⚔️🔥ƘARFE A WUTA🔥⚔️
MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
BRIGHT PENS SECOND BATCH
Writer of
Gaba da gabanta
Ƙanwar maza
Cutarwa
Ruɗin ƙuruciya
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on
BISIMILLAHIRAHMANIRAHIM
Labarin ƙarfe a wuta, ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.
Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗
Page 1
Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC.
Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako.
Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.
"Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?"
Cikin ƙulewa wata babbar mace ta ce "Dama wani sakamako ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta taɓa mage ba, abun da na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa, yanzu ta nuna maka ita ƴar kunama ce"
Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da nadamar abubuwan da suke gudana ba a ƙasan ranta, a zahiri ta ce "Ba mummunan sakamako bane ba, abun da ka tarbiyantar da ni a kai ne, gaskiya ita nake tsaye a kai, bani da niyyar cutar da kowa a gidan nan, kowa aikinsa yake yi, yakamata ayi mini adalci, ba a goyi bayansa a nuna ni ce nake kan ƙarya ba, a bari nima na yi nawa aikin"
Cikin tsawa ɗaya matar ta ce "Har wata gaskiya ce da ke.....
Dattijon ya ɗaga mata hannu ya ce "Ya isa haka, tashi ki je, ba na ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin ya dace da ke".
Cikin rauni da tashin hankali ta ce "Abba, ba ka son ganina ka ce?"
"Eh mana, idan har ki na gudun ɓacin raina da fushina, dole ki ba wa ɗan uwanki duk wani cikakken haɗin kai, domin gudanar da aikinsa yadda yakamata"
Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata...? Yakamata a ji ta bakina Abba"
Bai tsaya sauraron mai za ta ce ba, yayi gaba zai bar falon. Cikin matsanancin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta na fashewa da kuka.
"Haba Abbana, me yayi mini saura a duniya, idan har zan rayu ka na fushi da ni, ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce in sha Allah" tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska, tsantsar nadama da damuwa suka mamayeta, ta din ga kuka da sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa ya yi gaba.
Yana barin falon, tamkar mutanen falon za su cinyeta ɗanya, haka suka yo kanta sa surutu, kowa da abun da yake faɗa.
Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.
