Acikin Rayuwa Book 1 page 1 by Zee Bature

 

Acikin Rayuwa

Boss Ladies Writers 

 *Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai*

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), Mai kowa, Mai komai, wanda Ya bani ikon fara wannan sabon littafi nawa mai suna “A Cikin Rayuwa.”

Ina roƙon Allah Ya sa littafin nan ya amfane ni da ku gaba ɗaya,

Ya Ubangiji, Ka bani ƙwarin gwiwa da nutsuwa; yadda muka fara lafiya, Ka sa mu kammala a cikin ƙoshin lafiya. Allah Ka kiyaye ni daga rubuta abin da zai cutar da ni ko da al’umma baki ɗaya.

Ameen.

*BAYANI NA MUSAMMAN (Disclaimer)*

Labarin nan ƙirƙirarren labari ne, ba na gaske ba. Duk wani suna, wuri, ko yanayi da ya yi kama da na ainihi, hakan ya faru ne bisa bazata, ba da niyya ba. Na rubuta wannan littafi ne da nufin isar da saƙo game da rayuwa, soyayya, ƙaddara, da darasin da ke tattare da su, ba don nuna wani mutum ko abin da ya faru a zahiri ba. Idan wani ya karanta littafin ya ga wani abu da ya yi kama da shi ko da rayuwarsa, to hakan ba wai na nufin shi ba ne, domin ni ɗan’adam ce, ba ni da ikon sanin yadda rayuwar wani ke gudana sai dai abin da Allah Ya bani damar hasashe a kai. Manufar littafin ita ce bayyana darasi, motsa tunani, da kawo haske cikin tafiyar rayuwa, ba don cin zarafi ko kushe kowa ba.



*Godiya ta Musamman*



Jinjina ta musamman ga ƴan ƙungiyata, Boss Bature, QueenMarh, da Hafsat Amjad.

Nagode da goyon baya da kalaman ƙarfafa gwiwa a koda yaushe. May Allah continue to unite our hearts and raise *BossLadiesWriters* higher. Ameen.



Wannan littafi tukuici ne gare ki, *Mommy Kubrah*.

Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, Ya bar mana zumunci har Aljanna.



_Beloved sis, Hafsat Bature, your support means everything to me._


_There are no words enough to express my gratitude, all I can say is, may Allah bless and strengthen you always._



Ya Rabb! Bless and have mercy on all mothers, especially my mother. 🤲❤️


_My P.A, Munarh Bature, a ɗaura damarar komawa fagen daga, let’s go again!_




*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*



_By Zainab Bature (Zeelaluh)_



CHAPTER ONE



Farkon Tafiya



_A cikin rayuwa, wasu abubuwa ba su faruwa a bisa kuskure, sai don a koya mana darasi._

_Bata san cewa ƙaddararta za ta haɗa ta da wani da duniya ke kallon sa a talabijin ba._

_Amma kafin soyayya ta zamo haske a gare ta, dole ne ta ratsa cikin duhun da rayuwa ta tanadar mata, duhun da ke ɗauke da sirri, hawaye, da ƙaddarar da za ta canza mata rayuwa har abada....._



Kaduna State,


Saturday, 10:00am



Babbar harabar makarantar cike take da mutane, kasantuwar yau ne suke yin bikin yaye ɗalibai da bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi ƙwazo (speech and prize giving day). Mahalarta taron sun haɗa da iyaye da ƴan'uwan yaran da suka gama karatu a matakin primary da kuma secondary, saura sun haɗa da manyan baƙi da aka gayyata ciki har da masu manyan muƙamai a gwamnati. Duk da makarantar bata gwamnati bace mai zaman kanta ce (private school) amman kana gani kasan babbar makaranta ce, tana  da tsarin gini mai matuƙar kyau da kuma bangarorin karatu ukku, (Nursery, Primary, Secondary). Gaba ɗaya mahalartan suna zaune a cikin manyan rumfuna da aka kafa a bangarorin babban filin makarantar, bangaren da iyaye tare da ƴan'uwa da abokan arziki suke daban, haka manyan baƙi suna a bangare na musamman an tanadar masu da abubuwan ci da sha a saman teburan dake gaban manyan kujerun da suke zaune, daga cikin manyan baƙin akwai matar kwamishinan ilimi na jahar Kaduna mai suna Hajiya Aisha, da wasu daga ma'aikatar ilimi ta jahar. Iyaye da ƴan'uwan ɗaliban da ke karatu a makarantar kowa ya yi shiga ta alfarma wadda kallo daya zai bayyana maka kowa yana da hali daidai da nasa, kasantuwar karatu a makarantar na da kuɗi ba laifi, amman kuma  makarantar na bada ilimi sosai. Suma ɗaliban makarantar suna a cikin rumfa daban, gaba ɗayansu suna sanye da kayan makarantar, yayin da ɗaliban da ake yayewa suke zaune daga gaba kowanne na sanye da uniform na makarantar daga sama sun daura rigar da ke nuni da sune suka kammala karatu (graduation gown and cap). 


Kowa ya natsu yana kallo da saurar diramar turanci da wasu daga cikin ɗaliban suke gabatarwa kan muhimmancin ilimi, a diramar gidan wani magidanci ne dake da mata ɗaya da kuma yara mata guda biyu Fa'iza da Maryam, sai dai ba uwa ɗaya ta haife su ba su duka, matar gidan ta kasance tana gatanta wadda itace ɗiyarta da ta haifa wato Fa'iza, komi yarinyar take so tana yi mata, yayin da ɗayar da ba a so mai suna Maryam mahaifiyarta ta rasu a wurin haihuwarta take fuskantar tsangwama da ƙyara, sai mahaifinta na gida ne take samun ɗan sassauci don shi yana matuƙar son ta da tausaya mata, duk da shima ba wani katabus gare shi ba a gidan. Haka ake ɗaura ma wadda ba a so talla safe da yamma duk da ta kasance tana matuƙar son yin ilimi amman an hana ta zuwa makaranta, saboda aminiyar matar babanta da ke ruƙonta ta bata shawarar kada ta sake ta bari yarinyar ta yi karatu, a cewar ƙawar tata yadda take tubarkalla kyakkyawa idan ta yi karatu ta goge to ƙarshe ba ƙaramin mutum ne zai aure ta ba. Duk wasu aikace-aikacen gidan ita ce take yin su, idan ka ganta ba wata suturar kirki haka wurin kwanciyarta a ƙasa ta ke kwana saman wani ɗan mataccen zani, duk da cikin gadon kayan mahaifiyarta da ta samu har da katifa amman an hana ta kwanciya a kai. Saboda son karatun da take yi ne yasa duk idan aka ɗaura mata talla da safe ta kai wata makaranta, sai ta je bakin tagar wani aji tana sauraren abubuwan da ake koya masu, wani lokacin idan aka yi tambaya ma ita ce take bada amsa daga waje, wannan dalilin ya sa wani malamin turanci ya rinƙa siye abun da take sayarwa ya raba ma ɗalibai ita kuma sai ya saka ta shiga cikin ajin ta zauna don ta faɗa masa halin da take ciki a gidansu da hana ta karatun da aka yi, daga baya ganin irin ƙoƙarin ta ya sa malamin ya tunkari shugaban makarantar da lamarinta. Da taimakon shugaban makarantar da malamin suka sa ta fara yin karatu kyauta. Saboda ƙwazonta bayan gama karatun ta na primary ta samu tallafin karatu (scholarship) daga gwamnati har zuwa jami'i zata yi karatu kyauta. A ƙarshe ta yi nasarar zama ƙwararriyar likita, yayin da ƴar'uwarta Fa'iza ta saka shiririta da yawon bin maza har ta yi cikin shege wanda mahaifiyarta da ƙawarta suka yi ƙoƙarin zubar da shi kamar yadda suka saba yi mata amman ya ƙi zubewa, ƙarshe ta haɗu da lalura bayan ta haife cikin ba rai, yar'uwarta Maryam da ta zama likita ita ta yi mata aiki har ta samu lafiya, ita ta gina masu gida take kuma tallafa ma rayuwar su. A ƙarshe suka ƙare da yin kukan dana sani.


Bayan gama yin diramar mutane suka shiga tafa ma ɗaliban kan irin ƙoƙarin da suka yi diramar ta tafi daidai ta yi ma'ana sosai, da kuma musamman yadda suka rinƙa yin magana da turanci cikin gwanancewa ba tare da wata tangarɗa ba, ɗalibar da ta fito a matsayin Maryam wato wadda ba a so mai suna SALMA BASHIR, ta fi samun yabo a wurin mutane ganin duk da ƙananun shekarunta don bata wuce shekara sha biyu ba amman ta nuna ƙwazo sosai a diramar. Bayan gama diramar an ci gaba da yin programs daban-daban na ilimi kuma kowanne akwai dalibar nan mai suna Salma Bashir wadda ta kasance kwakkyawar gaske, kanta na sanye da hular rigar kammala karatun jikinta, tana da gashi mai tsawo sosai don kitson da aka yi mata na gaba ya sauko har zuwa ƙirjinta. Abu na ƙarshe da aka yi shine bada kyaututtuka ga ɗalibai masu ƙwazo, Salma Bashir ta samu kyaututtuka da dama ciki akwai ta ɗalibar da ta fi ƙwazo a matakin primary, akwai ta bajinta da ta yi a diramar da aka yi kan ilimi, sannan a bangaren english club ɗin makarantar an bata kyauta cikin daliban primary masu ƙwazo a bangaren debate da quiz, haka a bangaren wasanni wato sport nan ma ta samu kyauta. Kyauta ta ƙarshe da za a bata aka bayyana matar kwamishinan ilimi hajiya Aisha a matsayin wadda zata bata kyautar, bayan Salma ta je gabanta, hajiya Aisha tana murmushi ta fara miƙa mata hannunta da ya sha gold suka yi musabaha ta ce, "Congratulations, Salmat. Keep working hard and stay focused, the sky is your limit." Jinjina mata kai Salma ta yi da faffaɗan murmushi akan fuskarta ta ce, "In sha Allah. Thank you maa." Jinjina mata kai Hajiya Aisha ta yi da murmushi akan fuskarta, bayan ta bata kyautar ta dakatar da ita, ta juya tare da miƙa ma ƙawarta da suka zo tare suke zaune a wuri guda hannu, buɗe jaka matar ta yi ta fiddo rafar kudi yan dubu guda biyu wato dubu ɗari biyu ta miƙa mata, hajiya Aisha ta ɗaura ma Salma a saman kyautar ta ce mata itama ga tata kyautar nan, gaba ɗaya wurin aka saka tafi masu ɗaukar hotuna da vedio suna ta ɗaukar su, godiya Salma ta yi mata ta juya ta koma wurin zaman ta, bayan hajiya Aisha ta koma ta zauna ƙawarta hajiya Zulaihat tana murmushi ta ce, "Yarinyar ta burge ni sosai, ga kyau ga ƙwaƙwalwa. Da ta zo gaban ki sai na ji inama a ce ɗiyar ki ce don har ɗan yanayi na ga kun yi." Murmushi hajiya Aisha ta yi don ta san dalilin yin maganar tata, bai wuce sanin cewa Allah bai bata ɗiya mace ba sai maza, sai dai itama a cikin ranta ba ƙaramin burgeta yarinyar ta yi ba har ta ji sha'awar inama a ce Allah Ya bata ɗiya mace kamar ta. 


Bayan kammala taron mahaifiyar Salma wadda ta kasance farar mace sannan tana da ɗan jiki amma ba sosai ba, yanayin ta bata da tsawo amman kuma ba gajera bace, tana sanye da wani haɗaɗɗan lace, tun daga wuyanta zuwa hannunta zinari ne, kana ganin ta ka ga wayayyar mace ƴar boko, ta rungume Salma jikinta cike da farin ciki tana yaba mata kan ƙwazon da ta nuna a wurin, muryarta da tsananim farin ciki take faɗin, "I am really proud of you my baby. Allah Ya raya min ke ya ci gaba da albarkantar rayuwar ki. In sha Allahu sai kin zamo abun alfahari ga kowa, ina jin hakan a raina." Ɗagowa Salma ta yi da murmushinta mai burgewa ta ce, "Thank you my aunty Kubra, nima ina alfahari da ke." Ƙara rungume ta ta yi tana jin ƙaunar yarinyar na ƙara ninkuwa a cikin ranta, ƙawar aunty Kubra da suka zo tare mai suna Naja'atu itama ta kamo Salma jikinta ta taya ta murna tare da bata kyautar da ta kawo mata, ta yi mata addu'oin fatan allkhairi a rayuwarta. 



"Aunty, daddy bai zo ba? Ban gan shi ba." Salma ta tambaya tana kallon Aunty Kubra da farin cikin dake kan fuskarta ya ɗan canza jin tambayar da Salma ta yi, ganin Salma ta kafe ta da ido alamar amsar ta take jira ta yi ɗan murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Wani uzuri ne ya taso masa bai samu zuwa ba, na san idan muka koma gida zai taya ki murna." Kai Salma ta jinjina tana murmushi, kallon juna suka yi ita da Naja'atu, ganin fuskar Kubra ta nuna alamun damuwa ta ɗan girgiza mata kai alamar kada ta yi hakan. Bayan gama komai suka nufi wurin da aunty Kubra ta faka motarta, a seat ɗin baya aka saka kyaututtukan Salma, aunty Kubra ta shiga mazaunin driver, Naja'atu ta zauna a kujerar gaba yayin da Salma ta zauna baya. Bayan sun hau hanya, akai akai Salma take kallon kyaututtukanta farin ciki ya bayyana a kan fuskarta, ta cikin madubin motar aunty Kubra ke ta kallonta yayin da a daidai wannan ga6ar ita kaɗai ta san abun da ke kai kawo a cikin zuciyarta. "Da alama kin ji daɗin kyaututtukan da kika samu ko baby?" Da sauri Salma ta kalli Aunty Naja'atu da ta juyo ta yi mata maganar, kai ta ɗaga mata tana yin ƴar dariya, aunty Naja'atu ta ce mata haka nasara take kawo ma mutum alkhairai don haka ta ci gaba da bada himma kan karatunta, Salma ta amsa mata da in sha Allah. Ba gida kai tsaye suka wuce ba, wani babban shopping mall aunty Kubra ta kai Salma ta ce ta zabi duk abun da take so, itama ta zabar mata wasu abubuwan, aunty Naja'atu ma ta ƙara siya mata wasu kyaututtukan, daga nan wani eatery mai kyau suka wuce suka ci abinci aunty Kubra ta yi ma Salma takeaway ɗin small chops da su ice cream kafin suka wuce gida.



Misalin ƙarfe tara na dare Aunty Kubra ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin, tana sanye da doguwar rigar bacci kanta ta saka hula, idonta akan Salma dake kwance a saman gado tana sanye da kayan bacci riga da wando da kuma hula a saman kanta, kitson gabanta sun ɗan rufe mata gefen fuskarta da ta ɗaura jikin ƙaton teddyn da ɗazun aka siya mata a mall, a bakin madaidaicin gadon kalar na yara aunty Kubra ta zauna tana ci gaba da kallon Salma da ke yin bacci hankali kwance, ta ɗan dauki lokaci tana kallon fuskarta yayin da a cikin zuciyarta ba abun da take yi face kukan zuci, yanzu shike nan dole ta rabu da yarinyar nan ta mayar da ita wurin iyayenta, dama tamkar ara mata ita aka yi saboda tsananin ƙaunar ta da take yi, gashi wa'adin da ta ɗauka na ruƙonta ya cika, ko ba haka ba, dole ta haƙura ta maida ta wurin iyayenta ko don saboda yawan sa6anin da zamanta ke haddasa masu da mijinta, ƙiri-kiri yake nuna yana yin kishi da yarinyar, a cewarsa Kubra ta fi fifita yarinyar fiye da kula da shi, ko da yaushe a cikin ƙorafi yake kan tafi bawa abu biyu muhimmanci, wato aikinta na asibiti kasantuwar ta babbar nurse, sai kuma Salma, a cewarsa koda yaushe idan tana gida to lokacin ta na Salma ne ba shi ba. Ta san duk ba komai bane ya sa take matuƙar ƙaunar yarinyar face haihuwa da Allah bai ta6a bata ba gashi har ta ɗan fara manyanta, idanunta ne suka ciko da ƙwalla, daga baya ta kifa kanta a saman gadon tana yin kuka a hankali, da sauri ta ɗago bayan ɗan lokaci jin an dafa mata kai, suka haɗa ido da Salma wadda ta farka tana kallonta da idanunta dake ɗauke da bacci, "Aunty Kubranah mi aka yi maki kike kuka?" Salma ta tambaya da muryarta da bacci bai saka ba, da sauri Kubra ta kai hannu tana share hawayen fuskarta tare da gyara zamanta, ɗan murmushi ta yi mata ta ce, "Ba abun da aka yi mani baby, ba kuka nake yi ba." Salma ta bita da ido ta ce, "Ba na ji kina yin kuka ba, kuma har kina share ƙwalla. Daddy ne ko?" Fuskar Kubra kamar zata ci gaba da yin kukan ta girgiza mata kai alamar a'a, "To don Allah autynah tell me, mi yasa kike yin kuka?" Ta kai maganar itama kaman zata fara yin kukan, ta san idan har bata faɗa mata ba itama kukan zata yi, hakan ya sa ta ƙara matsawa tare da kamo hannunta, cikin karyayyar murya ta ce, "Ba wani abu bane baby, kawai na ji har na fara missing ɗin ki ne, za ki tafi ki bar ni." Ɗan shiru Salma ta yi tana kallonta, sai kuma ta ce, "To idan baki son in tafi zan zauna nan ba zan koma ba." Da sauri ta girgiza mata kai, "No baby, iyayenki da ƴan'uwanki suma suna son ki a kusa da su, idan baki koma ba zan zama mai son kai, ke kan ki rayuwarki a nan cikin kaɗaici kike yin ta, koda yaushe daga ni sai ke, ga zarya da nike yi da ke wani lokacin sai dai in tafi da ke asibiti wani lokacin in kai ki gida, can kuwa kin ga kina da ƴan'uwa, zaku yi wasa ku ci abinci tare ku yi hira, gara ki koma cikin ƴan'uwanki don suma suna muradin ki a kusa da su, musamman Sageer, duk muka yi waya kin ga sai ya tambayi yaushe zaki koma." Shiru Salma ta yi tana kallonta, aunty Kubra ta ci gaba da kwantar mata da hankali, a hankali Salma ta ce, "To ki daina yin kuka aunty Kubra, ai zan rinƙa zuwa hutu nan, kuma zamu rinƙa yin waya har da vedio call." Da sauri ta ce mata ta bari ba zata ƙara yi ba, ɗan yatsa Salma ta miƙa mata ta ce ta yi mata promise ba zata ƙara yin kuka ba, faffaɗan murmushi Kubra ta yi, har da irin yadda yarinyar itama ta damu da ita ke ƙara mata ƙaunarta, yatsanta ta bata suka yi promise ɗin, tambayarta Salma ta yi daddy ya zo ta ce mata a'a yau ba nan zai kwana ba, Salma ta ce, "To ki kwanta a nan." Aunty Kubra na murmushi ta ce, "To ai zan takura maki kin ga gadon ƙarami ne, sai dai mu je can ɗakina mu kwanta." Salma ta ɗaga kai, dama duk idan ba a gidan mijin aunty Kubra ɗin zai kwana ba da yake yana da wata matar, a ɗakin aunty Kubra suke kwana, safkowa suka yi don tafiya bedroom din nata, aunty Kubra ta duƙa ta ce ma Salma ta hau bayanta, dariya Salma ta saka tare da hayewa saman bayan nata, bayan ta miƙe Salma dake ta dariya ta ce, "Aunty Kubra har yanzu wai ba ki jin nauyi na da kike goya ni?" Tana dariya itama yayin da take nufar kofa ta ce, "Ko kin fi haka zan goya ki babyna." Daɗi ya kama Salma ta kwantar da kanta saman bayanta daga haka suka fita.





Five years later (bayan shekaru biyar....)



Abuja Nigeria.



Nnamdi Azikwe International Airport.



Wednesday, 11:30am




Iskar safiyar laraba tana kaɗawa cikin natsuwa, a hankali gudun private jet ɗin da ya sauka ya fara ragewa yayin da yake yin tafiya akan hanyarsa, hasken ranar da ya haske jikin farin jirgin ya sa shi sai sakin sheƙi yake. A gefe guda cikin tarmac ɗin wasu mutane ne a tsaitsaye, wanda daga gani tarbar wani suka zo kuma mutanen masu matsayi ne kasantuwar ba kowa ake bari ba ya je wurin da jirgi ke sauka.



A hankali ƙarar jirgin ta fara raguwa, yayin da yake neman tsayawa, bayan da jirgin ya tsaya sai da aka ɗan dauki lokaci kafin ƙopar shi ta fara sauka a hankali tana buɗewa, jim bayan ɗan lokaci a nutse wani matashin saurayi ya sako kai waje daga cikin jirgin, dakatawa ya yi a bakin ƙopar jirgin ya ɗan ɗaga kansa tare da lumshe idanunsa ta cikin baƙin gilashin fuskarsa, wai aka ce komai daɗin wuri gida daban ne, a hankali ya buɗe idanunsa wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali yake ji na ziyartarsa. A yanayin halitta, matashin saurayin dogo ne amman ba irin tsawon da ya wuce misali ba, fatar shi fara ce tas irin farin nan mai tafiya bai ɗaya, daga fatar tasa zaka fahimci hutu ya zauna masa sosai yadda take sumul, yana da kyawun fuska wadda da idanu sun kalla zasu shaida hakan, kwantaccen sajen dake zagaye da fuskarsa ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tasa, duk da gashin baida cika sosai wanda hakan ya sa ana iya ganin ɗan lotsawar da gemun shi ya yi wato yana da chin dimple, sumar kansa da gani tana da tsawo yadda aka yi baya da ita ta kawo har saman wuyansa baƙa wuluk da ita sai sheƙi take alamar ta sha gyara, a jikinsa yana sanye da tailored suit farare ƙal, maƙale a jikin wuyan kayan bow tie ne kalar green mai ɗan duhu haka a jikin aljihunan jacket ɗin kayan nan ma an yi adon kalar green, daga jikin ƙasan zagayen hannun kayan nan ma akwai ratsin green, ƙafafunsa na sanye da haɗaɗɗun rufaffun fararen takalma, haka wutsiyar hannunsa na ɗaure da rantsattsar farar agogo, saman kan agogon sai sheƙi yake yana ɗaukar ido tare da bada launin green.



 Shin wanene wannan matashin mai cikar halitta da ya gaji da haɗuwa?



NURADDEEN IBRAHIM AMBASSADOR ke nan, wanda fitacce kuma ƙwararran ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai ne dake buga wasa a babbar ƙungiyar ƙwallon kafa ta IMPERIAL LONDON FC (ILFC) dake a England. Asalin tushen shi ƙasar Nigeria ne duk da ba anan aka haife sa ba, mahaifinsa Alhaji Ibrahim Nuraddeen ɗan asalin jahar Katsina ne haifaffen garin Funtua. Kakansa marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador ɗan asalin garin Funtua ne wanda tushen family ɗin su babban family ne da suka yi gadon arziƙi a garin. A lokacin da Alhaji Nuradden na raye ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje wato Ministry of Foreign Affairs inda ya yi aiki a wasu ƙasashe da dama har ya kai matakin ambasada kafin ya yi ritaya. Yaran Alhaji Nuradden da ya haifa biyar amma ukku ne yanzu ke raye a duniya, Alhaji Sa'ad shine babban ɗan shi wanda yanzu haka yana zaune a garin Funtua tare da iyalinsa. Alhaji Sa'ad ya gaji mahaifinsa ta bangaren aiki in da shima ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje har zuwa yin ritayarsa, yanzu yana harkar kasuwanci da kuma noma wanda dama gadon family ɗin su ne. Mahaifinsu wato Alhaji Nuradden Ambassador lokacin da yake raye babban manomi ne da ya mallaki manya da ƙananun gonaki a sassa daban-daban a cikin ƙasar nan, suna da ma'aikata da dama dake aiki a ƙarƙashin su, yayin da wasu gonakin nasu kuma ake yin hayar su. A duk shekara ba ƙaramin noma ake yi a gonakin nasu ba, akwai gonakin da irin su auduga kawai ake nomawa da waɗanda ake noma sauran abubuwa daban-daban, kuma musamman akwai manyan kamfanoni da ke siye amfanin da aka noma da zarar an gama wanda ba ƙananun kuɗi suke samu ba. Bayan noma kuma suna yin kiwo a manyan gidajen gonakin da suka mallaka.



Alhaji Sa'ad yana da yara shidda, Fahad shine babban ɗansa wanda yanzu haka likita ne dake aiki a Zaria, daga shi sai Sadeeya tana karatu a ABU Zaria, akwai Ibrahim suna ce masa Khalil sai Abubakar Sadeeq da Fatima suna ce mata Binafa sai auta Muhammad Ayden.


 

Alhaji Ibrahim shine na biyu wanda yanzu haka ɗan majalissar tarayya ne dake zaune a garin Abuja shi da matarsa Hajiya Jameela suna da yara guda biyar, Nuraddeen wanda ya ci sunan kakansu shine babba sai Omar da Haleema suna ce mata Leemarh don sunan kakarsu ta wurin uwa aka saka mata wato mahaifiyar Hajiya Jameela, sai Sa'ad wanda ya ci sunan yayan mahaifinsu suna ce mashi Sultan sai autar su Fateema wadda ta ci sunan kakarsu ta wurin uba suna ce da ita Batool.



Aunty Murja ita ce ta ukku, Malamar Jami'a ce tana aure a garin Kano tana da yara ukku, biyu mata sai namiji ɗaya.



Hajiya Binta ita ce matar marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador wadda yanzu haka take zaune a cikin garin Funtua, ta kasance dattijuwa mai matuƙar kirki da karamci, tana da mutunci sannan ga alheri musamman ga mutanen da take rayuwa da su, ta kasance a koda yaushe burinta ta saka farin ciki a cikin zukatan al'umma musamman marasa ƙarfi, mutanen gari suna yi mata laƙabi da Hajiyar Ambasada haka ƴan cikin unguwar da take suna kiran gidanta da gidan Hajiyar Ambasada.



Dangane da yadda Deen ya zamo ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai kuwa, akwai ƙanwar mahaifiyarsa mai suna Aunty Safnah da suke zaune a London ita da mijinta Maleek sai ɗiyarsu guda ɗaya Basma wadda ita kaɗai ce Allah ya basu. Maleek ya kasance babban abokin mahaifin Deen wato Alhaji Ibrahim, ta sanadiyar abotar su ne har   ya haɗu da ƙanwar Hajiya Jameela ya aureta. Maleek ya kasance ƙwararren injiniyan fasaha da ya mallaki babban kamfani a birnin London, tun bayan da Deen ya kammala karatunsa na ƙaramar  secondary anan Nigeria ya koma wurin su da zama, bayan saka shi a makaranta don ƙarasa karatunsa na secondary,  lokacin malamansu suka fahimci yana da baiwar ƙwallo, don yadda yake bada himma a kan ƙwallo baya ba karatu himma, hakan ya sa malamin su na wasanni ya fara magana kan idan aka goya mashi baya zai zama babban ɗan kwallo har suka tuntu6i mahaifinsa  mai ruƙonsa wato Maleek, bayan ya tuntubi Deen don jin ra'ayinsa, ya nuna masa yana son zama ɗan ƙwallo, hakan yasa Maleek ya tsaya masa da taimakon malamin nasu aka maida shi makarantar koyon ƙwallo, cikin lokaci ƙankani ya fara samun ƙwarewa sosai. Tun yana buga kwallo a junior team har ya koma yana bugawa a senior team, yana a shekara 17 ya yi signing da babbar kungiya ta farko da ya fara buga ma wasa a nan London, daga baya ya koma wasu kungiyoyi biyu har kawo kungiyar da yake buga ma wasa a yanzu, wadda Tsohuwar ƙungiya ce kuma sananna. Laƙabin da ake yi ma ƴan kungiyar shine The Imperials ko The Lions of London, suna da babban filin wasa mai ɗaukar dubbanin mutane mai suna Imperial Crown Stadium. Yanayin launin rigarsu ta gida wato jersey shine fari da ratsin golden wanda ke nuna daraja da iko, rigarsu ta waje kuma tana da launin baki da ja, sai kalar rigarsu ta ukku mai launin shuɗi mai duhu. Kungiyar Imperial London FC ta samu manyan nasarori masu tarin yawa daga manyan gasannin ƙwallo, an san su kuma da yin kasafin kudi mai tsada wajen sayen fitattun ƴan wasa daga ko'ina cikin duniya. Sannan club din na da salon suna mai ɗauke da alamar ƙarfi, mulki, da tarihi, irin wanda ke  da alaƙa da masarautar Birtaniya.




Ba ƙaramar shahara Deen ya yi ba a harkar ƙwallo don ya iya ta sosai ya san duk wasu dubarun cin ƙwallo, mutane na kiran sa da ɗan baiwa, da wuya ka ga an yi wasa da ƙungiyarsu bata ci ba saboda ta haɗa zaratan yan ƙwallo, hakan ya sa ƙungiyarsu tana ɗaya daga cikin wadanda ake jin shakka. A shekaru Deen ba wani babba bane don bai wuce 26 ba, sai dai in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun sosai saboda ƙirar jikin shi irin ta zaratan ƴan kwallo ce.



Wannan ke nan game da fitaccen jarumin ɗan ƙwallo, wanda a duniyar ƙwallo aka fi sani da DEEN JR. Wasu kuma suna kiran shi da NUREE JR.




Cigaban labari.....




Maida idanunsa ya yi kan mutanen da suka zo tarbarsa, a hankali ya saki wani ƙayataccen murmushi tare da gyara zaman jacket ɗin shi kafin a nutse ya fara taka matattakalar jirgin yana saukkowa cikin aji, daga yanayin shigar kayan jikin shi zaka fahimci ya yi shigar ne don nuna girmamawa da kuma ƙauna ga ƙasar shi don kayan na ɗauke da kalolin tutar ƙasar Najeriya ne wato kore da fari. Daga yanayin yadda kayan suka amshi jikinsa zaka fahimci musamman shi aka ƙera ma kayan kuma ba ƙaramin kyau shigar ta yi masa ba. 



Tun kafin ya ƙaraso ƙannansa Leemarh da Batool suka rugo wurin sa, ganin su ya sa shi ware masu hannu yana sakar masu murmushinsa mai saka mutum shagala wurin kallon sa, ɗan rankwafawa ya yi lokacin da suka ƙaraso jikinsa ya haɗe su tare da rungume su, ɗagowa ya yi suna kallon juna cikin washe masa baki suka furta, "You are welcome big bro." Amsa masu ya yi. "Thank you my lovely sisters, Leemarh and Batool, I'm so glad to see you guys." Suna ta washe baki suma suka ce sun ji daɗin ganin shi, Leemah wadda ke da ɗan tsawo ta kai hannu ta cire glasses ɗin da ya rufe idanunsa, tsarki ya tabbata ga ubangijin da ke tsara halitta, abun da na ayyana a raina ke nan a lokacin da na yi tozali da kyawawan manyan idanunsa da suke farare tas tamkar an ɗiga zaiba, ƙwayar cikin su baƙa ce wuluk har sheƙi take yi. Kama hannuwansu ya yi suka nufi wurin sauran mutanen. A cikin waɗanda suka zo tarbar shi akwai mahaifinsa Hon. Ibrahim Nuraddeen Ambasada sai mahaifiyarsa Hajiya Jameela da sauran ƙannansa, ministan wasanni na tsaye daga gaba cikin shigar baƙaƙen suit, tare da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF President), sai jami'an ƙwallon ƙafa, akwai wakilan wasu manyan kamfuna dake da alaƙa da harkar wasanni, sai manyan ƴan jarida da kuma shuwagabannin ƙungiyar matasa masu son ƙwallon ƙafa. Suna isowa wurin sauran mutanen ya saki hannuwan ƙannan nasa ya nufi mahaifinsa dake ta sakin murmushin farincikin ganin tauraron ɗan nasa, rungume juna suka yi dad din ya furta, "Welcome home, son." Ya yi maganar yana shafa bayan shi, ɗagowa Deen ya yi yana murmushi ya yi ma mahaifin nashi godiya tare da furta yana farin cikin ganin su, cike da jin daɗi Dad din ya furta suma sun yi matuƙar farin cikin ganin sa, maida idon shi ya yi kan mahaifiyarsa dake gefe ta yi shiga ta hamshaƙan manyan mata, doguwar rigar rantsattsiyar lace ce Abuja boubou a jikinta ta soke ɗaurin kallabi ya zauna daram akanta, saukar da gyalenta ya yi saman kafaɗa ya bayyana yalwataccen gashinta dake tufke ƙasan kanta, lokacin da idanuna suka sauka a kan fuskarta har saida na furta Ma sha Allah ganin irin tsantsar kyawun halittarta, mace ce irin giant ɗin nan wato tana da tsawo da jiki, gata fara ce jajur da ita sannan ta bangaren fuska abun ba a magana don irin matan nan ne masu manyan kyau wanda kana kallon su ko ka hango su tun daga nesa zaka shaida kyawun su, tana da manyan idanuwa da dogon hanci wanda daga ƙasa ya ɗan yi faɗi kaɗan, haka bakinta ma madaidaici ne da zanen labbanta suka fita raɗam, daga yanayin gashin girarta ma zaka fahimci tana da yalwatacciyar suma, ɗan ɗigon baƙin dake gareta a gefen gemunta ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tata, gaba ɗaya tun daga wuyanta, kunnuwanta zuwa hannuwanta duk gold ne. Hajiya Jameela ta kasance jinsin mutanen nan da ake kira da sadakar yalla, mahaifinsu Deen ya auro ta ne daga jahar Kano wanda asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane.



Wani kallo Mom ɗin nasa ta yi mashi mai kama da harara, murmushi Deen ya sakar mata don ya fahimci dalilin kallon saboda ba ita ya fara runguma ba, nufar ta ya yi ya ɗan rungumo ta tare da fadin, "I missed u sweetheart." Murmushi ta saki, ya ɗago suka haɗa ido shima da murmushi akan fuskar tasa ta ce, 


"Welcome home, my pride." Godiya ya yi mata kafin ya ɗaura idanunshi akan ƙannansa Omar da Sultan, duk suka yi mashi sannu da zuwa cikin nuna farinciki duk ya rungume su, wurin ministan wasanni ya nufa, cikin washe baki ministan ya ba Deen hannu suka gaisa, cikin nutsattsiyar muryar shi mai taushi da daɗin sauraro ya ba ministan haƙuri kan rashin zuwa wurin su da wuri, da fara'a ministan wanda kirista ne ya furta, "Don't worry, first things first, and family is always first." Gaba ɗaya mutanen wurin suka yi murmushi tare da jinjina kai alamar gamsuwa da abun da minista ya faɗi, cikin nuna farin ciki NFF President ya ba Deen hannu tare da faɗin, "Nigeria is proud of you. Welcome home our champion." Da murmushi Deen ya yi masa godiya, haka duk ya gaggaisa da sauran mutanen suka yi masa barka da zuwa tare da nuna farin cikin ganinsa da yabon shi kan irin ƙoƙarin da yake yi a harkar ƙwallon ƙafa, ƴan jarida nata ɗaukar su hotuna da vedios. Sun ɗan dauki lokaci suna gaisawa da yin hotuna, kafin daga baya suka nufi hanyar barin tarmac ɗin wasu daga cikin security personnel ɗin Dad ɗin sa ne suka jawo jakunkunan kayansa da aka fito da su. Suna cikin tafiyar ne minista ke ƙara jinjina ma Deen Jr. kan irin ƙwazon shi a harkar ƙwallo da irin yadda yake saka ƙasa alfahari, yana maganar yana nuni da hannuwansa yayin da Deen ke ɗan murmushin jin daɗi. 


Lokacin da suka iso arrivals hall nan ma wasu tarin masoyan shi ne da masu goyon bayan ƙungiyarsa da suka zo tarbarsa, nan hayaniyar masoya ta cika wurin, cike da farin ciki suka shiga ɗaga hannuwa cikin ɗaga murya suka shiga yin sowar farin cikin ganin shi tare da koɗa shi da kuma kungiyarsa ta ILFC, har da masu rera waƙokin club din su, wasu daga cikin mutanen na ruƙe da babbar banner mai ɗauke da hotonsa jikinsa sanye da kayan ƙungiyarsu ya ɗaura ƙafarsa guda a saman ƙwallo yayin da bakinsa ke a buɗe, daga yanayin yadda ya rankwafa a cikin hoton zaka fahimci yana cikin yin gudu a cikin filin wasa aka yi shi, wasu kuma suna ruƙe da placards gaba ɗaya an yi rubutun barka da zuwa tare da yabo da jinjina a gare shi, da kuma masu ruƙe da tutar tambarin kungiyarsu mai dauke da shield wato garkuwa mai launin fari da zinari, daga tsakiya akwai zaki mai riƙe da ƙwallo wanda ke nuni da jarumta da jagoranci, daga saman tambarin akwai ƙaramin kambu(crown) wanda ke nuni da haɗin kulob din da masarautar Biritaniya. A ƙasan tambarin an rubuta a Latin, "Virtus et Gloria" (wanda yake nufin ƙarfi da ƙwazanta) tutar sai shawagi ta ke a sama. Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hargowar masoyan Deen hakan ya jawo hankalin sauran mutane dake kai kawo a cikin arrivals ɗin duk hankulansu suka dawo kan fitaccen ɗan ƙwallon, tuni ƴan jarida sun zagaye shi wasu na mashi tambayoyi yayin da wasu ke ɗaukar hotunansa da video, ƙayataccen murmushi ne akan fuskar Deen yana ta ɗaga ma masoyan nashi hannu tare da yi masu godiya, cike da alfaharin ɗan nasu iyayensa da ƴan'uwansa ke ta sakin murmushin jin dadi ganin yadda mutane ke nuna haukan son shi, mutane sai tutsetseniya suke don ganin sun samu saka hannunsa wato autograph wasu kuma hoto suke son yi da shi, cikin sakin fuska yake saka ma masoyan nashi hannu a wurare daban daban, wasu a jikin rigunansu, wasu a jikin hanky wasu a jotter da sauran su, wasu 'Deen Jr.' yake rubuta masu yayin da wasu yake rubuta masu, 'Nuree Jr." Wasu ma, 'Ambassador Jr.' yake saka masu a autograph din. Da ƙyar jami'ai suka dakatar da mutanen suka wuce da shi.



Bayan sun fito daga cikin arrivals din kai tsaye wurin da motocin da suka zo da su suke suka nufa, anan ya yi bankwana da minista da sauran muƙarrabanshi bayan sun sanar da shi game da welcome dinner da aka shirya mashi da daddare a Transcorp Hilton Hotel. A jere motocin suka fita daga cikin airport ɗin kowa ya kama hanyar da zai nufa. A cikin wata dankareriyar baƙar jeep  wadda gaba ɗaya glass din ta yake baƙi baka iya hango wanda ke cikin motar Deen da ƙannansa ke a ciki, yayin da iyayensu suke a motar dake biye da bayan ta su, gaba da bayan su motocin escort ne a jere suke tafiya. 

*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post