Jirgi Mai saukar Ungulu yayi sanadiyar rushewar Gidaje Hudu a Kaduna
A jiya Laraba 10 ga watan Satumbar Shekarar 2025 wani jirgi mai saukar Ungulu ya samu yin shawagi a garin Keke dake yankin Millennium City, a Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.
Jirgin da ya kai kimanin awa huɗu yana wannan Shawagin, a sanadin wannan shwagin da jirgin ya dauki lokaci yana kai komo, ya janyo rushewar gidaje da jikkata Wasu mutane na wannan yakin.
Masu unguwannin Gabas da na Yamma dake Keke B sun ce sunyi mamakin Al'amarin, don wasu lokuta akan sami irin wannan kaga jirgi yazo ya wuce, amma na jiya ya sha ban-ban, da tsoratarwa"
Har ila yau jagororin wannan yankin sun kara bayyana godiyarsu ga Gwamna Uba Sani na kokarinsa kan tabbatar ta tsaro a faɗin jihar.
Bayanan wasu da abin ya shafa sun bayyana takaicin faruwar Al'amarin, inda suka koka akan gwamnati da ta dubi lamarin, musamman a zamanin damuke ciki na rashin tsaro.
A wani lamarin kuma, Tawagar Jami'an Sojin sama ta Najeriya ta ziyarci wannan Unguwa don ganin abinda ya faru tare da Jajantawa waɗanda abin ya faru dasu.
Tawagar sun zagaya duk inda abin ya faru tare da jagorancin masu unguwann
in yankin.
Cikakken rahoto 🚁👇👇