Ginshikin Dutse page 15&16 Complete by Ummu Affan

Novels elite complete

GINSHIƘIN DUTSE...

    _True life store._

*BOOK 1*

     _Gawurtattu uku._


        ©UMMU AFFAN


*Page 15-16*

Surayyah tana fita ƙofar gidan suka haɗu da malam Nura. Da sauri ya ƙaraso gabanta da cewa, "Surayyah daga ina haka?"

Ɓata rai tayi a ranta tana cewa 'Yaga fa daga inda na fito amma yake tambaya.' Ƙasa tayi da kai kamar zata yi kuka da sauri ya ɗago fuskarta.

   "Lafiya kuwa?"

Ƙwaɓe baki tayi kafin ta ce, "Ai ka ƙyauta, jiya ba ka ce zaka zo ba?"

  "Kiyi haƙuri Surayyah, wallahi ina tsoran faɗan Appa ne, kin ga yaja mini kunne ban so ya ɗauke ni a mara jin maganar manya."

Kallonsa tayi tana mai jin ƙara ƙaunarsa a ranta, ko ba komi ta san idan ta auri Nura zai mutunta al'amuranta, gabanta ya faɗi tunowa da maganganun Baaba, sai ta ce,

   "Na shiga nemanka sai Zulaihatu ta cewa Baaba wai bana jin magana ina da rashin kunya, ita kuma Baaba ta hau ta zauna ta dunga zagina. Ni dai ban ce mata komi ba.''

Ta ƙarashe kamar zatayi kuka cike da maƙyirci. Numfashi ya fesar da cewa, "Kiyi haƙuri Surayyah idan na shiga zan mata bayani, ai bazata ɗauki maganar Zulaihatu ta bar tawa ba." Jin haka sai hankalinta ya kwanta cikin dariya ta ce, "Ɗazu na amso jarabawata naci kwaminiti."

  "Ah ma sha Allahu kin yi ƙoƙari sosai, Allah ya bada sa'a. Ki mayar da hankalinki yanzu kin shiga Secondary ba kamar Primary take ba."

   "Ana cin zali sosai ko?" Ta faɗa tare da ƙure shi da ido.

  "Idan kayi rashin ji ai za a zaneka, amma idan ka natsu ba mai bugunka."

Girgiza kai tayi a ranta tana ayyana ai kuwa duk malamin da yaci zalinta ba yarda zata yi ba.

  "Ki koma gida Surayyah shidda har ta kusa bana son yawan yawon nan naki wallahi."

  "To ai kai ne baka zuwa, ni kuma idan ban ganka ba damuwa nake shiga."

  "To zan dinga zuwa, amma kin san dai halin Appa."

  "Kar ka damu ka faɗa mini lokacin da zaka zo sai mu haɗu ko a bayan layinmu ne."

  "To zanzo gobe da yamma idan munyi sallar la'asar tunda naga gobe baku da islamiyya."

  "To Allah ya kai mu goben lafiya."

Sallama suka yi ta wuce tana ɗaga masa hannu shi kuma ya shiga cikin gidan da sallama, daidai Baaba na tuƙa tuwa.

   "Sannu da gida Baaba."

Ya faɗa tare da zama saman ɗan sumintin da ke ƙofar ɗakinta. Juyowa tayi da tubesa kafin ta juya taci gaba da tuka tuwan tana cewa,

   "Yawwa Dini ka shugo?"

   "Eh!"

Ya furta daidai lokacin da yake hararar Zulaihatu da ta fito daga banɗaki, da sauri tayi ƙasa da kai tare da ajiye butar, sumi-sumi ta doshi hanyar ɗaki, ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar kiranta.

   "Zulaihatu zo nan."

Jikinta a sanyaye ta ƙara so, domin ta san halin Yaya Dinin sam baya wasa da ƙannansa. (Haka suke kiransa a gidan da Dini wato Nuraddini.).

Ƙasa ta duƙa tun kafin ys fara magana ta ce,

  "Wallahi ni ba abinda ya haɗa ni da Surayyah, kuma ga Baaba nan ka tambayeta, rashin kunya kawai tazo ta dunga yi wa Baabarmu. Ko ba haka ba Baaba?"

Ta ƙarashe da tambayar Baaba wacce ta rufe tuwan ta taho gurinsu da niyyar ya sulala ta kwashe.

 Ta ce, "Idan ma ana maganar rashin kunya ai mai sauƙi ne, yarinyar ta shugo har gidana ta zage ni! Wallahi na tsane ta, Allah suturu buƙi wai na haɗa jini da wannan almurar 'yar, wa ya aike ni balle ya ga na daɗe a'a a'a wallahi ba da ni ba wai gaɗa a hurumi."

Nura da gabansa ke dukan tara-tara jin furucin mahaifiyar tasa akan masoyiyarsa, masu iya magana na cewa 'So hana ganin laifi.' Shifa duk abinda ake cewa Surayyah nayi sam idanuwansa sun rufe baya gani. Ya ce,

   "Baaba kiyi haƙuri, baki fahimci Surayyah ba, na san Zulaihatu ce duk taja komi da ta faɗa miki ƙarya akan ta."

  "Oh wo haka ta faɗa maka? Oh ni jikar mutum huɗu to bari kaji da babbar murya ba kai ba wannan fitsararriyar yarinyar. Yaushe ma ta tafasa balle ace har ta ƙone? Kai da a kakar bana nake sa ran aurenka da Nafisatu 'yar wajen Gwoggonka Binta, shi ne zaka yayifo mini wannan kwailar 'yar da ko irgar dangi bata fara ba, a'a ba da Ramatu za a yi haka ba na ma faɗa maka."

Ƙasa ya yi da kai domin duk faɗan Baaba sam baya iya jayayya da ita, shiɗin yana da biyayya ga mahaifiyarsa har mamaki ake yadda Allah ya bata Nura a matsayin ɗa. Domin ko Muttaƙa ƙaninsa sam baya jin maganar Baaba sai ma mugun halinta da ya kwaso, duk a yaranta ba ɗaya tamkar dubu ya Nuran.

Ganin yaƙi cewa komi, daman ta san a rina domin bai cika bata amsa kai tsaye ba ta ce,

   "Nifa a wannan gaɓar ba na son shuru, maganantuwa zaka yi domin tun wuri ka fitar da wannan yarinya a ranka don nikam bazan yarda ka aureta ba."

Ɗan murmushi ya yi wanda zallarsa yaƙe ne.

  "To me zance Baaba? Tunda Zulaihatu ta gama shirga miki ƙarya?"

  "Oh haka zaka ce? Nifa ba abinda Zulai ta faɗa mini wanda ban gani da idanuwana ba, ai har yanzu da sauransu ban makance ba."

  "To Allah ya baki haƙuri Baaba."

Juyawa tayi tana ci gaba da jan tsakinta ta nufi wajen kwashe tuwanta sai masifa take, bai ce komi ba sai hararar Zulaihatu da ya dunga, kafin ya miƙe ya ɗauki buta jin an fara kiran sallar magrib.

 A daidai lokacin Surayyah ce liƙe ƙofar wani gida tana hango Appa yana alwala a ƙofar gidansu, tunda ta shawo kwana daga yawan da suka koma da Hindu tun bayan barowarta gidansu Nura sai yanzu suka dawo. Hango Appa da tayi zaune da buta a ƙofar gida yasa tayi tsayuwarta a gurin, lokacin da ya taso zai yi alwala da aka fara kiran sallah sai ta ɓoye jikin gidan da take tsaye domin kar Appan ya hangota. Tana gurin har ya idar da alwala, Yaya Auwalu taga ya fito ya amshi butar ya mayar cikin gida kafin ya fito suka wuce masallaci.

Ajiyar zuciya ta saki tare da fitowa daga maɓoyarta ta dushi ƙofae gidan. Har ta shige bata kuma cin karo da kowa ba da alama sauran yayun nata duk basa gida, Mardiyyah ce bakin rariya tana alwala sai Innana da ke kwashe tuwon jiƙaƙƙiyar masara a kwanuka. 

  "Sannu da gida Innana." Ta faɗa cikin kame-kame, kallo ɗaya Innana tayi mata ta kauda kai ba tare da ta ce mata ko ci kanki ba. Ganin haka ta san yau da daru kenan tsakaninsu, ɗan kaɗa kai tayi tare da ɗaukar butar da Mardiyyah ta ajiye ta zuba ruwa, banɗaki ta fara shiga kafin ta fito ta hau alwala duk ta neman sulhu ce don bayi take ba.

  A ɗaki ta iske sauran 'yan'uwanta duk suna sallah. Daman ko cire hijabinta bata yi ba ko alwalar da shi tayi ba shafar kai da ta kunne, wani tsumma ta jawo ta shimfiɗa tare da tayar da sallah.

 Kubrah wacce ta fara idarwa ta bita da na mujiya tana girgiza kai, 'yar baki ba yawa sai lada tayi. Kubrah da ta kasa jurewa ganin har ta riga Mardiyyah idarwa ta ce,

   "Nikam Surayyah sallah ki ka yi kuwa? Kamar fa baki karatu sai dai kiyi ruku'u ki yi sujjada aka ake sallah?"

  "Idan baka yi ba ace kaƙi yi, idan kayi kuma ace baka iya ba, to ya ake so mutum ya yi?"

  "Ni dai nasihata gare ki ki gyara ibadarki Surayyah domin akwai gyara sosai."

  "To naji!"

Ta faɗa tare da murguɗa baki ta miƙe ta cire hijabinta ta koma kan katifa, daidai shugowar Innana sai jin saukar bulala tayi ta ko ina a jikinta. Ihu ta kurma don da farko bata ɗauka Innana ba ce tayi zaton ko Appa ne, amma ɗagowar da zatayi taga Innana ce.

  "Na shiga uku ni yau, to me na miki ki ke buguna?"

Surayyah ta tambaya cike da rashin kunya.

   "Ubanki kika mini, na ce ubanki kika mini Surayyah. Ke wacce irin shaiɗaniyar yarinya ce, kina mace amma ba zaki zauna a gida ba tun rana sai yanzu zaki shugo gida saboda shegen gantali da yawonki."

 Faɗa take kuma bata daina bugunta ba, da sauri Surayyah ta miƙe tana tura baki ta ce, "Gidansu ƙawata fa naje, to ina kuma zanje da ya wuce can, kullum ku ba kuyi mini fatan alkhairi sai na tsiya."

  "Ni ki ke faɗawa haka don ubanki? Yau sai na fasa bakin." Ta kai mata bugu a bakin ai kuwa ya fashe, zafin da Surayyah taji ne ya saka ta sakin ƙara tare da riƙe bakin, ganin ta lakutu jini kuwa ta kama Innana da kokawa.

  "Na ba ni na shiga uku, wayyo ni wayyo Allahna wayyoh!!!"

Surayyah ke faɗa tana ƙara jijjiga Innana wacce tayi suranda ganin Surayyah na neman jigata ta. Mardiyyah ce ta ture Surayyah da ƙarfi har tana faɗuwa saman katifa da sauri ta miƙe, ta ce,

   "Ke baki da hankaki ne? Da Innana zaki yi kokawa?"

Ai sai Surayyah tayi kukan kura ta afkawa Mardiyyah yadda ta tura da da karfi har tana bige Innana gabaɗaya suka faɗi ƙasa warwas Innana ta fashe da wani irin kuka....

GINSHIƘIN DUTSE...

    _True life store._

*BOOK 1*

Post a Comment

Previous Post Next Post