A Cikin Rayuwa Page 9 Complete - Abokiyar Hira Novels

A Cikin Rayuwa Page 9 Complete - Abokiyar Hira Novels

_Bossladieswriters_

_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q

WhatsApp Group

https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*     

_By Zainab Bature_   

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 9

....Bayan sun fito cikin babban falon, kaitsaye tea corner dake a wani bangaren falon suka nufa, nan ma wurin kan shi wata duniyar ƙawa ce, akwai babban teburin  gilashi mai salo na zamani, saidai ba irin tebur bane da aka saba gani, wannan interactive glass coffee table ne, teburin yana da touchscreen surface gaba ɗaya. Idan aka taba  saman gilashin sai haske ya kunnu ta ƙarƙashin glass ɗin, ya bayyana ƙananun menu icons tamkar wayar hannu, ana iya amfani da shi wajen buɗe Internet wato mutum zai iya browsing, duba email ko labarai kai tsaye a saman teburin. Sannan ana iya kallon hotuna ko bidiyo daga  wata na'ura kaman waya, ta hanyar yin connecting ɗin bluetooth ko Wi-fi su bayyana a saman teburin, sannan za a iya matsar da hotunan ko vedio da yatsa, a zagaya ko a faɗaɗa su. Banda waɗannan kuma za a iya kunna waƙa da bidiyo, sannan teburin yana haɗe da tsarin sautin gidan (surround system), ta yadda idan aka kunna waƙa daga teburin sauran kayan sautin gidan suma za su kama ko ina za a ji. Ana iya yin wasanni wato games ta teburin sannan akwai app dake bada damar kashe fitilu,daidaita labule ko kunna AC duk daga saman gilashin. Ta ko ina dai a gidan fasaha ce ke aiki. Bayan sun iso cikin tea corner ɗin, Maleek ya ce su zauna shi zai haɗo masu coffee, a saman kujerun dake zagaye da coffee table ɗin suka zauna, Basma ta ce mashi ita hot chocolate take so ya ɗaga mata hannu ya ce, "Alright baby...." Hannu ta kai saman glass ɗin teburin da idan ba a cikin yin amfani dashi a ke ba yana nuna wasu artistic wallpaper, wato wani zane mai motsi tamkar ruwa da kuma mai kaman walƙiya, wanda hakan yana sa shi ya zama abin kallo ko da ba a kunna shi ba, game ta buɗe ta ce ma mom su yi  kafin a kawo masu, gefe a cikin wurin Maleek ya nufa wanda a wurin akwai na'urar haɗa coffee da sauran abubuwan sha, da kuma china cabinet dake ɗauke da kufuna iri-iri da kayan haɗa abubuwan sha daban-daban, komai na wurin dai ya gama tsaruwa, within few minutes ya gama haɗa masu, Basma ya fara kai ma hot chocolate ɗin ta, bayan ta amsa ta furta, "Thank you, one and only dad." Ya wani kashe mata ido, a waje wanda bai san shi ba zai ce bai da irin barkwanci haka saboda yadda fuskarsa ke cike da ƙwarjini da haiba, bayan ya ɗauko masu coffee ɗinsu shi da Sapnah, a nutse duk suka fara sha, bayan wani lokaci ya kai hannu saman teburin, menu icons suka bayyana ya buɗe in da jerin karatuttukan alqurani suke, karatun alaramma Ahmad Sulaiman Kano ya kunna don tana daga cikin ƙira'oin da yake su gashi kuma ɗan garinsu, kan ka ce me gaba ɗaya kayan sautin falon suka kama karatun cikin madaidaicin sauti mai kwantar da zuciya da saka natsuwa....


 Bayan sun gama Basma ta kwashe mugs ɗin da suka yi amfani ta je ta saka a wani injin dake a wurin wanda ke wanke maka kayan da aka yi amfani fess, ta maida su wurin ajiye su sannan ta dawo, Maleek ya ce ma Sapnah su je su raka baby part ɗinta ta amsa da ok, kafin su tafi ta hanyar wannan glass table ɗin ya rage hasken gaba ɗaya cikin falon zuwa mai duhu ya kuma gyara duka labulayen falon, abun dai kamar siddabaru! Kamar lokacin da za su zo yanzu ma saka Basma tsakiya suka yi suka kama mata hannu, lokacin da suka fara hawa matattakalar benen sai ma suka ɗaga ta sama ba tare da tana taka steps ɗin ba, Basma nata ƴar dariya suma duk ita ce akan fuskokinsu har suka haye da ita sama, kana ganinsu ka ga happy family, ɗakinta dake a saman benen suka kaita wanda shima yake da zubi irin na zamani, an tsara shi da tsadaddun furniture daidai da matashiyar budurwa, har saman gadonta da ya sha lallausar shimfiɗa suka kai ta tare da kwantar da ita, gaba ɗayansu suka yi mata addu'oi kafin duk suka sumbace ta a goshi suka yi mata sai da safe, tana murmushi ta furta, "Gud nyt mom, gud nyt dad, I luv u so muchhh." Hannunta Maleek ya kama ya sumbaci bayan shi ya furta, "We luv u too, our happiness." Ya ɗan kanne mata ido, sai da ya rage mata hasken ɗakin daga mai haske zuwa mai duhu kafin suka fita suna yi ma juna bye-bye, tana ganin sun tafi ta ɗago ta kai hannunta saman side drawer ta ɗauko wayarta don ta duba ta ga ko Deen yana online. Su Maleek na fitowa daga ɗakin nata ya duƙa ya ce ma Sapnah ta hau, dama duk zai ɗauke ta ya fi goya ta, don a cewarsa ƙirar jikinta ta saka ta yin nauyi, tana dariya ta kuwa haye bayan nashi, a tunaninta za su koma ƙasa ne sai ta ga ya wuce da ita part ɗinsa dake a nan saman benen don duk suna da part a nan, har Deen ma a nan saman part ɗinsa yake a gidan. A can hawan ƙarshe kuma ba ɗakuna bane, anan akwai Home Cinema wato babban wurin yin kallo kamar gidan kallo, an saka babban screen a jikin bango da manyan kayan sauti, akwai kujeru masu motsi dake ɗauke da wurin ɗaura kofin abun sha, akwai kuma Entertainment Zone wanda ɗan madaidaicin wuri ne don yin game, bayan su akwai kuma Mini Lounge inda ke da mini bar an saka glass shelves masu ɗauke da drinks kala-kala, Sai Relaxation Spot wanda area ɗin balcony ne aka yi ma ado ta hanyar zagaye sa da glass, akwai kujeru da table masu matuƙar jan hankali da fulawoyi masu tsari. Musamman akwai glass elevator da ke kai mutum can sama ba tare da an sha wahalar taka matattakala ba. Tabbas gidan Maleek ya amsa gidan mammalakin kamfanin fasaha, abu mafi ƙayatarwa shi ne yadda aka haɗa duk na’urorin gidan da smart home system, ta yadda ake iya sarrafa su ta amfani da murya ko kuma ta wayar hannu. 


Ganin sun nufi part ɗinsa, Sapnah ta tambaye shi ba aikin zai je ya ci gaba da yi ba, ya ce mata bai son shiga haƙƙinta su je ya sakata ta yi bacci idan ya tashi da dare zai ci gaba, ba ƙaramin daɗin hakan ta ji ba ta lafe a bayansa sai ka ce wata ƙaramar yarinya, koda yake gaba ɗayansu basu ɗaukar kansu a masu shekaru wurin nuna ma juna soyayya, a koda yaushe soyayyar su ga junansu sabuntuwa take yi kamar dai yadda ma'aurata turawa suke, yawan shekaru baya hana su nuna ma juna soyayya. 


Maleek mutum ne mai tsananin bawa iyalinsa kulawa tare da ƙoƙarin sauke masu hakkokin su duk da kasancewar sa mutum da yake yawan kasancewa busy. Sai dai ba iyakar iyalinsa kawai yake kyautata mawa ba, shi mutum ne mai tsananin alkhairi ga mutanen dake kewaye da shi, waɗanda ya sani da ma waɗanda bai sani ba alkhairinsa na isar masu, kamfaninsa na ɗaya daga cikin manyan kamfuna dake bada gudunmawa da tallafi a ƙasar, haka ma a Nigeria, yana ɗaya daga cikin mutanen da ake neman tallafi a wurinsu idan buƙatar hakan ta taso, kamar 6angaren gina makarantu, masallatai, hanyoyi da sauransu. Da zarar ƙafarsa ta dira a garinsa wato Kano, mutanen unguwarsu suke cika da farin ciki sanin cewa suna cikin alkhairi dumu-dumu,  sannan duk da kasancewarsa mai tsananin arziƙi da yawan uzururruka hakan bai hana sa kula da addininsa, yana da ruƙo da addini sosai, a duk daren duniya indai yana da ƙoshin lafiya sai ya yi ibadu, a ganinsa in dai zai rinƙa tashi yana yin aiyukan da suka shafi aikin sa to ba shi da uzurin da zai hana sa yin ibada, wani lokacin sai ya gama yin ibadunsa sannan ya dasa da aiki, ko kuma bayan ya gama yin aikin, haka iyalinsa ma yana matuƙar ƙoƙari wurin saka ido kan abun da ya shafi ibadarsu.



ABUJA



A zazzaune suke a dining area suna yin breakfast, gaba ɗaya sun shirya dad ɗinsu na sanye da ƴan cikin manyan kaya na light blue ɗin shadda, babbar rigar su na can part ɗinsa sai ya gama in zai tafi aiki zai saka, a sauran kujerun su Leemarh ne da ƙannanta duk sun shirya cikin uniform don tafiya school, babu Omar a ciki don shi ba in da za shi ba da wuri zai yi breakfast ɗin ba, mom ɗinsu ma na zaune jikinta sanye da baƙar abaya mai buɗaɗɗan hannu ta yafa ƙaramin mayafin rigar a saman kanta, itama lokacin zata karya don zata fita da wuri ne zata je yin wani uzuri. Dama kuɗin da ta amsa jiya a wurin daddynsu ƙarya take ba wani Ammin su da zata tura mawa don buƙatar kanta ne ta amsa, ba a daɗe da ta sa ya bata miliyoyin kuɗi ba wai zata ƙara ma zinaranta girma, shiyasa yanzu ta fake da Ammin su na da buƙata. 



A natse suke cin abincin an shaƙe tebur ɗin da kayan breakfast kala-kala, wanda duk cin su baza su iya cinye su duka ba, Leemarh tana cin abincin amman hankalinta na kan Fahad ta ƙosa ta saka shi a idanunta saboda ba da su suke yin breakfast ɗin ba, saboda an san ya yi wuri da yawa shiyasa ba a yi masu maganar su fito su yi breakfast ɗin ba, daga gefen su masu aiki biyu ne a tsaye suna serving nasu abun da kowa ke so.


Leemarh ce ta fara miƙewa ta ce ta ƙoshi, tana barin wurin ta nufin hanyar bene tana sanye da ɗan gajeran skirt da iyakar shi gwiwa na kayan makaranta, sai doguwar farar safa data kawo har bakin inda skirt ɗin ya tsaya, ƙafafunta na sanye da rufaffun baƙaƙen takalma na makaranta masu ɗan karen kyau, kanta na sanye da ƴar hijab himar sosai kayan suka yi mata kyau sai faman sakin kamshi take, lokacin da ta isa bakin bedroom ɗin ta tsaya ta yi sallama, sai dai kusan sau biyar tana yi shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta yanke ta leƙa ta gani ko basu tashi bane, bin ɗakin ta yi da kallo da ɗan alamun mamaki lokacin da ta hango gadon wayam ba kowa, sai dai alamun ba a daɗe da tashi daga sama ba don zanen gadon da duvet ɗin a ɗan yamutse suke, ƙarasa shiga ta yi tana tafiya a hankali kamar mai yin sanɗa tana bin cikin bedroom ɗin da kallo, a tsakiyar ɗakin ta tsaya tana yin ƴan waige-waige ko zata hango wani cikin su, har can ciki wurin closet ta duba amman bata gan su ba, har bakin toilet ta tsaya tare da ɗan yin knocking nan ma shiru bata ji alamun mutum ba, hanyar fita ta nufa a cikin ranta tana mamakin to ina suka tafi da sassafen nan, bayan ta fito falo har ta nufi ƙofar fita ranta ya bata to ko suna a sashen baƙi? Yin wannan tunanin ya sa ta juya da sauri ta nufi ɗayar ƙofar da zata sada ka da bayan gidan wanda ta nan ya fi kusa da  sashen baƙin, lokacin da ta  je a rufe ta iske part ɗin alamar ba kowa a ciki, komawa ta yi cikin gidan tana ta tunanin ina suka tafi, bayan ta shigo ciki hanyar dining area ta nufa har lokacin suna a zazzaune basu ƙarasa yin breakfast ɗin ba, 


   "Mom, wai ina su ya Deen da ya Fahad suke?" Ta tambaya bayan ta tsaya daga gefen mom ɗinsu, ba tare da ta kalle ta ba hannunta riƙe da tea cup tana sipping ta ce Deen ba yana a part ɗinsa ba,


   "To ai yanzu daga can nike amman ban iske kowa ba, har cikin bedroom na shiga nan ma wayam ba su nan." Dakatawa mom ɗin ta yi ta kai idanunta kan ta, "To ina Deen ɗin zai tafi da sassafe?" Hannu Leemarh ta yarfa mata alamar itama bata sani ba, shiru mom ɗin ta yi alamar tunani, a ranta ta ayyana ko saboda maganar da ta yi ma Deen ya sa shi jan Fahad suka koma bangaren baƙi, kallon Leemarh ta yi ta ce tana jin Deen ɗin yana a part din baƙi, yadda take ba Leemarh amsa sam bata sakawa da Fahad sai ka ce ba su biyu ta tambaya ba, 


 

  "Ai har can ma na je amman ba su nan, part ɗin ma a kulle ya ke fa." Jimm mom ta ɗan yi, lokaci guda zuciyarta ta ayyana mata ko dai hasashenta na jiya ya tabbata ran shi ya 6aci ya yi tafiyar shi har da Fahad ɗin! Da sauri ta ajiye cup ɗin hannunta har sai da ya yi ƙara, kallon dad ta yi ta ce, "Ko ka san in da Deen ya ke?" ɗan ɗage ido ya yi alamar tunani, "ehumm..tare dai muka je masallaci da su, bayan mun dawo ne suka wuce part ɗin Deen nima na wuce nawa." Wata zabura da ta yi kamar wadda shock ɗin lantarki ya ja, da sauri ta fita daga cikin kujerar da take ta nufi cikin falo tana tafiya jikinta na amsawa dama rigar jikinta irin abayar nan ce mai fidda shape, a tsiyace take taka matattakalar benen gabanta har ɗan faɗuwa ya ke, ita bawai ma in komawar ya yi ba ce tafi ɗaga mata hankali, tunanin tare ya koma da Fahad ne ya sa ta wannan ruɗewar, da ƙarfi ta bangaza ƙofar part ɗin shi ta shige, kamar yadda Leemarh ta iske shi haka itama ta iske wayam, cikin ɗakin ta kutsa tana faman ƙwala masa kira, "Deen! Deen...!!" Ba in da bata duba ba amman babu alamar su, tsaye ta yi tare da ruƙe ƙugu tama rasa tunanin da zata yi na inda suka tafi, walk-in closet ɗin shi ta sake shiga tana ƙara dudduba kayan ciki, lokacin da ta fahimci ba wasu daga cikin akwatunan da ya zo da su jiya wani irin tsinkewa zuciyarta ta yi, har wani duhu-duhu take gani lokacin da ta fito ta nufi sauka ƙasa da sauri kaman za ta tashi sama, ko kallon in da su Leemarh suke bata yi ba bayan ta saukko kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin falon, duk da ta san falon na su yana da girma amman sai take ganin kaman ya ƙara girma ganin ta ƙi kaiwa kofar duk da saurin da take zubawa, a cikin entryhall ta ja tunga ta fara ƙwala kira cikin tsananin ɗaga murya tana faɗin "Officer, officer at the gate! Call the officer at the gate!!" Ta ba wani jami'i dake tsaye gefen jibgegiyar baƙar jeep umarni, da sauri ya amsa mata da ok ya nufi hanyar gate, ba a ɗau lokaci ba wani jami'i jikinsa sanye da uniform yana riƙe da hularsa a hannu ya tunkaro ta yana tafiya da sauri, yana zuwa cikin girmamawa ya ce, "Good morning ma," 


"Did you see Deen go out of the house???


 Ta jefa mashi tambayar ba tare da ta amsa gaisuwar da ya yi mata ba, 


   "Yes, sun fita lately tare da brother na shi." Wani mugun kallo ta watsa masa, "Wane brother ɗin?" Sai ka ce bata san wa yake nufi ba,


  "I mean, his cousin brother Fahad." Wani gauron numfashi ta saki ta ɗan cije baki, "Sun faɗi maka ina suka tafi?" 


   "Yes, da na gan su har da kaya shine na tambaye su za su yi tafiya ne suka ce za su je Funtua." Da tsananin mamaki ta maimaita, "Funtua...?" Amsa mata ya yi da yes can Deen ya faɗi mashi za su tafi, har za ta juya ta dakata ta tambaye shi Deen ya tafi da jami'ai ya amsa mata da a'a su biyu kawai suka tafi, wata irin juyawa ta yi tamkar zakanya ta durfafi komawa cikin gidan, officer dake tsaye ya bi jikinta dake amsawa da kallo baki a buɗe har ta shige, a cikin falon ta haɗe da su Leemarh sun taho har da dad ɗinsu ya saka babbar rigar shi yana tafiya yana gyara zaman hular shi,


    

"Ka ga irin abun da nike faɗi maka ko! Yanzu Deen har ya kai ya yi tafiya ba tare da ya sanar mana ba! Rashin amfanin mu har ya kai haka a wurin shi? Ko da yake nasan wannan duk aikin ƙanin ubansa ne wanda ya riga ya gama mallake shi sai yadda ya yi da shi!" Shiru dad ya yi yana kallon ta yadda take zazzaga masifa har rufe ido take, sarai ya san da su Deen ɗin sun tafi Funtua, bayan dawowar su daga sallar asuba ne ya faɗi mashi zai bi Fahad, anan har yake mashi magana kan abun da mom ɗinsu ta sanar da shi, Deen ya kwashe komai ya faɗi mashi har lokacin da 6acin rai a tattare da shi, ya ce ma dad din ya yi tunanin in ya zo zai samu kwanciyar hankali tun da ya daɗe bai zo ba amman tun yanzu mom dinsa ta fara ɗaga mashi hankali shiyasa gara kawai ya tafi Funtua ya san zai fi samun kwanciyar hankali a can, jin hakan ya sa dad ɗin nashi goya mashi bayan hakan, amman saida ya yi mashi magana kan yakamata su tafi da security saboda tsaro, Deen ɗin ya nuna mashi ba sai ya tafi da jami'ai ba in sha Allahu za su je lafiya, anan suka yi bankwana har da Fahad, ya ce mashi ya faɗi ma yayansa Alhaji Sa'ad wato mahaifin Fahad ɗin yana nan zuwa bada daɗewa ba.



Da alamun kamar bai san komai ba ya tambaye ta ina suka tafi ne, a hasale ta faɗi mashi in da aka ce sun tafi,


   "Tohh..Funtua suka tafi ke nan, kuma tun da sassafe kamar waɗanda aka kora, maimakon in ma tafiyar za su yi su bari gari ya waye sosai bayan sun yi breakfast sai su tafi." Wata uwar ƙwafa mom ta yi rai a matuƙar 6ace ta ce, "Wannan duk aikin Fahad ne, kuma wllh sai na ɗauki mataki akan hakan, in ba shi da bai da hankali ba ta ya daga zuwan shi zai ja shi su tafi wata Funtua, kuma ya san halin rashin tsaron da ake fama da shi shine zai ja shi ba tare da jami'ai ba, wato komai zai same shi ma ya same shi. Wama ya sani ko wani setup ne shiyasa ya ja shi suka tafi su kaɗai, dama ai an ce makashin ka yana tare da kai, abun da ke faruwa ke nan yanzu da na jikin mutum ake cutar da shi...." 



  "Subhanallahi! In sha Allahu hakan ma ba zai faru ba, ki rinƙa faɗin alkhairi pls." Dad ne ya faɗa jin irin maganganun da take faɗa mara sa daɗi, fuska a yamutse Leemarh take kallonta, wani 6acin rai take ji a cikin ranta jin yadda mom ɗin ke faɗan maganganu marasa daɗi akan Fahad, ga damuwar ya tafi ba tare da ta gan shi ba, kwantar mata da hankali dad ya shiga yi kan ba abun da zai faru in sha Allahu za su je lafiya, ganin ta wuce ciki ya sa shi tambayar ba taren za su fita ba? tana nufar cikin falon ta ɗan ɗaga masa hannu ta ce su tafi kawai ta fasa fita, ɗakinta ta nufa ta ɗauki wayarta ta shiga kiran wayar Deen sai faman jijjiga jiki take ta kasa tsayuwa a wuri ɗaya, 



Zaune suke cikin motar Fahad suna tafiya kan hanya, Fahad ne ke yin driving yayin da Deen ke a kujerar gefen sa, Fahad yana sanye da brown dress suit pant wato dogon wando ruwan ƙasa sai baƙar dress shirt ya yi tucking rigar a cikin wandon ya saka baƙin belt, ƙafafunsa sanye da luxury loafers irin rufaffun takalma marasa igiya, da gani ba sai an fada ba takalman masu tsada ne daga laushin jikin su da yadda suke salƙi, a nutse yake juya sitiyarin motar wutsiyar hannun shi na ɗaure da baƙin agogo shima sai salƙi yake, yayin da shi kuma tauraron ɗan kwallo wato Nuree yake sanye da farar high-end dress shirt tare da farin jeans ya ɗan matse daga ƙasa, a saman rigar ya ɗaura baƙar tailored blazer wato riga mai kaman jacket ta kawo mashi zuwa ƙasan kugunsa, bai saka ma6allan rigan guda biyu dake daga can ƙasa ba hakan yasa ana ganin farar ta ciki da ya yi tucking ɗinta da baƙin ubansun belt da kan shi ke wani irin ƙyalli, shima irin takalman dake ƙafar Fahad ne a tashi kafar iri ɗaya ya siya masu, hannun shi guda na ɗaure da agogo Rolex yayin da baƙar sumarsa ya yi baya da ita ya ɗaure ta daga ƙasa, Ya Allah! Yadda ya yi sai ka rantse hausa baza ta fito daga bakinsa ba, gaba ɗaya kana ganinsu ka san ba ƙananun kaya bane suka saka, yadda kayan suka yi fitting na su so well abun ba a magana sai daddaɗan ƙamshi ke tashi daga jikinsu, gaba ɗaya ya karaɗe cikin motar ya haɗe da sanyayyan iskan A.c, shima Fahad sumar shi ta sha gyara sai salƙi take, daga gaban Deen hular shi ce baseball baƙa ajiye wato irin hular da ake kira da face cap, tana da tambarin premium brand da aka yi ta daga gaba. A hankali sautin ƙira'ar da Fahad ya kunna ke tashi, dama shi haka yake da wuya ka ga yana driving ya kunna waƙa, duk da wani lokacin yana kunna music idan yana tafiya ba mai nisa ba ko cikin gari haka, Deen na zaune ya ɗan zamo jikinsa kaɗan ta yadda ya kwantar da kanshi a jikin seat ya lumshe idanunsa, idan ka gan shi zaka yi tunanin bacci yake, saidai ba haka bane yana bin ƙira'ar da ke tashi ne a cikin zuciyarsa, jefi-jefi suke yin magana tsakanin su sa6anin lokacin da suka taso hira suke sosai, yanzu da suka yi nisa ne suka rage yin magana ba kamar Deen da ya fara gajiya da zaman motan, har magana Fahad ya yi mashi na ko ya kwantar da seat ɗin ya ji daɗin zaman ya ce mashi a'a yadda yake ma lafiya lau. Tun da suka taho basu tsaya ba sai a checkpoint biyu da aka tsayar da su gaba ɗaya kuma da suka tsaya jami'an sun san fuskan Deen kuma dama suna da labarin zuwan shi, don akwai masu supporting team ɗinsa, hakan ya sa sun ɗan 6ata lokaci kaɗan a wurin gaisawa da su har da waɗanda suka yi hotuna da shi,


Sautin zazzaƙar muryar mace ne ya karaɗe cikin motar daga wayar Deen, irin muryar na'ura ne ke faɗin, 


    "Sweetheart is calling..." 


Saida muryar ta sake maimaitawa sannan Deen ya buɗe idanunsa, ɗagowa ya yi tare da gyara zaman shi ya kai idanunsa kan wayar tashi da ke ajiye gefen shi, lokacin da ya kai hannu ya ɗauko ta muryar ta sake sanar da shi contact mai sunan sweetheart na kira, a nutse ya furta, "Tell sweetheart I'm not available, am out of reach." Yana gama faɗin haka ya ɗaura wayar saman cinyar shi tare da mayar da kansa jikin headrest, daga sunan da aka sanar da shi ya san mom ɗinsa ce ke kira, kuma ko ya ɗauka ya san 6acin rai ne shi yasa ya ce a sanar da ita haka,


     _"Message sent: ' You're not available, you're out of reach."_ 


Muryar ta sake karaɗe cikin motar tana sanar da shi cewa ta tura saƙon abun da ya ce a faɗi ma sweetheart, shiru ya ɗan yadda suka yi da ita a daren jiya na sake dawo masa. Lokacin da saƙon da Deen ya ce a fadi mata ya riske ta na cewa baya available tamkar ta kurma ihu ta ji, sam ta kasa zama har lokacin sintiri take ta yi bata da burin da ya wuce Deen ya ɗauki wayar ta bashi umarnin ya juyo kada ya ƙarasa Funtua, sau wurin ukku tana kira duk saƙo ɗaya ake turo mata cewa he's out of reach, sanin cewa yana akan hanya ya sa bata kawo komai a ranta ba ta yarda da abun da ake faɗa mata, ranta ne ya bata ta gwada kiran Fahad tun da suna tare wataƙil shi ta same shi, hannunta har ƴar rawa yake wurin kokarin kiran Fahad, wanda ba zata iya tuna yaushe ne ƙarshe da ta yi waya da shi ba, akasi! Shima dai sanar mata ake da cewa baya available duk ta kira. Dama sanin zata iya kiran Fahad ya sa Deen ɗaukar wayar Fahad ɗin ya saka ta a flight mode shiyasa shima ta kasa samun shi. Ƙarshe jefa wayar ta yi saman gado tsabar takaici ta zauna a baki tana ta huci kamar zakanya. Lokacin da suka iso Kaduna Fahad ya yi mashi maganar bari su je wani eatery su yi breakfast, Deen ya ce mashi a can Zaria ba eatery mai kyau, Fahad ɗin ya amsa mashi da akwai har a cikin asibitinsu, Deen ya ce mashi ok lafiya lau shi baya jin wata yunwa sosai za su iya bari su ƙarasa in dai ba shi yana jin yunwa ba, 


    

"Kai dai ka faɗi gaskiya idan kana jin yunwa, na san ƴan ƙwallo cin abinci gare ku sosai." Fahad ya faɗa tare da ɗan murmushi idanunsa akan hanya yayin da suke tafiya cikin garin Kaduna, ɗan murmushi Deen ya yi jin abun da ya faɗa, kuma gaskiya ne shi kan shi baya wasa da abinci, ce mashi ya yi lafiya lau zai iya kaiwa Zaria ai still safiya ne, suka ci gaba da tafiya......

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post