RANDAR CIKIN ƊAKA...
©UMMU AFFAN
Page 13-14
Tsit nayi, ina toshe bakina da hannu ɗaya, bagaɗaya jikina rawa yake, kakkarwar da bakina ke yi ya sa na kasa sake furta ko da kalma ɗaya ce bayan suɓul da bakan da nayi a farko.
"Nihlah!"
Naji Adyaan ya kira sunana a cikin sauti, kafin ya ɗaura da cewa.
"Ina son ganinki, a ina ki ke ganin za mu haɗu?"
"Kayi haƙuri hakan ba zai yuwu ba."
Na tsinci bakina da furtawa a hanzarce yana kai aya.
Numfashin da ya sauke ni kaina sai da na jiyo ta cikin waya, sai kuma naji ya tsinke kiran. Bin wayar nayi da kallo kamar ina hakaito fuskar Adyaan a jikin screen ɗin, ƙara lafewa nayi saman gado hawayena sun kasa daina zuba, ban san lokacin da wahalallan bacci ya yi awan gaba da ni ba.
Adyaan pov.
Bin wayar da kallo ya yi, yana nazarin halin da ya tarar da Nihlah. Tsaye ya miƙe ya duka saga faffaɗan bedroom ɗin shi, zuciyarsa tana ƙuna makamanciyar yadda ruwa ke tafasa a tukunya.
'Wacce hanya zan bi domin fitar da Nihlah a cikin wannan mugun halin?'
Wani sashi na zuciyarsa ke tambayarsa amma ya gagara samo amsar, tabbas ya so Nihlah kuma yana kan sonta har yanzu so irin wanda yake jin har abada ba zai bar gangar jiki ba har sai ranar da ruhi ya fice a jiki. Naushin iska ya kai da hannunsa cike da ƙololuwar tashin hankalin. Tunanin kiran Muzammil ya yi, sai dai da ya duba agwogwo sai ya fasa tunawa da ya yi bai kamata ya kira mai iyali a daidai wannan lokacin ba. Komawa ya yi ya zauna bakin bed tare da ciro hoton Nihlah a lokar gefen gadon ya ƙura mata ido, yana shafa gewayyiyar fuskarta mai cike da annuri. Hoton yasa a ƙirjinsa tare da kwanciya fuskarsa na kallon silif, da haka bacci ɓarawo ya sure shi.
Ƙarfe shidda Hajiya taga har lokacin Adyaan bai fito ba, ƙa'idarsa ne in dai yana gari to idan ya tashi da asuba sai yazo ya duba Hajiyarsa ya ga ko ta tashi, duk da kuwa kullum sai ta riga shi tashi amma baya gajiyawa sai ya shiga ya duba sannan ya wuce masallaci, amma yau shuru kamar malam yaci shurwa. Shidda da rabi tayi shuru, tana ganin bakwai ta ƙyasta ta miƙe, jiki a matuƙar sanyaye tana fargabar halin da zata je ta iske tilon ɗan nata. Ta daɗe bakin ƙofar shi kafin tayi ƙundunbalar shiga cike da zullumi da fargaba.
Ganin shi kwance kamar gawa ya ƙara furgita kwanyarta, "Adyaan!" Ta kira sunansa, shuru ba amsa, da sauri ta ƙarasa tare da girgiza ƙafarsa. Ganin yana miƙa ta sauke ajiyar zuciya.
"Adyaan lafiya kuwa, har bakwai tayi ba tare da kayi sallah ba?" Da sauri ya miƙe, yana jin kansa na ciwo, take hoton Nihlah ya faɗo saitin ƙafar Hajiya. Bin hoton tayi da kallon kafin ta dube shi cike da tuhuma.
"Tunanin matar wani yasa baka kwanta da wuri ba bayan hirar da muka sha kuma kazo ka ɗaura da tunaninta ko, har ka kasa bacci ka makara a sallah?"
Ganin hawaye na bin fuskar Adyaan ya girgiza zuciyar Hajiya.
"Kuka akan mace Adyaan? Yaushe zuciyar maza ta faɗi har ka ke kuka akan macen da ke gidan aurenta?"
"Kiyi haƙuri Hajiya zuciyata ta riga ta raunana, tabbas Nihlah tana cikin mugun halin da take taimakon wani a al'amarinta."
"Bana son shashanci Adyaan, shin bata da dangin ne ita kaɗaice da kake son taimakonka? Ina hanarka da shiga hurumin da ba naka ba."
"Amma Hajiya..."
Ɗaga masa hannu tayi,
"Ya isa haka, kaje kayi wanka kayi sallah ina jiranka a parlour."
Daga haka ta fita daga ɗakin nasa, bin bayant ya yi da kallo zuciyarsa na ɗillin-ɗillin.
Yaya Md pov.
"Farrah wai me ki ke nufi ne?"
Wani kallon tara saura kwata tayi ma shi.
"Komi ma nake nufi Mudassir tunda har zaka iya cin amanata, wai ashe wannan shegiyar farar ƙafar ciki gareta? Na rantse da mai busan numfashi bazaku haihu tare ba, ina neman hayyar figeta a rayuwarka ashe kai kana can kana shagalinka da ita. To wallahi ba za a gogawa 'ya'yana gashin jaki ba, talauci ya yi ta bibiyarsu wallahi sai cikin ya zube in dai Farrah ne sunana."
Bin ta ya ke da kallo cike da mamakin jin furucinta.
"Shin idan ciki ne a jikin Nihlah aibu ne? Ai da ubansa ba shege ba ne sai da kowa ya shaida a ciki kuwa har da mai jar hula."
"Zagina ka ke Md? Eh naji mahaifina yana cikin 'yan ɗaurin aure amma wallahi sai cikin ya fita, ba za a shafawa yarana kashin awaki ba. Wannan ma da aka ɗanɗana mana ya isa. Idan da tunani ai da yanzu yaci ace ka rabu da wannan ƙarfen ƙafar, tayi sanadin salwantar danƙareran gidanka, haka kasuwancika yanzu sai raragefe, da motocinka uku yanzu ba ko ɗaya a babur kake yawo, ɗan'uwanka Muzammil da ƙarƙashinka yake yanzu kaine ƙasansa, ko wannan bai isheka isharar sakin Nihlah ba?"
"Ko dai me zaki ce sai kiyi Farrah, ke baki isa kisa na rabu da matata ba."
"Idan ka dawo yawo a keke ai ka sake ta."
"Sai kiyi kuma, kan ki ake ji."
Rigarsa ya ɗauka yana kiciniyar sakawa sai ga Maamah da Najma sun shugo.
"A'a Maamah lafiya kuka dawo School tun yanzu?"
Kuka Najma ta saka tare da faɗawa jikin Maminsu yayin da Maamah ta ƙara so jiki a mace ta ce"Daddy an koro munu ne wai tame biyu ba ka biya mana kuɗin makaranta ba."
"To kukan me Najma ta ke?"
"Wai don an saka yara suna mana tafi ba mu biya ba shine take kuka."
Da sauri Farrah ta amshe, "Ai dole tayi kuka, lokacin da ka saka Maamah school kuɗin shekara guda ka biya mata amma Najma ta shiga a lokacin mai farar ƙafa, gashi duka ka kasa biya musu don Allah Md ko wannan ba zai sa ka rabu da yarinyar nan ba mu dawo rayuwarmu mai daɗi da rufin asiri."
Miƙewa yayi daidai gama saka rigarsa ya dafa kan Najma ya ce"Kuyi haƙuri yaran Daddy in sha Allahu zan biya muku kuɗin makaranta." Yana gama faɗa ya fita, ya daɗe a waje yana tunanin irin wannan sauyin rayuwa da ya shiga kafin ya tada babur ɗinsa ya fita, bulayi yayi tayi a titi yana tunanin mafita gashi lokacin biyan kuɗin yahar gidan da suke zaune ya kusa ga kuɗin makarantar yaransa, babbar makaranta ce suke zuwa akan layin da suke haya take, hakan yasa yaran da kansu suna iya zuwa kuma su dawo duk da dai indai yana gidan shi ke kai su tunda Maamah shekarunta goma yanzu Najma na da bakwai. Daga ƙarshe gidansu ya wuce kai tsaye mahaifinsu yana da rufin asiri amma mutum ne mai yin komi a tsare ba lallai ba ne idan ya tambaye shi ya ba shi kuɗin ta cikin daɗin rai, zai shiga sassansu ya hango Maman Nihlah tana ta aikin ƙuli da yake shine sana'arta, ƙarasawa ya yi tare da duƙawa yana gaisheta ta amsa cikin fara'a da tambayar iyalinsa ya tabbatar mata da suna lafiya. Sanin ƙorafin Umma ya ƙarashe shiga ya gaisheta don ya san ta jiyo muryarsa,
"Ya haƙuri da mai farar ƙafa, wallahi duk ka faɗa Muddasiru, aure ko wata biyar ba a yi ba amma ka haɗu da iftala'i kashi-kashi, lallai kana haƙurin iya zama da ita, Allah dai ya ƙyauta."
Bai iya amsa mata ba ya fito kawai tare da yiwa Mama sallama ya wuce can part ɗin su.
"Subuhanallah Muddassiru zonan, maza zo kusa da ni." Babu musu ya ƙarasa kusa da kakar ta su.
"Ciwo kayi ne kwana biyun da ban ganka ba ko yaya? Ka ga kuwa yadda ka lalace ka fita a hayyacinka?"
Murmushin yaƙe ya yi tare da furta,
"Babu komi Hajja, na same ku lafiya."
"Wallahi ban yarda ba, aradun Allah kaima ta fara lashe maka kurwa kamar yadda uwarta ta lashe na Musa. Dangin nufawa dangin maita ai kuwa da sake, na jure da ɗan cikina bazan iya jure na jikana ba, Muddassiru ka sauwaƙewa Nihla ila ba'asan babu lalai ba dole aradun Allah sai ka sake ta a yanzu...."
*LAST FREE PAGES ZAKU SAMU COMPLETE A WAJENA YANZU HAKA* 08104335144
Masu buƙatar littafin za suyi magana ta lambar da ke sama ko a tura kuɗi kai tsaye 500 ta 8104335144 Opay wallet Fatima Rabiu Sunusi sai a tura shaidar biya ta 08104335144 na gode.
#Nihlatulkhair
#YahMd
#YahMz
#Adyaan
#Amal
#Farrah
#UmmuAffan
#RandarCikinƊakaa
#2025