https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt
*_✨A CIKIN RAYUWA✨
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 10
Alhamdulillah sun iso Zaria lafiya. Kaitsaye ABUTH dake Shika suka nufa, inda anan Fahad ke aiki matsayin Specialist a Family Medicine, bayan sun isa cikin asibitin, General Outpatient Department (GOPD) suka nufa, Fahad ya parker motan a inda aka tanada don hakan, Deen ya ɗauki hularsa ya saka kafin ya fito, yadda gashin shi da ya faka ya ɗan fito daga baya ba ƙaramin kyau ya yi ba, Fahad da shima ya fito yana kallon sa da dan murmushi ya yi masa sannu da gajiyan hanya, shima murmushin ya mayar masa ba tare da ya ce komai ba suka nufi shiga wurin, nan fa Deen ya zama abun kallo a wurin mutanen da ke kai kawo a arean, duk da ba a gane ko waye saboda hular shi ta ɗan yi curved daga gaba kuma ya ɗan sauke fuskarsa, idan ba ya ɗaga kai ba ba a ganin fuskar tashi sosai, duk in da suka wuce sai sun bar ƙamshin jikinsu sai faman kallon su ake, hatta mutane masu aji kallon su suke, suna shiga block ɗin suka haɗu da wani likita ya yi shigar light blue ɗin dress shirt da dogon baƙin wando sai nicktie, a wuyansa ya rataya stethoscope, gaisawa suka yi da Fahad cikin harshen turanci, dama bayerabe ne sunan shi Dr. Hakeem kamar yadda Fahad ɗin ya kira shi da suna gaisawa, yana ɗaura idanunsa akan Deen za su gaisa ya gane shi, da alamun ɗan mamaki ya kalli Fahad da har za su wuce ya ce, "This man looks like your footballer brother?" (Wannan mutumin kaman ɗan uwanka ɗan ƙwallon ƙafa?"
"Yes." Fahad ya amsa mashi fuska a sake.
"Ahhh! Nice to meet you. I am a huge fan of yours and support your club, I love your playing style." Dr Hakeem ɗin ya faɗa ya ɗan kama bakin shi dake a washe cike da farin cikin ganin Deen, da ɗan murmushi Deen ya yi mashi godiya ya nuna shima ya ji daɗin haɗuwa da shi, yadda Dr. Hakeem ɗin yake magana da yake yana da budaɗɗiyar murya hakan ya jawo hankalin wasu dake wurin da basu lura da shigowar su Deen ɗin ba, kan ka ce mi, ai Dr. Hakeem har ya fara shelar zuwan Deen, gaba ɗaya hankulan mutanen wurin ma'aikata da wanda suka zo ganin likita ya dawo kan su, nan fa aka shiga zuwa ana gaisawa da shi kowa yana nuna farin cikin ganinsa tare da yabon shi, nan fa wurin ya cika da ma'aikata manya da ƙananu har da mata, daga bangarori daban daban na asibitin ake ta zuwa ganin Deen, mutane sai yin hotuna suke da shi, Fahad dai na tsaye gefe yana murmushin jin dadin yadda ake ta nuna haukan son ɗan'uwan nasa, ana haka sai ga Medical Director (MD) na asibitin, babban mutum ne ya ɗan manyanta kuma yana son kwallon ƙafa, sannan yana goyon bayan kungiyarsu Deen, yana kuma bala'en yin Deen sosai, yana shigowa wurin aka shiga bashi girma ana gaida shi, cike da zolaya yake ce ma mutane shi bata so yake ba su matsa ya ga tauraron shi, duk mutane suka yi dariya, yana zuwa wurin Deen ya jawo shi jikin shi tare da rungume shi, bayan ya ɗago shi cike da farin ciki yake faɗi mashi yadda yake son wasan shi da kuma kungiyarsu, sosai ya shiga yabon Deen da ke ta sakin murmushi, hotuna ya saka aka shiga yi masu da wayarsa, bayan an gama janye Deen ɗin ya yi ya ce duk mai son ganin shi ya zo office ɗin shi, tafiyar su taba Fahad damar fara yin abubuwan da ke gaban shi, workstation ya nufa don shirya fara duba marasa lafiya. Bayan zuwan su office din MD a can ya sa aka kawo ma Deen lafiyayyun abincin breakfast suka ci a tare dama MD din yana cikin cin abinci aka sanar da shi game da zuwan Deen ya tashi ba tare da ya ƙarasa.
Fahad bai daɗe sosai ba yana duba marasa lafiya a consultation room ya tashi, dama bashi kaɗai bane akwai wasu likitocin a sauran ɗakunan da suke duba wasu marasa lafiyan, office ɗin MD ya wuce wurin Deen, a can shima ya yi breakfast duk da rana ta riga ta yi, saida suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi kafin suka hawo hanya zuwa Funtua. Wuraren ƙarfe biyu saura suka iso garin Funtua, lokacin Deen ne ke yin driving ɗin, tun bayan da za su baro Zaria ya amsa har Fahad na ce mashi zai iya driving mai tsawo kuwa a titin Nigeria, yana murmushi ya ce mashi lafiya lau zai iya, ga shi har Allah Ya kawo su lafiya.
Daga cikin wani ɗan lungu ta 6ullo, tana sanye da uniform riga da wando sai ƴar madaidaiciyar hijab wadda daga bayan saman kanta ya yi tudu sosai, tsaf-tsaf da ita duk da daga gani lokacin tashin su aka yi, amman sam ba datti a tare da kayan jikinta, a hannunta na hagu ƙatuwar baƙar jakar makaranta ce sargafe, yayin da ƙafafunta ke sanye da baƙaƙen takalma sneakers, kana ganinta ka ga ƴar makaranta mai natsuwa da tsafta. Tana ƙarasowa bakin hanyar ta tsaya tana dubawa ko akwai abun hawan da ya taho, bata hango wani abu ya taho ba bayan mashin ɗin da ya wuce daga 6angaren hagu, sai kuma motar da ta hango ta taho daga 6angaren dama, ganin kamar motar na ɗan nesa har ta tsallaka ba tare da ta ƙaraso ba ya sa ta hau hanyar da sauri a ƙoƙarinta na ta tsallaka, da alama idanunta sun hango mata ba daidai ba, don tana kaiwa tsakiyar hanyar motar da ta taho da matsakaicin gudu ta cimmata, kiɗimewa ta yi ta ruɗe ta rasa in da zata nufa tsakanin ƙarasa tsallakawa ko kuma komawa jin horn ɗin da aka shiga sakar mata a jere, ƙarar uban burkin da motar ta ci a dab da ita ne ya sa ta ƙara gigicewa ta saki jakarta tare da durƙushewa a wurin, gaba ɗaya ta saka tafukan hannuwanta ta rufe fuskarta gam, duk a tunaninta motar ta tashi da ita jikinta sai faman kerma yake, kamar yadda idanunta ke runtse haka ma Deen ya runtse idanunsa ganin haɗarin da ya kusa afkuwa, gaba ɗaya hannuwansa na riƙe da sitiyari gam, yayin da gaban shi ke ɗan faɗuwa, tun da suka taho lafiya lau yake driving ɗin shi bai haɗu da wata matsala ba sai yanzu. Da yake hanyar ba babban titi bane ba wasu ababen hawa sosai sai jefi-jefi, sai kuma wasu ƴan mutane da ke a ɗan can bakin hanya wasu a bakin shaguna, hakan ya sa ba idanun mutane sosai a kan su, sai waɗanda suka hango suka saki salati ganin abun da ya faru, horn mai ƙara da aka yi mata ya sa ta saurin ɗagowa, tana ganin gaban motar dab da ita bata ta6a ta ba ta yi saurin miƙewa, ko ta kan jakarta bata bi ba ta ƙarasa tsallakawa ta tsaya har lokacin jikinta bai bar kerma ba, cike da 6acin rai Fahad ya buɗe ƙofar motar ya fito idanun shi a kanta,
"Ke baki da hankali ne? Baki ganin abu ya taho zaki hawo saman hanya!" Cikin yar tsawa ya yi mata maganar, kikkafta idanu ta shiga yi ta fara motsa baki sam ta kasa magana sai nishi take, "Baki ji ana maki magana!" Ya kwatsa mata tsawa ganin ta kafe shi da ido,
"K...ka yi haƙuri, na yi zaton har zan tsallaka bata ƙaraso ba ne..." Katse ta ya yi a hasale ya ce, "Da yake baki da hankali, ko ke dabba ce? shiyasa kika kasa gane ko motan zai ƙaraso wurin ki?" Duk da halin da take ciki sai da ta ji maganar a cikin ranta, yanayin fuskanta ne ya sauya ta ɗan daure fuska,
"C'mon go take your stupid bag ko mu take ta mu wuce, idiot." Wannan karon ɗan buɗe baki ta yi alamar al'ajabi, zata iya cewa tun da take ba wanda ya taba kiranta da waɗannan sunayen sai yau, motsa baki ta shiga yi tana ɗan gunaguni tana yi mashi wani kallo mai kaman harara ba tare da ta motsa daga inda take ba,
"Zagi na kike yi??" A fusace ya tambaya, da yake rainon Sagir ce ya koya mata rashin tsoro da kuma kada a yi mata abu ta kyale, rai bace ta ce, "Ni ba zagin ka nike ba, kawai ya zaka ce mani mara hankali dabba kuma idiot bacin tun farko na baka haƙuri..." Mamaki ne shimfide akan fuskar shi jin yadda ta maida mashi magana tana yarinya ƙarama,
"To an ce maki dabban ma, da akwai abun da zaki iya yi ne? Ai gara ma dabba dake don ita ba yadda za ai ta bari har mu ƙaraso mu same ta a saman hanyan." Rai 6ace ya yi maganar dama abun ka da mai zuciya, ƙwarjini ya yi mata ta kasa ce mashi komai sai ɗan ƙunƙuni da take yi, tafiya ta fara a hankali don ta je ta ɗauko jakarta, tsoki ya ja ya ce, "Ƙaramar mara kunya kawai..." Cak ta dakata da yin tafiya ta kalle shi a ɗan harzuƙe murya na rawa kaman zata yi kuka, "Ni dai ba mara kunya bace, kuma ni ba dabba ba ce wllh, koda na yi shiru ai ba don ina jin tsoron ka bane, kawai dai na san idan mutum ya kira ka da sunan abu kuma kai ba abun bane to..." Sam ta kasa ƙarasa maganar don sosai ya yi mata ƙwarjini, ko maganganun da take yi kawai ƙarfin hali ne, kashe shi da mamaki ta yi yanzu, daga yadda yanayin fuskarsa ya canza zaka fahimci hakan, ɗan ƙanƙance ido ya yi tare da ɗan yamutsa baki irin yaro bai san wuta ba sai ya taka,
"Ni ne dabban ke nan?" Ya faɗa ya ɗan ɗage gira, juyar da kai ta yi tana ɗan motsa baki, ƙarasa fitowa ya yi daga jikin marfin motan yana faɗin bari ya zo sai ya ji da kyau abun da take faɗa, Deen na jin haka ya fara kiran sunan shi yana faɗin ya ƙyale ta pls amman bai bi ta kan shi ba, ya san abu mara daɗi na iya faruwa hakan ya saka shi saurin kai hannu ya buɗe motar, Fahad na zuwa kusa da ita ya ɗaga hannu zai zabga mata mari, bata yi ko gezau ba duk da ta fahimci abun da yake ƙoƙarin aikata mata, saidai ta ɗan tsorata da hakan da sauri ta runtse idanunta,
"Pls ya Fahad let her be..." Deen da ya tare hannun nashi ya faɗi, sam baya son attention ɗin mutane ya dawo kan su saboda ya lura da wasu mutanen idanunsu na akan su duk da ba lalle in sun fahimci abun da ke faruwa ba, daddaɗan sautin muryar da ta ji ya ziyarci cikin kunnanta ne ya sa ta yi saurin buɗe idanunta don ta ga waye ya yi maganar, ita bata ma san su biyu bane a cikin motar ba saboda tinted ce ba a ganin wanda ke a ciki, kuma saboda ruɗewar da ta yi tun farko da motan ta kusa buge ta ya sa bata ma iya ta tantance Fahad ko daga bangaren direba ya fito ba, bin su da ido ta yi lokacin Deen ya kama hannun Fahad sun juya, saida ya kai shi har bakin mota ya roƙe shi ya yi haƙuri kada su zamo center of attention, bayan ya Fahad din ya shiga Deen ya juyo don ya koma side ɗin shi, lokacin da suka haɗa ido da ita har saida gabanta ya yi wani irin bugu da ƙarfi ganin irin tsantsar kyawun halittar shi, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke idanun shi ya wuce, tamkar rainon sakarai haka ta ɗan saki baki ta bishi da ido, ba komai ya fi jan hankalinta tattare da shi ba face sumar shi da ya faka, kokonto ta shiga yi a cikin ranta na shine ya yi maganar da ta ji ko kuwa, sai take ganin wannan ai kaman baya jin hausa ma, sai da ya kai bakin ƙofar motar ya dakata tare da kallo ta,
"Ki je ki ɗauki school bag ein ki ko mu bi ta kan shi mu wuce!" Cike da bada umarni ya yi maganar fuskarsa a ɗan ɗaure, mamaki ne ya cika ta jin da gaske shi yake yin magana da hausa, wucewa ta yi ta ɗauko jakar ta juyo suka haɗa ido ya shige cikin motar, tsaye ta yi a bakin hanyar tana bin motar da kallo har suka wuce, ita kam a rayuwar ta zata iya cewa tun da take bata ta6a ganin mutum mai kyau ba a zahiri kamar shi, sai dai ko a fina-finan ƴan ƙasar waje amman duk da haka gani take wannan kyawun na shi ma na musamman ne, tunanin ko su ɗin su waye ta shiga yi sai kuma take jin kamar ma ta ta6a ganin fuskokinsu ba kamar wanda ya kusa marin ta, wata zuciyar ce ta raya mata a ina zata ta6a ganinsu daga ganin su ba ƴan Nigeria bane ba kamar mai gashi a ƙulle, to amman suke yin magana da hausa? Ta jefa ma kanta tambayar, wataƙil suna zaune anan ne shiyasa suka iya ko kuma shi wanda ya kusa marin nata ne ɗan nan ƙasar, mai gashin a ƙulle ɗan ƙasar waje ne to sai ɗayan ya koya mashi hausar, haka ta dingi yin tunane-tunane a cikin zuciyarta tana tafiya sukuku da ita, a karon farko take jin kaman bata kyauta ba abun da ta yi masu, to amman koma miye wanccan ya ja duk da ta bashi haƙuri ya ce mata dabba, fuska a tur6une take tafiya tana raya hakan a cikin ranta. Lokacin da ta zo daidai bakin wani shago da wani ɗan magidancin mutum ke a tsaye yana kallon duk abun da ya faru ya ce mata,
"Salma lafiya, mi ya faru ne tsakanin ki da waɗannan mutanen da suka wuce?" Fuska a yamutse ta kalle shi ta bashi amsa da ba komai sun kusa buge ta ne, daga haka ta wuce yayin da zuciyarta ke ta tariyo mata da fuskokinsu.
Tun da suka ci gaba da tafiya Fahad ke ta ɗan jan tsoki tare da yin ƙwafa, ya so Deen bai hana shi ba da ya wawwanka mata marikan da gobe bazata sake yi ma wani rashin kunya ba, haƙuri Deen dake driving ke bashi yana ce mashi ya manta kawai irin yaran haka suke basu da ɗa'a,
"Mtsww, ban san mi yasa su dad zasu bar hajja tana rayuwa a irin wannan local unguwan ba, ba komai a cikinta sai tarin illiterate mutane." Ya faɗa yana ƙara daure fuska,
Suna wuce wata kwana dake a 6angaren hagun su, a daidai bakin gida na farko dake a bakin hanyar ya fara ƙoƙarin karya kan motar, cikin wasa ya ce Allah Ya sa nan ne gidan hajjan bai manta ba, yanayin fuskar Fahad ne ya ɗan canza kaman zai yi murmushi ba tare da ya ce komai ba sanin da wasa ya yi maganar, kana gani kasan ba ƙaramin babban gida bane yadda katanganar shi ke da tsawo a bakin hanyar, jami'ai biyu ne zaune a bakin tangamemen baƙin gate ɗin shiga gidan, daga yanayin yadda aka tsara ginin katangar gidan ma zaka san cikin gidan ma ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, akwai shuke-shuken fulawoyi masu kyau da tsari da fitulu a wajen, daga waje kana hango wasu shuke-shuken dogayen fulawoyi dake a cikin gidan. Jami'an na ganin motar ɗaya ya miƙe daga saman bencin da suke zaune don ya je ya buɗe masu gate sanin motar ko ta wacece, yana gama buɗewa motar ta kutsa kai jami'an na ɗaga ma motar hannu don duk a zaton su Fahad ne kawai a ciki.
"Ko dai shine ya iso?" Wani matashin mutumi ne ya faɗi hakan daga bangaren daman dake kallon gidan suna zaune su ukku a bakin wani shago,
"Anya kuwa, idan shine ai ba zaka ganshi ya zo a mota ɗaya ba kuma ba tare da jami'ai ba, sannan bana ma tunanin zai hawo waccan motar sai dai wadda ta fita." Guda ne a cikin su ya furta.
"Ai bama shi bane, waccan motar ta wannan jikan gidan likita ce, ya ma sunan shi...yauwa, Fahad ɗin nan." Wanda shine mai shagon ya faɗa. Su nan duk ƴan ƙwallo ne zaman dakon zuwan Deen suke tun da suka gani a facebook cewa yana a Zaria, shine suke tunanin daga can ƙilan nan Funtua zai wuto.
"Amman bakwa gani ko tare suke? Ai dama hoton da muka ga ni ɗazun an yaɗa a Zaria ne suka yi shi kuma tare da likitoci suka yi shi." Wanda ya fara yin magana tun farko ne ya sake fadin hakan, cike da kokonto na biyun ya ce gaskiya dai ƙilan shi likitan bada motar ya je wurin aiki ba don ba yadda za ai Nuree Jr ya yo irin wannan shigowar, haka dai suka yi ta faɗin hasashen su.
Kai tsaye babban parking space ɗin gidan suka nufa wanda zai iya ɗaukar motoci shidda, bayan sun faka a kusan tare suka fito Deen na riƙe da hular shi a hannu, ƴar miƙa ya yi tare da faɗin Alhamdulillah, Fahad dake kallon shi daga ɗayan bangaren da ɗan murmushi ya ce halan ya gaji,
"Sosai, it has been a long time ban yi driving haka ba, and tuƙi a Nigeria sai mutum ya saka kula sosai saboda yanayin hanyan ba kyau." Murmushi kawai Fahad ɗin ya yi, officern da ya buɗe masu gate yana gab da rufewa ya ga sun fito, dakatawa ya yi yana kallon Deen cike da mamaki, sam bai kawo ma ransa zai ganshi ya fito daga cikin motar ba, duk da suma sun ga hotunan shi da aka wallafa cewa yana Zaria, da sauri ya juya kan abokin aikin shi ya sanar da shi ga Nuree nan sun zo tare da Fahad, yana jin haka ya yi saurin miƙewa yana tambayar shi da gaske, tare suka shigo cikin gidan suka nufo su, da ɗan ɗaga murya guda ya fara faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...." Ya yi hakan ne don ya dakatar da su ganin suna ƙoƙarin shiga cikin gidan, cikin washe baki suka shiga gaisawa da shi suna mashi an zo lafiya, yana amsa masu cikin sakin fuska Fahad na daga gefe shima suka yi mashi sannu da zuwa, bayan sun gama gaisawa har za su wuce, ɗaya daga cikin officers ɗin ya ce mashi pls bari su ɗan yi hoto yana fiddo waya, Deen ya basu damar hakan, bayan sun yi hoton suka wuce suma su officer ɗin suka nufi komawa gate cike da zumuɗin zuwa su yaɗa labarin zuwan shi da hoton da suka yi. Harabar gidan na da girma sosai, bangare biyu ne a cikin gidan, akwai bangaren iyayen Deen wanda ƙaton ginin bene ne yana daga can ciki amman tun a bakin gate kana shigowa zaka hango ginin saman benen, 6angaren hajiya shine a farko wanda shima babban flat ne mai kyawun gaske, daga gefen ginin hajiyan ana hango wani 6angare na jikin ginin su Deen kuma ta nan ake bi zuwa can bangaren.
WAIWAYE......
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
