_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q
WhatsApp Group
https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 5
.....Bayan Salma ta gama yin wankin, cikin barandar ta dawo, har lokacin duk suna a zaune itama ta koma gefen babansu ta zauna, hira suka ci gaba da yi don lokacin ya gama cin abincin,
"Auwalu yau bazaka je can wurin aikin bane?" Baban ya tambaya idanunsa akan Auwalu dake lallatsa wayar shi shima tuni ya gama cin abincin, ɗan sosa kai ya yi ya ce mashi wllh ya dawo daga makaranta ya gaji ne yau sun sha lectures kuma gashi yana da assignment da zai yi saidai zuwa gobe in Allah ya kaimu, jinjina kai baban ya yi ya amsa da Allah Ya kai mu.
"Kai Sagiru gaba ɗaya ma so kake ka watsar da karatun naka ko? Yanzu kusan fin shekara da ka kammala karatunka na sakandare amman ka tsaya shiririta ka ƙi ka maida hankali ka ci gaba." Ɗan kikkafta idanu Sageer ya shiga yi yana dan murmushi bai ce komai ba.
"Shi wai nan babban ɗan kwallon ƙafa yake son zama." Salma ta faɗa, jinjina maganar baban ya yi tare da maimaita abun da aka ce yana son zama,
"Dama ka tsayar da hankalinka ka yi karatu, ka dai san a ƙasar nan sai mutum yana da hanya, akwai waɗanda suka iya ƙwallo sosai, da in aka taimaka masu ba ƙananun ƴan ƙwallo zasu zama ba, amman saboda basu da hanyar hakan gasu nan sun kare da bugawa a cikin unguwanni suna wahala basu samun komai." Auwalu ne ya faɗa cikin nuna girma.
"Ka ji abun da ɗan uwanka ya faɗa, don haka ka daure ka ci gaba da karatun ka kada a yi biyun babu, idan Allah Ya ƙaddaro zaka zama abun da kake so ko ba yanzu ba zaka zama, amman yanzu ka yi ta zama haka nan bai kyautu ba, ga ɗan uwanka nan ya dage da karatu kuma yana zuwa wurin sana'a, amman kai gaba ɗaya ka ƙi ka maida hankali kan sana'ar sosai. Rayuwa gudu take yi nan da ɗan lokaci kaɗan zaka ga an kai munzalin tara iyali, gara tun kan lokaci ya ƙure ma mutum ya samu madogara, don ajiye iyali bai yuwuwa ba tare da mutum yana da hanyar da yake samu ba, in kuwa ba haka ba mutum ya ce zai tara iyali ba wata ƙwaƙkwarar sana'a tabbas zai jefa kan shi a matsala babba, wahalhalun rayuwa su taru su yi mashi katutu, ina amfanin mutum ya tara iyali madadin ya ji da su dadi sai su ƙare da shan wahala."
A nutse Sagir ya ce, "In sha Allahu zan maida hankali in ci gaba da karatun, dama ina jira a fara sayar da form na Jamb zan siya in yi."
"To Allah Ya bada sa'a. Ku daure ku dage wata rana zaku ci ribar karatun, tun da mu bamu samu muka yi ba shiyasa muke son ku ku yi. Duk da Alhamdulillah, dai dai gwargwado da sana'a Allah Ya rufa mana asiri, amman in mutum ya haɗa da aikin zai fi wadatuwa, ita kanta sana'a in aka haɗa da ilimi tafi faɗaɗuwa, mutum zai ƙara sanin hanyoyi da dubarun da zai inganta sana'ar ta samu karbuwa ba a iya inda yake ba a fadin duniya baki daya." Duk sun natsu suna sauraren shi, ba tun yanzu ba ya saba zama ya yi masu nasiha kan abun da zai amfani rayuwarsu, akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin shi da iyalan nashi,
"Ke mamana ba zaki siya form na Jamb ɗin bane.?"
Kai ta ɗaga mashi ta ce, "Eh, abun da nike son karanta ba sai an yi ta ba."
"Ita ka san Auntynta Kubra take so ta gado, itama karatun aikin jinyar take son yi, a yadda ma suka tsara can Kaduna zata je ta yi karatun in ta ci jarabawa." Kai mahaifin nasu ya jinjina jin bayanin innarsu Salma yana murmushi,
"To sai ki dage, duk da nasan baki wasa da karatu. Allah Ya yi maku albarka, Ya baku sa'ar duk abun da kuka saka gaba na alkhairi, Allah Ya ƙara shiryar da ku a bisa tafarkin manzo (S.A.W)." Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin amsawa, "Ameen." Kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi, suna matuƙar jin daɗi in mahaifin nasu na yi masu addu'a haka.
"Yau baza ku yi awaran bane?" Auwalu ne ya tambaya yana kallon Salma, kafin ta bashi amsa baban nasu ya ce, "Af, ka ga na shafa'a ma, Sagir jeka waje akwai sauran katakai dana tattaro masu suna nan a bayan mashin." Cike da jin daɗi Salma ta ce yauwa dama tafi son yin amfani da sauran katakan akan gawayi.
"Amman mamana ai gawayin kaman ya fi sauki ba hayaki ko?"
Ta ce matsalar gawayin in ya cinye sai mutum ya ta saukewa yana girgijewa ya ƙara, shi kuwa icce ko katako kawai sai dai ta iza. Shigowa Sagir yayi hannuwan shi ruƙe da katakan da aka ɗaure, a gaban kitchen ya ajiye Salma na ganin su da ɗan yawa ta fara washe baki,
"Gasu nan, amman waɗannan biya na za a yi gaskiya, sai in ta kawo abu ana yin sana'a amman ba a bani komai, kuma nima ai siyo katakon muke yi." Dariya duk suka yi jin maganar baban.
"Amman ai kana cin awaran ko, kullum sai an ɗibar maka mai yawa, sannan kuma idan babu wasu abubuwan kamar magi da gishiri da sauran abun abinci ba Innarmu take badawa ba a siyo, watarana ma har abincin da za a dafa take bayarwa a siyo." Salma ta faɗa tana dariya, hannu baban nasu ya kai ya ruƙe ha6a ya ce,
"Tohh, abun yau gori za a mani ke nan." Suka saka dariya gaba ɗaya,
"Yau mun ji tsakanin ku, gashi nan duk yadda ka ke ji da ita amman ta yi maka gori." Hararar Sagir da ya yi maganar Salma ta yi ta ce, "To an ji, kanwa uwar gami."
"Ba abun da ya shiga tsakaninmu, ai tsakanin uwa da ɗanta sai Allah."
Ƴar ƙarar daɗi Salma ta saka ta fara yi ma Sagir gwalo tana fadin an gwasale shi. Hira suka ci gaba da yi cikin nishaɗi gwanin burgewa, sallar la'asar da aka fara kira ya tashe su, baban nasu ya yi masu sallama don komawa wurin aiki daga can in ya yi salla, suma kowa ya miƙe. Malam Bashir ya kasance mutumin arziki ba ga iyalinsa kaɗai ba, hatta mutanen da yake mu'amala da su suna yi mashi shaidar hakan, shi ɗin abun koyi ne ga duk wani magidanci mai iyali, rayuwar shi da iyalan shi ta kasance abun bada misali. Duk da bashi da wadata sosai amman yana da wadatar zuciya sosai, a ganin malam Bashir in har mutum zai tara iyali ya bari rayuwarsu ta tagayyara to miye amfanin tarawa, kullum ƙoƙarin shi ya wadata iyalansa ta bangaren abinci da sutura, gaba ɗaya yaran shi sun fita daban a cikin layin su, tun tasowar su haka zaka gan su tsaf-tsaf cikin sutura ta kirki bai barin su cikin tsumma, ta bangaren karatunsu da lafiyarsu nan ma a tsaye yake yana bakin ƙoƙarin shi, shi yasa sam yaransa basu da damuwar komai, tun tasowar su ba a ta6a kama su da laifin sun ɗauki abun wani ba saboda sun wadata, itama mahaifiyarsu ba zaune take ba tana yin ƴan sana'oin da take tallafa ma mijin nata sun taru sun rufa ma kan su asiri.
ABUJA.
Tun bayan gama sallar magrib su Leemarh suka fara yin shirin tafiya dinner da aka haɗa ma Deen. Tsaye yake gaban dresser idanunsa na kan madubin gaban shi yana gyara zaman waistcoat ɗin jikinsa, wato irin riga mara hannuwa da ake ɗaurawa saman riga ƴar cikin suit mai kaman falmara bayan ya saka ta cikin baƙa mai dogon hannuwa, yayin da Fahad ke can gefe saman kujerar gaban gado ya ɗan zamo jikinsa yana latsa wayarsa, shima da alama ya shirya yana sanye da baƙaƙen suit sai salƙi suke, daga gaban kayan zuwa ƙasan hannunsa farar rigar ciki ta fito don bai saka ma6allan kayan ba, yayin da wuyansa ke sanye da necktie baƙi, damtsen hannun shi ya ɗaura silver din agogo itama sai salki take, haka ƙafafunsa ya saka dress shoes wato rufaffun baƙaken takalma da suka matuƙar ƙara ƙawata shigar tashi, a kallo ɗaya in ka yi masa zaka yanke hukuncin yana daga cikin matasan Abuja da suka taso cikin hutu da jin daɗi saboda yadda shigar ta amshi jikinsa, sumar kansa da ta fuskarsa sun sha gyara sun kwanta luf.
Shigowa ta yi cikin ɗakin ko sallama babu, motsin da Fahad ya ji ya saka shi ɗaga ido ya kallo ta suka haɗa ido, mom ɗin su Deen ce ta shigo, da alama itama ta shirya tana sanye da wata jigunanniyar abaya maroon mai duhuwa, kallo ɗaya in ka yi mata sai ka firgita da kyaun da ta yi a cikin rigar, ta matuƙar amsar jikinta farinta ya fito sosai wani fayau, saman kanta ta naɗa gyallen rigar yayin da fuskarta ta yi makeup har da janbaki kalar rigar wato maroon, ƙafafunta tana sanye da takalma half cover masu dan tsini kalar aikin rigar wato golden, haka hannuwanta ta riƙe purse wadda da gani mahaɗin takalman ce itama golden, ta dai yi kyau sosai ba ƙarya.
Cikin ɗakin ta shige ba tare da ta ƙara kallon in da Fahad yake ba, shima ganin bata bi ta kansa ba yasa shi maida kan shi ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya tanka mata ba, gaba ɗaya ɗakin ya ƙara karaɗewa da ƙamshin turarenta sai ka ce ba matar aure ba, kuma a haka zata je ta shiga cikin mutane, wurin da Deen yake ta nufa tana tafiya cike da isa da izza, tun da ta taho Deen ya hango ta ta cikin mudubi har ta karaso ta tsaya daga bayan shi ta gefen shi, haɗa ido suka yi ta cikin madubin ya ɗan yi mata murmushi, itama shi ta mayar masa kafin ta maida idanunta akan sumar gemun shi da yake ƙara gyarawa sai ƙyalli take, ganin bata yi mashi magana ba yasa shi maida hankali kan shirin shi, wani box mai kyau dake ajiye a saman dresser ɗin ya ɗauko ya buɗe, kan shi kwalin abun kallo ne balle kuma abun da ke a ciki, saida ya cicciro wasu fararen takardu masu kauri kaman kati da wani mai kaman ɗan littafi kafin ya kawo in da abun da ke ciki yake, wata rantsattsiyar agogo ce ya fiddo silver bayan ya warware abun da aka naɗe ta da ita, nan take ta fara walainiya da gani ba sai an faɗa ba sabuwa ce lokacin aka fara buɗe ta kuma jikinta ya bayyana mai tsada ce, yana ƙoƙarin ɗaura ta a hannunsa mom ɗin shi ta matso tare da miƙa mashi hannu alamar ya bata, dakatawa ya yi ya bata ta shiga jujjuya ta a hannunta,
"Amman da gani agogon nan zata yi tsada sosai ko?" Ta tambaya tana ɗage gira, kai ya ɗaga mata tare da faɗi mata kuɗinta, ɗan waro idanu ta yi jin miliyoyin da ya faɗa.
"Ku dai ƴan ƙwallo da alama kuɗin ku duk a wurin siyan kaya masu tsada suke tafiya, komai ka siya sai a ji shi da uban kuɗi!" Ta ƙare da alamun mamaki, murmushin gefen fuska ya saki still ta cikin madubin yake kallon ta cikin sautin muryan sa mai daɗi ya furta, "Ta hakan muke samun wasu kudin." Da alamun rashin fahimta ta ce, "What do you mean...?"
"Kaman muna yin talla ne, and, wasu kamfunan muna da hannun jari in aka gani a jikin mu za a siya kayan, sannan muna ƙara samun followers saboda gayun." Ya ƙarasa yana ɗan murmushi, jinjina kai ta yi idonta akan shi yana ta ƙara gyara zaman bowtie ɗin wuyan rigars,
"Suma followers ɗin biyan ku ake da su ko?" Kai ya jinjina mata alamar eh,
"Wato harkar ƙwallon nan dai ba ƙaramin kuɗi ake samu da ita ba, ba kamar in mutum ya ɗaukaka, shi yasa na so a ce ka taimaka ma Omar shima ya zama kamar kai amman ka ƙi bada goyon bayan hakan." Ta faɗa da ɗan alamun bacin rai, hannunsa guda akan gemunsa yana ƙara gyara sumar wurin da alama dai yana ji da ita, a taƙaice ya furta, "Ba abun a tare da shi ne." Yamutsa fuska mom ɗin ta yi, tun farko lokacin da ta nuna tana son Omar ya zama kamar shi ya faɗi mata cewa bai da baiwar hakan don ya gwaggwada shi, ko ya fara yin ƙwallon ba inda zai je.
"To shi Adam fa? Shima ka ƙi ka ɗaura shi a hanya kuma yana son zama ɗan ƙwallo sosai, kuma shi dama ko a Kano yana bugawa, har tura shi na yi London wurin ka amman shima still baka goya mashi baya ba." Shiru ya yi jin tana magana akan ƙaninta, ko ta ina zai zama wani babban ɗan ƙwallo mutumin da babu abun da ya sa a gaba sai shiririta tuni ya kashe rayuwar shi da shaye-shaye har da neman mata.
"Ka yi mani shiru!" Ɗan yamutsa fuska ya yi, "To mi zan ce mom? I thought mun gama wannan maganan since." Ta6e baki ta yi, a hankali ta juya ta kallo wurin da Fahad yake, saidai bata hango shi ba a inda ta gan shi zaune da alama fita ya yi daga cikin ɗakin, juyowa ta yi a cikin ranta tana ayyana daga ganin kayan da ta gani a jikinsa masu tsada ne sosai.
"Can i have it?" Ya faɗa tare da miƙo mata hannu alamar ta bashi agogon.
"Suma su Omar ka kawo masu kayan ne?" Ɗan yamutsa fuska ya yi ba tare da ya bari ta gani ba don ya gane saboda kayan da ta gani ne a jikin Fahad ya sa ta yi mashi tambayar.
"Bai nuna maki bane?" Ya faɗa yana ɗaura agogon, yamutsa fuska ta yi ta ce, "Yea na gani, Allah Ya sa masu kuɗi ne ka siyo masu, don na san ka iya fifita bare akan jininka." Wani guntun murmushin gefe ya yi, wai ya iya fifita bare, ko waye baren? Ya faɗa a cikin ransa, ganin ta kafe shi da ido fuska a haɗe ya sa shi ɗan juyowa ya kalle ta ya ce, "You can google to check their prices." Daga haka ya wuce can wurin closet ɗin shi ya shige, bai ɗauki lokaci ba ya fito daga ciki hannunsa ɗaya rataye da navy blue ɗin jacket ɗin kayansa yana tafiya cike da ƙasaita saidai shi ba da wani abu yake yin hakan ba haka tafiyarsa take, haɗaɗɗun rufaffun takalman kafarsa wanda su kan su miliyoyin naira suke sun ƙara fito da kyawun shigar tashi, sai faman baza ƙamshi mai narkar da zuciyar wanda ya shaƙa yake, wurin ta ya nufo ya tsaya daga gabanta yana ƙoƙarin saka jacket ɗin, bayan ya gama saka ma6allan mom ɗinsa da ke ta faman bin shi da ido ta ce, "Kyau a ce Basmah tana a gefen ka, da sai gayun naka ya fi fitowa." Lokaci guda ya ji wani abu ya ziyarci ransa mai kama da 6acin rai, ya yi shiru bai ce mata komai ba,
"Duk da ka ce wai saboda makaranta yasa baka taho tare da ita ba, da ka so ai zaku iya tahowa duk da hakan, I don't know why baka bata muhimmanci yadda yakamata, and she's your fiancee yakamata ace kuna samun kusanci da ita sosai ko ina ya kasance kuna tare, kamar yadda zaka ga wasu sanannun mutane suna nuna matan da suke so, ko za su aura, amman kai bana tunanin ma an san da ka tsaida matar da zaka aura." Shiru ya yi yana ta kallonta har ta gama maganar, a ransa ya ayyana matar dai da aka tilasta masa ya aura, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "Mom, yanzu ya za ai a ce duk inda nike mu kasance tare da ita, is that even possible? Kuma miye amfanin mutum ya yi ta bayyana ma duniya ga wadda zai aura? I think idan lokacin da zamu yi auran ya yi dole za a sani no need sai na bayyana hakan yanzu." Ganin yanayin da fuskarsa ta nuna kaman bai ji daɗin maganan ba ya sa ta sassauta muryarta ta ce to amman ai ko nan ɗin da sai ya taho da ita su ganta tun da sun kwana biyu basu gan ta ba, ci gaba da saka ma6allan rigarsa ya yi, ya bata amsa da idan lokacin da suke zuwa vacation ya yi za su zo ne sai su ganta, ta yi sototo tana kallon sa don duk wasu alamu na rashin son ya kusanta kan shi da Basma sun riga sun bayyana, sai dai ta sha alwashin matuƙar tana raye bashi da mata in ba Basma ba, kallon ta ya yi bayan ya gama daidaita rigan a jikin shi, ɗan murmusi ya yi mata tare da ɗage gira ya ce, "Can we go?" Ƴar harara ta wurga mashi ta ce wato ta zo ta ishe shi da haushi ko, still murmushin ne akan fuskarsa ya ɗan lanƙwasa mata hannunshi, tana ganin haka ta ɗan saki murmushi ta saƙa nata hannun a cikin nasa kamar yadda turawa saurayi da budurwa suke yi suka nufi hanyar barin ɗakin, duk da kasancewar mom ɗin tasu mai tsawo kuma ga takalma masu tsini amman sai gashi Deen ɗin ya ɗara ta tsawo ko don tana mace.
Bayan Fahad ya fito daga part ɗin Deen, kai tsaye matattakalar bene ya nufa don sauka ƙasa, a natse yake taka matattakalar daidai ya kai tsakiya sai ga Leemarh ta ƙaraso zata hawo benen, a kusan tare suka tsaya cak suna kallon juna, wato ni kaina na girgiza da ganin matuƙar kyawun da ta yi, abun ka da farar mace kuma sai ta yi shigar red hakan ba ƙaramin kyau ta yi a cikin shigar ba, doguwar rigar ɗanyen jan material ce ta saka, rigan straight gown ce ta kamata hakan yasa shape ɗin ta ya fito, hannun rigar na material ɗin ne ba a saka wani abu a ciki ba hakan yasa ana hango jikin hannun nata amman ba sosai ba don daga yanayin material ɗin yana da ɗan kauri, sosai material ɗin ya haɗu duk da bashi da kwalliya sosai wasu gashi-gashi ne a jikin shi masu salƙi daga gani zai yi taushi, a hannunta hadaddiyar purse ce silver sai takalman ƙafarta mahaɗin jakar ne, duk da ba gajera bace takalman nata masu tsini ne irin wanda daga sama suke da maɗauri, a wuyanta yar ziririyar sarƙa ce tare da ƴan kunnayenta sai ka ce na diamond wataƙil ma su ne, a hannunta guda ta ɗaura agogo itama silver, a saman kanta jan head ne wanda ba irin yadin material din bane wani material din ne daban, shi kan shi ɗaurin ba ƙaramin kyau ya yi ba, ɗauri mai steps aka yi mata ta yadda daga gaban kan gashinta da aka tsaga tsakiya ya ɗan fito an faka shi ta baya, musamman ƙwararriyar mai yi masu make-up ta zo ta yi masu ta kuma shirya su. A hankali suka shiga sakar ma juna murmushi ba tare da sun motsa ba, Fahad ne ya ci gaba da saukowa idon shi akan ta har ya iso bakin benen ya sauka ƙasa, fuskantar juna suka yi sam kowa ya kasa magana sai murmushi kawai,
"Who could resist this beauty?" Bayan ɗan lokaci ta ji Fahad ɗin ya furta, kunya ce ta kama ta don ta fahimci dalilin da ya sa ya faɗi haka, saboda maganar da ta yi masa lokacin da yake cin abinci na akwai wanda take so amman tana tsoron ya ƙi amincewa in ta sanar da shi, shine yanzu ya yabe ta ta hanyar cewa 'waye zai ƙi wannan kyawun?" Hannunta guda ta sa ta ɗan rufe fuskarta alamar kunya, ga jan lallen da aka yi mata dama na zuwan Deen mai kyau mara yawa ya bayyana ya yi ja shar gwanin burgewa.
"Kin yi kyau sosai. U look like a bride." Cire hannun da ta rufe fuskar ta yi, tana murmushi ta ce, "Thank you ya Fahad. Kai ma ai ka yi kaman ango." Ɗage gira ya yi ya ce ango da irin shigan shi,
"Eh, kaman groom ya yi shigan dinner." Ɗan faffaɗan murmushi ya yi ya ce, "To ko angon ne? Dama gashi shigan dinner ɗin na yi, amman kuma ba bride en, ko idan muka je sai in samu a can?" Ƴar dariya ta yi ta ce, "Ya fi dai ka tafi da amaryan."
Dariya ya yi dimples dinsa suka lotsa, ya riga da ya gama fahimtar ta, da hannu ya yi mata alamar su je cikin falon, suka jera suna tafiya a nutse sai ka ce ango da amaryan yadda suka dace, duk da Leemarh ba wata babba bace amman shigar da ta yi ta ƙara mata girma. Saman kujera mai mazaunin mutum biyu suka zauna suka ɗan karkata ta yadda suke fuskantar juna, hira suka shiga yi yawanci shine ke mata tambayoyi akan karatun ta da wasu abubuwan.
Lokacin da suka ƙaraso bakin matattakalar Deen ya saki hannun mom ɗin nashi suka fara saukowa, suna kaiwa tsakiyar benen idanun mom suka sauka akan Fahad da Leemah dake ta hirar su cikin nishaɗi suna ta murmushi, wani baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi ta ɗaure fuska tamkar ta ga wani mugun abu, a cikin ranta ta shiga cin alwashin sai ta raba su koda a ce ba soyayya suke ba sai ta kawo ƙarshen wannan shirin nasu don ba shi take haifa ma yaran ba da kowa zai rinƙa shiri da shi suna son shi sosai, kafin su ƙarasa safkowa ƙasa Batool ta fito daga hanyar bangaren su itama doguwar rigar material ce a jikinta ruwan madara, an yi mata makeup itama an gyara mata gashinta ya sauko har bayanta an ɗaura mata net ya yi kaman hula ta fito a yar matashiyar mace yar shekara sha biyu, tana hango su mom ɗinsu ta ambaci sunanta tare da nufar wurin su, a tare Fahad da Leemah suka juya jin sunan mom da Batool ta kira, miƙewa suka yi ganin sun nufo cikin falon, wata muguwar harara mom ta shiga wurga mata, Leemarh ta yamutsa mata fuska tana ɗan tura baki, wani irin ƙamshi ne ya gauraye wurin kasantuwar kowa da kalar abun kamshin da ya shafa, murmushi Fahad ya shiga sakar ma Deen ganin yadda ya yi kyau sosai, shi kan shi ya burge shi, hannu ya ɗan dunƙule ya miƙa ma Deen shima ya yi ma nashi hakan suka ɗan buga irin gaisuwar gayu, Fahad ya ce, "You are looking sharp! You are the GOAT, on and off the pitch!"
Yar dariya Deen ya yi jin yabon da Fahad ɗin ya yi masa har yana kiransa da suna mai matuƙar girma wanda samun sa ba ƙaramin aiki bane a duniyar ƙwallo, amsa ya bashi da, "Tukunna dai, Ya Fahad." Ya faɗa tare da ɗan jinjina kai yana murmushi.
"Ya Deen, in sha Allah you are going to break all the records, trust us you are going to be the GOAT (Greatest Of All Time)" Leemarh ta faɗa tana murmushi, ita kanta gayun na shi ya tafi da ita, dama ba tun yanzu ba sun san yayan nasu da iya ɗaukar wanka, wanda har da hakan ke ƙara mashi masoya musamman mata ba ƙaramin tafiya yake da imanin su ba, gaba ɗaya duk suka amsa ma maganar da Leemah ta yi suma suka furta in sha Allah har da mom ta furta ƙasa ƙasa, yana murmushin jin daɗi ya yi masu godiya. Suna haka sauran yan gidan su Omar da Sultan duk suka fito suma duk wankan suit suka yi sun yi kyau ma sha Allah, daga ƙarshe Dad ɗin su shima ya fito daga bangarensa ya nufo cikin falon jikinsa sanye da suit ruwan toka, sosai kayan suka amshi jikinsa ya fito a babban mutum mai ƙwarjina da haiba, duk idanunsu na akan shi fuskokinsu ɗauke da murmushi har ya ƙaraso wurin su shima yana masu murmushi,
"Wow! Gaskiya dad ka tashi kaina! Ka gan yadda ka yi kyau sosai?" Leemarh ta faɗa ta ɗan buɗe ido, yana murmushi ya yi mata godiya ya miƙo hannu ya ɗan rungumo ta ta gefe.
"Dad, wllh ka yi kaman su ya Deen." Batool ta faɗa tana dariya tare da noƙe kai, itama ya janyo ta jikinsa yana yar dariya ya ce mata ke nan ya koma ɗan saurayi, ta ɗaga mashi kai tana dariya.
"Ki ce wataƙil ma wata ta yaba da wankan nawa in samo maku aunty a can ke nan." Duk suka saka dariya ban da mom da ta hade fuska, ya saci kallonta bayan ya yi maganar suka haɗa ido ta wurga mashi harara, ɗan murmushi ya yi shima yasan ya faɗa ne kawai.
"Are we good to go?" Dad ya tambaya yana kallon Deen da murmushi ganin yadda ɗan nashi ya yi kyau sosai, kallon agogon hannunsa ya yi kafin ya kalli dad din ya ce mashi zasu iya tafiya kusan lokacin ya yi, gaba ɗaya suka nufi hanyar barin falon suna tafiya cikin natsuwa, kana kallon su ka ga waɗanda hutu da jin daɗi ya zauna musu sosai. Tuni an jera motocin da za su tafi da su a gaban entryhall, bayan sun fito aka shiga bubbuɗe masu, Deen da Fahad wata haɗaɗɗiyar baƙar Mercedes S-Class ce suka shiga sai uban sheƙi take irin na sabunta, motar tashi ce ba a jima da kawo ta ba kafin ya zo, dama akwai wasu motocin da ake amfani da su a gidan waɗanda shine ya siye su, dad da mom ɗinsu suma mota ɗaya suka shiga sai sauran yaran har da Omar suka shiga cikin wata ƙatuwar baƙar jeep, tsaye Leemarh ta yi har saida ta ga mom ɗin su ta shiga cikin mota sannan ta yi saurin nufar motar su Deen ta buɗe kofar baya za ta shiga, Fahad da Deen dake zaune a bayan a tare suka kalle ta, ta ɗan yamutsa fuska ta sigar shagwaba ta ce masu a motar su take son tafiya, ɗan murmushi Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fito daga bayan ya yi mata alamar ta shiga da hannu, shi kuma ya koma kujerar gaban motan ya shiga, bayan duk sun gama shiga a tare aka tashi motocin suka nufi hanyar gate abun gwanin sha'awa, dama ga su duka motocin baƙaƙe ne sai sheƙi suke yi, daga bayan su kuma motar jami'ai ce ke take masu baya......
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
