A Cikin Rayuwa Page 13 by Zee Laluh | Abokiyar Hira


 _Bossladieswriters_




_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q


WhatsApp Group


https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt




*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*



    

    _By Zainab Bature_



   

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._






Page 13



A 6angaren amarya da ango suna ta shan soyayyar su, saidai tun ba a je ko'ina ba hajiya ta fara fahimtar wasu daga cikin halayen Jameela, ƙiri-ƙiri take nuna bata son dangin su dake zuwa a fakaice take yi masu wulaƙanci da kora da hali, farkon kawo ta sosai take ma Hajiya biyayya kullum sai ta je ta gaishe da ita ta tambayi ko akwai abun da za ta yi mata, ko da hajiyar ta ce mata babu komai sai ta je kicin ta taya mai aikinta wani abun, a hankali ta fara janye ƙafa sai ta gadama sannan ta je ta gaishe da ita, sanin tana zuwa ya sa idan Hajiya ta ga an kwana an wuni bata je ba sai ta tambayi Ibrahim ko lafiya idan shi ya je gaishe da ita, wani lokacin har ƙarya yake mata ya ce Jameelar ce bata jin daɗi, daga baya hajiya ta fahimci hakanan ganin dama ne ya sa bata zuwa gaishe ta kaman yadda ta saba sai itama ta fita batun ta, iyaka idan Ibrahim ɗin ya je ta tambaye shi suna lafiya. Sai da ta kai har sai ya matsa ma Jameelar sannan wani lokacin zata je gaishe da hajiyan. Watan su biyu da yin aure ta samu juna biyu, a lokacin sai abun da ya ci gaba na iskancin ta, farko ma bata yi murna da cikin ba wai ita ba yanzu take son samun ciki ba gaskiya karatu take son ci gaba da yi, lalla6a ta ya yi ya rarrashe ta kan ta yi haƙuri ta haifi wannan daga shi sai su bari bayan ta kammala karatun sai ta sake haihuwan. Ba ƙaramin wahalar da shi take ba da buƙatun cikin, gaba ɗaya ta daina yin girki dama ba wani cika yi take ba sai ta gadama don ana kawo masu daga part ɗin hajiya, ga ƙazantar tsiya ko jikinta bata damu da ta gyara ba, gashi irin laulayin tofar da yawu take haka zata tofar a duk in da ta samu, yalwatacciyar sumar kanta ma duk ta barta ta harmutse bata gyarawa, ba uwar da take yi daga kwanciya sai cin abun da ta ga dama, ko wanka ma sai an ci sa'a dole Hajiya ta sa aka samo mata mai aiki,  wani lokacin in hajiya ta je duba ta ita zata matsa mata kan ta daure ta tashi ta gyara jikinta, haka za ta tashi tana ta ture-turen baki, ba ƙaramin jin jiki Ibrahim yake ba akan cikin don kuwa hakkin shi ma wannan ba a maganar shi gaba ɗaya ta hana shi wai bai tausaya mata. 


Tun ana gama bikin Alhaji Nuraddeen ya koma  wurin aikin shi, ita hajiya ta ce zata ɗan zauna saboda su Ibrahim ɗin, Jameela na a cikin halin laulayin take ma Ibrahim maganar wai yaushe za su bar ƙasar ai ya ce mata ba su cika zama anan ba, ya ce mata yana jira sai hajiya ta yi maganar lokacin da za su tafi, ganin har cikin ya kai kusan wata biyar ba ai zancen tafiyar na su ba ya sa ta matsa mashi lamba wai ita tafi son ta ci gaba da rainon cikin a ƙasar waje kuma ta haihu hannun ƙwararrun likitoci, ganin ta matsa ya sa shi samun hajiya ya yi mata zancen tafiyar su, a lokacin ta ce mashi tun da juna biyun matar shi ya fara girma bari ta yi ta sauka, jin haka ya sa shi ce mata wai da ya fi son su koma saboda tafi samun kulawa kuma ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci, duk da bai fito fili ya bayyana hakan ra'ayin Jameela bane hajiyar ta so ta fahimci hakan, cikin ɗan murmushi ta ce mashi duk nan ƙasar ba ƙwararrun da za su duba mashi matar tashi ne, ko yayan shi ba a nan aka haifa mashi yaron shi ba, bai dai ce mata komai ba a lokacin itama bata bashi tsayayyar magana kan komawar ta su ba, koda Jameela ta ƙara mashi magana kan hakan ya faɗa mata Hajiya ta ce anan zata haihu, aikuwa ta shiga yin tijara iri-iri, gaba ɗaya ta hana mashi zaman lafiya har tana cewa ita ta yi zaton ma suna yin auren za su tafi honeymoon ƙasashe amman an zo an jibge ta a ƙauye, ga yayan shi can da iyalinshi suna ƙasar waje sai ita don tana bare shine za a ƙi yi mata abun da take so, duk ƙoƙarin shi na ya fahimtar da ita shi Sa'ad aikin shi yake a can ta ƙi sauraren shi. Lokacin da cikin ya isa fara zuwa awo hajiya ta yi mashi magana, ya yi ma Jameela maganar amman fir ta ƙi fara zuwa wai ai ba a damu da lafiyar abun cikin nata ba shiyasa za a barta ma'aikatan asibitin ƙauye su duba ta, da abun ya ishe shi kawai sai ya kira dad ɗin shi ya roƙe shi kan yana son ya taho da Jameela don bata jin daɗi, ya ce cikin na wahalar da ita sosai yasan zata fi samun kulawa anan, hajiya ta yi mamaki lokacin da dad ɗin ya yi mata maganar, dama tun lokacin da ya fara neman auren Jameela ya fara ja da maganarta, bayani ta yi ma dad ɗinsu ta ce mashi ba wata wahalar da take sha kawai dai shine ya fi son hakan kuma ta bari cikin ya yi ƙwari sosai sai su taho, ya ce mata to in tana ganin ba matsala kawai su taho da itan dama itama yakamata ta dawo hakanan. 



Farin ciki a wurin Jameela ba ya misaltuwa lokacin da ta ji zancen tafiyar su ƙasar Australia da a lokacin nan dad ɗin yake aiki, Ammin su na jin zancen tafiyar tasu bayan ta sanar mata sai cewa ta yi wai ta tafi da Naila, haka ta sanar ma Ibrahim din cewa tana son tafiya da ƙanwarta don ta rinƙa taimaka mata, lokacin da ya yi ma hajiya maganar ranta ya 6aci ganin yadda Jameelar ke son mayar da su shashashu, cikin yanayi na 6acin rai ta ce mashi ba za a je da wata ƙanwarta ba ko ta ɗauka tafiyan kaman zuwa Kano ne, duk wata kulawa ai zata samu a can tun da anan ma bata rasa hakan ba, a karon farko da ta fara magana akan tsakanin shi da iyalinshi cikin ƙoƙarin ankarar da shi ta ce,


   "Ibrahim, yakamata ka isa da gidanka ka zama namiji, ba baki zan maka ba amman muddin ka ci gaba da sake ma iyalinka, ka ce duk abun da take so sai ka yi mata koda kai zaka takura da hakan to kuwa watarana zaka yi kuka da hakan, saboda mata ba a sake masu gaba ɗaya don abun zai ta ƙara gaba ne har ya kai girman   da lokacin da zaka so ɗaukar matakin gyara hakan ya fi karfin ka..." Cikin kwantar da murya ta ci gaba da nusar da shi illar dake tattare da hakan, cike da nuna gamsuwa da maganar ta ya yi mata godiya. Jameela ta ji haushin jin ba za a tafi da Naila ba, haka tai ta faman fushi ya bata haƙuri tare da nuna mata tafiyar da itan ne ba zai yuwuwa ba tun da ba a shirya hakan ba. Ba tare da wani ɗaukar lokaci ba aka gama yi ma Jameela duk wani shiri na tafiya, lokacin da ya rage saura sati ɗaya su tafi suka shirya zuwa Kano don ta yi bankwana, kuɗi masu yawa ta buƙata a wurin shi wai zata ba iyayenta tun da tafiya zata yi, ya nuna mata bashi da su tun da bai riga ya fara aiki ba dama yawanci ɗawainiyar su iyayen shi ke yi masu, rufe ido ta yi ta kama yi mashi masifa har tana faɗin ita da ta san irin rayuwar da zata fuskanta ke nan a gidan wllh da bata aure shi ba, a tunaninta zai yi mata duk abun da take so ta yi rayuwar aure mai daɗi, har da ce mashi tana da masu son aurenta da in ta auri wani cikin su ta san zata yi rayuwa mai dadi fiye da ta gidan shi, hankalin Ibrahim ya yi matuƙar ƙololuwar tashi jin kalamanta a lokacin, ba irin lallashinta da bai yi ba yana nuna mata in dai zata yi mashi adalci shima mai ta nema a gidan shi ta rasa, duk wani abu da take son ci shi ko sha tana samu, haka bata yin komai musammaman aka samo mata mai aiki, sannan duk ta buƙaci kuɗi yana bata, kawai wannan da ta buƙata ne sun yi yawa bashi da su a lokacin, amman ta yi haƙuri da ya fara aiki duk wata buƙatar ta ta kuɗi zai rinƙa yi mata, ya ce shi siyasa ma yake shirin fara yi don haka ma ya yanke yin master's degree ɗin shi akan political science.


  "Amman ai kuna da kadarori, ba ka faɗa mani har gonaki kana da su naka ba da ake maku noma, a sanina noma ana samun kuɗaɗe sosai to su ina suke da bazaka rinƙa yi mana amfani da su ba?" Ta tambaya fuska a ɗaure ta wani ƙanƙance idanu kanta ko kallabi babu sai baƙar sumarta tum, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ba ƙarya na faɗa maki ba, sai dai su waɗannan kuɗaɗen dama ba su shigowa hannuna suna wurin dad da su ne yake mana hidindimun da suka shafe ni..." Tun kan ya ƙarasa ta katse shi. 


"Wannan ai rashin ƴanci ne, kuɗi dai naka ne kuma yanzu ai ka mallaki hankalin kan ka tun da har kana da iyali, sai a damƙa maka hakkin ka ka rinƙa yin hidindimun ka, don haka sai ka kira dad ɗin ka nuna mashi kana buƙatan kuɗi sai ka bani." Shiru ya yi idon shi akan ta yayin da yake a tsaye ita kuma tana zaune a bakin gado ta juya mashi kai, cikinta har ya fito jikinta ya ƙara yin kyau sosai fatar nan kamar ka ta6a jini ya zubo, duk fa abun da ya ja wannan taƙaddamar kawai don ya zo yana neman ta bashi hakkinsa ne wanda tun da ta samu ciki sai ta gadama take bashi daman hakan, ya san indai ba yi mata yadda take so ya yi ba shima ba zai samu abun da yake so ba, tunanin yadda zai tunkari mahaifin shi da buƙatar kudi har miliyan ɗaya yake yi, yasan koda zai bashi to sai ya ji mi zai yi da su, jiki a mace ya nufi hanyar barin bedroom ɗin ta juyo ta bi shi da kallo fuska a ɗaure, ƙwafa ta yi bayan ya fita a fili ta ce wllh in dai ana son zaman lafiya to dole a yi mata abun da take so, kuma duk fa abun nan ba kowa ne ya haddasa shi face Amminsu, dama tun bayan auren take sata ta tura mata kuɗi daga dubu ɗari, ɗari da hamsin, dubu ɗari biyu, kuma duk yana bata, wannan karon sai ta ce wai ta sa ya bata miliyan ɗaya saboda tafiya zata yi buƙatu na iya haye masu. 


A falo ya zaune yay zugudum bawan Allah, haƙiƙa har ya fara gajiya da halayen Jameela, saidai kuma son da yake mata ya sa baya iya yin wani katabus kan hakan, ya ɗauki tsawon lokaci yana wasi-wasin kan shawarar da ya yanke ta kiran dad din su, cike da fargaba ya ɗauki waya ya kira shi, bayan sun gaisa ya yi shiru, dad ɗin ya fahimci da maganar da yake son yi ya kasa ya tambaye shi lafiya, da ƙyar ya ce mashi dama kuɗi yake so miliyan ɗaya, ɗan jimn dad ɗin ya yi kafin ya tambaye shi mi zai yi da kudi haka, cikin in ina ya ce mashi dama yana son zai ba wife ɗin shi wasu in sun je bankwana ta ba iyayenta sai kuma akwai uzururrukan da zai yi da sauran, bayan ya gama yi mashi bayani dad ɗin ya ce zai yi mashi magana suka yi sallama, suna gama yin wayar ya kira matar shi hajiya dama tsakaninsu ba su 6oye ma juna komai, ya sanar mata game da buƙatar Ibraheem ya ce mata in tana ganin lafiya lou ta tura mashi kuɗin, cike da 6acin rai ta ce mashi ya ƙyale shi ba za a bashi kudi ba haka, daga yanayin yadda ya yi magana ya fahimci da wani abu, ya tambaye ta mike faruwa, ta ce mashi Ibrahim so yake ya zama shashasha wanda mace zata rinƙa juyawa, ta  tabbatar matar ce ta buƙaci waɗannan kuɗaɗen, in ba haka ba har wani uzuri ne gare shi na kuɗi da ba zai iya yi da kuɗaɗen hannun shi ba, nan ta shiga faɗa mashi irin abubuwan dake faruwa har da buƙatar da ta kawo na a taho da ƙanwarta, ɗan murmushin dattako ambasada ya yi don ya daɗe da sanin kowace uwa bata son ta ga mace na juya mata ɗa, kwantar mata da hankali ya yi ya ce shi yana ganin a bashi kuɗin kawai tun da dama na shi ne, yama yanke shawarar zai mallaka mashi dukkan dukiyar shi ta ci gaba da kasancewa a wurin shi tun da ya mallaki hankali har ya aje iyali, hajiya bata nuna amincewa akan hakan ba ta ce mashi maganar ya mallaki hankali da saura tun da ya bari mace na juya shi, yana murmushi ya ce mata so ne ya ja mashi hakan ta rabu da shi a hankali zai dawo cikin hayyacin shi. Ƙarshe Jameela ta yi nasarar karbar kudin. 


Bayan sati guda suka tafi ƙasar Australia, farin ciki a wurin Jameela kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta a ƙasar waje, sosai ake kula da ita bayan ta fara zuwa asibiti, sai dai duk yadda take murna da zuwan ta ƙasar saida murnar ta so komawa ciki saboda yadda take muzanta sakamakon rashin iya turanci, kowa ya ganta bai yin tunanin bata iya turanci ba haka zatai ta faman raba idanu idan ana yi mata saboda bata iya komai ba in ba irin su 'Yes, come, thank you..' da sauran irin ƴan guntayen kalmomi, dole koda yaushe tana tare da Ibrahim saboda haka, ko a gida in suka yi baƙi haka zata yi wuriri sai dai hajiya ce ke zame mata tafinta in ana mata magana, hakan yasa duk ta bi ta raina kanta. Ba a ɗau lokaci ba ta roƙi Ibrahim kan ya rinƙa koya mata turanci, da yake tana tsananin son ta iya ta hakan ne shima yake samun yadda yake so a tare da ita ba tare da ta ja mashi rai ba, cikin daɗin rai ya fara koya mata, amman daga baya abun ya fara gundurar sa saboda yadda kan nata baya saurin ɗauka, daga baya kawai sai ya samo mata baturiyar malama da take zuwa tana koya mata, ita kanta malamar ba a ɗau lokaci ba ta fahimci kan Jameela baya saurin ɗaukar karatu, haka dai tai ta ƙoƙari tana koya mata tun da biyanta ake. 


Bayan cikinta ya kai wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta san6alo santalelen jaririnta kamar ɗan aljanu tsabar kyau, hatta turawa haka sukai ta yabon kyawun yaron, bangaren uwar yaron wato Jameela kuwa ba a magana sam fuskarta ta kasa boye farin ciki da zumuɗin babyn, ba kamar da farko ba da bata so samun cikin ba, ita kanta kakar shi wato Hajiya ba ƙaramin farinciki ta shiga ba da ganin kyakkyawan jikan nata tamkar ɗan balarabe, a Nigeria ma duk wanda ya ga hoton babyn sai ya yaba da irin kyawun shi sai murna dangi suke. Bayan yin haihuwar da kwana ukku Sa'ad suka iso ƙasar daga kasar France da a lokacin can yake aiki tare da matarsa Amina da kuma yaron su Fahad wanda a lokacin yake da shekaru ukku da ƴan watanni, shima Fahad tubarkalla kyakkyawa da shi don ya ɗauko haske da kyawun mahaifiyarsa duk da akwai kamanin Sa'ad a tare da shi, kuma shima mahaifin na shi yana da kyau ba laifi, tun da Fahad ya ɗaura idanun shi akan babyn ya fara son shi ya maƙale mashi, koda wani lokaci yana a wurin baby da an yi yunƙurin ɗaukar shi zai kama kuka sai da ƙyar ake raba shi da babyn ko idan ya yi bacci. Bayan sati ɗaya da yin haihuwar gaba ɗaya suka taho Nigeria, nan yan'uwa da abokan arziki suka shiga zuwa barka, da sati ya zagayo aka yi taron suna inda yaro ya ci sunan kakan shi wato Nuraddeen   (Deen) A lokacin Jameela ta ji haushin ƙin bin ra'ayin ta da ba a yi ba na a saka sunan mahaifinta ko kakanta, dad ɗin Deen ya bata haƙuri kan in suka ƙara haihuwar namiji sai a saka mashi, ƴan'uwanta na Kano duk sun zo har da Ammin su, suna na gani na faɗa aka yi inda saboda jin daɗin saka sunan Ambasada da aka yi ya bada ƙaton shanu aka yanka ma baby, ba ƙaramar zalama dangin Jameela suka nuna ba a wurin sunan inda duk suka kwashe naman suka ba su Hajiya ɗan kaɗan, kowa kuma ya fahimci abun da suka aikata har da shi kan shi dad ɗin Deen, amman ba wanda ya tanka masu don sun fi ƙarfin hakan, bayan gama suna haka suka ƙi tafiya har da Ammin ta su sai bayan kwana biyar sannan suka tafi, Amminsu duk ta tattare kayan suna da Jameela ta samu abun takaici har da kayan baby da aka kakkawo mashi don zalama su basu kawo ba amman sun kwasa. 


A  lokacin an bar ma Jameela ƙanwarta Naila ta zauna mata duk da akwai dattijuwa da hajiya ta sa aka kawo mata tana kula da ita, lokacin Naila bata wuce shekaru tara ba amman bata jin magana tsagera ce ta gaske sam bata da kunya, ƙiri-ƙiri idan ƴan'uwan hajiya suka zo barka sai su hana su ganin jaririn koda yana a hannun wani tsakanin Jameela da Naila basu ba da shi a gan shi, akwai watarana da wasu ƴan'uwan hajiya suka zo daga ƙauye hajiya ta saka ƴar aikinta Asabe ta rako su part din su Ibrahim don su yi barka, a wulaƙance Jameela ta tarbe su, a lokacin ba don ganin idon ƴar aikin hajiya ba da ba abun da zai sa ta bari su zauna mata akan kujera, yadda take bin su da ƙasƙantaccen kallo tana yamutsa fuska sai ka ce ta ga kashi, dama lokacin tubarkalla jikinta ya ƙara cikowa ta yi dumurmur, suka gaisa ta amsa masu a daƙile, bayan ɗan lokaci ɗaya daga cikin matan ta kalli Naila dake zaune riƙe da Deen ko kallon su dama bata yi ba tun da suka shigo idonta na akan tv, dama ba iya gaida mutane ta yi ba, da yar fara'a matar ta ce mata ta kawo masu jaririn su gani ta yi kamar bata ji ta ba, sai da Asabe mai aiki ta sake maimaitawa ta ce bata ji ana mata magana, sannan ta juyo ta yi masu kallon hadarin kaji bata da niyyar tasowa ta kawo shi, ganin haka yasa Asabe ta nufe ta da niyyar kar6o masu shi, aikuwa Jameela ta yi saurin dakatar da ita cikin haɗe rai ta ce ita ta hana ta rinƙa ba mutane shi saboda idan baƙi suka ɗauke shi sai ya yi ta kuka har kan shi yay ciwo, gaba ɗaya sai da suka ɗan buɗe ido mamakin jin furucinta, 


Haka suka taso jiki a mace suka baro part ɗin, bayan dawowar su 6angaren hajiya, ɗaya cikin su ta kasa haƙuri ta gaya ma hajiya irin wulaƙancin da aka yi masu, ran hajiya ya 6aci sosai nan Asabe ta ƙara faɗa mata cewa ba wannan ne karo na farko ba don ko ranar da wasu danginsu suka zo ta saka ta raka su suma haka ta yi masu, bayan sun baro part ɗin su baƙin ne suka roƙe ta kan kada ta sanar ma hajiyan, Asabe na rufe baki hajiya ta miƙe, wata a cikin baƙin ta fara mata magiya kan ta rabu da ita kawai yayin da wadda ta faɗi ma hajiyar abun da aka yi masu cikin 6acin rai ta ce ta ƙyale ta, gara ta je ta ja mata kunne in ma zata rinka wulaƙanta mutane to ban da su da suke dangin su.


Jameela na ganin yanayin fuskar hajiya bayan ta isa falon ta sha jinin jikinta, tsaye ta yi a tsakiyar falon ba tare da ta zauna ba, Asabe da suka taho tare na daga gefen ta a baya, cikin yanayi na bacin rai tana kallon Jameela ta ce mata don me take hana mutane su ga Deeni kuma ma har da waɗanda suke dangin shi! Nan ta shiga ƴan kame-kame tana kifce-kifcen idanu ta ce  tun kwanaki da wasu suka zo aka basu shi bayan sun tafi ya yi ta kuka har jijiyoyin kan shi suka fito, da ta rasa mike damun sa sai ta kira Ammin su ta sanar mata, shine Ammin ta tambayi wani malami dake a layin su ya ce a daina ba ko wane mutane shi don mayya ce ta so kama shi, baki a kwa6e hajiya ke kallon ta har ta gama, sam bata ma yarda da zancen nata ba, daga yanayin fuskarta da yadda take yin maganar zaka fahimci karya take faɗi, bayan ta gama bayanin cikin ɗaure fuska hajiya ta ce mata to su kaf dangin su babu mai maita, kuma ba wannan bace haihuwar da kaɗai aka ta6a yi a familyn su da za a ce maitar bata ta6a shafar wani ba sai shi, don haka daga yanzu kada ta sake jin wai ta hana wani yaro koda bacci yake indai aka zo ganin shi to a ɗauko shi a ba mutane, in ba haka ba ranta zai 6aci,


   

 "Asabe je ki kar6o shi!" Cike da bada umarni ta ce ma Asabe, nufar Naila ta yi ta je ta amso babyn, juyawa hajiya ta yi tana faɗin Ibarahim ɗin zai dawo zata ji in har da shi ya bada goyon baya ake ma dangin shi hakan, Jameela da Naila suka bi su da kallon harara har suka fuce. Bayan wata ɗaya da yin haihuwar Maleek ya zo daga ƙasar India da a lokacin a can yake aiki da wani kamfani da ya danganci fasaha, kuma sannan yana ci gaba da yin karatun degree ɗin shi na biyu wato master's degree. A gidan su na Kano ya sauka, a ranar da daddare ya shirya zuwa wurin Sapna wanda shine karo na farko da zai fara zuwa gidan su tun bayan da suka shaƙu da juna, har abun ya juye ya koma soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, sai dai ba wanda ya sani sun bar abun a tsakanin su, Sapna ta yi farin cikin jin zuwan shi lokacin da ya kira ta ya sanar mata, duk da ta wani 6angaren tana ɗan jin fargaba saboda bata san yadda zata tarbe shi ba, a wata haɗaɗɗan ash din mota ya isa gidan su bayan la'asar, jikin shi sanye da jeans da t-shirt, kiranta ya yi ya sanar da ita ya iso, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana sanye da brown ɗin doguwar riga ta ɗaura ƴar ƙaramar baƙar hijab mai tattara a ƙasa, ta yi kyau sosai cikin shigar haskenta ya fito fayau, yana ganin ta ya sauke glass ɗin motar ya zuba mata ido yayin da take nufo motar tana tafiya a nutse, tun da suka haɗa ido ta sadda kanta ƙasa tana murmushi, yana daga abun da yake ƙara mashi son ta yadda take da kunya ga kamun kai, daga gefen ƙofar da yake ta tsaya tana kallon shi, haka shima idanunsa na a cikin nata suka shiga sakar ma juna murmushi, sam ta kasa yi mashi magana don tun da abun su ya juye zuwa soyayya basu ga juna ba,


    "Ko dai ba a murnar gani na?" Ya faɗa da muryarsa mai cike da natsuwa, ɗan girgiza mashi kai ta yi still tana ta murmushi, ɗage gira ya yi ya ce gashi nan ta ƙi yi mashi magana idan ta ji daɗin ganinsa ai baza ta ƙi yin magana ba,


   "To ai saboda murnan ne na kasa magana." Ta faɗa da ƴar zazzaƙar muryar ta, har saida ya ɗan lumshe ido yana murmushi, ce mata ya yi ta shigo cikin motan, ta yi ɗan jim tare da ɗan wawwaigawa ganin ba mutanen dake kallon ta ya sa ta zagaya ta shiga, wani ni'imtaccen sanyi haɗi da kamshi mai daɗi suka ratsa ta, gaishe da shi ta yi tare da yi mashi an zo lafiya ya amsa yana kallonta cike da so da kauna, shima ya tambayi yadda take tare da ƴan'gidansu ta amsa da duk suna lafiya, hira suka shiga yi irin ta masoya duk da ita bata cika yin magana sosai ba sai dai murmushi kawai, har yake tambayarta ya babyn su na wurin sister ɗinta ta amsa da duk suna lafiya, ya ce bai samu zuwa ya ganshi ba lokacin da aka yi haihuwar yana yin exams ne, kai ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba, ce mashi ta yi bari ta kawo mashi ruwa ya yi saurin dakatar da ita ya ce akwai ruwa a motan, ta ce to bari ta kawo mashi lemu, shima ya ce mata ta barshi, da ɗan yanayin shagwa6a ta ce ke nan yana nufin ba zai sha komai ba, murmushi ya yi ya fahimci ta iya shagwa6a duk da kunya na hanata yi sosai, tambayar ta ya yi ita ta haɗa lemun,


  "A'a na shago ne, ban san da yau zaka zo ba dana haɗa maka, kuma lokacin da ka kira ni ka ce zaka zo nan ba time sosai." Ta faɗa tana yi tana sauke idanunta,


  "Siyo mani kikai ke nan?" Kai ta ɗaga mashi, 


"Ok, tun da saboda ni aka siyo idan zan tafi sai a ɗauko mani." Kai ta jinjina mashi suka ɗan yi shiru,


  "Ya maganar karatun ki, yaushe ne zaki fara tun da kin samu points mai kyau?" 


Ta ce,"Yanzu ina jiran lokacin da zamu yi post utme ne." Kai ya jinjina suka ɗan ƙara yin shiru, 


 "Ai ina tunanin ci gaba da karatun ma anan babu shi..." Da sauri ta kalle shi, ya ci gaba, "I think ya kamata mu yi aure, da yadda na tsara sai na gama karatuna sannan, amman i have changed my  mind." Da sauri ta sadda kanta ƙasa jin maganar aure da ya yi, ƴar dariya ya yi, "Ko baki shirya mu yi aure ba yanzu?" Tana a yadda take ta girgiza mashi kai, ce mata ya yi ta ɗago sosai su yi magana wannan serious abu ne, ɗagowa ta yi tana kallon shi ya tambayi miye ra'ayin ta kan hakan, 



 "Duk yadda ya yi maka nima ya yi mani, amman tun da ka ce kafi son sai ka gama karatunka ko ka bari idan Allah Ya kaimu ka gama ɗin." 


 Iska ya ɗan furzar tare da shafa lallausar sumar kan shi ya ce, "Ai My Sapnah na ga nema kike ki hana ni maida hankali akan karatun, tunanin ki yana yi mani yawa gashi karatun mu baya son wasa, that's why I just decided in mallake ki ki kasance a tare da ni ko na tsayar da hankalina wuri ɗaya, idan muka yi auren a can sai ki ci gaba da karatun kawai."  Wani irin daɗi ne ya lullube ta ta shiga yin murmushi dake bayyana hakan, tambayar ta ya yi ta amince su yi auren ta ce mashi eh, a nan suka gama magana ya ce zai sanar da mahaifin shi a zo nema mashi aurenta tun da yana a gari ko mi ake ciki zai mata magana, da zai tafi ya bata tsarabar da ya yo mata. Cike da farin ciki Sapna ta ƙarasa yinin ranar duk da a cikin zuciyar ta tana zullumin kada a ƙi amincewa da maganar auren nasu.



Bayan ya samu dad ɗinsa da maganar ya ce mashi ya jira zai neme shi, mahaifin su Ibraheem dad ɗin Maleek ya kira ya shaida mashi game da auren da Maleek ɗin ke son a nema mashi na yar'uwar matar Ibrahim, ya tambaye shi shawara game da hakan, a nan ambasada ya ce mashi ya bari za su yi magana da hajiya don ita tafi shi sanin abun da ya dangance su, hajiya ta yi mamakin jin Maleek yana son auren ƙanwar Jameela, saidai ita kanta ta fahimci Sapna ta sha bambam da sauran ƴan gidansu tun daga bikin Ibrahim ta gane hakan, ko lokacin da suka zo bayan ta haihu ita kaɗai ce ke zuwa ta gaishe ta safe da yamma har aiki take yi mata, koda ta ce ta bari sai ta yi kamar gyara mata falo da taya Asabe aiki, har Ibraheem ta kira ta tambaye shi game da halayen Sapna ya tabbatar mata da ta fi kowa kyawun hali a gidansu Jameela, anan yake ji a bakin hajiya cewa Maleek ne ke son auren ta, aikuwa ya yi mamaki sosai don shi kawai ya san dai suna mutunci da juna amman bai san abun ya juye zuwa soyayya ba. 


A bakin shi Jameela ta ji zancen, aikuwa cikin rawar jiki ta kira Ammin su da maganar ta nuna ita bata san ma da Sapnah ɗin na soyayya da shi ba, cike da zumuɗi Jameela ta ce mata ta tashi tsaye duk yadda za ai kada ta bari a samu matsalar da zata sa a fasa auren nan, in ba haka ba za su yi babbar asara don iyayen Maleek sun fi na Ibrahim kuɗi kuma shi kan shi Maleek din a yanzu yana da kuɗi sosai, kuma idan aka yi auren India zai tafi da Sapna ɗin, nan fa jikin Ammin ya kama rawa har tana faɗin wllh da a ce Naila ta girma da sai ta sa an juye al'amarin ya koma kanta don bata tunanin za su rinƙa samun wani abun arziƙi idan aka yi auren da Sapna tun da ita sakarya ce bata son su da arziƙi, anan Jameela ta shiga bata shawarar ta ja Sapna ɗin a jiki ta yi ƙoƙarin canza mata hali, idan bata canza ba bayan an yi auren kawai ta saka bokanta ya yi aikin da za a canza mata ra'ayi ta rinƙa yin abun da ake so, sosai Ammi ta ji daɗin shawarar ta ce haka kuwa za a yi.  Bayan sun gama yin wayar haka ta rufe Sapnah da faɗan wai don me bazata sanar masu ba a yi mata shiri sosai yadda abun zai tabbata ba tare da wata matsala ba kamar yadda aka yi na Jameela, Sapna ta san abun da take nufi da a yi mata shiri don tasan tana biye biyen bokaye kuma ta tsani hakan, nan fa Ammin tasu ta shiga rawar jiki haka ma babansu bayan ta sanar mashi, har da cin alwashin zuwa wurin bokanta washe gari tana faɗin ba abun da zai sa a fasa auren, Sapna har nuna mata ta yi ita dai bata son ta saka a yi ma Maleek wani abu idan Allah Ya ƙaddara shi ɗin mijinta ne ba abun da zai hana ta aure shi, Ammin ta hau surfa mata masifa tana faɗin bata da wayau, yanzu waya faɗi mata abu irin wannan ana tsayawa wai a zura ido kowa tashi yake tsaye ya nemi taimako da sa'a, har da bata misali da ba ga ƴan mata nan ba da iyayen su suka lanƙwashe hannu basu nema masu taimako duk sun yi kwantai ba mazajen auren ba, ita dai Sapna duk da hakan ta nuna bata son ta je wani neman taimako. 



A daren ranar hajiya ta sanar ma ambasada game da bincikin da ta yi da kuma abun da ta sani na halayen Sapna, shi kuma ya kira Alhaji Usman ya shaida mashi. Cikin dare Sapnah ta tashi ta yi nafilfili ta roƙi Allah kada ya ba Amminsu sa'a a duk abun da zata sa a yi, tana ƙwalla ta roƙi Allah Ya bata Maleek a matsayin miji idan tana da rabo. Ikon Allah, washe gari Ammin ta tashi bata jin daɗi, duk yadda ta so ta fita ta kasa ba don ta so ba ta bari sai ta samu sauƙi. Bayan dad ɗin Maleek ya ƙara sakawa an yi mashi bincike anan Kanon aka tabbatar masu da cewa Sapna tana da halayen kirki ta fita daban a yaran unguwar ma baki ɗaya, mahaifiyar Maleek ce ta so ta ƙi goyon bayan abun saboda wata ɗiyar ƙawarta take son ya aura, dad ɗinshi ya ce mata tun da ya nuna Sapna yake so kuma an yi bincike bata da wani hali mara kyau kawai su ƙyale shi ya aure ta, ya ce mata ta san yaran zamani in aka ce za a hana su abun da suke so ko aka ce za ai masu dole kan abun da basu so abu mara daɗi na iya faruwa, har ya bata misali da lokacin da aka hana Ibrahim auran yayarta abun da ya biyo baya. Bayan dad ɗin ya sanar da Maleek cewa ya faɗa ma yarinyar iyayensa za su zo su gana da nata iyayen, a daren ranar ya kira Sapna waya ya sanar mata, baiwar Allah tamkar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda farin ciki har sujjadar godiya ga Allah ta yi, suma iyayenta sun yi farin ciki kamar me, duk da haka Ammin tasu bata haƙura da zuwa wurin bokan da ta yi niyya ba. Ana zuwa neman aure aka saka rana gaba ɗaya wata ukku masu zuwa.


Bayan Jameela ta yi arba'in har ta je Kano ta dawo ta yi ma Ibrahim zancen komawar su ƙasar waje don ta ci gaba da karatun ta, a nan yake sanar da ita baza su koma ba gaba ɗaya anan za su ci gaba da karatun shima zai yi master's degree ɗin shi kan political science don yana son fara yin siyasa, tubure mashi ta yi kan ita bata yarda ba gaskiya a can take son yin karatunta, ta ce idan ma shi anan zai yi to sai shi ya tsaya ita ta tafi, lalla6a ta ya shiga yi yana nuna mata manufar shi na su tsaya anan din ba don komai ba sai don su saba da mutane sosai yadda ba zai samu matsala a ƙi za6ar shi saboda ba zaune yake ba anan idan ya fito takara, ya nuna kuma dole sai itama ta tallafa mashi kan hakan 6angaren da ya shafi mata, ta ɗan ji tana goyon bayan shiga siyasar da yake son yi, sai dai ta wani 6angaren tana jin kishin yayan shi Sa'ad da matarshi dake a ƙasar waje ga kuma Sapna ma da an ɗaura auren su za su bar ƙasar, kasa 6oye abun da ke ranta ta yi ta ce mashi amman ita hakan ci baya ne a wurinta ga Amina can har ta yi degree ɗinta a ƙasar waje haka ma Sapna za ta je ta ci gaba da karatunta sai ita za a dankwafe ta anan ta ci gaba da karatu, nuna mata ya yi hakan duka na ɗan lokaci ne ai da zarar ya fito takara ya ci sai ƙasar da take so zata je, har ya bata misali da ai tana ganin yadda matan ƴan siyasa masu muƙamai suke fantamawa yadda ransu ke so, tana jin hakan ta ce mashi shike nan ta amince amman ta ya zata ci gaba da karatu a wannan ƙauyen garin, ya ce mata ta kwantar da hankalinta ya tsara masu komai, dad ɗinshi na da wani babban gidan gona a Zaria kuma akwai gida mai kyau a ciki can za su koma sai su ci gaba da karatun a ABU Zaria, cike da nuna gamsuwa ta ce mashi ta amince kuma zata taimaka mashi sosai a harkar siyasar shi amman sai ya yi mata alƙawarin idan ya fito takara ya samu duk abun da take so zai yi mata, yana murmushi ya ce mata ya yi mata alƙawarin hakan. 



A kwana a tashi bayan watanni ukku aka yi bikin Sapna da Maleek ana gamawa suka wuce India, kamar yadda Ibrahim ya tsara masu haka aka yi suka koma Zaria a can suka ci gaba da karatu ya yin da ya shiga shirye-shiryen fara shiga siyasa. Bangaren iyayen Fahad duk bayan lokaci suna zuwa Funtua wani lokacin ma anan yake barin su shi ya koma daga baya sai su bi shi. A kwana a tashi bayan shekaru biyu da wasu watanni dad din Deen ya kammala karatun shi ya tsunduma harkar siyasa yayin da Jameela ke cikin yin karatun degree dinta, cikin sa'a ta ubangiji a karon farko da Ibrahim ya fito takarar kujerar majalissar jaha sai gashi ya ci, don ya samu farin jini a wurin mutane duk da nasarar ta shi na da nasaba da mahaifinshi wanda yake mutum ne mai kyautata ma mutane sosai, zo ka ga murna a wurin Jameela ganin haƙarta ta fara cimma ruwa an zama matar ɗan majalisa, haka ƴan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa taya murna, bayan rantsar da su suka kama aiki, a lokacin dole ya raba ƙafa bai a Katsina bai a Funtua haka Zaria da har lokacin Jameela ke a cikin yin karatu. Abu na farko da ta fara buƙatar ya siya mata ita ce danƙareriyar mota, ba tare da ya gardama mata ba ya siya mata saboda ya san ta taka rawa sosai wurin ganin ya ci za6en, nan fa Jameela a ka fara fankama ba kama hannun yaro, bayan wani lokaci ta buƙaci ya siya ma iyayenta gida shima bai ƙi ba ya siya masu gida mai kyau a can Kano, a hankali ta fara saka shiririta a karatun ta duk da ta yi nisa ta fara mashi ƙorafin ya za ai tana matar ɗan majalissa ana ganin tana karatu hakan ma sai ya ja mata raini, ƙiri ƙiri ta aje karatun ta matsa sai dai ta koma ƙasar waje ta yi, hakan kuma aka yi sai dai ya rinƙa zuwa ko kuma in ta samu hutu su zo.


Suna gab da kammala tenure ɗin su ta farko Jameela ta gama karatunta ta dawo Nigeria, saidai ko da ta dawo matsa mashi ta yi kan sai ya siya masu gida a Abuja duk da a yadda ya so su koma Katsina da zama amman fir ta ƙi dole sai dai Abujar ya siya masu gida suka koma, son kai irin na Jameela a gabanta in dai ta ga zai yi ma dangin shi alkhairi sai ta yi ƙoƙarin hanawa, ta rinƙa ƙorafin shike nan don ya samu muƙami kowa ya dauƙo buƙatar shi sai ya kawo mashi ai koda aka za6e shi don ya yi ma al'umma aiki ne ba wai kowa ya zo da bukatarsa ba, amman kuma ita kullum cikin kawo mashi baƙatun da suka shafi danginta take. 


Bayan shekaru huɗu tenure ɗin su ta ƙare aka sake yin za6e, jam'iyarsu ta sake samun nasarar cin zaben hakan yasa duk suka samu yin tazarce, a lokacin Deen na cikin shekara ta bakwai, sosai suke son junansu shi da Fahad in suka haɗu kamar kar su rabu, a lokacin Fahad na cikin shekara ta goma, a wani zuwa da su Deen suka yi Funtua lokacin suma su Fahad suna a Funtua, gaba ɗaya Fahad ya dawo gidan hajiya anan wurinta suke wuni tare da Deen don tun a lokacin Fahad yake fuskantar tsangwama daga wurin Jameela shiyasa yake zama wurin hajiya, lokacin da su Deen za su koma Abuja haka yaron ya dingi kuka yana cewa a tafi da Fahad shima, da ƙyar aka raba su da yake shi Fahad ya ɗan girma sai dai ya yi ta zubar da ƙwalla. Ganin irin shaƙuwar da suka yi ne ya sa Hajiya ta yi ma Ibrahim magana kan ya ɗauki Fahad hakan zai saka su taso da zumunci mai ƙarfi, koda Jameela ta ji zancen da buɗar bakinta sai cewa ta yi a bari mana idan iyayenshi sun mutu sai a ce su ɗauke shi, amman yanzu ga iyayensa a raye miye na wani cewa ya dawo wurin su in ba son ɗaura masu ɗawainiya ba yaro ai sai iyayen shi, shi dai dad a lokacin nuna mata ya yi ba zai iya musanta ma maganar hajiya ba saboda haka ta yi haƙuri, wannan ne sanadiyar komawar Fahad gidan su Deen har suka ci gaba da yin karatu a makaranta ɗaya.


A 6angaren Sapnah tuni ta kammala karatunta na medicine a india, daga baya kuma Maleek ya koma ƙasar America ya ci gaba da yin aiki da wani babban kamfanin fasaha. Sapna ba ƙaramin gata take samu a wurin Maleek ba, gaba ɗaya ta canza kana ganinta kasan hutu ya zauna mata idan ma aka ce maka a Nigeria aka haifeta anan ta taso har ta girma sai ka ƙaryata, sai dai har lokacin basu samu rabo ba ko batan wata bata ta6a yi ba, tun suna a India aka binciki lafiyar su gaba ɗaya inda aka tabbatar matsalar daga wurin Sapnah take, ba ƙaramar damuwa ta shiga ba amman shi Maleek sam bai nuna damuwar shi ba duk da yana son ya ga ya samu rabo, shine yake rarrashin ta yana nuna mata ko da a ce bazata ta6a haihuwa ba yana son ta a haka kuma za su ci gaba da rayuwa ba tare da wata matsala ba har ƙarshen rayuwar su, 6angaren danginta lokacin da suka ji zancen matsalar rashin haihuwar tata sun shiga damuwa sosai musamman Ammin su da kuma Jameela, Ammin har tambayarta ta rinƙa yi sun tabbatar an yi binciken sosai kuwa? Sapna ta tabbatar mata da ƙwararru ne suka yi binciken, sosai Ammin tasu ta shiga baƙin ciki don ba abun da ke a ranta face yanzu shike nan idan bata haihu ba Maleek na iya ƙara aure matar ta zo ta hayayyafa idan ya mutu su cinye gado, wannan dalilin ne ya saka ta damuwa sosai ta shiga bin bokaye ido rufe kan a yi mata aikin da Sapna zata samu ciki ta haihu, saidai kuma shiru Allah bai sa ta samu cikin ba.




Bayan wasu shekaru, abubuwa da dama sun faru, ciki har da yin ritaya da ambasada ya yi suka dawo gida Nigeria da zama a lokacin shima mahaifin Fahad an maido shi aiki Nigeria. Cikin iko na Allah bayan shekaru goma da auren Sapna da Maleek Allah ya azurta su da samun rabo inda ta haiho ya mace wato Basma. Bayan yin ritaya ɗin ambasada da shekara ɗaya shugaban ƙasa na lokacin ya sake bashi muƙamin ambasadan Nigeria a ƙasar Spain, yana riƙe da muƙamin ne bayan wasu shekaru ya kwanta ciwon da ya zamo ajalin shi ya rasu, ba ƙaramin alhini ahalin shi dama al'ummar garin Funtua suka shiga ba na rashin dattijon arziƙi. Rayuwa ta ci gaba da gudana yayin da arziƙin iyayen su Fahad ya ninninku, mahaifin su Deen ya ci gaba da gudanar da harkokin shi na siyasa inda daga baya ya sake tsayawa takarar kujerar ɗan majalissar tarayya ya yi nasara.




CIGABAN LABARI......

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post