Nama ya Dahu - Romo Ɗanye Complete Document

Nama ya Dahu Romo Ɗanye

 NAMA YA DAHU....

      ROMO ƊANYE"

      GAWURTATTU UKU

DAGA ALƘALAMIN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

Lamba ta 1

JIHAR KANO:

Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano itace cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar ta Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba'in da hudu. Kana gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewayenta. Haka zalika  Kano gari ne babba wanda mazauna cikinta ke magana da harshen Hausa. Itace gari mafi yawan jama'a a Najeriya baki ɗaya.

Kanon ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.

Yawan mutanen da suke garin na Kano sun haura kimanin mutane miliyan goma (10.000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida. Jihar Kano tana da matuƙar tasiri a yawan mutane Najeriya, saboda ita ce ta fi kowacce jiha yawan mutane daga ko'ina a faɗin duniya, tun daga na  kudancin Najeriya, har zuwa ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya,hakq kuma za ka tarar da mutanen sin ( wato china) da kuma na ƙasashen larabawa har da turawan yammacin duniya mutanen Kano sun shahara wajen addini sosai.


Domin Sauke wannan littafin taɓa mahallin da aka rubuta DOWNLOAD a ƙasa👇👇

  

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post