Ginshikin Dutse page 13&14 Complete by Ummu Affan

Most Watched Youtube Videos 2025

GINSHIƘIN DUTSE...

    _True life store._

*BOOK 1*


      ©UMMU AFFAN


*Page 13-14*

"Kin shugo kenan? Ai na ɗauka a wajen zaki ta tsayuwa." 

Hindu ta faɗa ko a jikinta ganin shugowar Surayyah, tana zaune bakin wata yamutsatstsayir katifa wacce taji jiki, duk yadin jikinta ya gama fita a hayyacinsa. Kallon ɗakin Surayyah take a ranta tana ayyana 'Wannan ake kira gaba da gabanta, wai Aljani ya taka wuta. Domin duk yadda su Mardiyyah ke kiran rashin tsaftarta, ashe akwai iyayen gidanta.'

Shugowar Sabitu da saka sakatar shi ne ya sakata saurin zama kusa da Hindu tana sauke numfashi, domin ɗakin gabaɗaya warin jikin maza yake irin 'yan ciranin nan.

  "Wallahi Hindu ya kamata dai ki wayar da ƙawar nan taki, sam tana abu kamar 'yar ƙauye."

Gyaɗa kai Hindu tayi da cewa, "Ai yanzu na gama mata tsiya wai shugowa ne da taƙi sai kace wasu baƙi."

  "Ai abinda nima na gani kenan, yanzu mun riga da mun zamo ɗaya."

Farantin gurasarsa ya zamo, tare da ciro ledar da ya zuba musu gurasar ya miƙawa Surayyah.

   "Yau dai ga alƙawarinki, na huta gori na kullum."

Tana murmushin yaƙe ta ce, "Na gode Sabitu."

  "Haba ba komi ai kin fi haka a gurina."

Da sauri ta miƙe tana duban Hindu da cewa,

  "Ki tashi mu tafi."

  "Haba Surayyah kamar ana figar namanku, tun yanzu?"

Sabitu ya tambaya fuskarsa ba walwala.

  "Nima dai haka na gani, tunda ba kowa ai kya bari ko gurasar ce muci anan, kin fi so muna hanya muna ciye-ciye?"

Cewar Hindu tare da jawo hannun Surayyah ta koma zaune. Ita dai ba sabawa tayi ba, duk sai ta jita a ɗarare. Tun warin ɗakin na dabunta har ta daina jinsa sai sama-sama.

Hindu kuwa gurasar ta buɗe wacce taji ƙuli-ƙuli ga albasa da tattasai da kokonba duk an yanka a ciki har da kabeji. Ganin gurarsa ya saka Surayyah murmusawa ta fara ɗauka tare da kai bakinta, haka suka dinga ci ita da Hindu sai santi sukewa Sabitu wanda tuni ya dawo kusa da su hannunsa a hijabin Hindu.

Sam Surayyah bata lura ba sai daga bayan sun kusa cinye gurasar. Gabanta ne ya faɗi ganin abinda Sabitu kewa Hindu ita kuwa ko a jikinta, cire hannun ya yi yana lumshewa Surayyah ido wacce tayi saurin yin ƙasa da kanta. Nera ashirin ya ba Hindu ya ce taje waje akwai kanti ta amso musu ruwan leda guda huɗu (A lokacin ruwa biyar-biyar ne) Ba musu ta amsa shi ya buɗe mata ƙofar, tana fita ya dawo kusa da Surayyah tare da riƙe hannayenta. Ita kam nan take jikinta ya fara rawa abinda ba a taɓa mata ba, idan tana taya Hindu talla maza na kama hannunta amma saboda cikin jama'a ne bata maida hakan bakin komi ba, yau kam da take daga ita sai Sabitu kuma yadda suka kusanta da juna da ruƙon da ya mata sai jikinta ya ɗau rawar ɗari. Tana ƙoƙarin fincike hannun ya ƙara damƙewa da ƙarfi.

   "Wai ke Surayyah kina abu kamar 'yar ƙauye, shi ya sa naso kizo ki kaɗai domin muyi wani abu da muke yi da Hindu, kuma kuɗi zan baki idan kika saki jikinki, amma kina abu sai ka ce kidahuma."

Jin furucin Sabitu ya ƙara girgiza ƙwaƙwalwar Surayyah ta zuba mi shi ido cike da tunanin wanne abu ne yakewa Hindu har yake bata kuɗi? Bata da amsa hakan yasa ta dawo da natsuwarta jin yaci gaba da cewa,

   "Yau dai kin katse mana jin daɗi, amma ina so kiyi tunani idan kin koma gida daga baya idan mun haɗu sai ki faɗa mini hukuncin da kika yanke. Zan dinga baki kuɗi fiye da yadda nake bawa Hindu idan kika ba ni haɗin kai."

Jin ana ƙwanƙwasa ƙofa yayi saurin kai hannunsa ƙirjin Surayyah ya matsa da ƙarfi har ƙara sai da ta saki, jin abinda ya mata nan kuwa ƙirjinta ya dunga bugawa, ya miƙe tare da nufar ƙofar ya buɗe. Hindu ce ta shugo hannunta ɗauke da ruwan guda huɗu, amsar biyu ya yi ta miƙawa Surayyah ɗaya tana amsa kuwa ta miƙe.

   "Ni dai Hindu tafiya zanyi kin ga akwai islamiyyah yau."

Duk da ba zuwa take ba, amma a tunaninta wannan ce kawai mafitarta da zata faɗawa Hindu shima Sabitu ya yarda su tafi.

 Hindu ta ce, "Daman yanzu zamu wuce saboda nima yamma tayi nasan Inna tana can tana tunanin ko ban sayar ba ne."

Ɗari biyu ya ba Surayyah haka Hindu ma ya bata ɗari biyun, godiya suka yi ma shi sannan ya raka su har bakin hanya suka gangara.

Surayyah ta dubi Hindu ta ce, "Amma Sabitun nan ɗan iska ne Hindu, kuma a haka har ki ke soyayya da shi? Gaskiya Malam Nurana ba haka yake ba."

Taɓe baki Hindu tayi da cewa, "Ni dai babu ruwanki da cewa Sabitu ɗan iska, shima malam Nuran bai samu ba ne da kin ga halinsa."

  "A'a Hindu, wallahi Nurana ba ɗan iska ba ne, shi da aure yake sona. Amma na luwa Sabitu ɓata miki rayuwa kawai yake son yi."

  "To koma mene ne ai ni ce dai yake so ba ke ba, don haka naki ido. Komi Sabitu keso a gurina zan ba shi tunda shima yana ba ni, kuma tun kafin na haɗu da Alhaji Lawan yake hidima da ni, kuma aurena ya ce zai yi duk da dai yanzu Lawan nafi so akan shi amma ba zan iya yada Sabitu ba."

Ganin Hindu bazata fahimta ba sai ta rabu da ita amma tabbas ta yarda Sabitu ɗan iska ne tunda har ya dinga saka hannu a hijabin Hindu kuma ya daɗe bai cire ba, haka abinda ya mata ta kasa faɗawa Hindun don yadda ta kasa fahimtarta a maganar da suka yi ne ma yasa ta fasa sanar da itan.

Bayan ta ɗauki kayanta sai da Surayyah ta ragata gida sannan ta wuce unguwarsu Malam Nura, bata iske shi ƙofar gida inda ya saba zama ba, hakan yasa ta faɗa cikin gidan nasu ko sallama babu. Baaba zaune tana iza wutar karan da tukunyar tuwanta ke kai, yayin da Zulaihatu ƙanwar Nura ta uku wacce zasu zo sa'a da Surayyah tana zaune gefenta tana tankaɗe garin Dawa yana cikin ƙaramin buhu.

Ganin mutum ya faɗo ba sallama har sun tsorata, ganin Surayyah ce kuwa Zulaihatu taja tsaki, domin sosai ta san Surayyahn bokonsu ɗaya kuma aji guda kafin a cireta a mayar da ita wata. Baaba cikon faɗa da ɗaga murya ta ce, "Me zan gani haka? Mutum ko Aljan? Wannan wacce ballagazar ce zata shugowa mutane ba sallama?"

Da yake Baaba Ramatu mahaifiyarsu malam Nura irin tsofaffin matan nan ce masu faɗa da hargagi sosai. Baka shiga sabgarta ba ma ta tanka balle kuma ka shiga gonarta, sam bata da haƙuri ko kishiyarta Inna Tsaiba ba ƙaramin haƙuri tayi da ita ba tun da har zuwa mutuwarta, haka yaran Tsaiba sun sha matuƙar wahala a gurinta har yanzu da suka girma bata barsu ba.

  Tura baki Surayyah tayi cike da rashin kunyarta ta ce, "Malam Nura na nan?"

Jin wanda yarinyar ta tambaya yasa Baaba saurin miƙewa, domin bata gane Surayyahn ba tana da matsalar idanu kaɗan.

  "Nura! Ki ka ce Nura ki ke nema wace ce ke ɗin?"

Zulaihatu ta ce, "Baaba Surayyah ce fa yarinyar da nake baki labari Yaya Nura ya liƙewa."

Ai da sauri Baaba ta murza ido cikin faɗa ta ce, "Ke ƙundun ubanki, bayan liƙewa ɗana da kika yi a waje shi ne kuma har gida zaki biyo shi? To ni ban haifi ɗan iska irinki ba, maza ki fice kafin na kira Muttaƙa yaci ubanki a gurin nan. Shima Nuran ai na masa faɗa ya kiyaye ki, 'yar ƙanwata Nafisa zai aura ke kam ina ki ka tafasa balle maganar dahuwa, in ce Zulaihatu kin ce ajinku ɗaya a boko?"

Ta ƙarashe da tambayar Zulaihatu dake tankaɗe tana aikawa Surayyah harara domin sosai ta tsani Surayyahn basa shiri ko kaɗan.

   "Eh fa Baaba ajinmu guda wallahi."

Zulaihatu ta amsawa Baaba da sauri.

   "Kama gabanki ki bar gidan nan, 'yar ƙananun mutane. Ance mini fa kwararo-kwarari lungu-lungu haka ki ke yawo wa zai haɗa zuria da ƙafar kare irinki? Wallahi ko da kin isa aure bazan bari Nura ɗana ya aure mace irinki ba, mu haɗa irin bala'i."

Sosai duk Surayyah ta gama shaƙa da maganganun Baaba hatta wanda Zulaihatun tayi. Kallon Baaba take ba ko ƙifta ido, kamar zata kai mata duka. Baaba da ke ƙara buɗe ido ta ce, "Kurwata kur wallahi, idan ma ke mayya ce namana ɗaci ne da shi nafi ƙarfinki, na buga da dubunki ba sun bar ni balle ke ƙaramar alhaki mara kunya." 

Surayyah ƙarasowa tayi gaban Baaba, sai da tazo saitinta ta juya duwawu tare da sakin wata shegiyar tusa ji kake ɓurɓurrrɓurrr. Da sauri Baaba ta toshe hanci yayin da Zulaihatu ta miƙe ta nufi kwatar gidan tana kakatin amai.

   "Yau na shiga uku ni Ramatu, wannan wacce fitinanniyar yarinya ce ke, a hakan zan bari ɗana ya aure ki? To ba da ni ba gaɗa a hurimi, maza ki fitar mini a gida."

   "Ai kema ba gidanki ba ne na Babansu malam Nura ne." Cewar Surayyah cike da rashin kunya, tusar da tayi kuwa ko a jikinta.

  "In ce dai baki da gado a gidan? Don nikam ko ba ni da gadonsa ai 'ya'yana sun isa su cinye gidan balle yanzu malam ya faɗi ya fito har da ni a rabon gado."

Surayyah bata tankata ba ta kalli Zulaihatu da ta dawo tana mayar da numfashi ta ce, "Ke kuma Zulaihatu wallahi zamu haɗu a hanya ne, sai na miki ɗan karen bugun tsiya bar ganin kina gaban Innarki wallahi ko a nan ki ka kuma mini kan kara zan miki na ita ce, don bar raina allura ita ma ƙarfe ce."

   "Yau na shiga uku ni Ramatu, ke dan ubanki zo ki fitar mini a gida."

Hanyar waje Surayyah tayi sai da ta kai ƙofa ta kalli Baaba da ita ma ita take kallo ta ce, "Kuma ko kinƙi ko kin so sai na auri malam Nura ya dawo ƙasana." Tana faɗa ta ruga waje, yayin da Baaba ta riƙe haɓa cike da tashin hankali ta ce, "Wai ni kam Ramatu ina Nura ya yayibo mini wannan sheɗaniyar yarinyar? Ai kuwa zata gane ni ce na haifi Nura ba wata shegiya ta haifa mini shi ba, yarinya ƙarama tun yanzu kina wannan tsiyataku ina kuma da kin riƙa. To bada Ramatu za a ƙulla wannan ƙullaliyar ba."

Haka Baaba tacigaba da aikin tuwonta tana faɗa Zulaihatu na ƙara zugata akan ko da wasa kar ta bari Nura ya ce Surayyah zai aura don ba gamin kifi da kaska idan ba haka ba mallake musu ɗan uwa zata yi. Nan take ƙara sanar da ita irin gantalin da take a cikin gari..

Nan fa Baaba ta ɗaura ɗammarar yaƙi da duk wani da zai kawo mata tarnaƙi, ina ma zata yarda ta haɗa jini da wannan yarinya, sam bata ƙaunarta ko kaɗan, tayi kwafa tare da furta "Allah ya dawo da Nura gida lafiya, shima sai ya faɗa mini dalilinsa na kula yarinyar nan."

Tana aiki tana ƙwafa domin sosai zuwan na Surayyah ya ɓata ranta, har ƙarƙashin zuciyarta take jin tsanar yarinyar....

Post a Comment

Previous Post Next Post