*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣0️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Da zarar Ching Ching ta faɗo daga sama, Chief Onyx ya cafke ta a hannunsa cikin firgici..
Jikinta ya yi sanyi, numfashinta yana fita da ƙyar, jini kuma na zuba daga bakinta..
“Ching Ching… Ching Ching!”
ya ƙira sunanta da ƙarfi, amma babu amsa..
Gely ta matso kusa da su, fuskarta cike da nadama da tsoro. Idanunta shanye kamar mai jin bacci lokacin da ta ga yadda jinin ke ƙara fita...
“Boss… dole ne mu tafi asibiti yanzu nan,” ta faɗa cikin rawar murya..
Chief Onyx bai tsaya jayayya ba. Yana ɗauke da Ching Ching a hannunsa kamar jaririya, ya fice da sauri daga ɗakin... Siren na gaggawa ya fara ƙara a cikin harabar fadar, motocin tsaro suka fara motsi da kansu, suna sarrafa kan su, jira suke kawai a shige su, su fara tafiya...
Cikin mintuna kaɗan, sun shige cikin motar gaggawa mai sauri ba tare da masu tuƙa su ba. Kawai iya rubutu yayi a allon gaban motar ta ciki, ya rubuta yanda zai kai su.. shi kuma yana ɗauke da Ching Ching akan cinyarsa, idonsa a kanta kamar zai iya dawo da ranta da kallo kaɗai...
Motar ta ratsa titi cikin gudu, hasken ja da shuɗi na walƙiya...
Pavilion babban birnin zamani ya bayyana da fitilunsa masu sheƙi, amma a zuciyar Chief Onyx babu komai sai tsoro..
“Ki jure… ki jure Ching Ching,” ya faɗa a hankali, murya tana karyewa. “Ban gama dake ba… ba zan bar ki ba.”
Bayan sun isa Babban Asibitin Pavilion, likitoci da nas-nas suka ruga suna tura gadonta zuwa sashen gaggawa. Chief Onyx ya dakata a jikin ƙofar.. Yana kallon ciki dake glass door ne...
Gely ta iso daga baya, ta tsaya nesa tana kallonsa. A karo na farko, ta ga Chief Onyx cikin tsoro da tausayi..
A ta ciki kuwa, rayuwar Ching Ching tana rataye ne tsakanin rai da mutuwa.
A wannan ranar an shawo kan Ching Ching dake kwararrun likitoci ne a asibitin...nan danan suka gama..
✨✨
*Washegari*
Haske na safiya yana ratsawa ta tagar ɗakin a hankali. Na’urorin asibiti suna fitar da ƙananan ƙara masu natsuwa. Chief Onyx yana zaune a kujerar gefen gadon, idanunsa sun nuna alamun gajiya, domin bai ko motsa ba, hannunsa yana riƙe da na Ching Ching kamar zai ɓace idan ya sake ta...
Ching Ching ta motsa kaɗan, sai ta buɗe idanunta a hankali. Da farko duhu ta gani, sai fuskar Chief Onyx ta bayyana a gabanta. Ta ɗan lumshe ido, sannan ta yi murmushi mai cike da rauni...
“Uncle…”
ta ce da muryar da ke fita da ƙyar, “yanzu na zama jaruma ko? Ba ‘yar aiki kaɗai ba?”
Onyx ya sauƙe ajiyar zuciya, ya matse hannunta a cikin nashi, yana kokarin yin murmushi. Ya sunkuya ya sumbaci goshinta a hankali..
“Fiye da hakan, Ching Ching,” ya ce cikin tausayi.
“Ke ce zuciyar fadar Chief Onyx.”
Ta turo baki kamar yarinya ƙarama, idonta fari sol cike da barkwanci duk da rauninta..
“To… to kai ɗin mijina ne?”
Chief Onyx ya zaro ido da sauri..
“Eh? A’a! A’a!” ya ce cikin hanzari. “Ke yarinya ce, baki girma ba.”
Ta ɗan ɗaga gira, ta ce,
“To wacece zata zamo matarka ta haifa maka yara?”
Ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai kuma murmushi ya zauna a fuskarsa..
“Ke zaki zaɓa min da kanki.”
Nan take ta tintsire da dariya, duk da ƙirjinta yana ɗan mata zafi...
“Idan ka fita dani yawo, zan nema maka kyakkyawa… amma fa sai mai kirki!”
Onyx ya shafa kanta a hankali, ya gyara mata gashin kanta..
“Shikenan,” ya ce cikin murmushi mai cike da ƙauna..
A wannan lokacin, likita ya leƙo ta ƙofa yana kallon su da mamaki..
“Sannu patient,” ya ce yana girgiza kai, “an samu sauƙi kenam.”
Ching Ching ta juya kai ta ce,
“Likita, ka gani ko? Ni ba mara lafiya ba ce… ni special guest ce!”
Chief Onyx ya yi murmushin gefen baki kamar yadda ya saba idan yana tare da ita...
Bayan kwana 5 da kwanciya a asibiti, jikin Ching Ching ya murmure sosai. Likitoci sun sallame ta. Wannan ne karon farko da ta fito daga cikin fadar pavilion...
Bayan barinsu Hospital kai tsaye super shop suka nufa, zasu yi siyayya kafin su wuce gida..
Motar Chief Onyx mai tsaron kansa ta tsaya a harabar Super market.. Ƙofar ta buɗe a hankali, Gely ta fara sauka, idonta na scanning ko’ina kamar yadda aka saba.. Bayan ta tabbatar da komai lafiya, ta buɗe ƙofar baya...
Ching Ching ta sauko cikin fara’a, tana kallon ginin birnin kamar yarinya da aka kai ta sabuwar duniya...
“Wow…” ta furta, “ashe Pavilion City ba kawai labari ba ne...”
Chief Onyx ya tsaya gefe ɗaya, cikin baƙaƙen suits ɗinsa ta shugabanci, fuskar nan tasa tana nan cikin tsauri da natsuwa...
Mutane na wucewa suna gaishe shi cikin girmamawa, wasu ma na sunkuyar da kai. Mata da dama suna ɓoye kallonsa, amma shi ko ɗago ido bai yi ba...
Shugaban Pavilion City gaba ɗaya, matashi mai jiji da kai, kwarjini da girman kai. Kyawunsa ba abin jayayya ba ne, kuma shiru da sanyi da halayensa sun hana kowace mace kusantarsa. Ba ya kallon mata, balle ya bari zuciyarsa ta yi tunani a kansu...
Ta juya ta kalli Chief, ta ce,
“Uncle, mutane suna kallonka kamar ana kallon zinare a kasuwa.”
Ba tare da ya kalleta ba, ya ce a taƙaice,
“Ki yi tafiya a hankali.”
Ta murmusa, ta ce,
“Uh uh… ka ji yadda yake magana kamar robot, amma robot ɗin ma ya fi ka jin tausayi.”
Gely ta ɗan juya kanta, ta ce cikin murya ta robot,
“Correction... Boss yana da tausayi… amma ga ke kaɗai.”
Chief ya tsaya cak, ya kalli Gely...
“Gely.”
“Noted, Boss.” ta furta tare da yin gaba..
Ching Ching ta fashe da dariya..
“Kin gani ko? Yana abu kamar duniya aka ɗora masa a kai..!”
Ya ci gaba da tafiya, amma a karon farko, wani ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, murmushin da bai ma lura da shi ba...
Sun shiga wani tsararren super shop mai ɗaukar ido, gilashi masu sheƙi suna sarrafa kansu ga kuma fitilu masu walƙiya da kaloli mabanbanta, ga kayan alatu da ba kowa ke iya saya ba...
Ƙofar ta buɗe kai tsaye da na’ura, jama’a suka juyo a lokaci guda.
Bodyguards masu baƙaƙen kaya suka zagaye su, suna tafiya cikin tsari. Gely tana gaba, idonta na scanning kowane motsi. Duk wanda ke shop ɗin ya san Chief Onyx ya shigo...
Matan dake cikin shop ɗin suka tsaya cak. Wasu na masa kallon sha'awa da burge wa, wasu kuma na gyara tsayuwarsu, wasu kuma suka fara kallon Ching Ching cike da hassada...
“Wacece ita?”
“Me yasa ita ce kusa da shi?”
“Me ye matsayinta a wurinsa?”
Ching Ching kuwa idonta na kan kayayyaki..
Ta ga kayan ado masu sheƙi idonta suka haskaka..
“Uncleee! Ka ga wannan?”
Ta ɗauki abin wuya..
“Da wannan?”
Ta ɗauki zobe..
“Wannan kuma fa?!”
Ba ta jira amsa ba ta ci gaba da ɗauka tana ajiyewa a cikin trolley kamar yarinya a kasuwar kayan zaƙi...
Chief Onyx yana tafiya a bayanta cikin shiru, fuska a ɗaure. Bai ce komai ba, amma kowa da ya san shi, ya san wannan shiru ba alheri ba ne...
Matan shop ɗin suna kallon Ching Ching suna harararta duk da sun ji tana ƙiransa da Uncle..
“Ta ɗauka kamar komai nata ne anan wurin.” wata ta furta tana harararta domin ba'a san iya adadin matan da suke ƙaunar Onyx ba..
“Da shi take magana wai? Na ga ko ta kanta baya bi...”
Wata ta ba da amsa, "ta ya zai kula ta, kalan a raina shi, wannan kucakar yarinya ƴar hau..."
“Ai ba ta kai ya kula ta ba wallahi....”
A gefe guda kuma,
Ching Ching ta ɗauki wata rigar zinariya, ta ɗaga ta sama ta ce da ƙarfi,
“Uncle, wannan zata yi min kyau ko?”
Chief ya tsaya tare da wurga mata kallo ta gefen ido...
“Ki ajiye.”
Ta turo baki, ta ce,
“Me ya sa? Kana da kuɗi fa.”
Nan take iska ta canza.
Ya matso kusa da ita, yana zaro mata ido...
“Ba batun kuɗi ba ne.”
Ganin tana shirin zubar masa da girma yasa ya barta ta ɗauka...
Haka ta nufi wurin ciye-ciye taita jidan cake da sweet da abubuwan zaƙi...
Shiru ya lullube shop ɗin.
Sai kuma kuskuren da Ching Ching ta yi...
Ta juya, ta kalli wata mace dake tsaye gefe, sannan ta ce cikin ɗaga murya..
“Kin ga wannan? Shi ɗin mijina ne, Shi ne yake biya min komai... Wallahi kuwa...”
Tsit wurin yayi ana sauraronta..
Kamar an danna maballin tsayar da lokaci..
Chief Onyx ya ɗaure fuska gaba ɗaya.
Idonsa ya sauya, jijiyoyin wuyansa suka fito. Ya kamo hannunta da ƙarfi, cikin tsaurin iko ya furta...
“Na ce miki meye? Ni za ki kalla kice mijinki? Kina nan kwaila dake, me ya sa kike son zubar mun da kima ne? To ki kama kan ki, ni ba abokin wasan ki bane...”
Ta ɗan tsorata, ta ce,
“Uncle… wasa nake fa.”
Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido...
“Ni bana wasa da sunana.”
Ya juya ya kalli Gely.
“Gely. Mu tafi....Yanzu.”
Gely ta amsa nan take,
“Yes, Boss.”
Bodyguards suka matsa gaba, jama’a suka rarrabe gefe-gefe kamar ruwa..
Ching Ching ta tsaya cak, murmushin ya ɓace daga fuskarta. A karo na farko, ta gane cewa ta taka layin da bai kamata ba..
Sauran ƴanmatan kuwa dariya su ka shiga yi bayan fitar Chief,
"Waii miji....Su miji manya.."
Ching Ching bata ko kula su ba, itama ta fice..sauran kayayyakin da ta ɗauka duk an biya, wani bodyguard ne ya ji do su...
A cikin motar, Chief bai ce kalma ɗaya ba.
Ching Ching ta kalli gefensa, zuciyarta na bugawa...
“Na ɓata masa rai…”
Ta furta a cikin ranta...
A cikin motar alfarma, shiru ya mamaye ko'ina, Chief yana zaune gefen Ching Ching, fuska a daure, idanu na kallon gaba kamar ba kowa a gefensa..
Motar ta ratsa wani tsararren titi mai yalwa. A gefe, wani babban private school ya bayyana, ginshiƙai masu sheƙi, ƙofar zamani, fitilu masu launi..
A nan ne ɗalibai suka fara fitowa, sanye da uniform masu tsabta, suna wasa da dariya, ko wacce na magana da ƙawarta, wasu suna tafe da jakunkuna a bayansu... Bus ɗin makaranta na jiran su, ƙofar a buɗe..
Idanun Ching Ching suka manne a wajen ba tare da wani motsi ba..
Murmushi ya fara tsiro a fuskarta, murmushin da ba na wasa ba, sai na tsantsar buri...
Ta matso kusa da gilashin motar, tana kallon yadda ɗaliban ke hawa bus ɗin cikin farin ciki..
Ta ɗan ɗora hannunta a kan gilashin, kamar tana so ta taɓa abin da take gani..
“Uncle…” ta fara cikin murya mai sanyi...
“Ka gan su ko?”
Chief Onyx bai ko juyo ba, bai kuma amsa mata ba...
Ta ci gaba, kamar tana magana da kanta...
“Wallahi suna da sa’a sosai.”
Ta yi dariya kaɗan, mai ɗauke da wani irin baƙin ciki..
“Ni fa… ban taɓa shiga irin wannan bus ɗin ba.”
Ta waiwaya ta kalle shi, tana sa ran zai kalle ta.
Amma yana nan yadda yake, cikin shiru da ƙasaita, fuska na kallon gaba...
Ta sake murmushi, ta fara magana a hankali kamar yarinya da ta samu abin da ke faranta mata rai..
“Idan na shiga makaranta fa, zan zauna a gaba. Zan ɗaga hannu kullum. Zan yi rubutu sosai. Zan samu abokai da yawa…”
Ta yi tsallen tunani, ta ce cikin dariya..
“Watakila ma zan zama mai hayaniya a aji!”
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sannan ta ƙara da murya mai rauni..
“Amma ban taɓa zuwa ba.”
Motar ta ci gaba da tafiya.
Suka bar Bus ɗin makarantar a baya..
Chief Onyx har yanzu bai kalle ta ba.
Amma a cikin zuciyarsa wani abu ya motsa.
Hannunsa ya matse a hankali a kan cinyarsa.
Ching Ching ta koma ta jingina da kujerar, murmushin yana nan, amma idanunta sun ɗan yi ruwa.
Ta ce cikin raha, tana ƙoƙarin ɓoye abin da take ji..
“Da ace ina makaranta, da na zama shahararriyar ɗaliba. Kai ma da zaka zo Parents’ Day ka zauna ka yi shiru kamar yadda kake yi yanzu.”
Ta juya ta kalle shi..
“Kai kuwa ka je makaranta a lokacin da kake yaro ko? Kana son abin da nake nufi ko? Playground, library, school uniform mai kyau… duk abin da ke cikin movies na ke so in gani a gaske...”
Ta yi murmushi, ta kuma cewa..
“Ni ma na so in sami classmates da za su zama abokaina, in yi exams da su, in sami certificate… ba wai kawai ilimin gida ba...”
Haka ta rinƙa surutu ita kaɗai..
Motar ta nufi gida.
Amma tunanin makarantar…
ya riga ya shiga zuciyar Chief Onyx..
✨
Bayan kwana biyu, yanayi ya sake sauyawa...
Chief Onyx yana cikin wurin wankansa na sirri, yana ta ninkaya cikin ruwan private pool ɗin da ke kewaye da furanni da shuke-shuke masu tsada..
Jikinsa babu komai sai gajeren wando, wanda ya bayyana ƙarfinsa da jarumtarsa. Ruwan yana rufe faffadan kirjinsa yayin da yake shawagi a ciki cikin natsuwa..
Bayan ya ɗau mintuna a nutse cikin ruwan, da ga bisani ya ɗago ya sa hannu yana matse ruwan gashinsa da ya jiƙe, yana tsaka da wasansa sai ga Chingching ta bayyana ɗauke da tsintsiya da bokiti... Ta shigo tana rera wata waƙa da ƙarfi, kamar ba ta san inda take ba, wai ita a dole shara ta zo yi a daidai wannan lokaci!..
_“Sharar da ke da kyau, sai a yi shi a lokaci mai kyau…_
_Idan lokaci ya zo, sai a yi shi ba tare da jawa ba!”_
Waƙar da take rerawa kenan 😅
Onyx ya tsaya cak, ruwa na saukowa daga jikinsa. Ya kalleta cikin mamaki, sannan ya haɗe rai kaɗan, duk da cewa akwai murmushi da ya ɓoye a fuskar sa...
“Ke kuma,” ya faɗa cikin sanyin murya,
“sharar me kika zo yi a nan? Kin san sarai wannan lokacin nawa ne na shakatawa.”
Chingching ta ɗage kai, ta fara share ƙasa alhalin babu ko ƙura. Ta turo baki tana cewa..
“Aiki na ne ai, Uncle.... Gani nayi wurin nan ya fara datti. Ni ban son ganin datti. Ka ci gaba da wankanka, ni sharata zan yi na wuce.”
Sai dai duk da maganganunta, idonta na satar kallon jikinsa, zuciyarta na buga mata wani irin bugun da ba ta saba ji ba..
A hankali, ya fito daga cikin ruwan sharkaf, ya tsaya da ɗan takaitaccen taku a gabanta. Faffadan kirjinsa yana kyalli, ruwa na digowa a hankali. Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido, muryarsa ta sauya ta zama ƙasa-ƙasa..
“To tunda sharar kika zo yi, kuma baki son datti…
ki share jikina.”
Nan take Chingching ta ruɗe.
Ta tsaya tana nuku-nuku, hannayenta na wasa da juna, idonta a ƙasa...
Fuskarta ta fara canja launi saboda kunya da fargaba. Ta kasa motsawa, balle ta miƙa hannu ta taɓa shi.
Onyx ya lura da rikicewarta. Wani gajeren murmushi ya leƙo a gefen leɓɓansa.
Cikin ƙiftawar ido, kafin ta ankara, sai kawai ya sa hannu ya damko kunkuminta, ya ɗaga ta sama kamar yar tsana ya cilla ta tsakiyar pool ɗin...
Ruwa ya tashi sama, ya yayyafa ko’ina. Sai da ta nitse gabaɗayanta kafin ta ɗago tana faman fyace ruwa. Onyx kuwa tuni ya ɗauki tawul, ya rataye shi a wuya, yana kallonta cikin murmushi...
“Wannan ne ladan sharar da kika zo yi,” ya faɗa yana dariya a hankali..
Ya juya zai tafi.
Da ta ga hakan, ta zauna a cikin ruwan, ta fara kukan shagwaba, tana buga ƙafafunta a cikin ruwan...
“Haba Uncle! Don Allah ka dawo! Ka taimaka min! Ka duba yadda ka jiƙa ni, ni ba zan iya fitowa ba!”
Ta yi tsammanin zai tausaya ya dawo kamar yadda take gani a fina-finai...
Amma ina!
Onyx ko waiwaya bai yi ba. Ya ci gaba da tafiyarsa cikin natsuwa, har ya ɗaga mata hannu alamar ban-kwana, sannan ya ɓace daga wurin..
Nan take ta gane wasan ya zama gaske.
Ta tsagaita kukan, ta share idonta, tana kallon hanyar da ya bi. Ta murguɗa baki tana gunaguni..
“Lallai mutumin nan mugu ne ashe… ya bar ni a nan ni kaɗai, alhalin ya san ban iya ninkaya sosai ba.”
Ta fara jan jikinta a hankali, tana lallabawa har ta fito daga ruwan. Rigarta na ɗigar da ruwa, gashinta manne da fuskarta...fuskarta cike da ɓacin rai...
Ta zauna a gefen ruwan, tana huci...
“Wallahi sai ya ji irin abun da na ji… ba bashi a tsakanin mu saina rama....”
“Amma dai,” ta faɗa tana tsuke baki,
“sai na rama.”
A wannan lokaci…
Chief Onyx ya riga ya bar wurin pool ɗin tun da dadewa.
Ya shiga sashensa na kwana...
Wurin ya kasance shiru, tsabta, babu komai face kamshin turare mai sanyaya rai..
Ya cire tawul ɗin jikinsa.
Ya tsaya gaban madubi na ɗan lokaci, fuskar nan tasa, ba murmushi ba kuma fushi a fili..
Ya fara shiryawa cikin kaya masu tsada da tsari..
Ya lanƙaya agogon da kowa ke tsoro idan ya gani, da kuma takalmin da ke sa kowa ya san mai iko ya zo..
Gely ta bayyana a gefensa.
“Boss, motoci sun shirya.”
“Mu tafi.” ya furta a daidai lokacin da ya gama shirinsa...
Yana tafe, Gely na biye da shi a baya..
Bayan mintuna akan tsararren kwalta, motocin suka tsaya gaban babbar makaranta mai katanga ta alfarma..ga tambarin makarantar da tutoci na ƙasashe daban-daban suna kaɗawa a iska...
SUNAN MAKARANTAR... AURELIUS CROWN INTERNATIONAL ACADEMY
(Elite Boarding School for Global Leaders)
Makarantar da ba a biya da nairori sai tsantsar zunzurutun daloli kaɗai..
Makarantar sai ‘ya’yan shugabanni, sarakuna, attajirai, da ‘ya’yan jakadu ne kaɗai ke nan..
Bayan aka ga tambarin Chief Onyx, jami’an tsaro suka miƙe tsaye..
Ba tare da tambaya ko bincike ba.... Suka buɗe ƙofa kai tsaye..
Shugaban makarantar da kansa ya fito, tsoho ne mai farin gashi, fuska cike da annuri da ladabi ya furta..
“Your Excellency, Chief Onyx.”
Ya sunkuyar da kai.
“Abin alfahari ne samun zuwanka.”
Onyx ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi cewa,
“Na zo ne domin registration.”
Idanun shugaban makarantar suka buɗe..
“Cikakke?”
Domin ba kowa ke biyan full a lokaci guda ba, wani duk da kuɗinsa sai ya raba sau biyu, wani uku...
“Cikakke,” Onyx ya amsa a taƙaice..
Suka shiga babban ofishin makarantar.... Aka buɗe computer da ake tura kuɗi ta cikinta daga nan ya wuce babban bankin duniya...
Adadin ya bayyana a allon kwamfuta, ga daloli masu nauyi.
Adadin da zai sa yawancin iyaye su faɗi daga kan kujerun su...
Ba tare da tambaya ko jinkiri ba ya furta..
“Done,”
Cikin mintuna kaɗan, an kammala biyan kuɗin makaranta, uniform, litattafai da komai da komai da sunan Ching Ching...wato Firdousee Muhammad Nourdeen...
Shugaban makarantar ya yi murmushi cike da girmamawa...
“Dalibar za ta fara nan da nan. Makarantarmu tana alfahari da wannan suna.”
Onyx ya miƙe tsaye yana furta.
“Ba don suna na ba, sai don makomarta...”
✨✨✨✨
Bayan dogon lokaci, Sarki ya dawo masarauta cikin kwarjini da izzah. Nan take ya bayar da umarnin taron gaggawa na duk gimbiyoyinsa. A cikin fadar, an jera kujeru na alfarma, kowacce da kalar da ta dace da asalin gimbiyar da za ta zauna akai...
(Kamar yadda muka ce a last Page)
Kuma a lokacin Ayat a matsayin Inuwa tana wurin Master suna tattauna wani batu..
Jin sanarwar sarki yana son ganin GIMBIYOYINSA yasa ƙirjinta bugawa, tasan dole za'a je duba ta...
Shin ya zatayi ga master ya riƙe ta?..
Ta saddaƙar yau kam asirinta zai tonu domin za'a sanar cewa babu Gimbiya Aayat...
Tana ta jira taji wannan sanarwa..
Ta saddaƙar sosai..domin tana tsaka da aiki da master Ibrahim..
Sai addu'o'i take ta jerowa..
Daga can nesa, sautin motocin alfarma ya fara tashi... Masu shelar masarauta suka gyara muryoyinsu a lasifika..
Motar gimbiya Zayana ce ta tsaya fara sol, ta fito..
Mai shela ya fara ƙirari..
_"Haske uwar haske! Kyakkyawa ba gajiyawa. Sarauniyar sanyi, farar mace mai kyan hali da kyan jinsi. Jinin turawa, asalin Turai, wadda kyanta ya haska fadar Alhamra. Barka da isowa, Gimbiyar Alfarma, Zayana!"_
Mota kalar ruwan gwal ta bayyana, wato gimbiya Maayah..
Mai shela ya barke da cewa,
_"Zinariyar fada, asalin Indiya! Kyakyawa mai gashin kwance, wadda idanunta suka fi taurari haske. Ɗiyar Taj Mahal, mai tafiyar kyan gani. Maayah, tauraruwar dake haska duhun fada, barka da isowa!"_
Can sai ga
Gimbiya Yumna, motarta kalar silk ta tsaya... Itama aka fara mata ƙirari..
_"Bishiyar inuwa, Gimbiyar Fulani! Kyakyawa doguwa, mai hancin siffa. Farar fulani, uwar dangi, wadda kwarjininta ya cika fada. Yumna, bishiyar da kowa ke son ya huta a inuwarta, barka da isowa!"_
A ofishin Master Ibrahim, Ayat wato Inuwa tana tsaye, ƙafafunta suna rawa... zuciyarta na bugawa domin a yanzu ko wace gimbiya an kawo ta fadar sarki da mota, duk sun kammala amma babu gimbiya Ayat...
Lokaci guda ta ji an fara ƙiran sunan Gimbiya Ayat...
Zuciyarta ta kusa fitowa daga ƙirjinta..
"Na shiga uku! Wanene za a kira a matsayina?" ta yi maganar zuci..
Lokacin da aka duba asusun gimbiyoyi aka ga kowa ya halarta banda ita, sai ga wata baƙar mota ta silalo ta fake..
Ƙirarin Gimbiya Ayat ne ya fara amo..
_"Tauraruwar Gabas! Farar wata dake haska sahara. Asalin Larabawa, ɗiyar gidan mutunci. Ayat, wadda fuskarta ke rufe da kwarjini da labule. Barka da isowa, sarauniyar zuciyar sarki!"_
Inuwa ya zabura, ya nufi fadar cikin sauri, Master Ibrahim ya biyo bayansa cikin mamaki. Suna isa ƙofar fadar, Inuwa ya ga wata mace ta fito daga motar, siffarta, tsayinta, da kayanta duka IRIN NA AYAT NE! Fuskar mace dake rufe da mayafi ta sa Inuwa daskarewa...
"Wannan wacece? Wacece wannan dake wasa da raina?" Inuwa ya tambayi kansa cikin tsoro da matuƙar mamaki. Master Ibrahim ya kalle shi, "Lafiya Inuwa?" Inuwa ya gyara muryarsa,
"Lafiya Master, kawai kwarjinin gimbiyoyin ne ya ba ni mamaki."
Sarki ya kalli gimbiyoyinsa guda huɗu dake zaune, ciki har da Ayat ta bogi. Ya gyara zama, muryarsa ta daka cikin fadar..
"Na ƙira ku ne don in bayyana muku wani sabon sauyi. Kun girma, kuma lokaci ya yi da zan muku aure. Amma sabanin al'adar gidajen sarauta, na yanke shawarar kowaccenku ta faɗi wanda take so..."
Yayin da Ayat ta bogi ta juyo da idanunta masu kama da na Ayat ta gaske, ta kalli inda Inuwa yake tsaye acan nesa da su. Ta yi wani ɗan gajeren murmushi dake bayyana ta cikin mayafin fuskarta..
Zayana ce ta ce,
"Wani irin mijin aure bayan ba ma fita ko ina?..."
Sarki ya sanar musu cewa..
"To ni zan nema muku da kaina..."
Zaku cigaba da tsare har lokacin auren ku...
Ya sanar dasu cewa zai tura saƙo ga ko wani sarakunan yanki mabanbanta, da su nemawa ƴaƴansu maza auren gimbiyoyinsa...
Kaf gimbiyoyin jin haka, babu wanda ya nuna farin ciki a cikinsu,
Bayan sarki ya bayyana nufinsa na yi musu aure da ’ya’yan sarakuna, fadar ta yi tsit. Zayana, wadda ko a gaban sarki ba ta tsoron magana, ta gyara zama, fuskarta cike da nuna rashin amincewa...
"Abul, kayi haƙuri ka cire ni a wannan batun," Zayana ta faɗa cikin muryar isa..
"Domin ni akwai wanda nake jira. Da zarar ya bayyana zan yi aure, wato uban yarinyata Mimi."
Nan take fuskar sarki ta canza kalar, idanunsa suka yi jajur. Maganar Mimi da asalin mahaifinta babban rauni ne ga masarautar Alhamra, domin babban abin kunya ne da Zayana ta janyo masa. Amma ko a jikinta, domin ta san sarki ba zai iya kashe ta ba...
Sarki ya daka wata tsawa wadda ta girgiza dandalin fadar...
"Ya isa haka! Babu wata gimbiya da ta isa ta bijire wa umarni na. Maganar wancan mutumin ta ƙare tun ranar da kika janyo wa wannan masarautar abin kunya. Dukkan ku, ku koma sashen ku! Nan da kwanaki kaɗan zan aike da saƙo ga dukkan sarakunan yanki."
Kowace gimbiya ta tashi tana sosa ƙeya, Maayah da Yumna sun tafi cikin sanyin jiki, yayin da Zayana ta fice tana huci.
Ayat ta bogi ta miƙe cikin nutsuwa, tana taku ɗaya bayan ɗaya kamar yadda Ayat ta gaske take yi..
Inuwa dake tsaye kusa da Master Ibrahim, idonsa ya bushe, yana kallon yadda wannan matar take tafiya.
Inuwa ya kasa haƙuri, ya raɗa wa Master Ibrahim..
"Master, me suka tattauna a ciki? Ina ganin gimbiyoyin duka fuskokinsu babu annuri."
Master Ibrahim ya ja numfashi, "Sarki ne ya yanke shawarar ba da aurensu ga ’ya’yan sarakuna. Inuwa, kaga wannan gimbiyar dake ƙarshe? Ita ce Gimbiya Ayat. Mutane suna cewa tana da sanyi, amma tana da kwarjini a tare da ita domin kusan ta fi su..."
Inuwa ya kusan suman tsaye, "Idan sarki ya ba da aurena, wa za a kai gidan miji? Ni ko wannan matar?" Ya yi maganar zuci cikin matuƙar tashin hankali.
Suna fita daga fadar, Inuwa ya ga Ayat ta bogi tana shirin shiga motarta. Inuwa ya yi maza ya nemi izini wurin Master Ibrahim akan zai je ya duba wani abu a sashen tsaro, amma a gaskiya bin motar zai yi..
Yana isa kusa da motar, Ayat ta bogi ta zuro da kanta ta window, ta kalli Inuwa shi kuma yana cikin kakin PA.. Ta yi masa wani kallo mai zurfi, sannan ta raɗa..
"Kada ka ji tsoro, Inuwa.... Inuwa baya iya rayuwa ba tare da jikin da yake ba shi inuwar ba."
Ta ɗaga masa hannu, direban ya tada mota suka bar wurin. Inuwa ya daskare a tsaye. Wannan muryar... ya sani sarai ba muryar mace ba ce ta gaske ba..
Kowace gimbiya ta koma sashenta da damuwa..
Zayana tana huci tana shirin kiran mahaifiyarta don sanar mata da wannan auren...domin tasan ba ta sani ba..
Maayah kuwa tana kuka domin ta fi son karatu da makarantar da take zuwa fiye da zaman gidan miji...kuma ba ta jin a ransa zata rayu da ko wani namiji in ba Inuwa ba, ga damuwar Uncle Jalal da ya sako ta a gaba, yasa duk ta zubar da ƙimarta a gaban aji, a yanzu tana ɗaukan kanta ne a matsayin mutum-mutumi....
Yumna kuwa duk da tana matuƙar ƙaunar malamin da yake zuwa koyar da ita ba tare da ya sani ba amma tana addu'ar Allah ya ba ta mijin da zai so ta don Allah....
Shi kuma Inuwa, yana tsaye a tsakiyar fili, ya rasa inda zai dosa.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta isa sashensa na gimbiya cikin sassarfa, zuciyarsa na bugawa tamkar za ta fito...
Ya lallaɓa ta ƙofar sirri ya shiga ɗakinsa na ciki, inda ya tarar da waccan siffar tana zaune a gaban madubi, tana gyara mayafin fuskarta...
Inuwa ya watsa wa wannan siffar kallo mai cike da tsoro da tambayoyi...
"Wacece ke? Kuma waye ya ba ki izinin shiga siffata?"
Waccan Ayat ta bogi ta tashi tsaye a hankali. Takun ta, kamshinta, har ma da kalar idonta duka na Ayat ne.. Ta matso kusa da shi, sannan ta yi wata dariya mai sanyi, muryar King Diamond ta fito fili..
"Na gaya miki, Inuwa ba ya rayuwa idan babu jikin da yake ba shi inuwar... Idan ban bayyana a fadar nan ba, da yanzu Master Ibrahim da Sarki suna nan suna neman inda Gimbiya Ayat take..."
Ayat cikin kakin Inuwa ta zauna a ƙasa cikin sanyin jiki...
"Diamond, me kake shirin yi? Sarki ya ce zai ba da aurenmu. Idan ya kawo miji, wa zai aura? Kai ko ni?"
Diamond wanda yake cikin siffar Ayat, ya sunkuyo ya kalle ta...
"Ke za ki ci gaba da zama Inuwa, ki gina ƙarfi da ikon da kike buƙata don gyara masarautar nan. Ni kuma zan riƙa zama Gimbiya Ayat a duk lokacin da bukatar hakan ta taso... Game da maganar aure kuma... babu wanda ya isa ya aure ki muddin ina raye...
Ayat ta rufe fuskarta da hannayenta...
"Wannan hauka ne! Idan aka gano mu, kisa ne hukuncinmu."
Diamond ya yi murmushin raini...
"Kisa? Ni ne mutum na farko da aka taba kashewa amma ban mutu ba, Ayat. Ki kwantar da hankalinki..."
Bayan ɗakin ya yi shiru, Diamond ya saki siffar Ayat, hayaki ya rabe, ya koma asalin sa na King Diamond. Dogon namiji, kyakkyawa mai kwarjini, wanda kallo ɗaya zaka masa kasan ba mutumin banza ba ne...
Ayat ta miƙe tana kallon sa, kirjin ta na bugawa. Ganin yadda ya sadaukar da kansa ya shiga siffar mace don kawai ya kare mutuncinta a gaban Sarki, ya taɓa zuciyarta sosai. Ba tare da tunanin komai ba, ta fada kirjin sa, ta kankame shi tana kuka mai karfi...
Diamond ya rungume ta, ya dora habar sa a kanta, yana shakar kamshinta wanda ya dade yana mafarkinsa...
"Kiyi shiru Ayat," ya rada mata cikin murya mai daɗi..
"Babu wanda ya isa ya raɓe ki da sunan soyayya muddin ina raye. Ko Sarki ya aiko da sarakuna dubu, ke tawa ce, kuma ni naki ne. Ke ce zuciyata..."
Ta ɗago kanta tana share hawaye, ta kalle shi sama da ƙasa sannan ta fara bugun kirjin sa da kananan hannayen ta cikin sigar wasa da shagwaba...
"Ka samu matsala, Diamond! Taya mutum da aljani zasu yi aure? Allah ya kiyaye na auri aljani... cab! Ni mutum nake so, ba wani wanda yake narke wa ya zama hayaƙi ba," ta fada tana kukan dake gauraye da shagwaba...
Diamond ya tsaya yana kallon ta, wani irin murmushi ya subuce masa. Ya daga kafada irin na mutanen da suka san abin da suke yi...
"Aljani ko mutum, ni dai na san ke tawa ce. Idan lokacin ya yi, zaki gane cewa ba kowanne hayaƙi ba ne yake ƙonewa... wasu hayakin suna bayar da inuwa ne..."
Diamond ya koma gefe ya zauna a bakin gadon ta, ya miƙa mata hannu...
"Maganar wasiƙun Sarki kuma, ki kwantar da hankalinki. Ko ya tura su, ba za su taba isa inda aka dosa ba ga sunanki. Zan tabbatar an aurar da sauran, amma ke Ayat, zaki kasance cikin masarautar nan har sai ranar da zan zo daukarki a matsayin Sarauniyata..."
Ayat ta dan yi shiru, tana kallon fuskar sa da ta yi mata kwarjini. Akwai wani abu game da Diamond dake tunatar da ita Reems, amma tana ganin hakan ba zai taba yiwuwa ba tunda Reems mutum ne kuma tana tunanin ya daɗe da mutuwa...
"Yanzu ki huta," Diamond ya ce mata. "Gobe Inuwa yana da aiki babba a gaban sa. Sarki zai bukaci ganin PA ɗinsa... Ki zama jajirtacciya kamar yadda kika saba."
Ayat ta jinjina kai, tana jin wani irin kwanciyar hankali da ba ta taba ji ba tun bayan rasuwar mahaifiyarta. Tana jin cewa koda duniya zata juyo mata, tana da Aljani dake shirye ya yaƙi kowa don ita...
Ta buɗe baki cikin gaggawa kafin ya ɓace ta ce,
"Yauwa, ta ya kai shigo Masarautar nan alhalin a tsare yake?..."
Murmushi kawai Diamond yayi sannan ya ɓace ba tare da ya ba ta amsa ba....
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
.jpg)
Tnx
ReplyDelete