Ku Tsaya Matsayin Ku, Ku Daina Hassada Da Yarfen Siyasa, Shaikh Albaniy Bashi da Wata Alaƙa Da Zarge-Zargen Ku - Kwamared Salihi

Shaikh Albaniy

Ofishin Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari ya musanta zarge-zargen da aka yi wa Sheikh Jamilu Abubakar Albani, kan kwamitin shirya Gasar Karatun Al-Qur’ani a Jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa da aka fitar wacce ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga sunayen membobin kwamitin cewar "Malaman Alkur'ani Gwanayen Alkur'ani masu yaɗa Alkur'ani da koyar da tarbiyya a faɗin arewacin Najeriya su ashirin da biyu 22 sun fito sun miƙa saƙon su ga Gwamnatin jahar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Malam Uba Sani irin halin da suke ciki don ayi gyara tunda harkar Alkur'ani gaskiya ce shine wasu ke ƙaryata su har da cin mutumcin." karamar hukumar ta bayyana takardar korafin da aka aika wa Gwamna Uba Sani a matsayin "mugunta ce, siyasa ce kawai, kuma ba ta da tushe."

Shugaban Majalisar Matasa na kasa reshen Karamar hukumar Sabon Gari, Kwamared Jibril Suleiman Salihi ya bayyana hakan a matsayin hassada ne da yarfen siyasa.

"A binciken da muka yi min gano ainihin abinda ke faruwa in da muka gano wasu daga cikin jerin sunayen membobin sun tabbatar mana cewa ba su ne suka hannu a wannan takarda ba, suma ganin kawai sukayi wasu ma dake ciki ba Asalin yan kwamitin bane." Ina ji Kwamared Salihi.

Kwamared Jibril Suleiman ya ƙara da cewa " wannan abin da aka ɗauko ba zai haifar da da mai ido ba, cigaba da hakan zai zama cin mutuncin ne da ita kanta kungiyar Malamai ta ƙasa, Kungiyar Musabaqa ta ƙasa da Kungiyar addinin Musulunci da ma mu matasa baki ɗaya."

"Wannan abu anyi shine kawai saboda hassada da ƙiyayya don kasƙantar da Sheikh Jamilu Abubakar Albani a siyasance da kuma idon duniya." In ji Kwamared.

Kwamared Salihi yayi kira ga Kungiyar Malamai, da na Musabaqa ta ƙasa da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da kada su yarda bar wasu mutane su zubar da Mutunci da Ƙimar Musulunci.

Sanarwar  Ofishin karamar hukumar ta fitar ta jaddada sadaukarwar Sheikh Albani yayi wajen bunƙasa ilimin Qur’ani a jihar Kaduna tsawon shekaru goma, ta nuna irin yadda yake amfani da dukiyarsa wajen ganin nasarar gasar karatun Al-Qur’ani tun daga shekarar 2015.

Game da zargin amfani da motar Sienna ta gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, karamar hukumar ta bayyana cewa motar tana hannun kwamitin ne, kuma ana amfani da ita ne kawai don ayyukan hukuma. An cire alamar gwamnati a jikin motar ne saboda dalilan tsaro, don kauce wa satar mota da kuma amfani da ita ba da izini ba.

Karamar Hukumar Sabon Gari ta kuma sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Uba Sani tare da kira ga jama’a da su mayar da hankali wajen hada kai da ci gaba da tallafawa ilimin Qur’ani a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post