Malamin jami’a ya rasu a dakin Daliba lokacin da ya kai mata ziyara

Malamin jami’a ya rigamu gidan gaskiya a dakin Daliba bayan da ya kai mata ziyara

Wani Malamin Jami’a mai suna Abdulfatai Aiyede ya rasu a dakin wata daliba a lokacin da ya kai mata ziyara.

Malamin mai shekaru 53 ya fito ne daga garin Bida na jihar Neja inda ya kaiwa dalibar me suna Stella Joseph ‘yar kimanin shekaru 23 ziyara a Minna.

An bayyana ɗalibar tana karatun Nurse ne inda bayan da ya je dakin nata, ta dafa masa abinci.

Bayan da ya ci abincin ne sai ya yanke jiki ya fadi yana jijjiga, an garzaya dashi Asibiti inda likitoci suka tabbatar rasuwar sa.

Yanzu haka dai an kama dalibar inda shi kuma ake binciken gawarsa dan tabbatar da sanadiyyar mutuwarsa.

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post