🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Page 13/ 14
04 / 05 / 2025
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم
Maryam ta shafa gumi a goshinta, hannunta na rawa sai yanzu zafin jikin da ya ɗauke ta tun safe ya fara raguwa duk da haka, Idanunta sun ƙi buɗewa sosai, sai ihun zuciya da tafasar hawayen da take riƙe.
"Ihsan..." ta kira da rauni, "zan iya tafiya."
Ihsan ta rungume ta, hawaye na gangarowa daga idanunta. “kin ƙarfafa zuciyata fiye da yadda na zata,” ta ce cikin sanyi
Su Yazid, John da Ado sun zuba ido, zuciyoyinsu cike da yanke shawara basu da ƙarfi sosai, amma lokaci yana guje musu.
“Yanzu ko ba yanzu ba ne idan yanzu muka tsaya nan wata rana, za a cafke mu.” Yazid ya ce da ƙarfi, yana gyara jakar sa a bayansa.
sukai shiru har sai da aka ji murya kamar ƙarar iska daga can nesa sai suka lumshe ido, suka lumshe zuciya.
Su biyar suka tattara kayan su da ƙarancin haske suka ratsa cikin duhu, gaban su cike da fargaba, amma babu wanda ya waigo baya,
Gabar boda na ƙasar Libiya ba kasafai ake iya shige ta da sauƙi ba. Rana ba ta faɗuwa sosai a hamada. Gashi da ke fesowa daga ƙasa kamar harshen wuta, yana fitar da zafi da ƙamshi irin na ƙasa mai mutuwa babu bishiya, babu ruwa, sai yashi mai girma kamar kogon wuta.
Tsakanin dare da kwana biyu, sun ratsa titin ƙasa da ƙafa, su na bin jagorar wani tsoho wanda suka biya sauka-ka-tafi tsohon yana da hannu biyu kawai, amma gwaninta da sanin hanya sun fi soja da komfuta.
“Yanzu nan,” ya ce da ƙasƙantar murya yayin da suka isa ƙaramin rami da aka lulluɓe da dausayi. “Nan ne na ƙarshe kafin ku tsallaka Libiya. bayan nan, ba ruwa, babu tsaro kawai da zuciyar ku kuke tafiya.”
“Shikenan,” Yazid ya ce, yana gyara rigarsa. “za mu fuskanta.”
Maryam ta kama hannun Ihsan. “In muka tsallaka, to Allah ya bamu mafita.”
John ya lumshe ido. “I’ve never seen darkness this wide... but I feel hope.”
Suka shiga cikin hamadar da babu ƙyalli, suna tafiya suna shan iska mai zafi kamar wuta tana hura musu cikin hanci, cikin dare, rana tana walƙiya, ba saboda haske ba – sai saboda yashi yana motsi kamar ruwan teku.
Ado ya ce da jinjina kai, “wannan garin ba na mutane bane...”
“amma mu fa mutane ne da mafarki,” Ihsan ta ce, murya kamar zuma “mu ma muna da hakkin tsira".
Zuwa wannan lokaci, tafiyarsu daga bodar Libiya ta ɗauki kwanaki, daga na farko zuwa na biyu, ƙarfinsu yana ragewa. Na uku sun fara kwana da cikinsu babu ruwa, babu abinci rana ta huɗu, numfashinsu ya zama kamar na dabbobi, idanu sun ɗebe, fata ta bushe ta fara fashewa.
Hamadar Sahara ba fili bane na yashi kawai wani lokaci dutse ke cikinta, wani lokaci gami da koguna da suka bushe shekaru da suka wuce amma duk inda suka kalli yanzu, sun haɗu da komai: rairayi masu santsi, ƙasa mai zafi, iska mai ƙarfi da tsintsiya da ke ɗagawa daga ƙasa har sama kamar baƙin hayaki.
Maryam ta fara jan ƙafarta a jikin yashi. takalminta ya dade da karyewa, yanzu ƙafarta bare – jajaye sun yi, cike da toka, ƙyalli daga rana. “Ihsan... ruwa... just one sip,” ta furta kamar mafarki.
Ihsan na bin ta da ido, kanta yana juyawa. Idanunta sun canza launi, sun zama kamar ƙwai, ba su da ƙyalli gashinta ya manne da gumi da ƙura, har ta daina jin sauyin iska. “Ba ruwa, ba komai amma ki tsaya Maryam... ki tsaya.”
Yazid yana gaba, yana rarrafe, yana fitar da numfashi kamar wanda aka sakar daga ƙarƙashin ruwa. John yana masa baya, amma yazo ƙasa. “I can’t feel my tongue...” ya ce da harshen da ya fara murɗewa.
Ado, wanda shi ke riƙe da jakar kowa, ya durƙusa. “I’m seeing mirages I saw my mother – she was standing in water, calling me.”
Yashi ke rawa, rana ke ƙuna. Iska ta taso – iska mai nauyi, ƙamshi kamar zafi duka suka durƙusa, suka lulluɓe kansu da tsintsiya da kaya, amma iska ta kwashe su kamar hayakin gobara sun yi ta birgima kamar jakunkuna, har aka jefar da su zuwa wani ƙaramar rami – wani tsibiri a cikin sahara, tamkar tafkin dutse da ya bayyana daga ƙasa, cikin haka suka faɗi su ka suma.
Wani lokaci daga baya...
Cikin ɓangararren inuwa da aka samu daga wata harsashen dutse, suka farka jikinsu a sanyi, amma cikin yashi babu ganye, babu ruwa, babu abinci. sai ga jikinsu ya fara nuna alamar rushewa – la'bbansu sun fashe, hancinsu ya bushe, idanunsu ba sa kallon juna, fatar hannu da ƙafa sun fara murɗewa, ta rikiɗe tamkar kaho
“Zan mutu,” John ya furta, yana kallon sama, “Ba ruwa na sha fitsari na jiya ba zai isheni yau ba.”
Yazid ya kalli jikin sa, ya ji kamar naman jikinsa yana motsi. ya taɓa fatarsa – ta cire. “Wallahi mun gama.” ya fashe da kuka, amma ba kukan da kake ji ba ƙara, sai hawaye masu zafi kamar gawayi.
Ihsan ta lumshe ido, ta kai bakinta ga wani ƙaho da ke ƙunshe da ragowar fitsari. ta sha kadan gaban Allah, ya fi komai wannan ba lokacin kunya bane, ko tsoron mutuwa. wannan yanayi ne da rayuwa take ƙi barin jikinsu , Maryam na jingine da dutse, tana kallon jikin ta kamar ba nata bane. “I’ve become sand,” ta ce. “Even my voice sounds like wind.”
Daga nesa...
Ado, wanda ya fi ƙarfinsu kaɗan saboda tsawon jikinsa da kwazon zuciyarsa, ya fara bin duwatsu da sandar da ya kakkarya bayan lokaci – sai ya hango wani abu wani rami mai zurfi da ke wani rami kamar tukunyar wuta. Yayi tsalle, ya kalla – ƙananan ragowar ruwa!
Yayi ihu kamar kura mai murna: “Ruwa! Wallahi, ruwa!” ya dawo da gudu yana faɗuwa, yana hura numfashi kamar za a sa wuta a jikinsa. “gashi chan ! gashi chan!”
Suna ta matsowa da karfin halin da ba su san inda ya fito ba. kowa da dabara, suka tsinke leda, suka tattara ƙwanƙwaso daga jikin su, suka kai bakin su... dan kadan, amma ceto. sannu a hankali zuciyarsu ta dawo ba da kyau ba, amma da rayuwa suka kwanta, suka kalli sama, tsibirin da suke kai tsaye ne a tsakiyar Sahara, ba ruwa sosai, amma nan ne Allah ya basu mafaka.
Yazid ya ce da karamin dariya, “Idan muka tsira daga nan sai na ce duniya ba baƙi bane. duniya rana ce da yashi, amma ina da mafarki.”
Ihsan ta ce, “Na fi son mutuwa da mafarki fiye da rayuwa babu buri.”
Maryam ta rufe idanunta " ya Allah mun gode maka da kyautar ruwa lallai ruwa zai rayu inda ba halitta amman mutum bazai rayu ba ruwa ba "..
Ruwan da suka tsinci ya zama tamkar aljanna. kowa ya samu ɗan kaɗan ya ji cikinsa ya huta. bayan kwanaki biyu a cikin wannan tsibirin – inda babu ciyawa, babu dabbobi, amma akwai inuwa da ƙaramin ramin ruwa – sai zuciyarsu ta ɗan dawo.
Ihsan ta janye rigarta mai sheƙi, ta taka da ƙafarta mai jini zuwa ga sauran su, ta ce cikin sanyin murya:
“Ku ji ni mana...”
“Mu ne matafiya,
Wanda ba su da gida,
amma zuciyarmu da rai,
suna cikin mafita...”
Maryam ta kama hannunta, suka fara juya da kasala, suna dariya da hawaye. Yazid da Ado suka buga ƙafa a yashi, John ya murɗa murya kamar yana wake, sai suka kama da karfi.
“Ruwan nan, ka ceci mu,
yashi da rana sun cinye mu,
amma muna raye,
muna tafe – cikin fata!”
Sai suka rungume juna – gaba ɗaya biyar – suna sharar hawaye, suna murza fatar jikinsu da suka rasa. Wannan rana ce da suka yi murmushi cikin azaba.
" Bayan wata akwai haske
Bayan wuya akwai daɗi "...
Bayan sati biyu a wannan wuri, ruwa ya kusa ƙarewa sai suka yanke shawarar ci gaba da tafiya, domin sun san idan sun zauna za su mutu da yunwa da ƙishirwa. sun ɗaura jakarsu da fata, suka fito daga tsibirin suna zamewa a yashi.
Kwana biyu sun yi suna tafiya cikin rana da yamma. rana na dafa ƙafarsu, yashi na kai musu zafi daga ƙasa. idanuwansu sun fara ganin abu biyu, zuciyarsu ta fara shakku da juna. Maryam ta fara rikicewa, ta yi ihu tana zagin Yazid tana cewa:
“Ka ce zaka kawo mu Dubai! ka ce za mu ci kuɗi! Ashe ba haka bane?!”
John ya zube a ƙasa yana dariya da kukan hauka. “We’re already in Dubai – in hell's part!” Ihsan da Ado suka kama su, suka kwantar da su kamar yara.
Bayan wata guda cikin tafiya da yunwa, sai suka hango wani gari daga nesa – amma ana shigarsu kusa da shi sai suka ji hayaniya. mutane masu bindiga da dabbobi ke yawo a kusa – mafarauta ne amma ba na noma ba – ‘yan fasa-ƙwauri ne da ke farautar masu tsallaka haddi don su sayar da su ga masu aikatau ko masu fatauci.
Sun kamasu a dare sun ɗaure su da igiya, suka ajiye su a cikin wani daki tamkar kurkuku da yashi a ƙasa. Maryam ta fara kuka, John ya yi shiru yana kallon su kamar wanda ya hakura da rayuwa. Yazid ya yi ƙoƙarin fita, aka yi masa dukan tsiya, aka zubar da jininsa.
Ihsan da Ado sun tsaya suna kallon juna da hawaye. Ado ya ce:
“Na rantse, idan muka tsira daga nan, ko ruwa ne, ko wuta, zan kawo ki gida da hannuna.”
Ihsan ta runtse ido. “Zan riƙe ka da zuciya har ƙarshe.”
Continued .............
by narnah ƙanwar soja ✍️✍️