Bayan wata Page 11&12 Complete

Abokiyar Hira Audio

🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗

AFTER THE MOON 


BY

NARNAH KANWAR SOJA 

( Sayeddan Addah )


💫Royal Star Association,💫

SADAUKARWA 

Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 

Zahrah Royal Star  




Page 11 / 12 

04 / 05 / 2025



Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,

mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya 

show me some love guy's 🩷 


بسم الله الرحمن الرحيم 

اللهم صل على محمد وسلم 



Sarkin ya umarci sojojinsa su buga ƙofar mai magani yayin da ya kwantar da sarauniya Rahila a ƙasa da hankali, 


Sojojin sun yi jinkiri, amma daga bisani sun buga ƙofar, sai mai maganin ta fito bayan ta tambayi wasu tambayoyi.

ta saba da mutane da ke kawo marasa lafiya zuwa gonarta a dare, don haka ba sabon abu ba ne a gare ta.


"Prince Tarhim shin ka tabbata da wannan? Mahaifinka sarki yana iya rashin jin daɗi da hakan, " mai maganin ta ce yayin da take duban  Rahila

Ta taba ganinta a lokacin da Prince ya jagoranci ta cikin sarautar su cikin ƙafa, kuma ta fara mamakin dalilin da yasa Prince ke ceton ta yanzu.


"Ni ne zan damu da hakan ke ceto rayuwarta kawai." Prince ya ƙi jin damuwarta.

"Zai yi Prince guba ta ratsa jikin ta gaba ɗaya." mai maganin ta ce "za ki iya ƙoƙarin, taimaka mata."  ya matsa, mai maganin ta fara maganin sarauniya Rahila nan take.


"idan Atishawa tayi bayan ta sha warin wannan maganin da zan kawo, to tabbas za ta tsira, amma idan ba ta yi ba, to ina baƙin ciki, babu abin da zan iya yi, ya Prince" mai maganin ta ce.


"To, sai ke ci gaba." yace ya amince.


Sojojin sun fara magana cikin husɓa suna kallon wannan abin da ke faruwa.

Prince ya koya musu cewa ba su da jin kai ga abokan gaba, kuma yanzu yana aikata abin da ya ke gargadi akai mai maganin ta tafi cikin ƙaramin gida na ta sannan ta dawo da wani haɗin ganyayyaki a cikin ƙaramin kwararan kwano.

da ta kawo warin kusa da hanci sarauniya Rahila, ta atisaye sau da dama amma idanuwanta sun kasance rufe.


"Yarinyar tana da ƙarfin zuciya." mai maganin tsohuwa ta ce, tana girgiza kai kamar tana gano wani sabon abu.


Gaskiya ta gano wani abu sabo saboda babu wanda ya taɓa samun damar atisaya bayan sun sha wannan maganin a irin wannan yanayi.


Ba kawai mai maganin ba ce, amma tana da baiwar ganin gaba, kuma ta iya gano cewa matar da take gaban ta ba ta cikin kowane irin yanayi na al'ada ba.


"Ya Prince za ka iya komawa gida yanzu, zan kula da ita. zai yi kyau." mai maganin ta tabbatar maii


Ya yi tunanin dalilin da yasa har yanzu tana cikin wannan yanayi duk da atisayar, amma mai maganin ta tabbatar masa cewa komai zai tafi daidai kuma ya yarda da ita.


Matar tsohuwa ta kasance mai taimako sosai ga mutanen Zuma, har ta kasance daya daga cikin masu maganin da suka kula da mahaifinsa, don haka me zai hana?


"Ba za ki taɓa faɗa wa kowa ba, har ma mahaifina, abin da ya faru a daren nan. sanan inason ke ɓoye ta zuwa lokacin da zan dawo bayan tafiya tafiya ta ," ya gargadi sojojin sa yayin da suka tafi gida sojojin sun amince da cewa ba za su ce komai ba ga kowa, amma ba abu mai ɗorewa ne ɓoyewa ba. da Prince Tarhim ya dawo gida, wasu tambayoyi sun ci gaba da gudu a cikin zuciyarsa.


me yasa ya ceci sarauniya Rahila kuma me zai faɗa wa mahaifinsa? Wane tabbaci yana da cewa sarauniya ba za ta kashe shi ba idan ta warke?......


BAYAN WANI LOKACI 


Rana na shirin faɗuwa lokacin da Prince Tarhim ya dawo fadar fuskar sa cike da shakku da ɓoyayyen tausayi yana sane da cewa idan aka gano cewa ya ceci Rahila, matsayinsa na ɗa ga sarki Mujse zai shiga haɗari, amma zuciyarsa ta yi shiru a kan komai – ya fi yarda da abin da yake ji fiye da hukunci ko hukuma.


A ɓangaren mahaifinsa, Sarki Mujse  ana ta cigiyar ɗansa. hana mamakin dalilin da yasa bai dawo da wuri ba, amma yana zargin akwai wani abu da ɗan nasa ke ɓoye masa.


A cikin wani ƙaramin ɗaki a ƙasan ƙaton gida mai dakuna ashirin da huɗu, tsohuwar mai magani ta shimfiɗa Rahila akan shimfiɗa mai ƙyalli da ɗan kamshi na turare, tana jin jikin nata yana murmurewa, amma zuciyarta ba ta fahimtar inda take ba.


“Ki kwanta, ki huta. rayuwa tana juyawa,” in ji mai magani cikin murya mai laushi kamar ta uwa.



Prince Tarhim, ɗan sarki Mujse , ya dawo daga tafiyarsa ta tsawon wata uku a ƙasar Habasha inda ya je neman dabarun mulki da ilimin soji. Kyakkyawan saurayi ne, mai hikima da nutsuwa, amma ba ya shiga cikin al'amuran soyayya ko fadace-fadace na fada.


Da isowarsa, ya tarar da wata ƙatuwar shiru a fada  an ɓoye masa komai, amma ba don haka ba sai da hankalinsa ya kai ga jin cewa akwai wani abu mai ɓoye a gidan sarki.


A daren da ya dawo, ya shaida ganin wani bawa yana shiga ɗakin sirri da kwanon abinci. yayi mamaki, domin wannan ɗakin ba a yawan amfani da shi sai da wani sirri mai girma.


"Waye a ɗakin?" ya tambayi bawansa.

“mai martaba ne ya hana kowa magana akai, ranka ya daɗe,” bawan ya ce da kansa yana rawa Tarhim ya gyara tsayuwarsa, ya ce cikin natsuwa: “Na isa in sani. gobe da asuba, zan je kaina.”


Washegari da safe, Prince Tarhim ya leƙa ɗakin sirri. kafin ya buɗe, ya tsaya yana sauraron wani motsi.

daga ciki, ya ji murya mai rauni tana karanta addu’a cikin sanyin murya.

ya bude ƙofar da hankali... idanuwansa suka sauka a kan Rahila, wacce ta zauna cikin tabarma, tana daure da farin zani, gashinta ya bazu kan kafadarta.


Lokaci ya tsaya.


Rahila ta dago ido lkacin da ta kalli Tarhim, zuciyarta ta ɗan tsinke – ba domin tsoro ba, amma domin tunanin irrin halarci da ya mata na ceto rayuwar ta duk taye sanyi tasha tambaya kanta cewa me yasa har yanzu bai dawo garita ba har sarki Mujse ya gano inda take ya rufe ta yana azabtar da ita bisa laifin mahaifinnta duk gaba da faɗa da take tunkaho dashi tun da Prince Tarhim ya ceto ranta ta rasa dalilin faɗan da zataye akansa tabbas tana da. burin kashe su dukkan su to amma akan wani dalili tabbas mahaifin ta mugun sarki ne akan bayin sa ya aikata zunubi daban daban amman hakan ba wai ya na nufin a ɗauke fansa akan ta ba ita ma bawai tayi ta faɗa har tsawon rayuwar ta ba Amman rashin ganin Prince Tarhim ya tabbatar mata da tazama losser !..



Bai ce mata komai ba ya juya zuwa fada kai tsaye domin ganawar sa. da mahaifinsa Sarki Mujse ya  tsaya gaban sa  da ƙarfi da girmamawa " Ya kai baba na nasan rashin ɗa akwai cutarwa musamman idan ya kasance maƙiyanka ne sukaye galaba akanka" yakai Baba na Sarki Numan mutum ne azzalumi da duniyar mu ta sanshi akan mulkin sa baya barin kowa cikin sallama a haka muka samu nasarar shiga har fadar sa mukaye galaba akan sa shin Baba kasan dalili !?

Saboda karshen zalunci sa a hannun mu yake kuma karshen mulkin sa ya ƙare a dalilin mu mun raunata sa mun kashe sa har abada bazai dawo ba mun ɗauke fansar kashe mana namu da yayi ,to shine me laifin me yasa muma yanzu muka dawo azzalumai irinsa ka tuna mulkin da kakiye cikin aminci da adalci ya za'a yi mu azabtar da Rahila bisa laifin uban ta ?, 

shin ta kashe mu ko ta dauke fansa ko ta cutar damu a'a Baba to me yasa ka rufe ta kake azabtar da ita tsawon wanan lokacin "?.



Rungumar juna sukaye nan Sarki ya share hawayen sa da cewa " tabbas na aika ta kuskure mai girma na azabtar da wanda bashi da laifi kuma nasan cewa   soyayya mai girma ce a zuciya ka daga lokacin da kaganta shiyasa na fara gaba da ita don inason ka kasance da Afra matsayin mijin ta Amman nayi laife ka gafarta min yaro na ka zaɓi muradin ka a rayuwar nan sanan sanyi murabus zaka kuma kan sarauta nan da wata ukku za'a yi wanan bukin ...




BAYAN WATA UKKU 


Jama’a suka ɗaga kai cikin mamaki.


Dukka yankunan sun taro an tabbatar da Prince Tarhim a matsayin sarautar sa 


“Ban tursasa masa ba, ya aikata haka bisa adalci da tausayi kuma yanzu na yarda da zaɓinsa. Idan zuciyarsa ta karɓi Rahila, to hakan na nufin akwai wani ƙuduri na sama.”

Sanan Princeces Rahilat ta dawo daga muƙamin ta na asali yankunan mu na ƙarƙashin ta sarauta ɗaya ne kuma itace asalin jinin yankin Buga Afrika 



Rahila ta ci gaba da zama ginshiƙi a masarauta, yayin da ake yawan kawo mata mata da yara don karɓar yaƙi  da shawara ta zama cikakkiyar Princess nata a inda ta rungume jarumin ta Tarhim domin a duniya idan akwai wanda take muradun to mijin ta ne shine asalin jarumin da take buƙatar kasance wa dashi tsawon rayuwar ta......



---

BACK TO STORY

BAYAN WATA 



AJIYAR ZUCIYA


Ajiyar zuciya mai nauyi Ihsan ta sauke, yayin da ta buɗe idonta a hankali, idon ta kai ga duk sansanin da suka taru a kusa da wutar da suke zaune, idanun mutane sun cika da kewa, da kuma ƙaunar jin ci gaban labarin da ta kawo musu suna kallonta da nutsuwa, kamar sun manta da gajiyar hanya, yunwa da ɓacin rai tayi shiru na ɗan lokaci, sannan ta sake numfasa.


“Wannan shi ne labarin Princess Rahilat,” ta faɗa cikin natsuwa. “Ina fatan ya ɗan ɗauke muku kewa a cikin wannan mawuyacin yanayi.”

duk suka jinjina kai sai Maryam ta ɗaga hannu cikin annashuwa.


“A gaskiya labarin ya kayatar, Ihsan. Amma ina da tambaya,” ta ce tana kallon ta kai tsaye. “Meyasa kike mana labari da Hausa da Turanci a haɗe?”


Ihsan ta murmusa, ta gyara zama kafin ta amsa.


“Hakika tambayar ki ta da muhimmanci Maryam domin shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce, kafin turawa su shigo nahiyarmu, sukan ɗauki baƙaƙen fata tamkar bayi ne sun raina mu, sun mulke mu , amma akwai wani sarki mai suna Numan, wanda ya ƙwato yanki biyar daga hannun turawa, ya mayar da su 'yan ƙasa masu cikakken 'yanci.”


Ta dan yi shiru, tana kallon yadda idanu suka cika da sha'awa.


“Shi ya sa ya zama sarki na musamman a zamaninsa duk da kuwa mahaifin Rahilat azzalumi ne, amma saboda bajintarsa da yaki da turawa, aka ba diyarsa Rahilat sarauta – don ta ci gaba da kare mutuncin mutane kamar ku da ni. Wannan ne dalilin da ya sa nake haɗa Turanci da Hausa – domin har yanzu muna da ragowar tasirin turawan, amma da karatun irin wannan ne za mu dawo da mutuncinmu da fahimtar tarihinmu.”


Hannu suka sa, suka rungume ta duka daga gefe kuma Yazid ya ce da dariya:


“Wallahi, Ihsan, wannan tafiya tazo da darussa  labarin Rahilat ya ɗaga min zuciya!”

John ya ɗora: “It’s like traveling into history and coming back with strength.”

Ado ya jinjina kai yana murmushi, “toh yanzu fa dai na tabbata, Ihsan ke ce jigo a cikin wannan tafiya, bari mu ci gaba da tafiya gobe, amma yau... yau dare ne na tunani.”


Suka kalli juna da murmushi, suka miƙe suna shirin kwana.


Daga can gefen zuciyar Ihsan, sai ta ɗan lumshe ido tana tunani:


"Bayan wata... akwai haske kuma wannan shi ne farkon komai."





continued by narnah ƙanwar soja ✍️✍️


Post a Comment

Previous Post Next Post