Ramin Kura Page 5&6 Complete BY AMMEY LAYLERH ✍️

Ramin Kura 5&6

 ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼

*The power in rocket*

war

~Na Maryam Naseer Mirrah~

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️

Book One paid 

       ♡

Page 5&6


𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 


     ♡_Capricorn season_

 

ABUJA NIGERIA 

Bombila Barracks. 



  *NIGERIAN ARMY HEADQUARTERS ABUJA*


♡♡♡♡♡♡♡♡

 

Gaba ɗaya sansanin nahiyar filin sojojin cike yake maƙil da manyan sojojin ƙasar Nigeria, se famar kaiwa da komowa suke hankalin kowa ba'a kwance ba, Domin kuwa cikin tsakkiyar daren shekaranjiya  wayewar jiya aka samu wasu gungun ƴan ta'adda suka shigo har cikin anguwannu suka tada bama bamai, wasu kuma suka karkashe. Inda su shammaci tarin security ɗin dake zagaye a ko wanne lungu da saƙon da suka shiga suka yi ta'adin nasu. 

     daga can cikin ainihin barracks ɗin kuwa, Tsaye matashin baraten saurayin yake, yana fuskantar manyan sojoji ukun dake gabansa, hannunsa kafe a goshinsa. Hakan ya sanya babu abinda zaka iya kalla  a jikin sa inba lallausan gashin kansa da yake ɗauke cikin wani ɗan iskan aski ba, irin me kibiyar nan gefe da gefe, wanda ya tattara sauran ya ɗaure  a ƙasan ƙegarsa, daya sama sakkowa ta ƙasan pcarp ɗin dake kan sa, yana sanye cikin cikakkiyar shigar sojawa ta kakin su. Ɗan table ɗin dake gabansu masu ɗauke da tarin files Mr president  Auwal Ibrahim Marafa ya ɗan daka, tare da furta."Mun sani cewar zaka iya kawo mana wannan ɗan ta'addar har zuwa nan da ranshi, mene dalilin daya ka sheƙe shi?. Ina san kamin ƙarin bayani, domin idan da ace ka kawo shi nan da ranshi da mun sami bayanai masu yawa daga gareshi"

   *

Sara masa yayi tare da furta, "Yallaɓoi ai mun riga da mun sami duka tarin bayanansu masu yawa daga gare shi, nayi kutse ta cikin na'urar shi na gama gano komai!" a ɗan fusace ya miƙe a wannan karon tare da furta. "To me ya sa kuma zaka kashe shi?" ya cilla masa tambayar yana wani muzurai. "Yallaɓoi hakan shi kaɗai ne zaɓin da muke da, domin isar da saƙon mu!" Matashin ya sake faɗa a dake babu wata alama ta komai tattare dashi. "wanne saƙon ke nan?" Mr president ya sake tambaya tamkar wani journalist.  Manyan fararen idanunsa masu ɗauke da wani irin kwarjinin da a koda yaushe yake lulluɓe da fusata, wanda kuma yake ruguza zuciyoyin  maƙiyansa dashi. Domin kuwa  saboda tsabar cikar zatinsa yasa idan yana wuri babu wani mai iya ɗaga idanuwansa yakalle shi, bare kuma har mutum ya sami zarrar haɗa idanunsa da nashi.  "tell me kai nake sauraro" Mr president ya sake katse tunaninsa ta hanyar sake jefa masa wannan tambayar. "Idan har suna jin cewar zasu iya shigowa cikin ƙasar mu kuma su kawo mana hari, To su sani cewar mu ba gajiyayyu bane, kana kuma bamuyi lalacewar da ƴan ta'adda zasu yi nasara akan muba. Dole su san cewa muba sa'anninsu bane" ya furta yana risinar da kansa tare da sara masa. "Me ye kake nufi wai?, idan suka ƙara kawo mana harin kai menene abinda zaka iya eyeee?" ya faɗa a mugun fusace yana manta gaban wa ye yake, yana manta tare yake da wannan dai tsayayye jajirtaccen bazara ten matashin sojan yake. Wannan yake bada rayuwarsa akan ƙasar sa, wanda yake tinkarar mutuwa a yayin da kowa ke gudun ta, ya manta cewa shi ne shi ne shi ne  TANDARA tsaye a gaban sa, mutumin da mutuwa da kanta take tsoronsa, shi kuma a kullum kwanan duniya yana sake kusanta kansa gareta amma kuma tana sake ja da baya, domin ba dan ya mutu aka haife sa ba, don ya rayu yayi yaƙi bakin rai bakin fama aka haifesa.  Idanunsa da har suka fara sirka tsantsanar ɓacin rai ya ɗago yana kallar sir ɗin, tare da furta. 

       "Idan har basu tsorata ba to tabbas zasu iya kawo harin, idan har sun tsorata da saƙon dana tura musu, Hakan ze lalata kwarin gwiwwarsu, kana ba zasu iya yin komai ba...."  Wannan karon da ƙarfi sir ɗin ya daki teburin tare da furta. "Amma ai wannan ba itace amsar tambayar da nayi maka ba, Ka sani cewar yanzu dai basan sa ayi bincike akan kaba, amma idan har kaci gaba da nuna wannan isar da jiji da kan naka haɗi da nuna kwarewarka da kuma wannan zafin kan dake ɗibarka, To ka sani dole ka amsa tambayoyi............"


    Wani  kalan juyi yayi tare da ɗaukar ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman teburin dake gabansu, yana binsu da wani kalan kallo wanda yafi kama dana tuhumar nan, tare da furta." Nifa SOJAN ƘASAR NIGERIA ne?!, wanda ya taso cike da kishin ƙasar sa. Ina son ku dukanku ku sani cewar koda na daƙiƙa ɗaya bazan iya jinkirin baiwa ƙasa ta RAYUWATA ba, kuma sannan ku sani cewar babu wani binciken da zai iya ruguza kwarin gwiwwar da nake da ba, Ita kuma wannan zafin kan da jiji da kan ta kake maganar su da su ne aka haifeni, su ne ɗabi'a a koda yaushe..... "  Na tsakkiyar ne kanal Musa Bappa babayo, ya dube shi tare da furta." Miye kace? "

  Se da yaje har wajen bakin ƙofar fita daga room ɗin kana ya dakata tare da juyo da kansa ya kalle su su duka, kana ya furta." Ban zama soja domin tsira daga mutuwa ta ba, domin kuwa rantsuwa nayi da rai da rayuwata zan kare al'umma ta, Na zama soja ne domin kare waɗan da basu da ƙarfi, kana  A shirye nake da bincikenku yallaɓoi......" daga haka ya sanya kansa yana ƙarasa ficewa daga cikin room ɗin baki ɗaya inda ya bar su da mutuwar zaune, wacce dama ba shi ne karo na farko daya saba barin nasu a haka ba. Seda Kanal Musa Bappa babayo ya tabbatar da cewar captain AA yayi nisa da bakin kofar kana ya miƙe tsaye yana me furta. "Ni fa zafin kan yaron nan wllh bani tsoro yake, ɗan zafin kaine sosai. dabi'arsa kuma kan firgitar dani sammm baka taɓa gane alkiblarsa haka  baka taɓa sanin ko shi ɗin ainihin wanene shi, haka baya da tsoro domin shi kansa tsoron   firgita shi captain AA ɗin yake!?"  a zuciye Mr president ya miƙe tare da furta. 

     "Saime! Na ce saime dan ɗabi'arsa na firgitar da kai, zafin kansa kuma kan baka tsoro. toni sammm kwata² bana tsoron haka,  nima ɗan zafin kanne aiiiii ko ka manta waye General Murtala na goma na tuna maka a filin daga??"   Ya faɗa a fusace cikin fusatar zuciya yana shige wa cikin wani babban ɗakin na'ura da aka gina shi da zallar gilashi. 

      ✯

Captain AA kuwa cikin takun ƙasa ita da kuma izza haɗi da cikakkiyar kamala da haibar da subhanahu wata'ala ya masa yake tinkarar compound na sansanin zaratan manyan sojojin. Tuni sojojin wurin suka fara ƙamewa. *CAPTAIN ALIYU ABDULLAHI KAMAAL* kenan, wanda ya gama  amsa sunan sa a matsayin namijin mazajen fama, wanda duniya take alfari dashi kasan cewarshi sojan ƙasa da ƙasa..... Tsayayyen soja ne wanda duniya keji dashi, sedai manya na sama dashi kan ɗurƙusar dashi. Amma duk da haka yana cikin zukatan al'ummar garin Abuja dama kewayenta, Sammm baya da juriyar ganin ana aikata wani ba daidai ba a cikin ƙasa kuma ya jure..... 

    Tin kafin ya isa gaban rantsassiyar black car nashi wani soja yay hanzari zuwa ya  buɗe masa motor ɗin. Kansa ya ɗan jijjiga tare da masa alaman shi zayyi driving ɗin da kansa, sara masa yayi tare da bashi car key na motorn. Motoci biyun dake bayan nashi na shirin mara masa baya ya dakatar dasu da yatsun hannayensa biyu. Key yama motar tare da mata wani kalan ɗan iskan reverse yabar baki ɗaya harabar wurin.A hankali yake mirza starring motorn kamar baya, yana ta ƙoƙorin dannar zuciyar sa dake ƙoƙorin sake fusata shi, Ahankali wata sassanyar iskar dake tafe da hadari ta fara kaɗawa, Wanda garin yake dab da fara zubar da ruwa. Tamkar kuma wanda aka zabira haka yaja motar da wani irin bala'in gudu. Don ganin yacce garin ke ƙara yin baki, alamun ruwan sama kan iya sauƙa a koda yaushe, Kai tsaye yana nufar anguwar Asaroad, zuwa lokacin kuwa har an fara yayyafi. Wani ƙerarran gini wanda yafi kama da building ya taka birki, yana buga uban wani hong ɗin da ya sanya  Bala mai gadi dake zaune daga cikin ƙofar ɗakinsa, Saurin nufar bakin  ƙaton get ɗin gidan nasu. Kai tsaye shi kuma yana danna hancin motar nasa  ciki, yayin da ruwan da yayi ƙarfi sosai yake dukan glasses na motorn tamkar zaya fasa gilashin motar, domin ruwane harda ƙanƙara, lema ya lalubo  daga cikin motorn' domin a duniya idan da abinda bayaso to ya bi bayan dukan ruwa. domin yanzu yanzune ya rikita mashi al'amura da lissafi, Domin duk ranan da yayi ganganci ruwan sama ya taɓa lafiyar jikin shi to kuwa ranar sai kwanan hospital  yake.....kasancewar jikinsa da kuma  waizer nashi sammmm baya buƙatar  dukan ruwan sama, lafiyayyun ƙafa funshi ya fara Zirowa cikin ruwan, kafin yafito gaba  ɗayansa yana sauƙar da laimar zuwa saman kansa, Bala mai gadine yafara jeromai kirari kamar kullum.....


"Ginshi ƙin dutse, kowa ya yi karo da kai shika faɗi, Soja mazan fama! Namijin mazaje, Anbuga dakai ambarka, Saidai su buga su barka. domin kai ɗin hadari ne malafar duniya, funkasau kake babban girki!, kaɗangaren bakin tulu a barka ka ɓata ruwa a kasheka kuma  ka fasa tulu. Kabewar kan kabari baƙin cikin me taushe, murucin kan dutse kake baka fito ba saida ka shirya ALIYU ABDULLAHI KAMAAL, Allah yakawo albarka uban gidana"

   Haka Balan  ya jero masa duka uban kirarin nan, Duk wannan uban kirarin da yake shi kuwa BOSS ɗin harya wucewar sama bayan yazubamar kuɗin da shi kansa baima san ko nawa bane.  Directly yana nufar babban parlourn duka mahaɗan gidan. Tamkar yacce 

 ya tsammata kuwa babu kowa a parlourn, don haka kai tsaye ya nufi hanyar upstairs nashi  cikin tafiyar sassarfa domin wani irin turirin dake hurowa daga cikin tsaƙiyar ƙirjinsa. Bai son ya haɗu da kowa da komai a cikin gidan nasu nasu. Se dai kashhh adda'an nan tashi bata ci ba domin kuwa yana gab da isa upstairs ɗin ya tsinkayi muryan Mahaifinsa mafi soyuwa a cikin duniyar su. Yana me furta. "Lafiya kuwa  AA yau kake dawowa gida da wuri haka cikin wannan ruwan kuma?"  cakkk ya dakata yana sauƙe wata ɓoyayyar ijiyar zuciyar da tazo masa a hagunce. Tare da fasa taka ups ɗin yana nufo mahaifin nasa, "Babu komai Pappu Naaaaaaa kawai dai yau ɗin yana yin gajiya nake ji, kuma ban san hayaniya da ihun waɗan can marasa amfanin a aka!"  ya yi maganar yana wani lumsu idanun da dama kusan kullum suke a lumshen. (Gado ba karan bani ba) Mahaifin nasa ya furta yana ɗan shafa saman kan yaron nasa tare da furta." Ok to shi kenan maza aje a ɗan huta, dama ina ta tunanin yanda zan dakatar da wannan aikin naka haka nan"  Seriously ya dawo da duban nasa kacokam kan mahaifin nasa, domin a duniya idan da abinda yafi tsana shi ne raba sa da aikin da Mahaifin nashi ke yawon ambata mishi. Wani kwaɓe fuskar nan yayi like yaron goyen nan, tamkar ba wannan tsayayyen sojan bane gabansa. Ya buɗe baki kenan da nufin sake furta wata magana idanunsa ya sauƙa akan ƙanwarsa da ita kaɗai ce wacce ya mallaka a cikin duniyarsa.  Fuskarnan ya matse take domin ma gudun kada ta kawo mishi wani wargi ko wasa. Ita kuwa daga inda take tsayen ta zuba masa idanunta, tana sauraren bugun zuciyar ta akan yayan nata. A can ƙasan zuciyar ta take furta. ~Astougfiroulla waa'atubi ilaik~, domin shaiɗain ɗin da a kullum kwanan duniyar yake kwaɗaita mata wani abu me kama da son yayan nata, kwaya ɗaya talll da ALLAH ya bata a duniya.  Ko kafin ta dawo da dubanta zuwa gare shi har ya ɓace a wurin tamkar kububuwa. Wata nannauyar ijiyar zuciya ta sauƙe wanda yasa mahaifin ta dake tsaye dubanta kaɗan, shima yana sauƙe tashi ɓoyayyar ijiyar zuciyan, Yana me furta. "Nufaisan Pappu  bakiy bacci ba har zuwa wannan lokacin?"  kanta ta ɗaga mishi  cikin amintaccen sautinta ta ce. "Pappu zan duba jikin  AMMEY ne!" kansa ya gyaɗa mata ita kuma tana sauƙowa ta nufi ɓangaren mahaifiyar nasu da bata jin dadi, Dake ita ɗin cikakkiyar likita ce ya sanya da kanta take dubata a gida. 

   ♡ 

  Ɓangaren Captain AA kuwa tin da ya wuce samansa be fito ba se wajejen sha biyun dare, inda be dawo gidan ba se wajen karɓe biyu da wani abu. ☆ Sosai yasha barcin sa mai rai da  lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. domin bayan ya dawo daga fitar daren da yayi sosai yayi aiki a cikin laptop nashi,wanda ya raba dare yana yi. Sallar asuba ma daƙyar ya fita masjid dake cikin anguwar yayo. 

Ahankali ya soma buɗe lumsassun Idanunsa da har yanzun suke cike da barci, santala santalan  fararen sawayensa ya fara zubowa saman tattausan carpet ɗin dake gabansa.

 Kafin  A natse kuma ya miƙe yana nufar haɗaɗɗen bathroom nashi, shower ya sakamar kansa sosai ruwan ya dake shi, kana ya tara ruwa masu ɗumi da daɗin ƙamshi a cikin bathtub,Wanda gefe da  bathtub ɗin akwai  drawers masu yawa da wata full sized jaccuzi da kuma site ɗin wata striated rectangular glass shower, dake fidda wani irin ƙyalli, kamar ba'a taɓa amfani da shi ba. shima gefen sa da akwai fixtures masu ɗaukar hankali sosai. Yaja tsahon loƙaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe fari tasss mai azabar taushin tsiya da tsada, dan har wani ɗan maski-maski take yi tsabar taushi da kuma laushinta,da mini towel ɗin dake a hannunsa ya shiga tsane  jiƙaƙƙiyar  tulin sumar dake kansa mai tsaho, Fuskar nan a tsuƙe Samm babu alamun rahama a cikinta. Kai tsaye gaban ƙaton mirror'nsa ya nufa cikin tafiyar jin kai da kuma isa. Hand dryer dake saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da himilin sumarsa da tafi kama data ƴanƴan larabawa, lotions ɗin dake jere saman mirror'n ya shiga shafa wa jikinsa sama sama. Saida ya mulke jikinsa da spray's nashi masu azabar ƙamshi da tsada, kafin ya nufi gaban wardrobe nashi data kusan cinye bango guda.

  Tsabbb yayi shirinsa cikin wasu haɗaɗɗaun track suit baƙaƙe, sai glass ɗin daya sakaye idanunsa a ciki tare da facemask ƴar gadon, phone's nashi kaɗai ya diba yana nufar main Parlour, cikin takun cikakkun mazan dake ji da kansu. A natsensa yake saƙƙowa cikin wannan yanayin na kamewa da muskilanci yake saƙƙowa a saman stairs ɗin, Hannuwa sa zube cikin suit nashi. Hangota yayi zaune cikin babban parlorun nasu   hannunta riƙe da mug tana sanye cikin wata doguwar rigar  Jallabiya ta mata, gefen ta Kuma wata kyakkyawar mata ce da kallon farko zaka san cewar itace mahaifiyar wacce ke zaune kusan ta, Zaunen ya kai shima a kusanta yana amsar mug dake hannun Nufaisa ɗin tare da ɗan sipping shayin kaɗan bada yawa ba. "Kafito kenan?" Mahaifiyar nashi ta faɗi tana kallon sa, da kai ya amsa mata domin yana tashi yaji zuciyansa tamay nauyi, Seda ya ɗan seseta kana ya iya buɗar baki yana gaida ta tare da mata yaya jiki, da sauƙi ta amsa shi yana tambayarta Pappu fa?, ce wa mishi tayi ai be dawo daga masjid ba, Yana ƙoƙarin miƙewa muryanta ya dake cikin ƙofofin kunnuwansa tana furta. "Barka da safiya loly" da hannu ya amsa ta yana mata kallo ɗaya ya wuce abin sa. Itan ma zama kaɗan ta  ƙara tama  ammeyn nata sallama ta  fice zuwa wurin nata aikin. 


  A compound na gidan suka haɗu dake taga yau duk ɗin shi baya a cikin mood me dadi ne ya sanya ta shigewarta cikin tata motar, tare da mata reverse tana riga shi fita a gidan. Wata nannauyar ijiyar zuciya ya sauƙe yana dena bin motar nata da kallo. Wai shin me yake damun sa akan gudaliyar ƙanwar tashi?. Haka ya tambayi zuciyar sa. 


Tambayar da koni kaina AMMEY LAYLERH 🤗 bana da amsar ta lol😂😂 .....




Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 

A gimtse 🫰 🙃♥️✅


Haka ɗanɗanonsa yazo🤗🤗 🤗 🤗🤗  🤗  🤗, A kuma haka zamu bishi.......... 


_Duk wanda ya shirya bin wannan tubka tubkar se ya biyo ni AMMEY LAYLERH 🤗, domin jin wai a wannan karon ya take ne?, ya tafiyar zata kaya?...... _


*BY AMMEY LAYLERH ✍️*



_My phone _


08104493215

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post