*༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 1&2
The writer's of
Karen Bana
Jalaal Areef
Ƙauna Biyu
Mikiya
Ta Daban
So Dan Rayuwa
Duniyarmu
Duhu na Dukan duhu
And new Ramin Kura
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
_MY NAINERH TARH *WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKONSA, HAR ƘARSHENSA MALLAKIN KI NE SADAUKARWA NE GAREKI ƘAUNATA. INA MATUƘAR GODIYA BISA KARAMCINKI GARE NI, UBANGIJI YA RAYA MIKI ZURI'ARKI AMIN*_
_Alhamdulillah ala kulli halin, ahar kullum ina ƙara miƙa godiyana ga Ubangijiin Al'arshi, wanda ya bani Aron Rai da kuma lafiya, kana ya wadatani da tarin Ni'imominsa ta kowacce siga, To a yau ma shi ne ya nufeni da sake dawo muku a wannan karon tare ta wata tsaraba ta musamman, kana inason inyi amfani da wannan dama ta hanyar miƙa dubun gidiyana ga MASOYA na AMANA🤙🏻, masu ƙirana da masu tura min messages ganin bana online🫠, ina godiya ga tarin ƙaunar ku gare ni, 🙏🏻 kana ina roƙon ALLAH subhanahu wata'ala da yaci gaba da zame mana gata🤲🏻. wannan shafin nakune masoyana abun Alfaharina, fan's ɗina maganin kukana, fan's ɗina silar murmushina, Allah yabarmu tare daku har ƙarshen abada Ameen😍😍❤❤😘✍🏻_
_Capricorn season_
*JADYU*
♡♡♡♡♡♡♡♡
Lokacin dafa'i yayi, Kakar majefa kuma ta tsaya domin Idan anyita jifanka ba'a yin nasara, To idan majefin shu'umine zai jinkirta se a irin wannan lokacin da ake jifa farat ɗaya ya tashi. Jama'a a karkaɗe tsohon kundi har ma da sabbin ayi dafa'i bakin rai bakin fama. Domin kuwa kai tsaye wannan labarin ze fara ne akan wasu irin mutanen da basa tsoran duhun dare. Saidai suna tsoran duhun zukata ne, don duhun dare hasken alfijir kan iya tafiyar da shi. Amma duhun zukata basu da wani alfijir da za'ayi tsammanin gushewar wannan duhun......
Tamkar yacce ƙaddarorin rayuwarmu, suke bi biye damu tamkar taswira ce dake zane a takardar lissafin rayuwar kowanne rai me numfashi, duk yanda ka so gogesu ko san kauce musu ba lallai ne ka samu makaman yaƙin ba balle GARKUWAR kare kanka, daga isowarsu gareka ko mai gajartar tsahon shekaru ko yawaitarsu. Wanda akance wai duk iya gudun ka duk iya saurinka baka isa shallakema tarin ƙaddarorinka ba. A wasu lokutan mukanyi kuka ne da hawaye, sai dai kukan ZUCIYA shi ne mafi ciwo da ɗacin kukan da yafi kassara rayuwarmu da nasarorinmu, a ɓoye ko a zahirance da bama iya manta wa dasu. Akace salati baya hana ɗaukar rai, kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarorin da suke masa jerin gwano masu tarin yawa a cikin rayuwarsa, A kowacce duniya akuma koda yaushe ɗaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mune cikin farinciki ko akasin haka.kamar kuma Yanda babu wani bawa wanda ka iya gujema tarin ƙaddarorinsa,lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu ne kamar jini, akowace rana abubuwa mabanbanta suna faruwa, to haka itama ƙaddara takan iya sanjama bawa ako da yaushe, haka kuma babu bawan da yake iya sanja tarin ƙalubalen yadda ƙaddararsa tazo mai, kamar yadda ALƘALAMIN ✍️ ƘADDARAR zai fara rubuta kansa da kansa. Domin kuwa Ko wacce ƙaddara tana zuwarma ko wanne Muminine feji bayan feji haka ko wanne feji yana ɗauke ne da nashi salon rubutun. Kamar yacce A kullum kwanan duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗin kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce ƙaddararka ta zaɓar maka zata kaika ne zuwa makomarta, saɓanin shi ne kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya.
𝙎𝙐𝘿𝘼𝙉,𝘼𝘿𝘼𝙁𝘼𝙉, 𝘾𝙃𝘼𝘿𝙄
_Adafan wani yanki ne dake kusa da yankin Nahiyar Chadi da Sudan maso Arewa cin Sudan ɗin, yayin da junayna ta kasance a farkon Sudan ɗin_
𝙈𝘼𝙎𝘼𝙍𝘼𝙐𝙏𝘼𝙍
𝙐𝙈𝙈𝙐𝙇 𝙔𝙊𝙊𝘿𝘼
ma'ana jigo ga rayuwa ko kuwa uwa maba da mama ga al'umma. ♡
Masarautar Ummulyooda, wata irin masarauta ce me cike da ƙarfin iko,Masarauta ce da ba zan iya misalta muku girma da kuma tsarin taba, domin kuwa ta kasance tamkar gari guda haka take, wajen girma da kuma ƙawatuwarta.
Masarautace babba wanda ke ɗauke da ɓangararruka daban daban, hakanan taƙunshi ƙofofi kala da iri daban daban, tamkar yacce ta ƙunshi wasu irin mutane maban banta, masarautace me kyau don tun daga wajenta zaka gane cewar ita ɗin babbar masarautace wacce aka narka maƙudan kuɗaɗe gurin tsara gininta kawai. Tsayawa bayanin wannan masarauta kuwa wani ɓata ma kai lokacin ne me zaman kansa, don nasan kunsan kyauwun masarautu barin ma ace masarautar ta bar yankin Nigeria.
Mafari.
*1995.*
Tsaƙiyar dare ne me ɗauke da wasu irin abubuwa na ban mamaki da kuma ban tsoro a wurin ko wacce rai, data kasance adala kuma muminar ruhi ta hanyar jin tsoron duhun daren daya mamaye garin ko in ce duniyar duka. Don dade da hannun ka baka iya gani sabida yadda garin yayi duhu matuƙa ga kuma wani irin tsitt ɗin da yayi baka jin motsin komai, wanda ko ba'a faɗa ba yanayin garin kawai zai tabbatar maka da cewar dare ya tsala sosai ,tuni masarautar tai wani irin yin shiru me bada tsoro, don hatta ko kukan tsuntsaye ko irin iskar nan dake kaɗawa babu haka yake lumum. Amma banda wani shahi na daga cikin wannan masarautar, zaune fara tas ɗin dattijuwar matashiyar matar take kan ɗaya daga cikin Royal chairs ɗin da suka ƙawata tankamemen room ɗin, mai kama da na president saboda girma da ƙawatuwarshi. Kyakyawar matashiyar macece mai cikar halitta fara sol da ita, wanda kallo ɗaya za ka mata ka gane shekarun ta na haihuwa ba zasu zarce sittin zuwa da ɗaya ba a ma'aunin hankali.
Tun tana irga mintunan daren dake shuɗewa da wani irin buguwar zuciya, harta gaji ta miƙe tsaye hannuwanta goye a gadon bayanta, kafin cikin sauran cikar seconds ɗin data ɗiba su cika. Wata Dattijuwar mata ta faɗo ɗakin cikin rawar jiki tana zubewa ƙasa kan gwiwowinta.
Da wani irin kallon kinsha da ƙyar ɗin nan wannan matar tabi dattijuwar dashi, kafin Cikin buɗaɗɗar muryanta me amsa amo ta soma faɗin.....
"Buɗe kunnuwanki da kyau!, ki sauraren junayna, ki tabbar abinda na saki kin aiwatar maza maza yanxu yanzun nan, domin bana da buƙatar ko wanne yaro acikin wannan masarautar daya wuce Zayed!, Kinsan ance ko wanne kifi yana da nashi kalan ƙayan, kana kinsan masu iya magana suna cewa sanyi yana iya haifar wuta, To wannan ƙayar da wutar ne bana da bukatar a Haifa a cikin wannan masarautar"
Cikin rawar jiki da kuma tsuma da namomin jikin matar dake gurfane gaban wannan matshiyar matar ta furta. "An gama uwar gijiyata duk sanda kike neme daga gareni, Umarninki kawai shine abin jirana, alƙawari na ɗauka saina cika Miki shi!, ki kwanta kiyi kiyi barci harda min shari abunki, domin indai ina raye a doron duniya masarautar Ummulyooda ta Zayed ce" Hhhhhhhh aka sheƙe da wata Shu'umar dariya, kafin kuma wurin yayi tsittt yayi tasiri a wurin. Tamkar kuma daga sama tamkar sauƙar Aradu aka furta. " Indai har burina ya cika ni kuwa ina mai kwaɗaita miki cewar zaki zama ƴantacciya Acikin masarautar
Ummulyooda ta har gaban abada junayna" Kanta risinawa matar tare juyawa a hanzarce tana barin ɗakin baki ɗaya. Tana fitowa tabi wani surƙuƙin hanya ko tsoro ma bata ji, tana ɓillewa ta wani ɗan carridor haka ta shige cikin mutanen biyun da suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanyar, me ɗauke da wani irin duhu da shiru me bada tsoro, sedai su da duk kan alamu basu jin tsoron, domin kuwa tafiyar su suke yi cikin sauri sosai babu ma kamar ta gaban, wacce ta bayan take biye da ita itama zabga saurin. Wanda duk kan alamu suka gama nuna cewar tafiyar su ɗaya ce. Ta ƙarshen ma biye take da su duk inda suka jefa ƙafarsu itama nan take jefawa. Seda suka yi tafiya me ɗan zurfi kafin mata biyun suka dakata tare da tsayawa. Kansu yana ƙasa suka furta. "Shugaba kamar yanda kika buƙata mun gama shirya komai na oummul_jannah nan, tana can tana naƙuda a yanzun haka, wannan shi ne ruwan da zaki bata a madadin ruwan addu'an da zaki bata" ꨄ Ahankali ƙarar salati da kuma sautin karatun ke fitowa daga wani ƙawataccen shahi na daban. Dake cikin fadar. Salati da nishi ne irin na rai mutu kwakwai rai... Baki ɗaya tin daga farkon ginin sashen har ƙarshensa zagaye yake da Perry mian. (Dogarai, ko masu bada kariya). Ahankali matar dake sanye cikin riga doguwa baƙa ta soma ratsa mutanen, hannun ta ɗauke da wata ƴar ƙwarya. Duk inda ta gimla a sashen se Kaga ana bata girma, tamkar ba dare ba haka ɓangaren yake, kasancewar matar sarki ce da kanta take naƙuda zata haihu. A natse amintacciyar baiwar nata ta isa gabanta. Tana zubewa wani ɗan zufa²na karya ko mata. Ita kuwa matar dake kwance wacce take a galabaice ko motsin kirki bata iya yi. Domin wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sake sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata da gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Duk da cewar ba yau ne karo na farko data taɓa haihuwa ba,amma bata taɓa jin matuƙar wahala da azaba irin wannan ranar ba, domin kuwa ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi ne. Ko dai ana sassaƙar duk wani shahi na jikin ta. A hankali ta cije bakin ta tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu tana ambatar kalmar. "la'ila ha illah antas subhanaka inni kunti minazzalimin³"
Babbar baiwarta Ummul abeed kuma amintacciyarta da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, tare da fakar idanunta ta zuba mata maganin da aka bata akace ta zuba mata a madadin ruwan addu'ar da take mata na naƙuda ko wacce haihuwa. Miƙa mata ruwan tayi tana me furta. "Ki gafarce ni uwar ɗakina zan ƙarasa sashen me martaba in sanar dashi halin da kike ciki, don yace duk yacce ake ciki in sanar dashi." ta yanko wannan uwar ƙaryar nan take domin tsira daga tarkon a kamata. Ƙoƙarin mata magana take, tana kuma son riƙo hannun jakadiyarta jumaymah, sedai
zafin jikin da ya fara galabaitar da ita ne ya sanya ta gaza koda yin wani kwakkwaran motsine, wani irin azaba ne ke yankar marar ta, da kuma duka ilahirin jikin ta, wanda zafin gubar tsafin da aka bata ne ya gama baybaye jikin ta. Jumaymah kuwa tana fita cikin waige² take tafiyar, har ta isa ga babbar su wato junayna, nan take sanar mata cewar ta zuba maganin. Wani shu'umin murmushi junaynan tayi tana bama umayman warin ɗan kunnen gwal ɗaya. Ita kuma tana nufar ɓangaren uwar gijiyarta. A ƙasa ta zube tana sauƙe numfashi tare da furta, "Hutawarki lafiya Fulani uwar ɗakina me magajin masarauta, zinariyar mai martaba haskenki bai tsaya iya shi kaɗai ba kin haske lungu da saƙon cikin Masarautar nan, Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garnaƙaƙin dutse kike kowa ya ja da ke shi ka faɗi..." Wani lalataccen murmushi Fulanin ta saki tare tare da tambayar, "Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata, na kuma tsara ?" Murmushi jakatar tata ta saki wanda ya sanya Fulani mardiyya sauƙe ajiyar zuciya, duk da cewar ba ta kai ga jin amsar da junayna nan zata bata ba, amma aka ce wai labarin zuciya a tambayi fuska, don tuni ta san cewar sun yi nasara ta iyaka murmushin da junaynan kawai take yi, "Ranki shi daɗe an gama aiwatar da komai yadda ya kamata, kamar yacce kika tsara a halin yanzu gacan oummul_jannah zube rai a hannun ALLAH.... (Kunji fa koda ran a hannun ta yake kuma oho). Wani yalwataccen murmushi Fulanin ta saki tana jin ranta fess tamkar an wanke da Klein..... Kafin kuma tamkar wacce aka zabura ta miƙe tsaye tana furta, "Junayna aje a tabbar ta bata haihuba!, idan ma ta haihu ɗin ita da abin da ta haifa ɗin a sheƙesu....."
"Angama uwar gijiyata" ta faɗi tana irin kai tsintsiyar hannunta saman goshinta ta jinjina mata. Wannan karon kammm da kanta zata je, ta hanyar kayan likitocin da ummul abeed ta sato mata. Ahankali take tafiyar tana sanye cikin farar riga labcot ta likitoci da ash ɗin wando, wanda hakan ke bayyana cewar cikakkiyar likitar masarautar ce ita. Sedai fuskanta a lullhɓe yake, yi tayi tamkar irin zata yi tuntuɓe ɗin nan, se kawai ta faki idanun dogaran tana gangara wata ingeza ɗin mulhuf ɗin baƙar roba, me ɗauke da sleeping powder, wacce take gauraye da kayan asirinsu. Ta yi saurin faɗawa parlour'n da take jiyo nishi da salatin da sammm basa fita. Bayan da ta gama tabbatar wa da cewar sun kamu.... Shigar ta tamkar wacce dama haihuwar izininta take jira sanɓalelen yaron ya diro duniyar ta ƙafafunsa, irin haihuwar nan da ake cema ɗire... Sedai sammm yaron ko motsi be yiba, bare kuma irin kukan nan na jariran da suna faɗowa duniyar da shi suke farawa. Kamar kuma a gizo taji tamkar kukan jariri, don haka tayi saurin kallar wanda ke cikin jinin haihuwarsa, sedai babu alama ko kaɗan data gama nuna cewar shi ne yayi kukan. Sake kallon wurin haihuwar tayi da kyau da kuma idon basira da nazarta, "Tabbas akwai wani maharin bayan mu kenan?" tayi maganar babu ko ɗigon imani a ranta tana sanya wuƙa ta yanke cibiyar da take jikin jaririn da kuma uwar.....
☆
Wani irin nishi da kuma ƙaƙarin mutuwa ne ke fitowa daga cikin wani amintaccen ɗaki. Kafin dattijon da Hannunsa yake riƙe da ƙaho hannunsa da fuskar sa duka jini ya gama wanke su gaba ɗaya. Wani ɗan ƙaramin ihu mutumin da yake riƙe da ƙahon ya buga tare da zubewa kan gwiwowinsa ƙasa gaban kamilin mutumin da kallon farko kawai zaka masa kasan cewar sarki ne, domin rantsatstsiyar shigar dake jikin sa shi ne abin da ze fara tabbatar maka cewar shiɗin bazaraten sarki ne, irin adalan nan na amana da ta hanyar cikar zafin sa kawai, da kuma kamalar dake zagaye da kyakkyawar fara tasss ɗin fuskar sa. Wani nishi da numfashi me ɗan ƙarfi ya kawo, wanda ya sanya jini tittilo masa ta hanci da kuma baki, kafin cikin matuƙar dauriya da juriya ya ɗan ɗago hannunsa dake ɗauke da wani fari tass ɗin baby showel, Wanda jini ya gama wankesa shima. "KAMAALA ƊAN ASHFUD JIKAN KAMAALA RAHEEM DAWOOD....... Se kuma ya ɗan dakata sakamakon jinin daya ci gaba da anbulo masa jiki. Jikin mutumin daya kasance babban bafaden sarki ashfud ɗin ya soma rawa, wanda son zuciya da son kai na iyaye da ƴan uwansa suka sanya shi gamawa ga adalin sarkin nasu. Tsaye ya miƙe tare da sara hannuwansa yana yana sake sakin wani ihun me tafe da kuka ya shiga furta.
♡
"In kaji ana duhun dare mai ɓatar da Rigar sarki, Sarari mai ƙare gudun doki, kaja sunja basu ga da kyau ba, jeji kafi gaban Ayi maka ƙyaure, Jan zaki Maganin Abokan gaba, Sadauki Adalin Jagora_ kana Gaba kullum suna bayan ka, dama da hauni Lafiya Alheri na gida na uban gidana . Wasu mutanen tamkar hasken fitila ne acikin duhun dare, domin a duk inda suka kasance sai sun haskaka rayuwar mutanen da ke kewaye da su. Su kan ƙarfafa gwiwa kuma su taimaka a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Sai dai kuma kash! Ba mu cika appreciating saudaukarwar tasu ba, har sai bayan sun ɓace ma ganin idanuwanmu, ko kuwa duniyarmu. Idan ƙaddarar rayuwa ta nesanta mu da su, ko ƙasa ta rufe idanuwansu sai mu fahimci ashe su ne ginshiƙin rayuwarmu,
Su ne silar farinciki da jin daɗinmu
Abu ƙadan na faruwa sai mu ji _Ina ma ace wane yana nan…?_Wasu iyaye ne a gare mu, yayin da wasu suke kasancewa tamkar abokai suke gare mu. Amma sun mu'amalance mu tamkar ƴan uwa na jini, Wasu kuma malamai ne da suka saita rayuwarmu, Wasu kuwa maƙwabta ne, wasu kuma ma'aikatan lafiya ne da suka tabbatar da farin cikin mu garemu. Shin me ya sa ba za mu ya ba ba?, mu kuma jinjina musu ba?,
Me ya sa ba za mu sanya su farinciki kamar yadda su kai mana ba?, Me yasa za mu jira har sai lokaci ya ƙure?, Me yasa?, Me yasa hakan?.... Me yasa ni Qasem na kasancewa ɗaya daga cikin waɗan nan mutanen, me yasa ruyuwa ta zaɓa da tayi wannan mugun wasan dani?, Amma ba komai zanyi zanyi zanyi, ko dan na nuna musu cewar har gaban abada zakara shi kaɗai ne sarki. Na kuma nuna musu cewar kai ɗin KIBIYAR AJALICE WACCE SULKE BAYA IYA TAREWA, KAMAALA JIKAN KAMAALA ƊAN ASHFUDDEEN DAWOOD RAHEEM KAMAALA.... "
Wani kalar kyakykyawan murmushi sarki ashfud ya saki, duk da kasancewar irin azaba da raɗaɗin dake ci gaba da ratsa tsaƙiyar ƙirninsa.wani hawaye ne me tsatsanin zafi da sukar zuciya ya gangaro masa na gefe ɗaya daga ɓangaren hagu "Qasim Habeeb Alkawarin kare rayuwar KAMAALA nake son kamin!, da kuma alƙawarin inganta rayuwarsa tare da bashi cikakkiyar ilimin islama da boko nake son ka bani a wannan tafin hannun kafin ruhina yabar gangar jikina...." Wasu hawaye ne sosai suka ɓalle wa wanda aka ƙira da Qaseem ɗin, kafin kuma ya wani irin ɗauke kansa yana kallon bayansa. Sai kuma ya juwo tamkar wani zaki yana goge hawayen dake cike taf da idanunsa ya ce, " You don't have to cry since you have me, i promise In sha ALLAH to be there for you no matter the weather, I promise to you and I promise to be your one and only till the end of time!, Na ɗauki wannan Alƙawarin da duka imani na kuma sena cika kodan renonsa cikin aminci me kyau ta hanyar dawo dashi ma haifarsa don kawar da gurɓatattun dake ɓoye cikin wannan masarautar In sha Allah Me Martaba.... !!!"
Ya faɗi yana me kife hannunsa kan na me Martaba ɗin, wanda yaja wata iriyar iriyar zuciya yana haɗe nashi hannun tare dana Babban Bafadensa Qaseem, Wata nannauyiyar ijiyar zuciya ya sauƙe numfashi sa na barin gangar jikinsa cikin salama na alƙawarin bawa yaronsa kariya daga iyayen sa masu cike da matuƙar son kai da kuma son zuciya.Boyayyar ijiyar zuciya Bafaden ya sauƙe. Daidai kuma da bankowa ɗakin da wasu mutane uku da suka yi. Fuskar su tana ɓoye cikin shirami, ɗaya bayan ɗaya haka suka gama shigowa suna jeruwa, babban shi ne a gaba se tsaka tsakiyar cikin su a bayansa, se kuma bazara ten dake bayansu sunyi irin zama war nan"Yauwa Barde ka kammala aikin ka,sauranka yanke wannan ɗan ƙaramin maƙogwaron Qasim Habeeb!" saurin meda jaririn bayansa yayi, ganin haka ya sanya na tsakiyar nan matsowa shi ma yana me furta." Idan ba haka ba nan bada daɗeɗewa ba wannan jaririn ze iya zama maƙiyinmu, har ya fara jayayya damu yazo yana ihu a gaban mu, don haka yanke maƙogwaron wannan shi ne kawai ze kawo ƙarshen masalaharmu, maza ka sheƙeshi....."
Wata malalaciyar dariya ya saki yana me furta."Ku a daƙiƙin tunaninku zan aikata kuskure irin wannan a karon farko, kuma in yarda In sake maimaita shi a karo na biyu?" Na ƙarshen ne ya fito tare da furta. "Duk da tsananin biyayyar da kakamema sarki ashfud har ka iya kasheshi, to taya mu zamu iya yarda cewar mu ɗin ma ba zaka iya cin amanarmu ba?. Hakan yasa muka ɗauki matakin kota kwana, Bilal ka sheƙe Barde tare da wannan jaririn dake hannunsa....." ko kafin yayi wani yunƙuri tuni wanda aka ƙira da bilal ɗin har ya kai ma Qasim ɗin sara. Cikin zafin nama da sanin makamar yaƙi Qasim ɗin ya tare saran da ɗayan hannunsa dake riƙe da ƙahon nan har yanzun. Sedai kash cikin akasi garin jefar da takobin bilal ɗin takobin ta yanke shi a ƙafarsa, wanda ya sanya bilal ɗin sake fusatowa da yunƙurowa da nufin ɗauke masa kai, Sedai Qasim da suke ƙira Barde kafin shi ya sauƙe masa shi kuma yayi hanzarin cake maƙogwaransa da ƙahon dake hannunsa. Yana ɗaga wuyan sama kana ya yi cilli dashi, yana faɗuwa matacce wuyan sa na yin tsartuwar jini.... Na farkon ne ya sake yunƙurowa da nufin tinkarar Barde ɗin, Sedai na biyun yay gaggawar dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, domin yafi ɗan uwan nasa wambai sanin irin hatsabibancin dake tattare da Qasim ɗin.
Da ƙahon dake hannunsa wanda yake tsiyayar da jini ya nuna su, yana me furta.
***
"Ku sani sarkin ku na gaba wato
KAMAALA ƊAN ASHFUD JIKAN KAMAALA RAHEEM DAWOOD
dashen ALLAH NE, hadari ne shi malafar duniya duk wanda yace zaiyi dashi yaja da ikon ALLAH. Dole wannan karon dan zaki ya bayyana akan miƙiyansa kuma maha'intan iyayen sa, ku ji rayi lokacin Dawowar SARKI ASHFUD a karo na biyu, inda masu gudu su gudu ma domin kowa ya shirya ma bayyanuwarsa a karo na biyu.... "
Ya ƙarasa faɗar maganan nashi a fusace, "An ce Mara dabara shi ne yake barin ruwan sama ya jiƙa shi, mai hikima kuwa tun kafin ruwan ya fara sauƙa ya riga ya gama samo wa kansa mafaka. Idan ya kasance har a tsayin wannan shekaru mahaifinsa ya kasa ja damu, don me kake tunanin jaririn da yake baida mafaka ko wata majingina ko tsira da rayuwa shi ze rayu har ya bamu ciwon kai?. Bare ya ƙalubalencemu. Ka sani kana da zaɓi biyu ne kawai a cikin wannan duniyar, zaɓinka na farko ko dai ka bamu wannan jaririn ko kuwa kaida shi duk ku zama sheƙaƙƙu." Sake riƙe jaririn dake maƙale a hannun sa da kyau yayi, tare da furta." Se dai ku sani kun makaro, kun kuma zo a mummunan loƙaci, domin ƙaddarar itace da kanta ta zaɓeni bawai ni ne na zaɓeta ba, Wannan jaririn seya rayu, seya zame muku ƙadan garen bakin tulu, seya zame muku alaƙaƙai a cikin rayuwarku, seya sanya kowannenku gudun ceton rai.... "
Wata shegiyar dariya mutanen uku suka saki waɗanda fuskar su take ɓoye cikin rawani da shiramin da suka ɓoye dasu. Kafin ɗaya daga cikin su ya furta."Sai na tuna da maganar Malamin Falsafa Freud da yake cewa, Ko wanne mutum yana da zaɓi biyu! Na farko ya zaɓi wahalar aiki ko dai wahalar nadama. Frued yana nufin ko dai ka zaɓi wahalar jajircewa yanzu wajen gina gobenka ta hanyar yin watsi da daɗin kwanciya da kake yi a katufu, ko dai bayan fitowar rana, ko kuma loƙacin da dama ta wuce maka kasha wahalar nadama na ƙin huɓbasa da jajircewa da kaƙi yi wajen gina kanka a rayuwa, ta hanyar zaɓi da son gina rayuwar waninka ba wa kai ba"
Ƙafarsa ɗaya da take tsiyayar da jini ya ɗan dogara tare da numfashi yana me furta.
"Na farkon wanda tun kafin zafin rana ya keto, tuni ya fara shirin neman inuwar da zai sha inuwa, na biyun kuwa cewa yay wanda yake jiran rana ta fito sannan ya fara tunanin yadda zai samu inuwa. Manyanmu na cewa ba' a shuka a rana guda, kuma a yi fatan samun inuwa a wannan ranar.Idan kana da shekaru 25 zuwa 35, bai kamata ka zauna kana jira sai wani ya baka dama ba. Idan har a wannan shekaru ba ka kafa tushen kanka ba, to ta yaya zaka yi tunanin lokacin da kake mataki na girmantakarka, Sarki ashfud yana yawan cewa, Dole mutum ya ɗauki nauyin kansa. Idan ba ka yi hakan ba, sai wani ya ɗauka maka, amma ba yadda kake so ba.
Idan har kuna da tunanin cewar zan tsaya inci gaba da dogara daku to kunyi kuskure, ku sani cewa rayuwa ba ta jiran mai dogaro da wasu. Dole ƙwaƙwalwarka tayi aiki, dole in shiga cikin mutane kala-kala don koyon dabarun zama da mutane, Idan ka gaza yin hakan, za ka kasance cikin jerin mutanen da za a rubuta tarihi a kansu da kalmomin. _Ya rayu amma bai yi tasiri ba_
Domin duniya kamar motar haya haka take, idan ba ka hau ba, za ta tafi ta bar ka. Idan kana tunanin da akwai wani lokaci mafi dacewa da gyara rayuwarka, ku sani shekara mai zuwa ba ta taɓa bada tabbacin cewa za ka samu tikitin hawa wannan motar. To yanzu ne lokacin.
Ko ka tashi ka ɗauki ragamar rayuwarka, ko kuma ka zauna har duniya ta manta da kai, ni kuma bana da fatan hakan!... Ka na da wani mutum ƙwaya dal da ya haskaka rayuwarka? Daure ka yaba, ka kuma kyautata masa gwargwadon iko. Kada ka jira har sai bayan ya mutum a barka da dogon sharhin da ba shi da wata Alfanu, sedai ni na kuskurema hakan, amma zan gyara abinda na ɓata ɗin ta hanyar inganta rayuwa, Domin kuwa ita kanta rayuwar tamkar hanya ce mai cike da tsaunuka da kwari da tudu, mai cike da duhun dare da hasken rana. Daga shekaru ashirin da biyar 25 zuwa talatin da biyar 35, matashi yana cin karo da gagarumar jarabta, ba daga komai yake samun wannan jarabta ba sai da zuciyarsa. Wannan ne lokacin da rayuwa take tantance ko zai haye tudun nasara, ko kuma ya ci gaba da rayuwa na bayansa suna tattaka shi suna kaiwa ga Nasara, kun sami wannan damar tawa ne a baya ku sani wannan ba shi ke nufin zakuci gaba da zuba min zaɓa ina caka ba, Tabbas duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya. Haka zalika duk wanda ka gani a matakin nasara, to kuwa tabbas acikin nasarar nashi akwai tarin ƙalubalen daya fuskanta kafin haka, SADAUKARWA 💪
.......
ꨄ
Bata dakata da tafiyar da take yi ba har seda ta danganka kanta da inda hasken aci balbal ɗin da take hangowa, Sema sake ƙaimi da tayi wajen ci gaba da sassarfa har ta isa inda take gano hasken aci balbal ɗin. Yadda take saurin kaɗai kamar zata kifa domin burin ta ta isa wajan, shi ne zai baka tabbacin lallai ko meke tafe da matar me girma ne haka, dutse ne babba a wurin sai yadi kalar ja da aka yanke saman dutsen dashi da kawunan skeletons sassaƙale a ko ina anyi ado dasu. Tin kafin ka isa wurin zaka fara jin wani gurnani da gunji gunji kamar bana mutane ba. Tana isa deda daf da dutsen wani katoton boka ya bayyana gabanta, bakiƙirin dashi katoton gaske wanke yake ɗauke da kan jakanya. Zubewa tayi a ƙasa gabansa, bayan ta gama dalalo masa wasu dalasiman da duk wacce take zuwa wurin sa dolene ta iya shi. Cikin ruɗu da kuma alhini da take a cikin sa ta furta "Ta haihu! Ta haifi yaro namiji, sedai an sama matsal.......
"Da ka ta domin anan bansan kalmar matsala ba Maddiyya, Domin kuwa dama can mun riga mun ga hakan zata faru. OUMMEEY zata haihu kuma ɗan zo girma. Me kike so a yiwa jaririn?, A kashe sa kamar yacce aka kawar da ubansa,? Ko kuwa a haukatar dashi tamkar yanda muka haukata uwar?, Ko kuwa so kike a lalata rayuwar sa ta gobe?, A juyar da tunanin sa?, a cikin waɗan nan jerin abubuwan dana lissafo sai ki zaɓa wanne kike so ayi ma yaron a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."" Ya faɗi cikin murya mara daɗin sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraron ta. Sai dai wani tarin abin mamaki amma matar nan bata ko yi ɗar ba, saima sake gyara zaman ta da tayi tare da fesar da wani mayen numfashi ta furta, "Na tsani jinin Razeenerh, bana son jinin OUMMEEY yayi wani kwakwkwaran motsi a cikin wannan masarautar har se naso, bana son jinin OUMMEEY ya ɗaukaka a cikin wannan duniyar, A kuma ko ina ze rayu, duk wannan maganar babu ita, domin kuwa Qasim bafaden sarki yaci amanar mutanen da suka aikesa game martaba sarki ashfud ya tsira tare da yaron, bayan ya kashe me martaba. Se dai ka sani wutar bata fara aiki ba, buyagin hayaƙinta ne kawai ke aikin cunkushe kwakwalan wasu tsirari na kaɗan daga cikin mutanen fada" wata kafurar dariya bokan ya kuma saki me kama da kukan jaki ya furta. "Shegiyar uwa, uwar la'anannu, Shegiyar uwa, uwar tsinannu...... Ki an yanzune muka fara wannan yaƙin, wanda bashi da ƙarshe, ki jira girman sa, kowacce duniya zaki ga da kalar ɗabi'ar da zai tashi, ni ne nace zanyi in na faɗa kuma bana fasawa sai na tabbatar hakan, sedai da sharaɗin cewa.....
Muryanta na wani irin rawa ta taryi numfashinsa ta hanyar furta,
"Meye shi sharaɗin?." wata kafurar dariya ya sake bushewa da ita yana me furta. "Kome ze faru daga baya babu ruwan mu, karkiga laifin mu, aikin mu mun riga munyi in kika ga wani canji ko saɓanin hakan daga baya, domin kuwa ƙaddarar yaron me ƙarfi ce, tin kafin yazo duniyar yake nuna min hakan. Jeki la'ananniya karkiyi kuka dani, Jeki akwai sakamako, akwai sakamako......
Miƙewa tayi tamkar zata bar wurin, Se kuma zaram ta zare ƙahon dake jikin ta ɗaure ta gefen jikin ta tana lumawa bokan a ƙahon zuciyar sa ta tsakiyar ƙirjinsa. Tare da furta. "Sai dai ka sani kayi babban kuskure boka na ambatar kuskure da sakamako bayan aikina, ina so ka sani Mardiyayya bame tsoro bace, domin shi matsoraci baya taɓa zama gwani, ni kuma gwanar nake da buƙatar zama. Ka sani duk wahalar aiki, duk ƙalubalen da zan fuskanta ba a bakin komai suke ba, sedai bana taɓa ɗaukar faɗuwa a cikin wasa da kasada ta, duk tashin hankalin sa na amince zanyi babu wani sakamako Se wanda na zaɓarwa kaina da ƴaƴayena boka a sauƙa lafiya....... " ta ƙarasa maganar tana fisge ƙahon daga tsaƙiyar ƙirjin nashi. Wanda yayi saurin dafewa yana kuma fashewa da wata mahaukaci yar dariya, wanda gaba ɗaya dajin ya ɗauki." Ki sani dole akwai sakamakon! Dole ranar zata riskeki, dole zaki girbi abinda kika jima shukawa mardiyya, za ki yi nadama, zakiy nadama, fatan nasara da kuma rashin nasara anan gaba, sena dawo ɗaukar fansa ta tare da miki dariya wata rana, dole nima zan rayu akwai bukatar na dawo wata ranaaaaa" daga haka wata Guguwa ta baybaye dajin kafin kuma ɓatttt ta ɓace tare da bokan......
ꨄ
Hhhhhh Na ce Idan ana dara fidda uwa ake, ina gwanar wata ga tawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin dake cikin suger da kuma zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da wani ɗanɗano, yayin da ita kuma zuma ta kasance tana wanke ƙwaƙwalwa ne tasss, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, kuma ƴar baiwar ku AMMEY LAYLERH, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na tsaya bashi labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha,LITTAFIN RAMIN KURA ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, zalunci, sarƙaƙiya, gami da Izza, *RAMIN KURA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yazo, gashi da kaifin gaske kaifin yankan domin zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa?, Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *AMMEY LAYLERH* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da tsantsar mugunta Zanba cikin aminci, labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa, kun san dai alƙalamina baya taɓa rubuta shirme, ku dai kawai ku biyo ni *AMMEY LAYLERH* taku cikin wannan zazzafan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake, da kuma yadda zata kaya, haɗi da warwarar wannan ƙullaliyar zare da abawar dake chakuɗe cike da sarƙaƙiya.......
Waɗanda suka karanta littatafanta irin su. *MIKIYA, DUNIYARMU, TA DABAN, KAREN BANA, JALAAL AREEF, ƘAUNA BIYU, SO DAN Rayuwa DUHU na DUKAN duhu,* Sune kaɗai zasu san ya ɗanɗanonsa yakeeee.... Hajiya karki bari ayi tafiyarnan babu ke. Domin kuwa ta manya ce, ta kuma musammance...
Chart mee or call🤙
08104493215
Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰
A gimtse 🫰 🙃♥️✅
*BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅*