Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi karin bayani kan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin rasuwar mata 16 ’yan kai amarya, bayan motar da suke ciki ta yi taho-mu-gama da wata mota.
’Yan sandan sun bayyana cewa suna zargin hatsarin ya rutsa da amaryar, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko angon ma yana cikin hadarin da ya afku a hanyar Dutsinma zuwa Karofi ba.
Rahotanni sun nuna cewa motoci biyu ne suka yi karo da juna, inda aka ce suna dauke da mutum 30 gaba daya.
Kakakin Hukumar Kula da Hadurra ta Jihar Katsina, Shamsudeen Babajo, ya shaida wa BBC cewa hadarin ya faru ne a ranar Asabar, 31 ga watan Janairu, 2026.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa motar da ke dauke da ’yan kai amarya na tafiya ne cikin gudu a lokacin da hadarin ya faru.
“A cikin motocin da suka yi karo akwai mutum 30. Mutum 16 daga cikinsu, dukkansu mata, sun rasu. Mutum hudu ba su samu rauni ba, yayin da mutum 10 suka jikkata, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawa,” in ji shi.
