_Bossladieswriters_
https://chat.whatsapp.com/ITci6VU5Aq17xeCr82mD00?mode=wwt
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_By Zainab Bature_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._
Page 4
Bayan sun isa dining room, a ɗaya daga cikin kujerun ya zauna Leemah ta shiga yin serving na shi, bayan ta gama ta zagayo kujerar dake fuskantar tashi ta zauna, a nutse ya fara cin abincin yayin da take ɗan satar kallon sa, ita dai bata san ya akai ba komai nashi burgeta yake ba tun yanzu ba, ba kamar kwantaccen sajen shi da irin gyaran da ake mashi burgeta yake sosai, tana cikin kallon nashi maganganun da suka yi da mom ɗinta suka shiga dawo mata, jikinta ne ya yi sanyi tasan halin mom ɗinsu, idan har ta nuna bata son abu to fa ba a isa ba a yi, tasan tun da ta nuna bata son alaƙar soyayya a tsakanin su to kuwa mawuyacin abu ne in ma sun fara yi ta bari su auri juna. Ta yi nisa a duniyar tunani ya ɗago ya kalle ta, daga yanayin fuskarta ya fahimci kamar wani abu na damunta, ɗan gyaran murya ya yi shiru bata dawo hayyacinta ba,
"Leemahh..." Ya kira ta da wani irin sauti, ɗan firgit ta yi ta kalle shi,
"What's wrong with you?" Ya tambaya bayan ya ajiye cokalin hannunsa, ɗan kikkafta idanu ta shiga yi bata san mi zata ce mashi
ba,
"Tell me, mi ya faru?" Cike da nuna kulawa ya tambaya, sauke idonta ta yi tana ci gaba da kikkafta idanu, ɗagowa ta yi ta kalle shi ya kafe ta da nasa idanun alamar amsarta yake jira, motsa baki ta fara, slowly ta furta, "Mom ce..." Ta faɗa kaman zata yi kuka, shiru ya yi yana ci gaba da kallon ta, bai ji yana son ya tambaye ta abun da ya faru ba saboda ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, da wuya abun da ya haɗa ta da ita in ba akan shi bane.
"Ki yi hakuri, they're our parents komai suka yi mana sai dai mu yi haƙuri, and sometimes suna yi mana abu ne for our own good." Shiru ta yi fuskarta a ɗan ɗaure, ɗage mata gira ya yi alamar ta ji, a hankali ta jinjina masa kai, murmushi ya yi tare da ɗaukar cokalin ya ci gaba da cin abincin, after a while ya ƙara dakatawa tare da kallon ta ya ce mata ta zuba abincin itama,
"Na ƙoshi, bamu daɗe da muka ci ba ka zo." Ta faɗa da murmushi,
"Shine ni kika tsare ni don ki ga yadda nike yin loma ki yi mani sharri?" Dariya ta yi har fararen haƙoranta suka bayyana,
"Ai nasan baka yin loma Ya Fahad." Ɗan murmushin gefe ya yi kafin ya ci gaba da cin abincin, ganin ya tsaya yana ƙoƙarin zuba lemu ta miƙe da sauri ta zuba mashi, miƙa masa ta yi ya kar6a tare da yi mata godiya, bayan ya sha ya ajiye glass cup ɗin, kallon ta ya yi suka haɗa ido ya ce, "Ya school, an kusa gamawa ko?" Kai ta jinjina tare da faɗi mashi lokacin da ya rage,
"Da an gama sai a ci gaba ko, mi kike son karanta ne?" Tsintar kanta ta yi da kasa bashi amsa ta bishi da ido tana kikkafta su, shiru ya yi yana nazarin ta, can ya ɗan yi murmushi slowly ya furta, "Ko aure zaki yi?" Har saida gabanta ya faɗi jin abun da ya faɗa, nan ma kasa bashi amsa ta yi, ganin kallon da yake mata ya sa ta sunnar da kanta tana ɗan motsa baki,
"Leemah..." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, "Speak your mind, ai ba laifi bane in shi kike son yi abu ne mai kyau." Motsa baki ta yi da ƙyar ta ce, "Duk abun da Allah Ya za6a mani."
"Amman kin fi son ki yi aure?" Abu ta haɗiya kafin ta ce, "Ni da ko saurayi bani da Ya Fahad." Ya yi ɗan murmushi,
"In kin yi saurayin za ki yi auren ke nan?" Shiru ta ɗan yi tana kallon sa tana ɗan murmushi yayin da zuciyarta ke ta tunzura ta kan ta fallasa mashi sirrinta, kai ta jinjina, ta ce, "In muna son juna." Dariya ya yi duk dimples ɗin sa suka lotsa,
"Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya baki saurayi na gari wanda zai so ki saboda Allah ya kula mana da ke sosai." A hankali ta amsa da Amin tare da sauke idanunta, ji take kamar ta faɗa mashi cewa tana son shi saidai tana jin fargabar hakan ba kamar da yake matsayin yayanta kada ya ƙi amincewa ya kuma tsawatar mata kan hakan, a nutse ya ci gaba da cin abincinsa tana ta ɗagowa tana satar kallon shi,
"Amman na yi mamakin jin baki da saurayi, yadda sister nawa take tubarkalla, ko dai ke ce baki amincewa in an ce ana son ki....? Ko da yake kamata ya yi dama yanzu ki focus kan karatun ki ba wannan ba, gashi kuma kin ce aure kike so to kuma ba boyfriend, ya za a yi ke nan?" Ya ƙare yana sakin murmushi, tura mashi baki ta yi a shagwa6e ta ce, "Ni fa Ya Fahad ba cewa na yi banson karatu ba ko, ba kai ne ka matsa in faɗi maka ba har ka ce abu mai kyau ne, ni shiyasa na ce ina so kuma na ga ko an yi aure ana iya yin karatu."
"To yanzu ya zamu samo boyfriend en?" Ya faɗa yana ɗan shafa gemun shi da hannunsa na hagu, wani kallo ta yi masa ta ce, "Ai ina da wanda suke cewa suna so na, wasu yaran friends ɗin mom ne wasu kuma na dad, amman ni duk bani son su, akwai wanda nike so amman shi bai sani ba..." Ta ƙare maganar ƙirjinta na ɗan bugawa,
"You should tell him.." Ya faɗa tare da ɗan ƙanƙance ido ya shigar da lip ɗin sa na ƙasa,
"I'm scared he might reject me...ban so na zubar da ƙima ta." Da ƙyar ta faɗa tana ta ƴan kame-kame, ƙayataccen murmushi ya saki ya bita da wani irin kallo da yasa duk ta sha jinin jikinta, lokaci guda ta ji kallon na neman haifar mata da kasala, ta kasa tsaida idanunta akan shi sai ƴan kifce-kifce take tare da kallon ƙasa,
"Bana tunanin akwai namijin da zaki furta ma hakan ya ƙi amincewa, with your beauty inside and out, I'm sure he will adore you. Kawai yanzu kamata ya yi ki maida hankali kan karatu, forget about any relationship for now, lokacin hakan zai zo, and you will meet the right person to marry " Ɗan jinjina mashi kai ta yi kafin ta sunnar da kanta ƙasa, hannu ya kai ya ɗauki glass ɗin lemu ya kai baki, a hankali yake kur6ar ruwan lemun idanun shi akan Leemah kamar mai nazarin wani abu.
Bayan Deen ya dauko wayarsa, babban falon ya dawo ya zauna a ɗaya daga cikin saitin kujerun ciki, bayan ya shiga shafukan shi na sada zumunta waɗanda yake da mabiya miliyan ɗaruruwa, tarin sharhin masoyansa ya taras, a nutse yake bi yana dubawa, yawanci fatan alkhairi ne suke mashi kan ziyarar da ya kai ƙasarsa, da masu gwarzanta shi da nuna yadda suke ƙaunar shi, akwai tarin saƙonni daga wasu ƙananu da manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Nigeria suna roƙon shi da ya kai masu ziyara su yi wasa tare da shi, wasu kuma roƙon shi suke kan ya basu dama don su haɗu da shi. Yayin da yake ci gaba da bin saƙonnin, ɗan murmushi ne akan fuskarsa, wasu yana basu amsa wasu kuma ya yi liking dama shi ba mutum bane mai shariya ga masoyan sa, da wuya ya share in an turo mashi saƙo mai muhimmanci, yana matuƙar ƙoƙari wurin ganin ya samu lokaci ya bada amsa ga saƙonnin da suka dace. Duk da wasu abubuwan da yawa da suka shafi social media accounts dinsa personal manager din sa ne ke kula da su.
KATSINA STATE
Funtua L.G.A
Madaidaicin gida ne irin wanda kana gani zaka fahimci mamallakan shi masu ƙaramin ƙarfi ne, akwai ɗakuna guda biyu masu baranda a gaban su daga 6angaren hagu, daga 6angaren dama akwai ɗaki ɗaya ware yana kallon barandar wanccan ɗakunan, idan ka shigo gidan daga ƙofar waje akwai rufaffan zaure daga ciki akwai ƙofa da taga irin ɗakin zaure, kana shigowa cikin gidan daga bangaren hagu gefen baranda anan wani ɗan ɗaki ne mara girma yana da buɗaɗɗun ƙofa da taga daga yanayin shi zaka fahimci kitchen ne, daga bangaren gefen ɗakin da ba a cikin baranda yake ba ɗan fili ne, akwai rijiya a wurin da wurin yin wanke-wanke sai wani zagayayyen ɗaki mara rufi akwai kofa a jiki da gani banɗaki ne. Gaba ɗaya tsakar gidan malale yake da siminta sannan ginin gidan bai ji jiki ba sosai.
Daga can gefen rijiya wata matashiyar budurwa ce zaune akan kujera ƴar tsugunno, daga gabanta roba ce mai ɗan faɗi tana yin wanki ta gicce, ta yadda robar ba a tsakiyar kafafunta take ba a gefenta take, a jikinta tana sanye da doguwar rigar atamfa yayin da kanta ke sanye da hula daga tsakiyar kanta ya yi tudu sosai alamun tana da gashi ko kuma ƙaton ribbom ne ta saka, saidai kana kallon gaban kanta da suma ta kwanta zaka fahimci tana da gashin, yanayin kalar fatarta warm caramel ce, irin kaman wankan tarwada amman wadda ta fita daban da ake kira fata mai tsada don ba kasafai aka fiye samun masu ita ba musamman mu a nan, yadda ta juyar da fuska ta ɗan sadda kanta ya bayyanar da hancinta wanda ke da tsawo sosai tamkar an tsaga kara.
Daga can gabanta saman tudunkar baranda wani matashin saurayi ne da a shekaru zai iya kai wa shekara ashirin da ukku zuwa da huɗu, duk da girman namiji in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun ma, jikin shi na sanye da riga mara hannu irin ta shan iska da wando tiri kwata, daga gaban shi tsakankanin ƙafafuwansa plate ɗin abinci ne dauƙe da shinkafa da wake da mai da ya ji har da salat, hannun shi na dama na ruƙe da cokali da yake cin abincin da shi yayin da hannun hagun shi ke ruƙe da waya android yana ɗan latsa ta, yana yi yana kai idonsa akan abincin in zai ɗebo ya kai baki,
Wani matashin saurayin ne ya shigo cikin gidan yana sanye da singileti da gajeran wando, da alama daga cikin ɗakin zaure yake, a shekaru zai kai shekara ashirin zuwa da ɗaya, wurin inda matashiyar budurwar take ya nufa hannunshi ruƙe da wasu kaya, daga gabanta ya tsaya tare da sakin kayan ƙasa ya ce,
"Salma ɗan wanke mani su yanzu ki shanya mani su bushe, muna da match anjima su zan sanya." A hankali ta ɗago da fuskarta ta jefa mashi wani kallo mai kama da harara, ma sha Allah! ganin irin kyawun fuskarta, baya ga dogon hancinta tana da madaidaitan idanuwa farare tass da su, idan ka ƙura mata idanu zaka fahimci ƙwayar idanun nata baƙin su bai ciza ba sosai ta yi ɗan kalan ruwan ƙasa, haka ma labbanta kalar su brown ne da ya ɗan ciza, da kallo ɗaya zaka fahimci kyawunta, kana ci gaba da kallonta za kai ta ƙara ganin ƙaruwar kyawun nata.
"Ni fa gaskiya Sageer na gaji, duka yaushe na dawo daga makaranta, ba don uniform ɗin nawa sun yi datti ba da bama zan yi wankin ba hutawa zan yi, gashi ka kawo mani kayan ƙwallo masu dauɗar tsiya, safar ma sai wari take yi wllh." Ta ƙarasa tana kallon kayan tare da tura baki, harara ya jefa mata ya ce, "Dole ki wanke su!" Yana faɗin haka ya juya zai bar wurin, bin shi ta yi da harara, tunanin abun da zata yi ta fanshe fushinta ne ya zo mata a rai, wata ƴar dariyar gefe ta yi ta buɗe baki ta fara yin waƙa, "Delu ƙanwar maza, ta fi mazan wayau...." Idanunta akan saurayin dake zaune yana cin abinci wanda sam bai kalle ta ba kamar ma bai ji mi take cewa ba, kallon Sageer dake nufar zaure ta yi shima bai bi ta kanta ba, ganin haƙarta bata cimma ruwa ba ya sa ta ƙara ɗaga muryarta mai daɗin sauraro ta ƙara yin waƙar,
"_....Ni Delu ƙanwar maza, duk na fi mazan wayou...._" Tana rufe baki matashin dake zaune yana cin abinci ya kai hannunshi ɗaya ya ciro ƙaton takalmin robar dake ƙafarsa, ɗagowa ya yi tare da saita ta ya jefo mata shi, da sauri ta goce tana dariya, shi kuwa Sageer maimakon ya fice sai ya nufi ƙofar kicin dake gefe, fitowa ya yi hannunsa ruƙe da muciya ya nufo ta yana faɗin, "Yau zaki gaya mani ubanwa kika fi wayou..." Tana ganin abun da ya ɗauko ta yi zumbur ta miƙe, miƙewar da ta yi ainihin suffar jikinta ta bayyana, sam ba gajera bace za a iya kiranta da doguwa, jikinta dum-dum bata da sirantaka sosai, daga wurin ƙugunta ya ɗan buɗe alamar tana da hips ba laifi, hakan ya sa straight gown ɗin jikinta ta fitar da shape ɗin ta gwanin burgewa, nufar wurin ƙofar banɗaki dake wurin ta yi cikin ɗaga murya ta shiga faɗin,
"Wayyo Innarmu! Ga yaya Auwalu da Sageer nan zasu kashe maki ni...." Bada jimawa ba ƙofar ta fara yin ƙara alamar za a buɗe, wata mata ce ta fito daga ciki, a yanayin shekaru zata iya kai shekaru arba'in zuwa da ɗaya, sam jikinta bai nuna manyantaka ba, ta fuska ne zaka ɗan iya fahimtar hakan, tana da tsawo sannan bata da jiki, yanayin fatar ta za a iya kiranta da wankan tarwaɗa, jelar kitson dake a kanta ta sauka a tsakankanin kafaɗunta alamar tana da gashi ba laifi, akwai ɗan yanayinta a tattare da yaran dake wurin duk da tafi mazan haske don su baƙaƙe ne ba kamar Auwalun, shi Sageer ɗin ya ɗan daukko haskenta amman ita kuma Salmar tafi ma uwar haske koma in ce sam kalar fatar su ba ɗaya bane.
Bayan mahaifiyar tasu ta je ta 6oye tana leƙen Sagir da ya tsaya hannunsa ruƙe da muciya ya ɗaure fuska,
"Mi ya haɗa ku da ita?" Innar ta tambaya da ɗan murmushi akan fuskarta,
"Innarmu ba kina jin ta ba, mu sa'aninta ne da zata rinƙa yi ma wannan waƙar!" Ya faɗa cikin fushi,
"To ai da wasa take yin waƙar..." Katse Innar ya yi, "Wllh ba wani wasa, kuma mu ai ba tsaran wasanta bane, kawai don kina goya mata baya ne ya sa duk ta bi ta raina mu, ko Auwalu bata ƙyale ba balle ni, in kuma za a ɗauki mataki a kanta ki hana shiyasa ai take ci gaba da yi ma mutane iskanci." Ya ƙare yana ta hura hanci, daga bayan innar tasu ta leƙo da kyakkyawar fuskarta tana ƴar dariya ta ce, "In haka ne kaima ai ka raina yaya Auwalu ba gashi nan ko yaya baka iya ce mashi..." Bata ƙare maganar ba ganin ya yo kukan kura yana ƙoƙarin kwaɗa mata muciyar, ihu ta saka tare da ƙara ƙanƙame innar tasu kamar zata kayar da ita ƙasa ta shiga fadin, "Wallahi idan ka doke ni sai na faɗa ma aunty Kubra, ka san kuma ba ƙyale ka zata yi ba (Aunty Kubra ita ce wadda ta riƙe ta ta yi karatun primary a wurinta, kuma cousin ɗin innarsu ce, wato mahaifin innarsu yayan mahaifin aunty Kubra ne. Aunty Kubra ita da iyayenta suna zaune a garin Kaduna, saidai mahaifiyarta ta rasu, yayin da ita kuma innarsu iyayenta na zaune a nan garin Funtua, sannan mahaifin aunty Kubra dan boko ne kuma ma'aikacin gwamnati sa6anin mahaifin innarsu Salma da ba ɗan boko bane manomi ne) Dariya innarsu ta shiga yi ta tare Sageer ɗin tana cewa, "Sageer kana da hankali kuwa! Kashe min ita kake son ka yi dama kana ganin ita kaɗai Allah Ya bani yar mace...."
Cikin huci muryarshi da 6acin rai ya ce, "Wallahi innarmu duk ke kika sa ta raina mu, ko muna tare da abokanmu rashin kunya take mana don ta san ba ki bari mu hukunta ta."
Girgiza kai Innar ta yi tana ci gaba da yin dariya ta ce, "Duk fa yadda Salma ta kasance kai ne sila Sageer, nan yarinyar nan ta taso ba ruwanta shiru-shiru da ita magana ma sai ta kama take yi, amman ka dage sai ka canza ta kana ce mata sakarya, ba dama daga waje a yi mata abu ta yi kuka sai ka hau yi mata faɗa kana cewa in bata ramawa sai ka duke ta. Har fa yadda zata rinƙa yin dambe kake koya mata a cikin gidan nan, sai yanzu kuma da ta ɗauki horon ka ta kasance yadda kake so ka ce kuma zaka hukuntata kan hakan?"
Gyaɗa kai Salma da ta leƙo da kanta ta yi alamar atoh, cikin 6acin rai Sageer ya ce, "Amman dai ai ban koya mata ta rinƙa yi ma na gaba da ita rashin kunya ba ko?"
"A'a, ai Salma bata yi ma na gaba da ita rashin kunya, ku ma don kawai ta ɗauke ku kamar abokanta ne shiyasa take maku hakan matsayin wasa, kuma hada ƙarin bata da ƴan'uwa mata sai ku."
Daga bayan Innar Salma ta furta, "Hakane innarmu..." Harara Sageer din ya watso mata ta saka dariya, shi dai Auwalun bai ma ƙara bi ta kan su ba ya ci gaba da cin abincin shi, dama shi ba kamar Sageer yake ba bai cika hayaniya ba sai ta kama, Sageer ne dai sarkin zuciya abu kaɗan ya fara hargowa, ko cikin abokansa baya ɗaukar rainin wayo yanzu ya dambace da mutum gashi yana da ƴar ƙirar ƙarfi a jikinshi saboda yawan ƙwallon da yake yi.
Suna cikin haka aka yi sallama daga bakin ƙofa duk suka kai idanunsu wurin, wani babban mutum ne ya shigo wanda a shekaru ba zai gaza yin arba'in da biyar ba. Malam Bashir ke nan wanda shine jigon wannan iyali, da shi da matar tashi duk ba wani manyanta suka yi ba da yake irin auran wurin nan ne suka yi, mahaifiyarsu tana gama makarantar sakandare ta aure shi lokacin duka bai fi shekaru ashirin da ukku ba, lokacin da ya auri innarsu wato Fiddausy shima ya kammala karatun shi na sakandare, saidai bai ci gaba da karatu ba sai sana'ar kafintancin da yake yi wadda ta kasance gadon gidansu ce, suna da babban gareji da suke yin sana'ar shi da ƴan'uwanshi da kuma mahaifinshi wato kakan su Sageer kafin Allah ya yi mashi rasuwa, da wannan sana'ar da har yanzu ita yake yi yana da ɗan rufin asirin shi da yake kula da iyalinsa kuma daidai gwargwado yana ƙoƙari wurin sauke hakkokin su da ke kan shi.
Hannunshi ruƙe da babbar leda ya shigo cikin gidan, jikinsa sanye da ƙananun kaya riga mai dogon hannuwa da ma6allai da wando irin na magidanta, amsa mashi sallamar shi suka yi ya ƙaraso cikin gidan, kallon saitin da suke ya yi innarsu na murmushi ta ce mashi sannu da zuwa ya amsa, fitowa Salma ta yi ta nufe shi da sauri, a gaban shi ta tsaya tana murmushi ta ce, "Sannu da zuwa babana." Shima murmushin ya yi ya amsa mata, "Yauwa mamana. Ya gidan? Mike faruwa na gan ku kun yi tsaye cirko-cirko?" Satar kallon Sageer da ya ƙaraso wurin tare da innarsu ta yi tana murmushi, maida idanunsa ya yi kan innarsu Salma dake mashi sannu da dawowa, amsawa ya yi tare da kallon Sageer da shima ya ce mashi sannu da zuwa, ganin yadda ya ɗaure fuska kamar bai ta6a yin dariya ba yasa baban nasu tambayar innar mike faruwa,
"Ba komai, kawai ƴan diramar gidan namu ne suka fara." Yana jin haka ya gane Salma da Sageer take nufi don ya san sune koda yaushe cikin rigima suke ko don suna mabiyi da mabiyi,
"Mamana mi ya haɗa ki da yayan naki.?" Dariya ta kama yi tana kallon Sageer da har lokacin ya ƙi ya saki fuska, ganin ta ƙi bashi amsa ya kalli Sageer ya tambayi mi ya haɗa su, cikin 6acin rai ya ce, "Wllh baba yarinyar nan ta raina mu, kuma in muka zo zamu hukunta ta inna ta hana, don ta ga kuna goya mata baya kuna hana a ɗauki mataki a kanta ya sa take ma mutane rashin kunyar da ta gadama." Ya ƙarasa yana hura hanci,
Ƴar dariya baban ya yi jin har da shi ake zargi cikin wanda ke goya ma Salma bayan abun da take yi,
"Mamana faɗa mun abun da kika yi masa." Ya faɗa yana kallon Salma da ɗan murmushi, itama murmushin take ta ce, "Wai daga na yi waƙa, kuma ni da wasa nike..." A fusace Sageer ya ce, "To mu abokan wasan ki ne? In ni kin raina ni kina ɗaukana tsaran ki duk da na baki shekaru shi Auwalun tsaran ki ne? Baba, wannan ƴar iskar waƙar take mana tana cewa wai ko ita kande ƙanwar maza duk tafi mazan wayau...ko a gidan ubanwa ta fi mu wayau, yarinyar da inda ba don na taimaka mata ba da yanzu a sakarya ta taso wllh." Gaba ɗaya suka saka dariya har Auwalu dake can gefe saida ya ɗan dara,
"Mamana mi ya sa kike tsokanar su?" Ɗan kikkafta idanu ta shiga yi tana murmushi ta ce ita da wasa take yi masu.
"Tun da sun nuna basu so ki daina kin ji, koda zaki yi masu wasan ki rinƙa yi masu wanda baza su ga kin yi masu rashin kunya ba, banson ana cewa mamana bata da kunya." Tana yar dariya ta ce, "To babana na daina daga yau." Ya furta yauwa, harara Sageer ya wurga mata ya ce da dai wata ba ita ba, baban nasu ya ce tun da dai ta ce ta bari yasan bazata ƙara ba,
"Ka dawo an ƙi bari ka shiga ciki ma ka huta." Innarsu ta faɗa tana murmushi, amsa mata ya yi da to ya zai yi dole ya tsaya ya kashe wutar da mamanshi ta kunna, nufar wurin ɗakunan suka yi Salma na ruƙe da ledar da ya shigo da shi, yana ƙoƙarin shiga cikin barandar ya kalli Auwalu ya ce, "Auwalu an dawo daga makarantar?" Kai ya ɗaga cikin girmamawa ya ce, "Eh baba, sannu da dawowa."
"Yauwa, to ba a haƙuri a ajiye wayar sai an gama cin abincin a lallatsa, ko kuwa sai ka je ka tura a cikin hanci." Ya faɗa yana ƙoƙarin tsallake tudunkar barandar, duk su Salma suka ɗan yi dariyar maganar tashi, tabarma innarsu ta ɗaukko daga cikin ɗaki ta zo ta shimfida mashi a cikin barandar, bayan Salma ta ajiye ledan, can ƙarshen barandar daga gefen kicin ta nufa, a saman wani tebur dake ɗauke da kwandunan kayan wanke-wanke ta tsaya, bayan ta ɗauki wani ɗan babban farantin roba mai kyau ta wuce cikin kicin, bada jimawa ba ta fito ta ɗauro wata kula da sauran abubuwan dake ɗauke da mahaɗin abincin a sama, gaban baban nasu ta je ta ajiye kafin ta miƙe ta koma ta ɗauko plate da cokali ta kawo mashi, sake miƙewa ta yi ta je ta kawo ruwa, bayan ta ajiye tana murmushi ta ce, "Bismilla babana ga abincinka nan, bari na zuba maka." Jinjina kai ya yi da murmushi, zuba mashi komai ta yi bayan ta gama ta ce to ga shi nan ya ci, godiya ya yi mata tare da saka albarka a nutse ya fara ci.
"Yanzu dai Salma kin hana in rinƙa samun ladan kawo ma baban ku abinci, kullum yana dawowa ke ce zaki sauri ki kawo masa." Innarsu ta faɗa da sigar wasa, Salma na dariya ta ce ai itama ladan take so ta samu kuma itama ba tana samun ladan a wasu abubuwan ba, ko jiya da daddare ai ta yi mashi gugan kayan shi ko,
"Ba wani neman lada, neman suna dai kawai." Sageer ya faɗa yana harararta,
"Kai ka ta6a ganin inda uwa ta yi neman suna a wurin ɗanta?" Babansu da ya dakata da cin abincin ya faɗa, kafin Sageer ya ce wani abu wani ɗan matashin yaro wanda zai kai shekara sha biyar da alama shi yake bi ma Salma ya fito daga can ɗakin dake ƙarshe ya ƙaraso wurin, tsugunnawa ya yi ya ce, "Sannu da dawowa baba." Da murmushi ya amsa mashi, "Yauwa Imrana, dama kana gidan?"
Kai ya ɗaga, "Eh, ina can ina yin Assignment ne ban san ka dawo ba, sai daga baya na jiyo muryar ka." Kai baban ya jinjina ya ce Allah Ya bada sa'a suka amsa da Amin.
"Ina Hamza, da Usman autan baba? Su ban gan su ba."
"Duk suna can suna bacci, shi Hamza tun bayan da ya dawo daga makaranta ya ci abinci ya kama yin bacci, gashi ma lokacin islamiyya ya taho dole ya tashi." Kai baban ya jinjina ya ce ya kwaso gajiyar makaranta ne shiyasa yake bacci, hannu ya kai ya ɗauki cokalin ya ci gaba da cin abincin, miƙewa Imrana ya yi zai tafi, kallon shi Salma ta yi da murmushi ta ce, "Yau ba a gayyata ta yin assignment ɗin.?" Shima murmushi ya yi ɗan kyakkyawa da shi sak komai na mahaifiyarsu ya ɗauko har haskenta, amsa ya bata da assignment ɗin baida wuya ya ga zai iya yi shiyasa bai kawo mata ta nuna ma shi ba, kai ta ɗaga mashi ya wuce.
"Salma da Allah tashi ki je ki wanke mani kayan lokaci na ƙurewa gashi har so nike su bushe."
Yamutsa fuska ta yi, "Allah Sageer ko na wanke su ba lalle har su bushe ba, gara ma kayan, amman wancan murtikekiyar safar bazata bushe ba, kamata ya yi ma a jiƙa ta ta kwana don ta yi dauɗa sosai har wari take yi." Ce mata ya yi to ta je ta wanke mashi kayan sai ta jiƙa safar yana da wata da bata yi datti sosai ba sai ya saka.
"Kowa yana zaune yana hutawa miyasa zaka takura mata ka saka ta wanki a cikin ranar nan." Babansu da ya dakata ya faɗa,
"Ai daman wankin take cikin yi na bata ta haɗa."
Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce ma baban nasu wllh haka yake takura mata ko da ba wankin take ba sai ya kawo kayan ƙwallon shi ya ce sai ta wanke mashi, harararta Sageer ɗin ya yi ya ce a da kafin a rinƙa kai kayanta wanki bashi ke wahalar wanke mata ba...
"Ke nan ba don Allah ka yi ba?" Innarsu ta faɗa tana ƴar dariya. "Don Allah na yi, amman dai dole a rama ma kura aniyarta." Ganin ta ƙi tashi ta je ta yi wankin ya kai hannu zai buge ta ta miƙe da sauri, innarsu ta ce mashi shi yake ja take mashi abu kuma ya zo yana faɗin ta yi mashi rashin kunya, wucewa Salmar ta yi don ta je ta ƙarasa yin wankin.....
*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*
