyayya a tsakanin su, maido idonta ta yi suka shiga cikin na shi, "Do you even care how I’m doing?" Ta tambaya da ɗan yanayin fushi, yadda ta yi maganar cikin salo da sarrafa labbanta, still murmushin ne akan fuskarsa yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba,


  "Now that you are settled after arriving at your destination yesterday, i thought you would want to catch up on how I’m doing. It feels like I’m not a priority." Ta faɗa da  London accent, 


Shafa sumar kansa ya yi ya ce, "Don't think that way, I'm not fully settled yet. Na daɗe ban ziyarci nan ba, and you know my career as a footballer keeps me busy with so many things." 


Har ta ji sanyi a ranta hakan da ya faɗa, shiru ta yi tana jefa mashi kallo mai cike da so da ƙauna, "Ya dad da mom?" Amsa mashi ta yi da suna lafiya, ta tambayi suma bai tuntu6e su bane tun da ya bar nan? ya bata amsa da sun yi magana, "Ni ce baka samu lokacin ka yi magana da ni ba?" Ta yi maganar tana mashi kallon tuhuma,  da ɗan murmushi kan fuskarsa ya ce mata no ba haka bane ya bari ya samu isasshen lokaci ne da za su yi magana, su dad kawai sun gaisa ne, har ta ji daɗi daga murmushin da ta yi.


   "Ya hutun ka? Are u enjoying it?" Kai ya jinjina mata alamar yana jin daɗin hutun, ta ce, "Mom ta faɗa man kana garin su dad, ta ya za ka ji daɗin hutu a nan ƙauyen?" Murmushin gefe ya yi, ya bata amsa da ai sai ya fi jin daɗin hutu a nan tun da bai saba da irin wurin ba sosai, ta6e baki ta yi kafin ta tambayi yaushe zai koma ya faɗa mata, 


    "Ba don bana son zuwa 9ja ba da zan biyo ka ne, ko da ba a yi hutun skul ba." Ta faɗa tana kanne mashi ido, tambayar ta ya yi saboda mi ba ta son zuwa? 


  "Kawai bana jin daɗin zama a country ɗin." Ɗan jinjina kai ya yi, ya ce "Yakamata kuwa ki koyi jin daɗin zama tun da kaman ƙasar ki ce, parents ɗin ki nan ne asalin su." Ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba. Magana suka ci gaba da yi, yawanci duk ita ce ke yin maganar ya bata amsa, jin alamar an shigo ya sa shi kallon wurin kofar ɗakin, Fahad ne ya shigo ganin waya a hannun shi ya dakata daga bakin ƙofar tare da tambayar shi yana waya ne Deen ya ɗaga mashi kai alamar eh, amsa masa ya yi da ok bari ya gama, "Da wani abu ne?" Har zai juya ya ji Deen ya tambaya, dakatawa ya yi ya ce mashi dama mom ce ta ce a tambaye shi ko yana buƙatan wani abu na ci ko sha, ɗan murmushi ya yi ya bashi amsa da no ai sun ci abinci.


  "Ba ka buƙatan tea ko coffee? Ta ce ta san ku turawa kun yi sabo da shan su kafin ku yi bacci." Ɗan faffaɗan murmushi Deen din ya yi ya ce kamar kuwa ta sani ya yi sabo da shan coffee kafin ya kwanta, amma ba sai sun wahalan da kan su ba, Fahad ya ce to miye abun wahala ko Sadeeya sai ta haɗa mashi, "Ba kana kan waya bane?" Fahad ya tambaya, Deen ya ce, "Yea, Basma ce." 


  "Ka ce kai da amarya ne ake shan luv na zo na katse ku." Wani kallo Deen ya yi mashi wanda nan take Fahad ɗin ya fahimci mi kallon ke nufi, ɗan murmushi Fahad ya yi tare da juyawa ya fice, tambayar shi Basma ta yi waye suke magana bayan ya maida fuskarsa kan screen ɗin wayan ya bata amsa Fahad ne, da yake ta san Fahad ɗin ta ce yana ina su gaisa, wani kallon baki da hankali ya jefa mata ganin da irin shigar da ke jikinta take cewa za ta gaisa da wani, ya san a wurin ta hakan ba wani abu bane, amman koda ba wani jin ta yake a ransa ba nan da ɗan lokaci za ta zama iyalinsa dole ya yi kishin a gan ta haka, amsa ya bata da Fahad ya fita ta amsa da ok, ƴar hira suka ƙara yi kaɗan ya ce mata yana son ya kwanta ya huta sai sun ƙara yin magana, ba don ta so su gama yin wayar ba a lokacin, ta ce sai yaushe za su ƙara yin magana ta san sai bayan wasu kwanakin kuma, gudun jan maganar ya sa shi ce mata da ya samu lokaci zai kira ta, ta amsa da tana jira idan kuma ta ji shiru ita za ta neme shi dama ta fi damuwa da shi, murmushi kawai ya yi ya ce mata good night, 


    "Just gud night? Ta tambaya ta dan ƙanƙance ido, gaba ɗaya ya ƙosa da wayan ya san idan bai yi mata yadda take so ba ba za a gama wayan ba, ya sake ce mata, "Gud night. I luv u." Murmushi mai fadi ta yi ta farfara mashi ido itama ta ce mashi, "Luv u more honeypie. Gud nyt and dream of me." Ta faɗa cike da salo da kisisina, lumshe ido ya yi tare da ɗan ɗaga mata kai daga haka ya kashe, wurgar da wayan ya yi gefe ya ɗage kan shi a jikin gado tare da rufe idanunsa kamar mai yin tunani, turo kofar ɗakin aka yi Fahad ya shigo hannuwansa ruƙe da kofuna tiriri na fitowa, sauke kai Deen ya yi yana kallon shi ya ƙaraso bakin gadon tare da miƙa mashi kofi ɗaya, "Thank u mah friend." Deen ya faɗa yana murmushi bayan ya amshi mug ɗin, a gefen shi bakin gadon ya zauna yana rike da ɗayan kofin, tambayar shi ya yi har ya gama shan luv din, Deen ya yi faffaɗan murmushi tare da shafar sumar gemunsa, a tare suka fara sipping coffee din, Deen ya ɗan dakata yana tambayar Fahad shima yana shan coffee ke nan da daddare, "No, jefi-jefi. Na fi shan black tea." Wayar Fahad ce ta fara ruri ya kai idonsa kan ta, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ganin mai kiran nasa wato Leemarh, a saman bedside drawer ya ɗaura kofin coffee din, ɗaukar kiran ya yi ya kara a kunne a nutse ya furta bari ya kira ta, katse kiran ya yi ya sake kira, jin ta yi shiru bayan ta yi picking ya ce, "Sis Leemarh..." Ciki-ciki ya ji ta amsa, murmushi mai ɗan faɗi ya yi don ya fahimci dalilin amsa masa hakan da tayi, "Hope kuna lafiya?" Ya tambaya, yadda ta amsa da ya kira sunan ta yanzu ma haka ta ba shi amsa da eh, "Tell me, ya aka yi ne na ji muryan ki haka?"  Ya tambaya still da murmushi akan fuskarsa, kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ya ji ta fara cewa, "Ba kai bane..." Hannu ya kai ya shafi sajen shi ya ce, "Uhuym, ina ji mi na yi?"


   "Ai ka sani...shi ne zaka tafi without saying goodbye." 


   "Eyya, I am sorry for dat idan baki ji daɗi ba. Amman ai dama kin san ba da shirin kwana na zo ba, kuma ke ce kika roƙi in tsaya in kwana, dama ba zan wuce yau ba."


   "Na sani, amman sai kawai ka tafi ba za ka bari mu tashi mu yi bankwana ba." Murmushi ne bayyane akan fuskarsa.


  "Ok na amshi laifi na, ina son zuwa wurin aiki ne shi ya sa muka taho da wuri." 


  "To yaushe za ka ƙara zuwa?" Shafa sumar kan shi ya yi, "Sai wani lokacin kuma." Da sigar shagwa6a ta ce ita dai ya faɗa mata lokacin da zai ƙara zuwa, faffaɗan murmushi ne akan fuskarsa ya ce mata da a ce Deen na nan Abuja ne to sai ya ƙara zuwa wurin shi, amman yanzu suna tare.


   "Shike nan, ni idan aka yi  mana hutu zan zo nan." A cikin ransa ya ayyana Allah Ya sa wannan mom ɗin taku ta amince, a fili ya ce hakan ya yi za su jira ta, tambayar shi ta yi zai ji daɗin zuwan nata? ya bata amsa da sosai ma ya san kowa ma gidan zai yi farin cikin zuwanta, 


   "What are you doing now? Ko kana chat da girlfriend ɗin ka?" Murmushi mai ɗan sauti ya saki jin tambayar da ta yi mashi, ya ce, "Ga ni tare da Deen muna shan coffee. Ni bani da girlfriend ai" Tambayar shi ta yi da gaske? ya bata amsa "yea," "To yaushe zaka yi?" Still d murmushi ya bata amsa da sai ya shirya yin aure sannan don bai son wasting time din shi da na wata, ƴar hira suka ƙara yi kaɗan ta ce bari ta bar shi ya sha coffee ɗinsa suka yi sallama. Haɗa ido suka yi da Deen dake sipping coffee a natse, ɗage mashi gira ya yi ya ce, "An gama luv en?" Ƴar dariya Fahad ya yi don ya gane tsokanar da ya yi mashi ɗazun ce shima ya rama, ɗaukar coffee ɗin shi ya yi tare da bashi amsar cewa ai ya faɗa mashi ba soyayya suke da Leemarh ba, kawai sun shaƙu da juna ne, miƙewa Deen ya yi yana faɗin in ma da abun da suke 6oyewa ai lokaci zai bayyana ya wuce toilet don ya wanke baki, lokacin da ya fito Fahad ya gama shan coffee ɗin,


"Ina zaka je ne?" Fahad ya tambaya ganin ya miƙe da kofunan da suka gama shan coffee, ya ba shi amsa da zai fita da mugs ɗin ne, dakatar da shi ya yi ya ce ya bari Sadeeya zata zo ta ɗauka......

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post