A Cikin Rayuwa page 11&12 by Zee Laluh | Abokiyar Hira


 _Bossladieswriters_




_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don samun abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLJJlLKWEKhK3TRyp0q


WhatsApp Group


https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt




*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*



    

    _By Zainab Bature_



   

   _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._






Page 11&12



WAIWAYE




Lokacin da Hajiya Binta ta  auri mijinta marigayi Amb. Nuraddeen, duka bata wuce shekaru goma sha huɗu ba, lokacin iya karatun ƙaramar sakandire ta yi, sai bayan shekaru da yin auren su lokacin suna zaune ƙasar waje ta samu ci gaba da karatun ta in da har ta kai matakin digiri na biyu a fannin kasuwanci, hakan yasa ta kasance babbar ƴar kasuwa ce dake yin kasuwancinta tsakanin ƙasashe daban-daban, ta kasance tana siyar da furniture na ƙasashe daban- daban da kayan sakawa da su akwatuna, jakunkuna, takalma, tana da plaza fin ɗaya dake da manyan shaguna na kaya da ake kula mata da su anan Funtua da kuma Zaria, haka kuma tana da motoci da ake haya manya da ƙananu da kuma keke napep da mashina, sannan kuma itama tana gonaki da ake mata noma sosai. Koda yanzu Hajiyar Ambasada ta tsufa har yanzu kasuwancinta na saro kaya daga ƙasar waje na tafiya lafiya lau don ta kafu sosai, tana da connection mai ƙarfi da kamfunan da take sarar kaya na ƙasashen waje, kuma tana da amintattun mutane dake mata hidimar komai. Mahaifin su Fahad ne ɗanta na farko da ta haifa bayan shekaru ukku da yin aurenta, a yanzu yana cikin shekara ta hamsin da bakwai, sakamakon ya fara yin aiki da wuri hakan yasa ya yi retire kafin ya kai shekaru sittin. Lokacin da ya kammala karatun shi na degree mahaifin su babban ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje ne hakan ya sa aiki bai mashi wuyar samu ba. Sai mahaifin su Deen wanda a cikin shekarar da ake yake cika shekaru hamsin da biyu, gaba ɗaya karatun su ba anan ƙasar suka yi shi ba hakan yasa suke kammalawa da wuri. 


Bayan mahaifin su Fahad ya fara aiki bada jimawa ba yana da shekaru 27 aka   yi auren shi da Hajiya Amina, auren zumunci ne aka yi masu don ƴar'uwar su ce matsayin cousin ɗinsa take, tun kafin ya kammala karatun shi soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su a zuwan da suke yi, anan Funtua mahaifin shi ya gina mashi gida wanda shine har yanzu suke a ciki, bayan shekara ɗaya daidai da yin auren aka haifi Fahad. 


Daga baya lokacin da Alhaji Sa'ad ya yi kuɗi sosai ta hanyar aiki da sana'ar noman da suke yi ne ya ƙara faɗaɗa gidan da suke tare da ƙawata ginin daga flat ya koma babban ginin bene. Da yake irin aikin mahaifin shi ne ya yi hakan yasa suma sun ɗan zauna a wasu ƙasashen sai dai basu kai yawan ƙasashen da mahaifinsu ya yi aiki ba, kuma shi bai samu kaiwa matsayin Ambassador ba ya ajiye aiki amman ya kai daga cikin manyan matsayi a aikin.




A bangaren Jameela mahaifiyar su Deen, ta kasance ita ce babba a gidan su, sai mai bi mata wato Sapna, Bashir shine na ukku sai mai bi mashi Naila, akwai ƙanwar su ta biyar Aseeya sai ɗan autan su namiji Adam dama su shidda ne a gidan su.


 Su Jameela sun kasance ƴan Kano duk da asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane daga Nijar suke, ahalin su sun kasance nau'in mutanen da ake kira da sadakar yalla, wanda suke wani rukuni daga cikin mutanen da ake kira buzaye. asalin garin kakanninsu a Nijar ya kasance ɗan karamin gari a hamada, inda rayuwa take matuƙar wahala, sun shigo Najeriya cikin ayari da ya ƙunshi dangi da kuma wasu ƴan garin su don samun sauƙin rayuwa. A lokacin iya yayan mahaifin su Jameela mai suna Amadu kawai suka haifa, daga baya a nan Kano aka haifi mahaifinsu Jameela wato Abdullah, sai ƙanwarsa wadda ita ce kuma ta ƙarshe a ɗakin su babansu mai suna Maryam. Mahaifiyar su Jameela wato Haleema ta kasance yar'uwar babansu ce, matsayin ɗiyar ƙanin babanshi ce, kuma har da iyayen nata aka zo garin Kano. Itama Haleema a nan Kano aka haife ta kuma ita kaɗai iyayenta suka haifa, mahaifiyarta na da cikinta Allah ya yi ma mahaifinta rasuwa sanadin mota da ta buge shi, bayan watanni da haihuwarta itama mahaifiyar tata ta rasu, hakan yasa rainon ta ya dawo hannun mahaifiyar baban su Jameela. Farkon zuwan kakannin su Kano, sun kasance basu da taƙamaiman matsugunni, daga baya suka fara aikin gadi a wuraren da ake manyan gine-gine ana basu wurin zama. Amadu yayan babansu Jameela ya kasance jajirtacce mai ƙoƙarin neman na kai, tun yana ɗan matashi yake bin kasuwanni yana yin aikin yaron shago da dakon kaya, daga baya ya fara yin sana'oi irin su sayar da turare, ƴan kunne, zabba da sauran su, sa6anin mahaifin su Jameela da ya taso a malalaci saidai komai Amadu ya yi masa. Sosai Allah Ya buɗa ma Amadu har ya siya ma iyayensu ɗan madaidaicin gida gaba ɗaya suka koma, ya kuma saka mahaifin su Jameela a makaranta tare da ƙanwarsu  sai mahaifiyar su Jameela da iyayen su ke riƙo wadda kusan sa'ar Maryam ce. Daga baya Amadu ya auri wata bahaushiyar yarinya da suke soyayya yar nan Kano mai suna Hafsa, wadda da ƙyar iyayenta suka yarda ta aure shi saboda asalin sa. Ƙanwar su Maryam na aji ukku na sakandire wani alhaji ya fito neman aurenta aka bashi musamman ganin yana da kuɗi, a lokacin ne shima Abdullah ya bayyana ma iyayensu cewa yana son auren Haleema, farko ta nemi bijire ma auren shi saboda tana ganin Maryam ta samu babban mutumi mai kuɗi, shi kuma ta raina ma girmansa gashi bai da komai ya ƙi kuma tsayawa ya yi sana'a, duk in da ya fara aiki ba a ɗaukar lokaci ake sallamarsa saboda maular tsiya ga rashin gaskiya, ga kuma shaye-shaye da ya fara sakamakon biye ma abokan banza. Duk da Haleema ta nuna bata son auren Abdullah, haka iyayen shi suka tursasa mata har da su gorin rainon ta da suka yi, tana ji tana gani aka yi mata auren dole da shi, suka tare a ɗakinsa dake a gidan, ita kuwa Maryam gidan da aka kaita mai kyau har da gate. Farko Haleema ƙin amince ma Abdullah ta yi, sai da ta kai sai ya haɗa mata da bugu sannan abu ke shiga tsakanin su, da ta yi mashi laifi sai ya kai ƙarar ta wurin iyayensu a yi ta mata faɗa, a haka ta samu cikin Jameela ba wata kulawa da take samu ta buƙatun mai ciki daga wurin shi, sauƙin ta Amadu da ke taimaka mata, dama duk shine ke ɗaukar dawainiyar su, wanda a lokacin babbar mota yake ja yana kai kaya  da ɗaukowa daga kudu, ta 6angaren Maryam ma tana taimaka masu bakin gwargwado. Lokacin da cikin Haleema ya kai wata tara ta haifo santaleliyar ɗiyarta, tun a asibiti ake ta santin kyawun Jameela, haka ma mutanen unguwa musamman jin yadda ake zuzuta kyawun jaririyar wasu ke zuwa barka, tun da Allah Ya sa Haleema ta ɗaura ido kan kyakkyawar  jaririyar tata wata irin ƙaunar yarinyar ta shiga zuciyarta, wannan dalilin ne kuma ya sa ta yada duk wasu makaman ƙiyayyar da take ma Abdullah ta saki jiki suka ci gaba da rayuwa irin ta ma'aurata. Ba irin ƙoƙarin da Amadu bai yi ba wurin ganin ya ɗaura Abdullah hanyar da zai gyara rayuwarsa ya kama kwakkwarar sana'a ba kamar da ya fara aje iyali, sai ya yi kaman ya canza sai kuma ya koma gidan jiya.  Bayan wasu shekaru kakannin su Jameela duk suka rasu, lokacin Maryam sun bar Kano sun koma Lagos da zama kuma tana ci gaba da taimakon su musamman da kuɗi.


 

Akwai wani makwabcin su mai suna Alhaji Mahmud, ya kasance attajirin mai kuɗi ne da ke yin kasuwanci ƙasashe daban-daban, lokacin da su Jameela suna yara mahaifin su ya ta6a yin aikin gadi a gidan Alhaji Mahmud ɗin, wanda gidan katafaren gida ne na gaske, daga baya ne Alhajin ya sallami mahaifin su Jameela saboda ya gaji da halin shi na maula, duk da albashin shi da ya tsare mashi yake bashi akan lokaci sannan da wasu alkhairan da yake mashi kamar na kayan abinci haka in salla ta yi har kuɗi yake bashi don ya yi ma yaran shi kayan salla amman hakan bai isa ba, duk wata matsalar shi sai ya kawo ma alhajin, ko iyalan shi ne basu da lafiya alhajin ne zai biya kudin asibiti ko magani, ganin gaba daya ya maido mashi nauyin iyalinshi da kuma yadda su Jameela suka mayar mashi da gida tamkar na su, a nan suke wuni su ci abinci wani lokacin har kwana, sau da yawa sai ya yi ma matarshi hajiya Aisha magana kan ta sallame su su koma gidansu sannan wani lokacin suke tafiya, waɗannan dalilan ne suka sa Alhaji ya sallami babansu daga yi mashi aikin gadin ya nuna mashi a yadda yake da iyali kamata ya yi ya nemi wata hanya da zai rinƙa samun isassun kuɗin da zai rinƙa ɗaukar nauyin iyalan shi, har da jari ya bashi don ya fara yin sana'a, sam baban su Jameela bai so hakan ba  don ya saba da samun komai bati, ƙarshe dai ba wata sana'ar kirki da ya kama haka suka cinye kuɗin ya koma yin maulan da ya saba da kame-kamen sana'oi, aka ce zama da maɗaukin kanwa, itama matar tashi ta yi aikatau a wasu gidajen masu kuɗi, sai dai duk abu ɗaya ke sa bata daɗewa ake sallamarta, ita ban da maula da rashin gaskiya har da munafunci, ƙarshe ta koma yin sana'ar kitso, gidanta ya koma matattarar gulma da ɗaura mata kan gur6atacciyar hanya. Duk da mahaifin su Jameela ya bar aiki a gidan Alhaji Mahmud hakan bai sa sun daina zuwa ƙwaƙwa ba, ba kamar Jameela da take ƙawance da ɗiyar Alhajin wadda tsararta ce mai suna Safiyya suna kiranta da Soffy.



A haka su Jameela suka taso a wannan gidan, saidai iyayen su sun kasance ba irin iyayen nan bane masu bama tarbiyyar ƴaƴansu muhimmanci, hakan yasa suka sake su suna abun da suka gadama, rashin halin iyayensu yasa wasu daga cikin yayan suka raina ma  arzikin iyayen suka zama masu kwaɗayi da hangen na wani, sun kasance irin waɗanda basu da gashin wanccan su ce sai sun yi kitson wance, hakan yasa suke liƙe ma yaran masu kuɗi ga yin samarin tsiya, da yake Allah Ya yi masu baiwar kyau, gaba ɗaya yaran gidan su ba munana bane saidai kyawun wani ya fi na wani, saboda kyawun dake gare su hakan yasa suke yin samari masu kuɗi ko yaran masu kuɗi, a wurin su suke samun kuɗaɗen da suke fantamawa suke yin rayuwa tamkar yaran masu hannu da shuni, wanda idan baka san su ba aka faɗa ma iyayen su talakawa ne har rantsewa kana iya yi cewa ƙarya ne aka faɗa maka, to da yake suma iyayen nasu masu shegen son abun duniya ne hakan yasa sam basa kwa6ar su kan yadda suke samo kuɗi, ba kamar da yake suma suna yagar rabon su kuma ana kawo masu kayan daɗi suna ci, gaba daya sun maida yaran nasu kamar jari har hure masu kunne suke yi kan yadda suke da kyawu kada su sake su rinƙa kula maza marasa kudi, har huɗuba suke masu idan aka ce ana son su da aure kada su amince su yi aure da wuri su bari sai sun gama cin ƙuruciyar su in ba haka ba da an aure su zasu daina samun duk alherin da maza ke yi masu su koma sai yadda aka yi da su. 



Da yake wani lokacin a gida akan samu wanda ya fita zakka, to suma a gidansu Sapna wadda ita ce ke bi ma Jameela ta fita zakka, tana da kamun kai da natsuwa gata tana son karatu kuma ba laifi tana da ɗan ƙoƙari, sa6anin Jameela da sauran ƙannansu waɗanda sam basu wani fahimtar karatu, Allah dai ya basu kyawun sura amman ƙwalwarsu yadda kasan dusa ce a ciki saboda rashin fahimtar karatu, ita Sapna karatu kawai tasa a gabanta sam bata kula samari, ba kamar Jameela ba da tun tana firamare take da samari kuma suke bata kuɗi, wani lokaci har faɗa iyayensu suke ma Safna akan rashin kula samarin da take yi, suna cewa wai tana masu baƙin cikin alherin da zata sama masu kamar yadda suke samu da ƴar uwarta Jameela, sam bata biye ma huɗubar iyayensu duk faɗan da zasu yi mata, karatunta na boko da islamiyya kawai ta saka a gaba, saboda rashin kula samarin da take yi yasa wani lokacin in ta kawo masu buƙatar da ta danganci karatunta sai su ƙi yi mata, su rinƙa cewa da tana kula samari tana samun kuɗi ai da ta rinƙa biya ma kanta buƙata har ma da nasu buƙatun, da yake tana son karatunta bata son abun da zai yanke mata shi hakan ya sa wani lokacin take tambayar Jameela kuɗi, idan ta ci sa'a ta bata, wani lokacin kuma idan Amminsu na kusa sai ta hana Jameela ta bata wai duk don ta ji matsi ta rinƙa kula samari amman hakan bai sawa ta canza. Akwai wani lokaci da ta rasa ina zata samu kuɗin da zata siya littafai don nata duk sun cika sai dai ta samu paper ta yi rubutu sai ta sa cingam ko kuma ta je jikin wata bishiyar makarantar su ta samo ƙwaro sai ta haɗe paper din da karshen  littafin, har ta kai bata da sauran paper din da zata rinka yagowa, data rasa mafita gashi gida an ƙi bata kuɗi ta siya, ƙarshe a 6oye ta je gidan su Soffy wurin mahaifiyarta Hajiya Aisha, tana ƙwalla ta sanar da ita halin da take ciki game da karatunta, saidai bata faɗi mata cewa saboda bata kula samari ya sa iyayensu basu bata kuɗin siya ba, kawai ce mata ta yi sun ce basu da kuɗi, lokacin Hajiya Aisha ta ji tausayinta sosai musamman yadda ta san halin Safna ɗin ba irin na sauran yan uwanta bane, bata da kwaɗayi ko ta saki baki ta faɗi matsalan da ta danganci kanta ko gidan su da sunan a taimaka mata, wannan ne karo na farko ma da ta kawo kukanta wajenta, a lokacin Hajiyar ta ce mata ta je gida zata bada a kawo mata littafan, amman sai ta nuna mata ba a san da ta zo ta fadi mata ba bata son hakan ya sa a buge ta in aka ji ta zo ta roƙe ta, Hajiyar ta fahimce ta ta ce mata shike nan ta je zuwa anjima sai ta dawo, bayan tafiyarta ne ɗiyarta Soffy ta shiga bata labarin irin wahalan da Safna din ke yi akan karatu, ta ce mata kullum a ƙafa take zuwa makaranta ta dawo, kuma wani lokacin ko kuɗin break ma ba a bata ga kayan makarantarta duk sun tsufa sun yage, Hajiya ta ƙara jin tausayinta ya kama ta dama ta na son yarinyar saboda natsuwarta. 


Bayan Sapna ta dawo da daddaren Hajiya ta sa ta zauna a falo, lokacin dad ɗin su Soffy na nan ta iske shi a falo, bayanin Sapna ta yi mashi ta roƙe shi kan ya taimaka mata a karatun ta, farko ya nuna shi ya yi masu duk abun da zai iya tun da ya ba mahaifinsu jari, wanda inda ya jajirce ya yi kasuwanci ai da duk ya ɗauki wata ɗawainiyar su, cikin lallami da kwantar da kai ta shiga nuna mashi yarinyar ta fita daban da yan'uwanta kuma tana son karatu, ta roƙe shi kan ya taimaka mata tun da su iyayen nata ba ɗaukar ilimin suka yi da mahimmanci ba, cikin nasara ta ja hankalinsa ya amince da zai taimaka ma karatun Sapna. Daga ranar Hajiya ta sa ta rinƙa zuwa da safe idan driver zai kai yaran gidan makaranta sai a tafi da ita a sauke ta a tasu makarantar, sannan duk wata buƙata ta karatunta ta ce ta rinƙa zuwa tana faɗa mata, har sabbin kayan makaranta da jaka da takalma suka siya mata, Sapna ta ji daɗin hakan kuma sosai ta ci gaba da maida hankali akan karatunta ba ruwanta da kula samari.



A shiriri ce Jameela ta kammala karatun ta na sakandire, daga nan bata ƙara bin ta kan karatu ba sai biye ma samari. Duk halin da suke ciki yayan baban su Amadu ya sani, kuma yana tsawartar ma iyayansu sosai kan rashin kula da tarbiyyar yaransu, ƙarshe sai suka maida shi tamkar abokin gabansu, Amminsu ta zuge abbansu wai baƙin ciki yake masu Allah Ya basu yara kyawawa suna samun alheri da su ba kamar nashi yaran ba, har da cewa baya son ci gaban su ya fi son kullum su yi ta zama ƙarƙashin shi yana taimaka masu, ƙiri-ƙiri suka yanke zumunci da shi, hatta yaran nasu suka dasa masu haushin shi a zuciya, ita dai Sapna ba ruwanta ba abun da ya canza daga bangarenta tana zumunci da su, hakan ba ƙaramin ciwo ya yi ma Amadu ba ya shiga damuwa sosai, matarsa Hafsa ta rinƙa kwantar masa da hankali ta ce ya rabu da su kawai tun da ya yi bakin ƙoƙarin shi ya sauke hakkinsa na ɗan'uwan su. Bayan ɗan lokaci da hakan Amadun ya haɗu da haɗarin mota wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuwarsa, a lokacin yana da yara biyar.



Lokacin da Soffy ɗiyar Alhaji Mahmud ta fara karatu a jami'ar BUK hakan ya ja hankalin Jameela ta ji tana son itama ta fara yin karatun jami'a, da yake a lokacin ta zama babbar yarinya idan ka ganta zaka yi tunanin ta girme ma shekarunta saboda tana da ƙira irin ta manyan mata masu diri, hakan ne ma ke ƙara jawo mata samari saboda kyawun surar ta, akwai wani babban mutum ɗan siyasa da take tare da shi a lokacin, tun farkon haɗuwar su ya nuna yana son aurenta amman ta ƙi amincewa ta nuna mashi ita gaskiya ba yanzu zata yi aure ba saboda yarinya ce ita ba wata babba ba, da yake yana samun yadda yake so a wurinta hakan yasa yake sakar mata kuɗi duk abun da take so yana yi mata. Lokacin shi ta yi ma maganar tana son ci gaba da karatu, saidai koda aka amso result ɗinta gaba ɗaya Waec da Neco abun ba kyawun gani duk F9, a lokacin alhajin nata ya ce mata ba yadda za ai ta samu ci gaba da karatu da wannan sakamakon, ganin ta shiga damuwa sosai ya kwantar mata da hankali da cewa hakan ai ba wata babbar damuwa bace, ya nuna mata su da suke da hanya za a canza mata wata jarabawar bama sai ta sake yi da kanta ba. Haka kuwa aka yi sai gashi an yi mata wata jarabawar kuma duk ta ci, ba tare da wata wahala ba sai gashi ta samu admission itama a BUK. Lokacin data fara karatun ita Soffy har ta shiga shekara ta biyu, amman duk da haka manne take da ita, duk ƙawayen Soffyn ta maida su itama ƙawayenta musamman da yake duk yaran masu kuɗi ne, cikin ɗan lokaci sai gashi ta yi suna a makarantar, ba iya yan set ɗinta da na Soffy ba, har cikin manya yan shekarar ƙarshe tana da abokai maza da mata, da yake abu mai kyau na da jan hankali hakan yasa duk waɗanda take manne mawa ta nuna tana son ƙawance da su basu gudun ta ko hantarar ta sai ma son ta da suke yi. 



Sam Jameela bata wani maida hankali akan karatu sai shiriritar abokai da samari, wani lokacin har makarantar ake zuwa a ɗauke ta, hatta cikin lakcarorin su tana da samari, gata yar ina da biki ce da ta ji cikin abokanta ana maganar biki sai ta je ko ba a gayyace ta ba har da su ƙarfin halin yin anko, ba kamar in ta ji bikin masu kuɗi ne ta dingi faman zura jiki har sai ta samu shiga. Da yawa waɗanda basu santa ba a makarantar sun yi zaton ɗiyar wani ce saboda kyawunta da yadda take saka suturu, wasu a tunanin su ita ɗin ƴar'uwar su Soffy ce, kuma sam Soffyn ba ta fallasa ko ita wacece, sai wasu daga cikin ƙawayen Soffy da suke tare tun kafin su zo jami'a kuma sun san gidan su da kuma alaƙarta da Jameela, sune suke fallasa ko wacece ita ganin irin yadda take rawar kai tana nuna kamar ɗiyar uban wani ce ita.



Ganin suna karatu jami'a ɗaya da Soffy yasa ta koma tana tarewa a gidan su, ta ci abinci ta yi wanka har aron kayan Sophia ɗin take waɗanda za su yi mata don ta fita garin jiki, duk da yawanci ma in ta arar mata kaya cewa take ta bassu, da yake mahaifiyar su Sophia din mutuniyar kirki ce sam bata da matsala hakan yasa Jamila ke cin karanta babu babbaka a gidan, saidai mahaifin Sophia ɗin bai cika son yana ganinta a gidan shi ba, har ƙawancen da take da ƴar shi baya so saboda duk an san yaran gidan su basu da tarbiyya, akwai lokacin da har magana ya yi ma mom din Sophia, kan baya son ƙawancen da take da ƴar shi bai son ta gur6a ta mata tarbiyya, lokacin mom din Sophia ta nuna mashi cewa raba su lokaci guda abu ne mai wuya tun da tare suka taso, kuma za a iya raba su su zagaye su koma a tare ta bayan fage, kuma hakan na iya haifar da abun da ake gudu, ta nuna mashi gara a ƙyale su su ci gaba yadda suke ana saka ido ana sanin wane hali suke ciki. Lokacin ya ɗauki shawararta, saidai ita kanta Jameela ta fahimci baya son zuwa gidan shi da take don duk ta zo ta iske shi ta gaishe shi haka yake amsa mata ba yabo ba fallasa, hakan ya sa sam bata sakewa yadda ta saba in har yana a gida, da yake kuma mahaifin Sophia bai cika zama ba yana yawan fita ƙasashen waje harkar kasuwancin shi, har da wannan ke bata dama take sakata ta wataya son ranta, har wasu cikin samarinta yaran masu kuɗi nan take kawo su a zuwan nan gidan ƴan'uwanta ne anan take zaune, da yake kuma maigadin gidan Garbati mayen son kuɗi ne, kuma shima dai ba wani na kirki bane sosai hakan yasa yake bata goyon bayan da take so ba kamar da tana bashi kuɗi masu yawa, wani lokacin da taimakon mai gadin wasu cikin samarinta har shiga take da su cikin gidan su zauna a cikin rumfunan shaƙatarwar dake a can gefe guda ba tare da sanin masu gidan ba har su yi zancen su su gama. 


Akwai wata rana da tana cikin yin zancen a gidan mahaifin Sophia ya ritsa da ita, ranshi ya 6aci sosai ganin har zance take mashi a gida, inda ta ci sa'a a ranar bai yi mata magana ba a gaban saurayin, sai da ya shiga ciki ya balbale mom ɗin Sophia da faɗa duk da ta nuna mashi bata da masaniya akan hakan amman bai yarda ba, shima mai gadin sai da ya sha faɗa sosai ya yi ta ba Alhajin haƙuri, yana cewa ya ga an bata dama tana zuwa gidan sosai shiyasa bai hana ta shigowa da samari ba a zaton shi Hajiya ta sani, lokacin alhajin ya gargaɗe shi akan kada ya sake bari ta shigo mashi da wani a gida in ba haka ba zai ja ma aikin shi, ya ƙara da cewa ko ɗiyar shi ya hana ta kula samari saboda karatu yake son ta yi akan me wata zata riƙa shigo mashi da ƙattakai cikin gida, jin hakan yasa Garbati mai gadi ya ce ma Jameela ta yi haƙuri ba zai ci gaba da barinta tana kawo samarinta ba kamar yadda suka saba ya faɗa mata yadda suka yi da Alhaji, sam a lokacin bata ji haushin alhajin ba don ta san gaskiya ya faɗa, ɗiyar shi Sophia ba ta kawo samarinta gidan duk da tana da su saidai su yi waya ko su haɗu a wasu wuraren.



Akwai wata rana bayan Alhaji Mahmud ya dawo daga tafiyar da ya yi ya ɗan kwana biyu baya nan, lokacin ya je masallacin dake a jikin gidan shi, bayan gama yin sallar ne suka gaggaisa da mutane da yake shi ɗin mutumin kirki ne da ya san hakkin makwabtaka, yana da taimakon mutane sosai musamman waɗanda basu da shi ko aka zo neman taimako wurin shi, bayan sun gaisa da limamin masallacin ne ya ce mashi in ba damuwa yana son za su ɗan tattauna wani batu mai muhimmanci, jin hakan yasa Alhaji Mahmud fasa tafiya ya zauna tare da tattara hankalinsa akan liman, a nutse ya fara yi mashi magana,


 

   "Wato Alhaji Mahmud dama magana nike son yi maka game da wani abu da ke faruwa, ina hango cewa idan aka yi sake al'amarin na iya haifar da gagarumar matsalar da ba a fata, hakan ya sa na yanke shawarar tunkararka da maganar a matsayin gyara kayan ka. Kuma ganin ana zama na amana da juna bai kamata a ce in an hango wani abu da ka iya zamewa matsala ba ai shiru ko don a fita hakkin juna...Dama game da ƴar wajenka ne Safiyya da kuma yarinyar gidan Abdullah Buzu..." Wani irin faɗuwa gaban Alhaji Mahmud ya yi jin abun da liman ya ce, dama sam hankalinshi bai kwanta da tarayyar su biyun ba, gyara zama ya yi sosai ya ce ma Liman wace matsala ce ya gani don Allah Ya faɗa masa kuma kada ya ji nauyin faɗa masa komai,


 

   "Su ƴa'ƴa da Allah Ya bamu Amana ne a gare mu  Alhaji Mahmud, kuma tabbas Allah zai tambaye mu akan yadda muka kula da wannan amanar, a matsayin mu na iyaye ya kamata muna kula sosai akan al'amuran yaranmu, mu kasance muna masu basu kariya daga dukkan wani mummunan abu da muka hango yana tunkaro su...Duk mun san irin halayen yaran dake a unguwar nan, ba zancen ganin ido ba Alhaji kowa ya san yarinyarka Safiyya tana da kyawawan halaye, kun yi ƙoƙari matsayin ku na iyayenta wurin ganin kun bata tarbiyya duk da kasancewarka ba mazauni ba, sai aka ci sa'a da mahaifiyarta ma jajirtatta ce wurin hakan...Ba sai na fito fili na bayyana maka irin halayen yaran Abdallah buzu ba don hakan a bayyane yake, kuma kai zaka ma fi mu sanin halayyar su tun da kusan a unguwar nan sun fi shiga gidan ka akan na kowa tun lokacin da mahaifin su yana aiki a ƙarƙashin ka..."  


A nutse cikin kwantar da murya ya shiga nusar da Alhaji illar da yake hangowa a ƙawancen Safiyya da kuma Jameela, ya kuma nuna mashi irin ƙarfin tasirin da abokai suke yi wajen canza halayyar junan su wanda ko iyaye basu cika yin wannan tasirin ba, ya haɗa da kawo mashi hadisai dake magana kan abokantaka da irin mutanen da ya kamata a yi abota da su. Hankalin Alhaji Mahmud ya ƙara tashi, har zuciyar shi ta fara saƙa mashi tunanin kodai wani mummunan abu ya faru da bashi nan an 6oye mashi, kasa haƙura ya yi sai da ya yi ma malam Liman tambaya kan hakan, ya roƙe shi akan don Allah Ya sanar mashi in dai da abun da ya san ya faru da bashi nan, Liman ya tabbatar mashi da ba wani mummunan abu da shi dai ya ji ya faru, sai dai hango hakan na iya faruwan ne ya sa ya yanke yi mashi magana kamar yadda ya faɗa tun farko.


  

 "Nagode sosai malam Liman, haƙiƙa kai masoyi nane na gaskiya da har ka hango illa da ka iya shafar ahalina ka sanar mani don daukar matakin guje ma faruwar hakan, haƙiƙa nima tun ba yanzu ba hankalina sam bai kwanta da tarayyar su ba, na so in raba su tuni, to sai mahaifiyar yarinyar ta nuna gara a ƙyale su ana saka masu ido akan a raba su, don suna iya zagayewa su koma tare ba tare da sanin mu ba, to wannan shawarar tata ita na ɗauka ya sa ka ga na ƙyale su amma ba wai don hankalina ya kwanta da hakan ba." Alhaji Mahmud ya yi bayanin da damuwa shimfiɗe akan fuskarsa, 



   "Ba wani abu Alhaji, ai duk yi ma kai ne, kuma fita hakkin juna ne a matsayin mu na maƙwabta. Sannan dama mu malamai a koda yaushe aikin mu ne idan mun hango wata matsala in muna da ikon gyara ta sai mu yi hakan, idan kuma bamu da wannan ikon sai mu tuntu6i wanda ke da ikon gyarawar don a ya gyara, idan ya ɗauka Alhamdulillah hakan muke so, idan kuma akasin hakan to mu dai mun yi aikin mu. Shi kan shi Abdullah Buzun na yi mashi nasiha ba sau ɗaya ba akan halayen yaran shi amman sam baya dauka, ƙarshe ma sai gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da zuwa wannan masallacin, wannan dalilin ne ya sa nima na rabu da shi, duk da mutane na yawan zuwa mani da ƙorafin yaran shi, to saidai in faɗi masu cewa na yi abun da zan iya sai dai kawai mu yi masu addu'a Allah Ubangiji Ya shirya su da zuri'ar mu baki ɗaya." Amsawa Alhaji ya yi da Amin, ya ƙara da cewa shima ya sha yi mashi magana akan hakan  sai ya nuna kamar ya ɗauka, ƙarshe da ya fahimci ba ɗaukar shawara ko nasihar yake ba sai ya tattara ya rabu da shi. 



Tun akan hanyar komawar Alhaji gida ya gama yanke shawarar matakin da zai ɗauka kan hakan, bayan ya isa gidan a falon shi ya kira Hajiya Aisha, tun da ta kalli fuskarshi ta fahimci akwai damuwa tare da bacin rai tattare da shi, ta shiga tambayar shi abun da ke faruwa, duk abun da suka tattauna da malam Liman ya sanar mata, anan ya ce mata ya gama yanke shawarar matakin da zai dauka, shine zai maida Safiyya ƙasar Turkey can wajen yayanshi dake zaune acan yana aiki da kasuwanci, sam hajiya bata ja da shawarar da ya yanken ba, don tun farko dama can ya so ya tura Soffyn ta yi karatu ita ce ta roƙe shi kan ya ƙyale ta ta yi karatun ta anan ta nuna bata son ta yi nesa da ita, to shima da yake bai cika son yaranshi su yi nesa da gida ba hakan yasa a lokacin ya ƙyale ta, fatan Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi ta yi ya amsa da Amin. A daren ranar ya kira Soffy ya sanar da ita kan ta fara shirin tafiya Instanbul a can zata ci gaba da karatu, ta ji ba daɗi amman bata shiga damuwa ba sosai saboda gidan yayan mahaifin nata dake can tamkar gida yake a wurinta, shima yana da yara har da sa'ar ta da suke ƙawaye, sannan kuma akwai ɗan shi Lukman da suke cikin yin soyayya da juna. Lokacin da Jameela ta ji zancen tafiyar Soffy ba ƙaramar damuwa ta shiga ba, saboda ba ƙaramin amfanuwa take da ƙawancen da suke ba, sannan kuma sun saba sosai da juna don tun suna yara suke tare, a lokacin ta ji inama ta bita ƙasar wajen itama sai ta ci gaba da karatunta na shiririta a can, sai dai ta san hakan ya fi ƙarfinta don ko cikin samarinta bata tunanin akwai wanda zai iya ɗaukar mata nauyin hakan, dama honorouble ne mai sakar mata bakin aljihu yadda ya kamata, to shima a lokacin ya ɗan ja mata baya tun da ya ce mata baya son tana kula samari sai shi kaɗai amman ta ƙi bin umarnin shi.



Bayan tafiyar Soffy haka Jameela ta ci gaba da shiririta a wurin karatun ta don saima abun da ya ci gaba. Ana haka ne su Ibrahim wato mahaifin Deen suka zo biki Kano, a lokacin bikin yayan abokinshi Maleek mai suna Saleem, wanda asali suma Maleek ƴan Funtua ne amman a kano iyayen su suke zaune, sai dai basu cika zama a Kanon ba suma sun fi zama a ƙasashen waje saboda irin aikin iyayensu ɗaya, dalilin ma da ya haɗa iyayen nasu kenan har suke abota suma kuma yaran nasu suka zama abokai, kusan duk sun zauna a ƙasashe guda kuma tare suka yi karatu tun suna yara, hakan ne ya sa Ibrahim bashi da babban abokin da ya wuce Maleek, shima Sa'ad abokin Saleem ne wanda suka zo bikin shi. 


A ranar da za a yi dinner party lokacin Jameela ta zo duk da gayyar soɗi ta zo don bata haɗa komai da masu bikin ba, wata ƙawarta ce ƴar jami'arsu ita ce ƴar'uwar su amaryar shine ta biyo ta, a wurin dinner ɗin idan ka ga Jameela bazaka ta6a yin tunanin cewa bata haɗa komai da masu bikin ba, yadda ta ci uban gayu zaka ce bikin nasu ne don har da su anko ta yi har ma tafi ƙawartata da ta biyo iya yi, ba ƙaramin jan hankalin samari ta yi ba a wurin kamar dai a kowane biki da take zuwa. Tun da Ibrahim ya ɗaura idanun shi akanta ya ji ya kamu da tsananin son ta, sai da ya yi yadda ya samu yin magana da ita tana ta faman yauƙi kai ka ce ɗiyar uban wani ce, ba tare da 6ata lokaci ba ya bayyana mata shi dai ya ganta kuma ya ji ya kamu da sonta, a nan ya bayyana mata kan shi da kuma alaƙar shi da masu bikin, ai fa tana jin cewa ba zaune suke a ƙasar nan ba ya ja hankalinta har ta saurare shi sosai musamman da ta ga tare yake da ƙanin angon wato Maleek, kuma dama ta fahimci angon ɗan masu arziƙi ne daga yanayin shi da dangin shi. Bayan gama dinner din ya amshi lambarta ya ce washe gari zai zo gidansu su gaisa da iyayenta, gudun ya je ya ga gidan su yasa ta ce mashi ya bari ai zata zo wurin bikin gobe sai su haɗu, duk yadda suka so su maida ta gida bayan gama dinner ɗin sai da ta zille masu. 



Washe gari don ƙarfin hali sai gashi ta je gidan bikin, anan suka sake haɗuwa da Ibrahim har ya nuna ma yayanshi Sa'ad ita matsayin budurwar da ya yi, ya so ma ya kai ta ta gaisa da hajiyar su amman ta ƙiya ta nuna mashi ya yi wuri da yawa, har kusan magrib ta na nan, a motar Maleek suka ɗauke ta da za a tafi kai amarya. A ranar duk yadda ta so ta zille masu ta kasa, su suka ɗauke ta don maida ita gida, tana ta zullumin kada idan suka ga gidansu ya guje ta, wannan tunanin ya sa ta yanke ƙin kai su gidan su, a bakin gidan su Soffy ta sa suka ajiye ta ta ce masu anan take da zama amman ba nan ne ainihin gidan su ba, saida suka so ta shigar da su don su gaisa da mariƙan nata amman ta ƙiya, ta yi masu ƙaryar babanta mai ruƙonta baya barinta kula samari su bari daga baya zata yi masu hanyar da za su gaisa. 



Bayan gama bikin da kwana biyu a ranar da za su koma Funtua ya buƙaci yana son su haɗu, a wani haɗaɗɗan wurin cin abinci ta yi masu mahaɗa, a nan ya sanar mata shi fa son ta yake da aure, idan ta amince yana komawa gida zai sanar da iyayen shi, ya ce mata so yake kafin su bar ƙasar a gama magana tsakanin iyayen su, tabbas ta ji tana son shi da aure musamman kuma saboda ya tafi da ita ƙasar waje kamar yadda ƙawarta Soffy ta tafi ta barta, lokaci guda ta ce ta amince zata aure shi. 


Bayan komawar su Funtua ne ya yi ma hajiya maganarta tare da nuna mata hoton ta a wayar shi, ta tambaye shi game da iyayenta, ya ce bai san wanene mahaifinta ba amman ɗan'uwan mahaifinta ne ke ruƙonta, har ya sanar mata cewa yayan shi Sa'ad ya ganta har sun gaisa, a lokacin nuna mashi ta yi shi da yake son ci gaba da karatun shi kuma ya zai kawo batun aure, ba kunya ya nuna mata ya canza ra'ayi saboda yana son yarinyar idan ya aureta ya ci gaba da karatun, hajiya ta yi mamakin yadda ya kamu da son yarinyar lokaci guda, ta ce mashi ya bari zata yi magana da mahaifin su. Bayan sun tattauna da mahaifin nashi ne suka sanar da shi cewa sai sun fara yin bincike game da yarinyar kafin akai maganar aure. Lokacin da ya sanar da Jameela hakan hankalinta ya tashi har ta yanke faɗa mashi gaskiya cewa ita fa ɗiyar talakawa ce, ya bata amsa da shi ai ita yake so ba wani abu ba don haka ba ruwan shi da hakan, ta ji daɗi sosai don bata fatan a ce bata aure shi ba, ta samu Ammin su dama tuni ta sanar mata game da Ibrahim, cike da damuwa ta sanar mata yadda suka yi da shi na cewa za ai bincike akanta, ta ce ita tana tsoron su yi binciken a faɗi masu wani abu da zai sa su ƙi yarda a yi auren, Ammin ta so ta ja ra'ayinta kan ta haƙura da shi kawai, amman Jameela ta nuna ita gaskiya tana son shi da aure da kuma manufarta na auren shi, jin hakan ya sa Ammin tana sakin shu'umin murmushi ta ce mata kada ta damu su yi binciken tana tabbatar mata ko sun yi ba abun da za su ji da zai sa a fasa saidai ko don saboda su talakawa ne, sosai Jameela ta ji daɗi don ta san wacece Ammin su a 6angaren hatsabibanci ga bin bokaye, ko farin jinin samarin da suke da shi ba haka nan bane. Mahaifin su Maleek wato Alhaji Usman Karaɗuwa shi daddyn su Ibrahim ya tuntu6a da maganar ya ce yana son ya saka a yi masu bincike game da yarinyar, da yake abu ne na manya ba 6ata lokaci ya wakilta wani kan hakan, bayan an tambayi Jameela ta faɗi sunan unguwar da take da kuma mahaifinta. 


Sam hajiya Binta bata ji tana son al'amarin ba bayan da aka sanar da su sakamakon binciken suka ji asalin Jameela da iyayenta, ba kuma don sun kasance talakawa ba don su basu gudun talaka, kawai daga yadda ta ji asalin na su ne akwai rauni, a hakan ma wai don basu ji halin su ba don Ammin su tasa an yi mata surkulle an rufe bakin mutane, kuma Allah Ya ara masu sa'a don kwata-kwata a binciken ba a faɗi wani abu mara kyau game da halin ƴan gidan ba. Hajiya bata goyi bayan auren ba ta ce ma Ibrahim ya haƙura da yarinyar nan shima ya yi auren zumunci kamar yayanshi, dama akwai ƙanwar Amina matar Sa'ad ita suke son su haɗa su, har ta nuna mashi in don kyawu ne itama tana da shi daidai gwargwado tun da fulanin asali ne, shima Alhaji Nuraddeen ya goyi bayan ra'ayin matar shi ya nuna ya haƙura kawai, aikuwa sun sha ruwan mamaki, don Ibrahim tubure masu ya yi kan shi dai ita yake so har da su kwanciya ciwo ya yi ta koke-koke, cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya rame, a haka lokacin komawar su ya yi suka tafi, ta bangaren Jamila itama hankalinta ya tashi jin iyayen shi basu amince ya aure ta ba, ta shiga damuwa sosai itama har da su kwanciya ciwo saboda ta ƙwallafa rai kan tafiya ƙasar waje, har da ita ke ƙara tayar ma Ibrahim ɗin hankali, in suna waya tai ta yi mashi kuka tana faɗin miye aibunta da iyayen shi za su ƙi amincewa da ita, idan don su talakawa ne ba shi ya ce hakan ba damuwa bane, sai da ta yi nisa a son shi ta rabu da duk samarinta masu son auren ta sai kuma a ce shima ba zai aure ta ba, waɗannan kalaman nata ke ƙara tayar mashi da hankali, sai gashi ciwo sosai ya yi mashi rigis, hankalin su Hajiya ya tashi lokacin da aka tabbatar masu da ya samu high bp, a lokacin likitansu wanda yake bature ya basu shawarar su bashi abun da yake so kada a rasa shi. Ƙarshe dole suka haƙura, wasu daga cikin dangin mahaifin shi dake Funtua aka wakilta su je nema mashi aure, Jameela ta yi farinciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha da ta ji zancen, dama sai da Ammin su tai ta ce mata ta kwantar da hankalinta, idan dai ba son su rasa yaron su suke ba to tabbas sai sun amince, don kuwa har da sharrinta ya sa son Jameela ya tsananta a zuciyar Ibrahim. 



Watanni kaɗan aka saka na bikin, zuwa bayan babbar salla za a yi, dama duk hutun karshen shekara suke zuwa sai kuma wani lokacin suna yin azumi anan amman duk babbar salla anan suke yin ta saboda sun fi son su yi layya anan, lokacin da aka yi bikin Saleem yayan Maleek har ya haɗu da Jameelar lokacin dama sun zo hutun ƙarshen shekara ne. 



A kwana a tashi har lokacin bikin ya yi, gaba ɗaya hidimar bikin a Kano aka yi ta gidan su Maleek suka zauna har aka gama aka ɗauko amarya zuwa Funtua, dama kafin bikin mahaifinshi ya gina mashi flat a cikin gidansu daga baya, wanda da babban fili ne har noma ake masu da damuna a ciki. A ranar da aka kawo Jameela da daddare bayan sallar isha Sapnah ƙanwarta ta fito daga part ɗin da suke na amarya ta nufo bangaren su hajiya, tana tafiya cikin harabar a nutse jikinta sanye da abaya ta ɗaura gyalen rigar a saman kanta, ita kanta bata san ina zata je ba ta dai fito ne kawai har ta iso gaban gidan, a daidai lokacin ango Ibrahim suka dawo daga masallaci tare da Maleek da wasu abokan su ƴan'uwan Ibrahim guda biyu, gaba ɗaya sun sha shadda sun fito a matasan samari yan hutu sai sakin ƙamshi suke, tun da suka shigo Maleek ya hango ta a tsaye daga gefen ginin, suna ƙarasa shigowa ciki ya gane fuskarta, har za su shige ya ce masu su je yana zuwa ya nufo ta, tana ganin ya nufo ta ta shiga yan kame-kame har zata juya ta bar wurin ya ƙaraso, 


   "Assalamu Alaiikum.." Sautin daddaɗar muryar shi ya sauka a kunnanta, ɗago idanunta tubarkallah ta yi ta ɗan kalle shi kamar tana tsoron amsawa ta amsa ƙasa-ƙasa, haɗa ido suka yi ya sakar mata murmushinsa mai burgewa, dama Maleek ba daga baya ba kyakkyawan saurayi ne sosai gashi dogo mai ɗan kaurin jiki, 


   "Sannu ko." Kai ta ɗaga mashi kawai. 


    "Zamu wuce ne na hango ki tsaye na yi tunanin ko kina neman wani ne?" Muryar shi ba dai daɗi ba, kana jin yadda yake magana kuma zaka fahimci turanci ya zauna mashi, baki ta fara motsawa tana kame-kame sam ta kasa magana saboda yadda ya kafe ta da idanuwa, tun lokacin da ake cikin hidiman bikin ya fara ganin ta, kuma ya fahimci bata da hayaniya sannan tana da natsuwa sosai, don lokacin da aka yi dinner yana ganin yadda ta natsu a wuri ɗaya bata tashi ta yi rawa ba kamar sauran ƴan mata ba, kuma an yi mata ɗinkin mutunci a ankon dinner ɗin,


   "Tell me if you need something." Ya faɗa tare da ɗage mata gira, da ƙyar ta buɗe baki cikin nutsattsiyar muryarta ta ce, "D..dama ina son in saka cajin wayana ne bansan na manto caja na a gida ba." Murmushi ya yi jin muryarta a karon farko,


   "Yanzu kina buƙatan caja ke nan?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce eh in akwai inda ake sayarwa,


   "Baki son in ara maki nawa?" 

Yanayin fuskarta kamar zata yi murmushi ta ce, "To ai bansan ko kaima zaka yi amfani da shi ba ne." 


  "Ko zan yi amfani da shi sai in haƙura in baki tun da ke baƙuwarmu ce, kuma an ce ka karrama baƙon ka." Dan faffaɗan murmushi ta yi duka kumatun ta suka lotsa, sosai ya ga ta ƙara yi mashi kyau murmushin da ta yi, tambayar ta ina wayar tata ya yi ta ɗago ɗayan hannunta dake riƙe da ita ta miƙa mashi, bin wayar ya yi da kallo bayan ya amsa ba wata babba bace kuma da gani ta ɗan kwana biyu, ɗagowa ya yi ya kalle ta suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta, haka nan ta ji kunya ta kama ta, murmushi ya yi kamar ya fahimci dalilin sunkuyar da kan nata,


   "Charger na ba zai yi ma wayan ba, amman idan ba damuwa mu je sai a siyo irin nata." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, da yake tana tsananin buƙatar ta yi cajin saboda karatun jarabawar Jamb da take yi hakan ya sa ta amince, tare suka nufi parking space ya nuna mata ɗayan side ɗin motar da yake ƙoƙarin buɗewa, ita tama yi tunanin a ƙafa ne za su je siyowa, da yake ta san shi tun da aka fara hidiman bikin take ganin shi, hakan ne ya sa bata ji tsoron ta bishi ba, 


  "Ya sunan malamar ne?" Suna cikin tafiya bayan sun hau hanya ta ji ya tambaya ta ce mashi Sapnah, 


   "Nice name.." Kallon shi ta ɗan yi a hankali ta ce mashi ta gode.


   "Ni baki son sanin nawa sunan?" Bayan ɗan lokaci ta ji ya tambaya, "Ina so.." Ta faɗa, 


   "No, baki so ai da kin tambaya." 


    "Da gaske ina so." Ta sake faɗa tana kallon shi, shiru ya yi idon shi akan hanya kamar ba zai faɗa ba,


   "Suna na Maleek Usman Karaɗuwa, ni best friend ɗin ango ne kamar ma dai ƴan'uwa muke da shi, don iyayen mu ma abokai ne sosai." Kai ta ɗan jinjina bata ce komai ba, kallon ta ya ɗan yi ya tambayi ita miye alaƙarta da amaryan, ta ce mashi yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya. Daga haka suka fara sabawa bayan an siyo caja sai da ya ɗan zagaya da ita wai ta ga gari ya siyo mata kayan ƙwalam sannan suka dawo gida, kafin su rabu sai da ya amshi no ɗin ta. 


Washe gari bayan an yi walima aka shirya maida dangin amarya, kafin su tafi saida suka yi sallama da juna ya kawo abu a cikin leda ya bata ya ce kyauta ce ya bata sai ta je gida sannan ta buɗe, ya yi mata hakan ne don daga yanayin ta ya fahimci idan ta san ko miye ba lalle ta amsa ba, haka kuwa aka yi sai da suka koma gida sannan ta buɗe ta ga sabuwar haɗaɗɗiyar waya a cikin kwalinta, ita tsoron ma wayar ta ji don wannan ne karo na farko da ta amshi abu irin haka a wurin wani namiji, ko wayar hannunta tsohuwar ta Jamila ce ta bata, aikuwa da ya kira ta sai da ta yi mashi ƙorafin wayar, ta ce wai zata bada a maido mashi ita bazata amsa ba tun da tana da ita, ya ce ya san da tana da itan ya bata kuma ai kyauta ce, da ta kafe kan sai ta maido mashi ya ce mata aikuwa idan ta yi hakan za su 6ata ba zai ƙara kiranta ba, tun da ta nuna mashi bai isa ya bata abu ta amsa ba duk da yanzu su kamar ƴan'uwa suke, jin hakan ya sa ta bashi haƙuri ta nuna mashi ba haka bane kawai ta ga tana da wayan ne, daga baya ta yi mashi godiya. A hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, har bayan su Maleek sun bar ƙasar yana kiranta akai-akai suna gaisawa har su yi hira don ta sake da shi, daga baya har kuɗi yake turo mata ya ce ta yi buƙatunta na karatu da za ta fara......

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post