Aure wata tsattsarkar sunnah ce ta Annabinmu, Annabin Rahama, Annabi Muhammad (S.A.W.). Ya sanar da mu cewa zai yi alfahari da yawaitar al'ummarsa ta hanyar aure a Ranar Alƙiyama. Bugu da ƙari, aure ibada ce, amma ba wajibi ba ce ga kowa! Yin aure ba ya ba mutum tikitin shiga Aljanna kai tsaye, haka kuma ba ya kai mutum Wuta kai tsaye. Sai dai yana zama wata hanya ta tara ayyukan alheri da za su kai mutum Aljanna, ko kuma ayyukan da za su jefa shi cikin Wuta idan bai kiyaye hakkokinsa ba.
Babban manufar aure da cikakkiyar fa'idarsa tana cikin maganar Allah Madaukakin Sarki ta samun soyayya da natsuwa tsakanin ma'aurata, domin a gina addini tare da taimakon juna wajen rayuwa ta gari da kuma more ni'imomin duniya. Saboda haka, soyayya da tausayi su ne ginshiƙan aure, domin yayin da shekaru ke ƙaruwa, tausayi da jinƙai sukan maye gurbin zafin soyayyar da aka fara da ita tun farko.
Ta sauke wani dogon numfashi mai nauyi, tana ƙara matse sitiyarin motarta yayin da ta ƙara gudun motar da kilomita talatin a cikin awa guda, tana sharar kwalta a kan babbar hanyar Legas.
Ba za ta ce maganganun Momma ba su taɓa zuciyarta ba, amma ta riga ta yanke shawarar cewa babu wata magana da za ta sake sa ta zubar da hawaye ko kuma ta bari a ci mutuncinta kamar tabarma da ake taka wa.
Ba za ta taɓa yin aure a wannan duniyar ba. Kuma babu wata magana mai zafi ko cin mutunci da za ta sa ta kusanci maza.
Ma dai me ya sa mutane suke aure? Don gudun aikata alfasha ko? To ita ba za ta aikata alfasha ba, saboda haka ba ta da buƙatar aure.
Tsananin ƙin auren da ke cikin zuciyarta ya sa ta zurfafa bincike kan littafin Al-'Ulama' Al-'Uzzab Alladhina Atharu Al-'Ilm 'Ala Az-Zawaj (Malaman da ba su yi aure ba, waɗanda suka fifita neman ilimi a kan aure). A cikin littafin ta karanta cewa malamai har talatin da bakwai ne suka koma ga Mahaliccinsu ba tare da sun taɓa yin aure ba. Cikinsu akwai manyan fitattun malamai da suka yi fice a tarihin ilimin Musulunci kamar Imam An-Nawawi da Ibn Taimiyyah.
Da wannan hujjar, ta gamsar da kanta gaba ɗaya, ta kuma watsar da tunanin aure baki ɗaya, balle ma soyayya.
A wannan lokacin babu abin da ta tsana fiye da maza. Har ta kai ga cewa tana guje wa mahaifinta; sama da shekaru biyu kenan ba ta gan shi ba, ba kuma ta ji muryarsa ba.
Ta tsani kalmar "Soyayya" ƙwarai, tana kallonta a matsayin wata guba da ta sha wadda ta lalata rayuwarta. Ta yi imani dari bisa dari cewa duk irin sadaukarwar da mutum zai yi saboda soyayya, ba ta biya shi da alheri. Abin da take bayarwa shi ne ciwo da baƙin ciki kawai.
A ganinta, soyayya ba ta da wani tsayayyen siffa, kuma ba ta san aminci ko riƙon alƙawari ba. Wata sha'awa ce kawai ta ɗan Adam. Domin soyayya ba ta wanzuwa sai da wani dalili. Kuma idan wannan dalilin ya gushe... sai soyayyar ma ta gushe tare da shi.
Sauke Safara a Taɓo Complete Hausa Novel
Danna maballin da ke ƙasa domin sauke littafin daga Google Drive:
📥 DOWNLOAD
Tags
Hausa Novels
