A Cikin Rayuwa Page 6 Complete - Abokiyar Hira Novels


_Bossladieswriters_

_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q

WhatsApp Group

https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt

*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*

    _By Zainab Bature_

    _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._

Page 6

Zaune suke a tsakar gida bayan sallar isha, da yake yanayin zafi ne ba a cikin barandar suke zaune ba, daga gaban ɗakin dake kallon barandar wanda ɗakin Salma ne a nan suka yi shimfiɗa, dama duk in ana zafi anan suke zama don ya fi iska, gaba ɗayan su suna zaune akan ƙatuwar tabarma suna cin abinci, Salma tare da innarsu suke cin tuwon gaban su sai ɗan autansu dake manne a jikin innar tana bashi a baki, daga gefen su Imrana ne tare da Hamza suma suna ci a wuri guda, gefe daga gaban su yayan su Auwalu ne zaune akan tudun baranda shima tuwon yake ci a cikin plate da cokali, sun natsu suna cin abincin jefi-jefi suke yin magana banda Auwalu da ya tattara hankalinsa akan wayar shi, da alama ya yi sabo da yana cin abinci yana latsa waya. 


Suna tsaka da cin abinci suka jiyo ƙarar kwaramniyar kwanuka kaman daga cikin kicin, da dan ɗaga murya innarsu ta tambayi waye a nan. 


"Ƙilan awakan gidan su Bello ne suka shigo." Imrana ya faɗa da tuwo a bakin sa.


 "Ba wasu awakai, mai hankalin gidan ne, ina ganin lokacin da ya shigo daga cikin zaure ya shige kicin." Salma na faɗin haka suka fahimci Sagir take nufi, fitowa ya yi ya nufo su jikin shi daga shi sai gajeran wando ko vest babu, hannun shi ya ruƙo wata yar madaidaiciyar kular abinci, tsaye ya yi akan su fuska da alamun 6acin rai ya ce, "Wai fisabilillahi baza a yi ma mutane abinci ba sai wannan? Da me mutum zai ji, da zafin da ake kokuwa da wannan da zai danƙara ma cikinsa?" Gaba ɗaya dariya suka saka banda Auwalu da hankalinsa na akan waya, itama innarsu ɗan murmushi ta yi ta ce, "To da yake ma ba wanda aka ma dole ai sai ya ci ko?" Yamutsa fuska ya ci gaba da yi yana mitar kullum ai ta abu ɗaya sai ya kashe mutum.


   "Amman yaya Sagir ai ba ko da yaushe ake yin tuwo ba da daddare, ko shekaranjiya ba taliyar hausa yaya Salma ta dafa ba muka ci da daddare..." Imrana ne ya faɗa tare da kai lomar tuwo bakinsa.

 

    "To ubanwa ya tambaye ka! Kuma ba an fi yin tuwon ba, sai a jera kusan sati ana yin shi kafin a canza wani abun.


  "Ai dama baka wahalar da bakinka ba Imrana, ko ka faɗa ba yarda zai yi ba, ka san shi da gardamar tsiya kaman makahon jaki, in banda sharri ko yaushe ake yin sati ana yin tuwo...." Salma da ta ɗauko maganar bata ƙarasa ba Sagir dake niyyar zama a gefen Auwalu ya aje kular tuwon hannunsa ya yo kukan kura kanta, yana zuwa ya tangare mata ƙeya da ƙarfi har saida hular kanta ta cire, tufkar kitson shaden dake kanta ta baje har gadon bayanta, a fusace ya ce mata uban waye makahon jakin! Da sauri ta janye jikinta gefe tare da kare kanta tana dariya ta ce, "To ai dai bani na fara faɗan haka ba ko, innarmu ce ke cewa ka cika gardama kamar maka...." Kanta ya yo yana fadin, "Wllh kika ƙara faɗar maganar nan sai na fasa maki baki!" Innarsu dake dariya ta ce mashi kada ya sake ya ƙara ta6a ta, rai a bace ya ce to ta ce ma Salmar kada ta ƙara ce mashi haka in ba haka ba sai ya gota ta Allah, kallon Salma ta yi ta ce mata kada ta kara faɗin haka ta gyaɗa kai tana ta dariya, ƙwafa Sagir ɗin ya yi ya koma inda ya ajiye tuwon ya zauna ya fara ci, ganin yadda yake ta buga loma Salma dake kallon shi cike da tsokana ta ce, "Ah, man Sagir ya na ga kana ta buga loma kuma, ai na yi zaton tun da ran ka bai son tuwon zaka ɗan tsakura ne kawai don dole..." Ganin yana laluben takalmi yasa ta yi shiru ta 6oye a gefen innarsu tana ƙyalƙyata dariya, cikin ɗan ɗaga murya innarsu ta ce mashi kada ya jefo masu takalmi cikin abinci, fasa ɗaukar takalmin ya yi ya ci gaba da cin tuwon yana yi yana leƙo abun da Auwalu ke kallo a wayarsa.


 "Yau mutumina Habu bai  leƙo ba da daddare." Salma ta faɗa tana ci gaba da cin tuwon, 


"Ai gara ma da bai zo ba, ni wllh bani son yana zuwa, kullum bai tashi zuwa sai lokacin da muke cin abinci kamar ya san lokacin da ake gama mana abinci, kuma duk in ya zo innarmu sai ta bashi abincin, wani lokacin ma in babu sai ta kwashe cikin namu ta bashi." Imrana ne ya yi maganar yana tura baki, da ɗan murmushi innar tasu ta ce, "Ai yanzu ma in ya shigo babu tuwon, cikin naku zan ɗebar mashi..." Da sauri ya ce, "Kam, Allah ni dai ba za a ɗibar mashi ba, in kuma mu bamu ƙoshi ba fa, saidai yaya Salma ta bashi dama ita ta saba haƙura da abincinta in ya shigo babu ta bashi har ta ce ya je su ci shi da ƙannanshi..." 


"Munahukar ba, tana nuna kamar ita ta Allah ce mai tausayi, dama tun da wurin soya awara tana  samu ta ci ta ƙoshi ta kuma zame wasu cikin cinikin ta siya abun da take so ba dole ta rinƙa yin  neman suna da abincinta ba." Sagir da ya maido da hankalinsa akan su ya faɗa yana ci gaba da cin tuwon gaban sa.


  "Kai Sagir! Banda sharri, ba wata awara da Salma ke ci, kuma koda ta ci sai ta sanar mani, sannan ko ta nawa na saka mata haka zata kawo mani kuɗina daidai ba tare da ta ɗauki ko naira biyar ba sai in ni ce na bata. Ita haka Allah ya yi ta da tausayi abun ta bai dame ta ba, kuma hakan abu ne mai kyau don duk abun da ka bada shine naka, idan kana badawa sai Allah Ya yi ta buɗa maka shi yasa itama bata rasawa, ko ban bata kuɗi ba bata rasa ƴan kuɗaɗenta da zata siya abun da ranta ke so cikin wanda Auntynta Kubra ke turo mata." Murmushi kawai Salma ke yi jin abun da innarsu ke faɗa game da ita, mita Sagir ɗin ya ci gaba da yi yana faɗin dama bata ganin laifinta shiyasa zata ce haka amman shi ya san tana cinye mata awara kuma tana zarar kuɗi cikin ciniki.


   


"Bara Ubannan...!" Bayan ɗan lokaci Suka ji Sagir ɗin ya furta tare da ƴar zabura idon shi akan wayar Auwalu,



  "SubhanAllahi! Sagir wane irin furuci ne haka? Mi ya faru?" Ɗan girgiza mata kai ya yi yana washe baki ba tare da ya kalle ta  ba ya ce mata ba komai, a ƙagauce ya ce ma Auwalu, "Wai mutumin har ya iso ke nan?" Kai Auwalu ya ɗaga masa alamar eh, a ɗokance Sagir ɗin ya ci gaba, "Wllh ni ban san ya iso ba, nasan dai da maganar zai zo Najeriya, da yake tun jiya ban hau online ba banda data, ɗazun kuma ban samu zuwa fili da wuri ba kuma match zamu buga ina zuwa muka fara dama ni ake jira shiyasa na san ban ji zancen zuwan nashi ba." Yadda yake maganar kana gani zaka fahimci ba ƙaramin dadin zuwan wanda yake magana akai ya ji ba,


   "Waye kuke magana akai ne?" Innarsu ta tambaya, da sauri Sagir ya bata amsa da, "Tauraron ɗan ƙwallon mu na ƙasar waje Nuree Jr." Bin shi ta yi da ido ta ce shine yake ta wannan rawar jikin?


  "Ba zaki gane bane innarmu, ina mugun yin shine wllh, bama ni kaɗai ba, yanzu a duniyar kwallo yana ɗaya daga cikin taurarin dake lokaci, mutanen da basu haɗa komai ma da shi ba sun mutu akan shi balle kuma ni..." Da yanayin mamaki Salma ta ce, "To kai ɗin ma wani abun ka haɗa da shi ne?" 


   "Ah! Ka ji yarinyar nan, ai kuwa na haɗa wani abu da shi tun da ɗan ƙasata ne ƙarewa garinmu ne tushen shi, uwa uba kuma gidansu a unguwarmu yake." 


  "Wai ba jikan Hajiyar Ambasada ɗan kwallon nan kake magana ba?" Innarsu ce ta tambaya, ya bata amsa da shi fa. 


"Ma sha Allah, ka ce dai shima ya ɗaukaka..." Auwalu ne ya ɗago ya bata amsa, "Daukaka sosai ma, don yanzu dai a duniyar ƙwallo yana ɗaya daga cikin waɗanda ake ji da su ake kuma maganar su saboda ya iya ta sosai.." 


Sagir ya yi saurin kar6ewa, "Ai tukunna ma dai, ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba Nuree Jr nan gaba ba ƙaramar shahara zai yi ba sai ya samu title din GOAT in sha Allah. A yanzu ma da ba wasu shekaru sosai ya ɗauka a duniyar kwallon ba ya fara breaking records, ko gasar Champions league da ba a daɗe da gamawa ba team din su ne suka ƙara ci, kuma shi ya ƙara samun kyautar Golden boot wato kyautar ɗan kwallon da ya fi zura kwallo a raga, kuma ba wannan ne na farko ba dama ya taba samu ban da wanda ya samu a gasar premier league, haka bayan kammala kakar wasannin bara ya samu Ballon d'or nomination, duk da bai samu kyautar ba, amman in sha Allahu muna saka ran zai samu bada daɗewa ba in dai ba an saka son kai ba kasancewarsa ɗan Africa ...." Haka ya ci gaba da faɗi ma innar tasu nasarorin da Nureen ya samu daban-daban, gaba ɗaya ma ya dakata da cin tuwon, ita dai Salma tana ta cin tuwon ta don abun da suke magana a kai ba damunta ya yi ba hasalima in suna hirar ƙwallon a gidan wani lokacin a ɗakin su na soro su da abokansu yadda suke hargowa da waƙe- waƙe haushi suke bata ta ji kamar ta je ta hau su da bugu. 



"Allah Ubangiji Ya ƙara ɗaukaka shi Ya kare shi. Ni da yake ba sanin ta kan kwallon na yi ba ban san haka ya shahara ba, kawai dai na san ana faɗin ya iya ta sosai ba kamar lokacin da ya ci ma Nigeria wata ƙwallo bansan dai ko wacce ba ce akai ta maganar shi..." Innarsu ta faɗa bayan Sagir ya gama bata labarin. 


"AFCON kike magana, wannan gasar zakarun nahiyar Africa ce da ake yi duk bayan shekara biyu, itace ya taba ci ma Nigeria, sai kuma gasar cin kofin duniya FIFA World cup, itama ya ta6a buga ma Nigeria sau ɗaya duk da basu yi nasara ba amman sun yi ƙokari sosai don sai da suka kai har quaterfinals wato mataki na biyun ƙarshe..." Auwalu bai kai ƙarshen maganar ba Sagir ya kar6e, "Ai duk kokarin da suka yi a lokacin shine ya yi shi, to lokacin ma bai kai gogewar da ya yi yanzu ba, nasan yadda ya ƙara ƙwarewa muna da hope din in sha Allahu a gasar cin kofin duniya da ke zuwa nan da shekara ɗaya zai ci ma Nigeria bi'iznillAh...Ai Nuree ɗan baiwa ne a ƙwallo, nima ina fatan wata rana in zama kamar sa, koma ban kai shi ba nima dai ina roƙon Allah Ya sa in zama shahararran ɗan kwallon kafa.." Innarsu na murmushi ta amsa mashi da Amin Ya Allah in hakan alkhairi ne a gare shi, Auwalu ma ya amsa da Amin kafin ya ɗaura da fadin, "Shi Nuraddeen harda farinjini da Allah Ya yi masa, yana da kyau na fuska da jiki ma sha Allah, bana tunanin akwai ɗan ƙwallon da ya kai shi kyau sai dai ko a samu mai irin ƙirar jikinshi amman dai kyawun fuska gaskiya da ƙyar ne." 


Cikin washe baki Sagir ya ce, "Ai kyaun fuska dai babu ma, kuma Nuree akwai physique, he is strong, powerful and fast, in ya kama ƙwallo ba kyau, Allah dai ya haɗa mashi komai wllh, gashi yanzu shima yana cikin jerin ƴan ƙwallo masu samun kuɗi sosai, kuma ba laifi yana da alkhairi, tun da ko da ba anan yake zaune ba yana tallafa ma mutane musamman matasa ta gidauniyarsa. In sha Allahu wannan karon sai na yi yadda na yi na samu na yi magana da shi tun da na san tabbas sai ya zo nan garin, ina son ya bamu shawarwarin yadda zamu inganta harkar ƙwallon mu ya kuma taimaka mana yadda za mu ci gaba." Amsa mashi Auwalu ya yi da Allah Ya bashi iko, ya ɗaura da faɗin amman dai hakan da wuya don ya san dole ya kasance cikin tsaro sosai, ita dai innarsu murmushi kawai take in ya yi addu'a ta amsa mashi da Amin, ita kuwa Salma tuni har hirar tasu ma ta fara gundurar ta ta fara yamutsa fuska, ƙarshe ma miƙewa ta yi bayan ta gama cin tuwon ta tafi wanko hannu.



Abuja.



Mutane ne tsaitsaye cikin harabar katafaren tsadaddan hotel ɗin sun kewaye Deen bayan da suka isa, kowa ka gani fuskar sa a washe suna ta gaisawa da shi, ba wasu mutane sosai don dinner din private ce iya masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallo da manyan masu muƙamai ne za su halarta sai makusantan su kamar iyalansu da sauran su, duk wanda ka ga ya samu zuwa to yana da hanya da wani babba a harkar ƙwallo ko kuma shima wani babban ne a ƙasa. Bayan sun gama tarbar shi suna niyyar shiga cikin hotel ɗin ƙarar jiniya ta dakatar da su kowa ya kai idanun shi kan babban gate ɗin hotel din wanda daga nan ƙarar jiniyar ke fitowa, kai tsaye jerin wasu motoci na gani na faɗa gaba ɗayan su baƙaƙe ne suka shigo, wadataccen hasken wurin ya haske su sai sheƙi suke yi, motocin jami'ai ne a farko sai wasu manyan jeep guda ukku a ƙarshe wata motar jami'ain ce ta rufo masu baya, suna tsayawa jami'an suka shiga dirowa suna nufar ɗaya daga cikin jeep ɗin, yayin da wasu jami'an masu ƙirar ƙarfi suka ja layi tun daga farko har zuwa ƙarshen motocin gaba ɗaya jikinsu na sanye da kaki sun riƙe bindigu,  idanun minista akan motocin tun kafin wanda aka buɗe mawa ya fito ya gane ko waye sakamakon ya san da sun kai mashi katin gayyata kasantuwar shi masoyin ƙwallon ƙafa ne sosai kuma yana yin Deen,


  "It's vice-president." Minista ya faɗa tare da ɗan kallon Deen yana murmushi, kai ya jinjina mashi shima da ɗan murmushin, bayan an buɗe ma mataimakin shugaban ƙasan ya fito jikinsa sanye da baƙaƙen suit, gaba ɗaya manyan mutanen wurin har da Deen suka matsa don su tarbe shi, cike da girmamawa suka shiga gaishe da shi tare da yi mashi sannu da zuwa fuskarsa da murmushi yake amsa masu, daga baya ya maida idanunsa kan Deen bayan ya dafa kafaɗarsa ya yi mashi sannu da zuwa ƙasar tare da yabonsa, bayan gama gaishe- gaishe kai tsaye suka nufi shiga cikin hotel ɗin, jami'ai ne a gaba sai Deen da Minister da VP na a biye, daga bayan su dad ɗin Deen ne tare da wasu abokansa ƴan majalisa, daga bayan su wasu daga cikin masu ruwa da tsaki ne a harkar ƙwallo sannan su mom ɗin Deen, Leemah na jere da Fahad sauran mutane suka rufa masu baya, yayin da ƴan jarida ke ta aikin ɗaukar rahoto, wani abun burgewa tun daga in da aka tarbo Deen din har zuwa ƙopar shiga cikin hotel din red carpet ne aka shimfida suke tafiya a sama wanda hakan ke nuna Deen wani mai muhimmanci ne. 


Wurin da za a yi dinner ɗin ballroom ne wato babban ɗaki kamar hall da akan yi a manyan tsadaddun hotels, saidai irin wurin ya fi tsaruwa fiye da irin hall da aka saba yin hidindimu, ɗakin an kawata shi don yin taruka na musamman, kana shiga wani irin ni'imtaccen sanyin Ac ne zai tarbe ka, tun daga kan ginin ɗakin zuwa kan yadda aka tsara shi da decoration abun kallo ne ga wanda bai saba tsintar kansa a irin wurin ba, adon da aka yi a ciki mai aji ne ba mai hayaniya ba kalar na taron waɗanda suka jiƙu da kuɗi, suna shiga sauran mutanen da ke a cikin wurin gaba ɗaya suka maido idanuwansu kan hanyar shigowar suna masu mararin ganin tauraron ɗan kwallon, lokacin da ya shigo wasu har da miƙewa fuskokinsu ɗauke da murmushin farin cikin ganin sa, nan fa aka shiga ɗaukar shi hotuna da vedio, a nutse yake ɗaga ma mutane hannu yayin da suke nufar cikin wurin, jami'an dake tsaron su na biye da su wasu daga gaban su wasu a gefe da gefe yayin da suke nufar wuri na musamman da aka ware ma manya, irin tsarin zaman cin abinci aka yi ma kujerun wurin wato tebur a tsakiya sai kujeru a zagaye da shi gaba ɗaya an lullu6e su da yadi kalar decoration din wurin, daga saman kowanne tebur an yi ado da fulawoyi masu kyau saman ɗan stand da aka yi ma adon wasu sarƙoƙi masu ƙayatarwa, wurin da aka ware ma su Deen za su zauna na daga gaba. A can babban gate ɗin shigowa hotel din jami'ai ne sun kasa sun tsare suna bincike mutanen dake shigowa cikin hotel ɗin, koda baka daga cikin waɗanda za a gudanar da dinner din sai an bincika ka, a bakin kopar shiga ɗakin da za a yi taron nan ma wasu samudawan jami'ai ne jikinsu da hannuwansu ɗauke da manyan makamai yayin da rabin fuskarsu ke a rufe iya idanuwansu ne ake iya gani wanda ko haɗa ido da su ka yi sai ka shiga taitayinka, duk wanda zai shiga wurin sai an bincike shi tun daga sama har ƙasa saboda tsaro.



Ba tare da 6ata lokaci ba bayan dinner guests ɗin kowa ya zauna an natsu mai girma ministan wasanni ya fara jawabi bayan ya miƙe an bashi lasifika, cikin harshen turanci ya fara bayanin dalilin taruwar su,"Ladies and gentlemen, distinguished guests, it is our pleasure to welcome home our very own football superstar, DEEN JR.!" Ya ƙare maganar tare da dafa kafaɗar Deen hakan ya sa shi miƙewa tsaye fuskarsa cike da annuri, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauka da ƙarar tafin mutane. Ministan ya ci gaba da cewa, "Your achievements on the pitch have brought joy and pride to our nation. Tonight we gather to celebrate your success and express our gratitude for being an inspiration to our youth." Ya ƙare maganar idon shi akan Deen yana yi mashi murmushi.


Shima Deen murmushin yake na jin daɗin yabon da ministan ke yi masa, yayin da mutane suka ƙara saka tafi, cikin natsuwa yake ɗaga ma mutane hannu alamar ya ji daɗin tafin da suke masa. Bayan ministan ya gama jawabin nashi mai girma mataimakin shugaban ƙasa shima ya yi wanda yabo ne da kalaman ƙarfafa guiwa ya yi ma Deen, haka wasu a cikin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa suma suka yi nasu jawabin wanda yabo ne akan irin ƙoƙari da jajircewar Deen a harkar ƙwallo da kuma yadda yake saka ƙasa alfahari. Bayan gama duk jawabe-jawaben aka fara ciye-ciyen abinci da abubuwan makulashe, daga can bangare guda na cikin ɗakin anan aka jere iyayen kayan abinci da masu aikin zubawa da rarraba ma mutane jikinsu sanye da uniform, sai abun da mutum ke so za a kawo mashi a cikin abubuwan cin abinci da kofuna na ƙawa sai walainiya suke, kowa saida aka zuba mashi duk abun da yake so duk da haka masu aikin raba abincin nata zagayawa suna tambayar mutane ko akwai abunda suke so akawo masu, iyayen Deen na daga can gaba daga bayan inda su Deen suke a zaune, Fahad da Leemarh da Omar suna a wuri guda gefe da su mom ɗinsu, an natsu ana ta ciye-ciye baka  jin ƙarar komai sai ta cokulla dake haɗuwa da plate ɗin ƙarau, kowane tebur bayan kayan abinci an ajiye masu kwalin tissue mai kyau don goge hannu da baki, kowa ka gani fuskarsa cike da annashuwa wasu suna ci suna ɗan yin hira, kamar Fahad da Leemarh suma suna cin abincin suna ɗan ta6a hira, suna haka ta ɗan debo ta kai bakin shi yana murmushi ya buɗe baki ya amsa, itama ya ɗebo ya kai bakinta hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba dama saboda tana son ya bata a bakin yasa ta fara bashi, duk abun da suke mom ɗinsu na kallo baƙin ciki ya turnuke ta kamar ta je ta shaƙe Fahad take ji, gaba ɗaya fuskarta ba walwala ta haɗe rai, lura da yanayinta da ya canza da kuma saitin da take yawan kallo ya sa dad  shima ya juya ya kalli wurin su Fahad ya ga yadda suke ba juna abinci duk da a lokacin shi har da Omar ya ga Leemarh ɗin ta ba abincin a baki hakan ne ya sa shi bai fahimci miye dalilin da ya sa mom ɗin daure fuska haka ba.



Bayan an yi nisa da fara cin abinci wasu ma har sun gama ci don abu ne na ƴan gayu da yawa ba wani sakin baki suke su yi ta cin abinci ba, wasu abu kaɗan suke tsakura shike nan sun ƙoshi tun da dama an saba cin mai dadi sa6anin talaka bawan Allah wani abincin sai dai ya gan shi a hoto sai kuma idan Allah Ya ci da shi ya tsinci kansa a hidima irin ta masu hannu da shuni ya samu ya ci. Kwatsam! mutane suka ga hasken cikin ɗakin  ya ɗauke, har hayaniyar mutane ta ɗan fara karaɗe cikin ɗakin ana tambayar abun da ya faru suka ga an kunna wasu ƙananun fitulu ba masu haske ba sosai a can sama, basu gama mamakin dalilin ɗauke ainihin hasken wurin ba suka ga wani hasken mai yawa ya fara bayyana daga can sama yake saukowa ta gaban ɗakin taron inda mutum ke hawa in zai yi bayani ko za a nuna ma mutane wani abu ko bada kyauta, lokaci guda suka fahimci screen ne da alama wani abun za a haska mutane su kalla kamar dai a cinema, fahimtar abun da ke faruwa yasa hankalin mutane ya kwanta kowa ya natsu yana jira ya ga abun da za a haska, wani mutum ne da alama m.c ne ya fara magana ta cikin lasifika ya ba mutane hakuri kan rashin sanar masu abun da za a yi ya ce hakan cikin bazata ne, nan ya sanar dasu cewa za a haska wasu daga cikin performance ɗin Deen ne a fagen ƙwallo, gaba daya ɗakin aka saka tafi raf, raf, raf murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskokinsu. Wasu daga cikin manyan gasannin ƙwallo da ya buga kuma ya yi nasara aka shiga haskawa, nan fa ɗakin ya karaɗe da tafi da sowar mutane, tamkar a lokacin ake buga ƙwallon, idan ya ci haka zaka ji wasu sun saka ihu suna faɗin, 'Goallllll!' gaba ɗaya wurin sai ya koma kamar stadium kamar a nan take ake buga ƙwallon ba haskawa ake ba, kowa idonsa na akan screen, tuni masu cin abinci sun daina hankulansu sun koma can, shima Deen idonsa na akan screen yana kallo yana ta sakin faffadan murmushin jin dadin irin yadda mutane ke ta faɗin kalaman yabo kan yadda ya iya ƙwallo, wasu daga cikin matan dake wurin musamman ƴan mata ba wai yadda yake yin ƙwallon bane ke burge su don wasu ma ba masoya kwallon bane kawai shi Deen ɗin ne yake burge su, tun bayan fara taron wasu cikin yan matan dake a wurin idanunsu na akan duk wani motsin shi, hatta iyaye mata da wasu da yawa daga cikin mazan duk burge su Deen yake yi. 



Bayan an gama kallon perfomance din sa sai kuma aka shiga haska mabambantan lokutta da aka bashi kyaututtuka a harkar kwallon, daga karshe aka yi replaying wuraren da ya ci ƙwallo daban-daban in slow-motion, gaba ɗaya ɗakin ya ƙara harmutsewa da hayaniyar murna, ba kamar ƙwallon ƙarshe da ya ci a extra time a gasar cin kofin zakarun nahiyar africa wato AFCON wadda ita ce ta saka Nigeria yin nasara. 


Bayan an gama haskawa, hasken ɗakin ya dawo lokacin Deen din ya mike smiling humbly, sauran mahalarta taron ma duk suka miƙe suna mashi tafi fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki, manyan mutane dake a kusa da shi suka shiga shaking hand da shi wasu suna patting bayan shi suna taya shi murna da kuma fatan alkhairi a harkar shi ta ƙwallo. Daga baya minister da sauran football officials suka karrama shi ta hanyar bashi lambar yabo tare da yi mashi godiya kan irin gudunmawar da yake ba harkar wasanni a Nigeria.


Bayan karrama shi shima ya yi godiya cikin turancin shi mai dadin sauraro, "....Thank you everyone for this incredible honor. I'm proud to represent Nigeria on the global stage, and I'm committed to continuing to make our country proud." Gaba ɗaya aka saka tafi, daga baya ya yi godiya ga iyayensa da ƴan'uwanshi kan goyon bayan da suke bashi da yadda suke ƙarfafa mashi guiwa ya bayyana hakan na daga cikin sirrin nasarorinsa, daga karshe ya yi godiya ta musamman ga ɗan'uwan sa mafi soyuwa a gare shi wato Fahad, ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya fara fito mashi da baiwar shi ta ƙwallo, ya ce duk da da bai manta yadda ya sha wuya a hannunshi ba in suna yin ƙwallon a cikin compound ɗin gidansu ya yi ta sa mashi kafa yana kayar da shi wani lokacin har ya yi fushi ya ce ba zai ƙara yin ƙwallon da shi ba, ƙarshe haka zai lalla6a shi ya rarrashe shi su ƙara yi kuma hakan ba zai hana ya ƙara cutar shi ba, ya ce sai dai a yanzu ya fahimci ba cutar shi yake ba a lokacin yana molding nashi ne to become who he is today, yana bayanin yana yin ƴar dariya idanunsa akan Fahad da shima yake yin dariyar, haka ma sauran mutanen dake saurara wasu dariya ce akan fuskokinsu wasu kuma faffaɗan murmushi, idan ka cire mom da ta tsuke fuska sam bata ji daɗin yadda yake yabon Fahad ba a gaban jama'a har da wani kiran shi dan'uwan shi mafi soyuwa a gare shi, kalmar ta matuƙar ƙona mata rai. Bayan Deen ya gama jawabin nashi shima Fahad ya miƙe ya yi kalaman yabo kan irin ƙoƙari da jajircewar dan'uwan nasa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga nan shima Deen ya ba wasu daga cikin manyan da suka haɗa mashi dinner ɗin kyautar jerseys ɗin kungiyarsu mai ɗauke da lamba 7 da yake bugawa, daga baya aka shiga ɗauke-ɗauken hotuna tare da shi.


Leemah na tsaye gefen Fahad bayan an yi masu hotuna da Deen wasu ƴan mata da suka gaji da haɗuwa suka ƙaraso wurin suna tafiya sai ka ce masu jin tausayin taka ƙasa, sun sha gayu da matsattsun dogayen rigunan lace ko mayafi babu da takalma masu uban tsini, kana ganin su ka ga ƴan mata zubin Abuja da alama ƴaƴan wasu manya ne a wurin, tun bayan da aka fara yin dinner ɗin hankalin ɗaya daga cikin su yake kan Deen don ba ƙaramin son shi take ba duk in za a yi kwallo da shi sai ta kalla, yau ne karo na farko da ta fara ganin shi a zahiri hakan yasa gaba ɗaya ya tafi da imaninta, a matuƙar ƙagare take da ta samu damar da zata yi magana da shi, ita kuwa ɗayar tun da ta ɗaura idanunta akan Fahad lokacin da Deen ke yabon shi ta ji ta afka kogin son shi, hakan ya sa suka yanke yin amfani da damar da suka samu ta yin hotuna da su sai su yi masu magana, cikin salon jan hankali budurwar dake son Deen ɗin ta ce mashi pls bari su yi hoto ya amsa mata da ok don duk wanda ya zo zai yi hoto da shi yana bashi dama duk da akwai jami'ai dake zagaye da shi don tsaron shi, lokaci guda Leemarh ta tamke fuska ganin ɗayar tana ma Fahad wani murmushi ta ce mashi tana son zata yi hoto da shi, aikuwa ba zato sai ji ya yi Leemah ta kama hannun shi ta riƙe gam, maido idanunsa ya yi kanta ya ga ta wani haɗe fuska tana farfari da idanuwa, ɗan murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba ya janye idanunsa, wani kallo budurwar ta yi ma Leemah don duk tana ganin abun da ke faruwa, fuskar budurwar ba yabo ba fallasa ta ce ma Leemah ta dan yi excuse nata za su yi hoto tare da Fahad, ta sakar mata wani kallo mai kamar harara ta ce mata ai bata hana ba ga wuri nan ta nuna mata gefenta, hakan ba ƙaramin ƙular da budurwar ya yi ba don sai ta ga ta ci mata fuska gashi tana ganinta ba sa'ar ta ba, ƙarshe dai dole a gefen Leemah ɗin ta tsaya aka yi masu hoton, sam Leemah ta hana kowace mace damar yin hoto da Fahad dole sai ta shiga tsakani, hakan ya sa wasu suka fara tunanin ko budurwarsa ce ita, ga shi ba yadda za a yi da ita don kana kallon fuskarta ba sai an faɗa maka ba zaka fahimci ƙanwar wanda aka yi taron domin shi ce don suna kama da Deen sosai, shi dai Fahad murmushi kawai yake ganin irin ƙarfin halinta. 



Alhamdulillah, dinner ta tashi lafiya kowa yana cikin farin ciki musamman masoyan Deen waɗanda ya kasance yau ne rana ta farko da suka fara yin tozali da shi har sun samu damar yin magana da kuma yin hotuna da shi. Kan ka ce mi tuni hotunan dinner ɗin sun karaɗe kafofin sada zumunta mutane nata tofa albarkacin bakin su, wasu daga cikin masoyan Deen da magoya bayan club ɗin shi ƴan Nigeria nata cika bakin wllh da sun san da za a yi dinner ɗin sai sun je ko da bala'e kuma sai sun shiga.....





*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post