_Bossladieswriters_
_Ku yi following link ɗin nan domin shiga WhatsApp Channel ɗin mu, don karanta littafin daga farko, da kuma abubuwa masu muhimmanci da za su amfane ku👇_
*_✨A CIKIN RAYUWA✨_*
_New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_
_ZAINAB BATURE_
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
22
Bayan sallar issha su Imrana na a ƙofar gida wurin tuyan awara shi da Hamza, ƙamshin da ya cika ma Imrana hanci ne ya sa shi saurin ɗagowa don ya gane irin ƙamshin mutumin da ya zo rannan har ya basu kuɗi ne, aikuwa shi ɗin ya hango a tsaye ɗan gaba da su, da sauri ya miƙe ya nufe shi ya tsaya daga gaban shi ya ce, "Ina wuni, awaran za a baka?" Kai Deen ya ɗan jinjina masa yana kallon sa yau ma fuskarsa na rufe da nose mask, "To ta nawa za a baka?" Imrana ya tambaya, shiru ya yi bai ce masa komai ba, ganin haka ya sa Imrana cewa, "Ko in kira maka yaya Salma?" Sai lokacin ya ɗan girgiza masa kai, hannu ya kai cikin aljihun wandon jeans din sa ya fiddo kuɗi ya miƙa masa, da sauri Imrana ya miƙo hannu har da ɗan kakka6e su kafin ya amsa, waro ido ya yi ganin kuɗin masu yawa, a ɗan ruɗe ya ce, "Ai awaran bata kai ta wannan uban kuɗin ba, duka ma wadda ta rage bata wuce ta dubu ɗaya ba fa." Har sai da ya sa Deen yin murmushi ta cikin mask ɗin ganin reaction din da fuskarsa ta nuna, hannu ya kai ya ɗan zame mask ɗin calmly ya ce masa ya kai kuɗin gida awaran da ta rage a raba ma mutane, da sauri ya amsa da to ya juya zan nufi gida, daidai nan Salma ta fito tana ƙwala ma Imrana kira jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta yafa ƙaramin gyale a kai, da ƴar sassarfa ya nufe ta sam bata lura da Deen ba, yana zuwa gaban ta ya miƙa mata kuɗin ya ce, "Yaya Salma kin gani wannan mutumin da ya zo shekaran jiya ne ya sake dawowa ya bada wannan kuɗin ya ce in kai gida, kuma a raba ma mutane awaran da ta rage." Har sai da gabanta ya faɗi jin abun da ya ce, da sauri ta tambaye shi ina mutumin yake ya juya yana nuna mata Deen da har ya juya ya fara tafiya, bin shi da kallo ta yi a ranta tana mamakin yadda yau ma ya dawo ya basu kuɗi, haka nan sai kuma bata ji daɗin zuwan da ya yi ya iske suna yin awaran ba, wani tunani ne ya zo mata a rai da sauri ta bi bayan shi, tunanin yadda zata tsayar da shi ta yi don bai ma san ta biyo bayansa ba, "Ya Deen..." Kawai sai ji ta yi ta kira sunansa da ɗan ɗaga murya ba tare da ta shirya ma hakan ba, cak ta tsaya ganin ya dakata tare da juyowa, slowly ta ɗan matsa kamar mai tsoron ƙarasawa gaban sa, jim ya ɗan yi yana kallonta kafin ya kai hannu ya zame mask ɗin fuskarsa, da yake akwai wutar nepa wasu gidajen layin suna da hasken globe a gaban su hakan ya sa suna iya ganin fuskokin juna ta hasken da ya ɗan haska, tana kikkafta idanu ta ce, "Ina wuni.." Kai ya jinjina sai kuma ta ji ya ce, "How are u?" Ta amsa da, "Lafiya lau," Kai ya ƙara jinjinawa suka ɗan yi shiru, wani irin ƙwarjini yake mata hakan ya sa ta rasa mi zata ce masa, "Any problem?" Ta ji ya sake tambaya, cikin ƴar in ina ta ce, "Dama yanzu ƙanina ya nuna mani kuɗi ya ce kai ka bashi ya kai gida..." Ya ɗaga mata kai alamar eh, "An gode Allah Ya saka da alkhairi....da innarmu ma ta ce kada a yi awaran yau, dama jiya bamu yi ba saboda wanccan kuɗin da ka bamu, ni ce na ce mata ai da ka bamu kuɗin ba cewa ka yi mu daina yin awaran ba..ita bata so a yi ba ni ce na nuna ina so a yi.." Cike da kama kai ta yi maganar ita kanta bata ma san miye amfanin yin wannan maganan ba, ɗan murmushi ta ga ya yi calmly ya ce, "Yea, ba don ku daina bane, it's just a gift." Ɗaga kai ta yi itama yanayin fuskarta kaman zata yi murmushi ta sake cewa, "Mun gode Allah Ya ƙara buɗi na alkhairi." "Ameen.." Ya amsa ƙasa-ƙasa, shiru suka ɗan ƙara yi kafin ta ji ya ce shike nan zai iya tafiya, da sauri ta ɗaga masa kai daga haka ya juya yana ƙoƙarin mayar da mask din, har zai fara tafiya da sauri ta ce, "Ko in zubo maka awaran?" Juyowa ya yi ya kalle ta ya girgiza mata kai ta cikin mask ɗin ta ji ya ce, "Thank you." daga haka ya juya ya ci gaba da tafiya cike da natsuwa, tsaye ta yi a wurin tana ta kallon sa a cikin ranta ba ƙaramin mamaki yake bata ba, juyawa ta yi bayan ta ga ya tsallaka hanya ta nufi gida, tana shiga ta ga innarsu a tsaye a bakin baranda tana riƙe da kuɗin da alama shigowar ta dama take jira, a sanyaye Salma ta ƙarasa wurinta, da alamun mamaki ta ce, "Salma ashe yau ma zuwa ya yi ya bada kuɗin kuma kamar na shekaran jiya yauma dubu ɗari biyu ne." Kai Salma ta ɗaga ta ce, "Nima ina fita Imrana ya nuna mani lokacin bai daɗe da ya bashi kuɗin ba don bai ma kai ga barin wurin ba, shi ne na bi bayansa na yi masa godiya." Shiru innarsu ta ɗan yi kafin ta ce,"Duk sai na ji wani iri wllh, kada a ce ganin ana yin awaran ne ya sa shi sake zuwa ya bada kuɗin." Itama Salma da irin tunanin a cikin ranta, sai kuma ta ce, "Ai bayan na yi masa godiyar sai da na faɗa masa baki so a yi awaran bama ni ce na ce da ya bamu kuɗin bai ce kada mu yi sana'ar ba, shi ne sai ya ce eh kawai matsayin kyauta ne ya bamu." Jinjina kai innarsu ta yi har ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, "An gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi. Gaskiya mutumin yana da kirki ba kaɗan ba kuma bashi da girman kai wllh, Allah Ya kara masa ɗaukaka." Salma ta amsa da Amin,
"Inna yanzu a je a rabar da awaran?" Imrana ya tambaya, da sauri ta bashi amsa da eh, kallon Salma ta yi ta ce, "To shi bai son awaran? Na ji hajiya ta ce kaman yana son ta." Salma ta ce, "Ai sai da na tambaye shi in zubo masa awaran ya ce a'a." Ƴar dariya innarsu ta yi, ta ce, "In ban da abun ki Salma ta ya zaki tambaye sa haka, a tunanin ki zaki zubo masa abu ne ya riƙe ya tafi da shi?" Shiru ta yi tana ɗan murmushi itama sai yanzu ta gane shirmen da ta yi,
"Yanzu kina ganin ko a haɗa masa sai ki je ki kai masa?" Kai ta ɗaga ta ce eh, "To yi sauri ki je ki ga idan Imrana bai ƙarasa soya ɗanyan da ta rage ba sai ki ɗebo nan mu haɗa masa da kan mu, dama akwai sauran cefane sai a yi masa yar sauce ko?" Da sauri Salma ta ce eh ta nufi hanyar fita, without wasting time suka shiga haɗa masa awaran ita da innarsu, suna cikin yin aikin ne Salma ta roƙi innarsu idan zai yuwu a cikin kuɗin da aka ƙara basu a bada a yi ma su Habu ɗinkin makaranta ko da ba su duka ba tun da suna da yawa, murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce mata kamar ta shiga zuciyarta itama hakan ya zo mata a rai, idan babansu ya dawo zata yi mashi maganar sai a ga abun da za a ba su ya ba baban su Habu ɗin a siya masu kayan makarantar, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma Salma ba. Ba tare da an ɗauki lokaci ba suka kammala, awara mai ƙwai da sauce suka haɗa gwanin kyau a ido sai ƙamshi ke tashi, har da ɗan coleslaw suka haɗa dama suna da mayonnaise, suna gamawa Salma ta je ta canza kaya duk da yau bata zauna sosai wurin tuyan awaran ba duk Imrana ne ya yi amman saboda aikin awaran da suka gama ya sa take ganin kaman kayan jikinta sun yi dauɗa, doguwar rigar material mai mayafi ta sako wanda kayan na daga cikin irin waɗanda auntynta Kubra ke aiko mata daga Kaduna, har da turare ta ɗan faffesa duk don ta fito fess yadda Deen ɗin zai ci awaran, don a yadda yake ta tabbatar ba zai rasa ƙyanƙyami ba, bayan ta fito innarsu ta fiddo mata da awaran da aka zuba a cikin wata ƴar madaidaiciyar kula mai kyau, daga cikinta akwai irin yar farar roba mai marfi a nan aka zuba sauce ɗin, sai coleslaw ɗin aka sa a cikin wata ƴar farar roba irin ta takeaway ana ganin abun da ke a ciki,
"To a ina kike ganin za a saka kayan?" Innarsu ta tambaya tana kallonta, "A cikin leda ko?" Salma ta faɗa, "Amman kina ganin lafiya lau a saka a leda? Na ga su ƴan gayu zaki ga a ɗan kwando suke saka kayan abinci." Dariya maganar ta ba Salma ta ce, "To ai mu ba ƴan gayun bane bamu da kwandon, in dai ba a cikin riyon Usman za a saka ba matsayin kwandon..." Dariya ta saka kafin ta gama maganar ganin irin kallon da innar tasu take jefa mata, ta ce, "Ta ya za a saka kayan abinci a cikin riyo in banda abun ki, ai sai ma ya kasa cin abincin." Still dariya Salma take yi ta ce, "To kema innarmu tun da kin san babu kwandon kawai a saka a ledan mana ai ba wani abu bane." Amsa mata ta yi da to ta ce tana zuwa ta nufi hanyar ɗakinta da sauri, fitowa ta yi hannunta riƙe da wata farar leda mai ƙauri irin ta siyayya ta nufo Salma tana faɗin, "Ina ganin zai fi a saka a wannan ledan, dama ganin mai kyau ce yasa na 6oye ta." Kai Salma ta ɗaga, bayan an gama saka kayan ta ɗauka tana faɗin sai ta dawo, innarsu ta ce mata to, lokacin da ta kai bakin soro tana niyyar fita innar ta ɗan ɗaga murya ta ce, "Ki faɗa ma hajiya a yi mana godiya ya bamu kuɗi." Ta amsa mata da to daga haka ta fice. Hajiya zaune a falo ta kara waya a kunnanta tana waya fuskarta ɗauke da fara'a, da sallama Salma ta shigo cikin falon, bayan ta ƙarasa ciki ta tsaya ɗan gefe da hajiyan tana jiran ta gama wayan, bata daɗe da shigowa ba hajiya ta kammala yin wayar bayan ta ajiye a gefenta ta ɗago ta kalli Salma, da murmushi ta ce, "Salma ce..." Ta amsa mata, "Eh, ina wuni hajiya." Bayan ta amsa ta nuna mata kujera ta ce ga wuri ta zauna, zama ta yi ta ɗan yi shiru haka nan sai ta ji nauyin yadda zata faɗi abun da ya kawo ta, "Ya maman taku da ƴan'uwanki?" Da ɗan murmushi ta kalli hajiyan ta ce mata duk suna nan lafiya lau, hajiya ta ce, "Ma sha Allah." Shiru suka ɗan ƙara yi idon hajiya na akan tv, can ta juyo ta kalli Salma ta ce aiken ta aka yi? da sauri ta ce, "A'a, dama innarmu ta ce in kawo wannan a bawa yaya Deen, sannan ta ce in faɗa maki a yi mana godiya ya bamu kuɗi." Murmushi ne akan fuskar hajiya ta ce, "To, mi Deen ya samu?" Miƙewa Salma ta yi ta kai ledan gabanta tana faɗi mata abun da ke ciki, godiya hajiya ta yi ta ce bari a kirawo shi yana nan, wayarta ta ɗauka ta fara dannawa kafin ta kara ta a kunne, tana murmushi ta ce, "Ka zo falo ga saƙo an kawo maka." Daga haka ta cire wayan tana faɗin, "Tun ɗazun da ya dawo gidan yake a ɗaki, dana ji shirun ta yi yawa har leƙawa na yi na iske shi wai suna meeting ne da mutanensu yan ƙwallo ta kwamfuta." Ɗan murmushi ne akan fuskar Salma ba tare da ta ce komai ba, after few minutes sai gashi ya fito, wani irin faɗuwa gaban Salma ya yi ganin a yadda ya fito daga shi sai wando 3-quarter, da sauri ta sunnar da kanta ƙasa, daga gefen kujeran da hajiya take ya tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa ta ce, "Sarkin jin zafi, har ta kai an cire riga ke nan." Ɗan murmushi kawai ya yi, nuna masa ledan dake gabanta ta yi ta ce gashi nan dama Salma ce ta kawo mashi awara in ji innarsu, ɗaura idonsa ya yi akan Salma da bata
yarda ta ƙara ɗagowa ba, don a yadda ta gansa har tsorata ta yi ba wai don bata ta6a ganin namiji ba riga ba, wannan ma ta saba gani wurin su Auwalu da Sagir, sai dai akwai bambancin ƙirar jiki a tsakaninsu da Deen nesa ba kusa ba, gaba ɗaya a murɗe yake ga six-pack din cikinsa sun fito baro baro, fatar jikinsa fara tass da ita ba ko ɗan ta6o, yadda cikinsa yake a ɗame tamkar baya cin abinci, maido idonsa ya yi ya sake kallon ledan da ɗan alamun mamaki akan fuskar tasa, "Tukuici ne aka aiko maka, ta ce in taya su yi maka godiya ka basu kuɗi. Allah Ya saka da alkhairi." Sai da ya ji maganar da hajiya ta yi ya fahimci komai, ganin yana niyyar juyawa ta yi saurin cewa, "Ba zaka tsaya ka ci yanzu ba, awara ce na san kuma kana son ta." Hajiya ta faɗa idonta a kan sa, da hannu ya yi mata alamar zai saka riga ne daga haka ya koma ciki, sai da Salma ta tabbatar ya bar wurin sannan ta ɗago ta bi hanyar da ya koma da kallo, bayan ɗan lokaci sai gashi ya sake dawowa, singlet ce ya sako fara ƙal da ita kai ka ce a lokacin aka buɗe ta a ledarta ta kama jikinsa, a ɗayan 6angaren ya zauna yana ɗago fuskarsa suka haɗa ido da Salma, da sauri ta ɗan sunkuyar da kai tana gaishe sa ya ɗaga mata kai kawai, "Salma kai masa, sai ki je kitchen ki ɗauko masa plate." Ta amsa da to tana miƙewa, tana niyyar nufar dinning area ya dakatar da ita da hannu, ce mata ya yi ta matso masa da c-table ta ɗaura a sama, bayan ta yi kamar yadda ya ce ta wuce kitchen ta ɗauko masa plate sai da ta yi tunanin wanne yakamata ta ɗauko masa tsakanin spoon da fork, ƙarshe dukansu ta ɗauko bayan ta sake wanke su, fitowa ta yi ta nufo inda yake, bayan ta ɗaura abubuwan da ta ɗauko a saman table ɗin ta fiddo kulan awaran da roban coleslaw daga cikin ledan, har zata buɗe ta yi serving nasa wata zuciyar ta kwa6e ta da ya saka ta yin hakan? Dakatawa ta yi ta ɗago ta kalle sa ta ga shima ya kalle ta, slowly ta ce, "In zuba maka?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, sannan ta buɗe kulan ta fiddo da roban sauce ɗin, da fork ɗin da ta ɗauko ta yi amfanin wurin zuba masa awaran, sai da ya dakatar da ita sannan ta daina zubawa, ta buɗe sauce ta sa cokali ta zuba masa da coleslaw ɗin, ɗagowa ta yi da ɗan murmushi ta ce masa gashi nan, ya ɗan lumshe ido tare da ɗaga kai a hankali ya furta, "Thank you.." Juyawa ta yi ta koma kujeran da ta taso ta zauna, "Wannan awara ta musamman ce aka haɗa maka, don daga jin ƙamshinta ba sai an faɗa ba zata yi daɗi." Hajiya ta faɗa tana murmushi, sadda kai Salma ta yi itama tana ɗan murmushi, tabbas yana da kula kan abincin da zai ci, amman ya ji lafiya lau zai iya cin abun da aka kawo masa saboda ya riga ya san awaran da ake haɗa masa yana ci sune suke yin ta, a hankali Salma take ɗan ɗagowa tana satar kallon shi yayin da ya fara cin awaran a nutse,
"Salma ya makaranta, ko da yake weekend ne ba makaranta sai dai islamiyya ko." Maganar hajiya ta sauka a kunnanta, juyawa ta yi ta kalle ta da murmushi ta ce mata eh, ɗan jinjina kai hajiya ta yi ta ce Allah ya bada sa'a, bayan Salma ta amsa hajiya ta sake cewa, "Kin kwance kan ki ne?" Ta tambaya tana kallon kan Salma da ta saka hula bayan ya yi tudu sosai, "Eh, ɗazun na kwance." Kai hajiya ta ɗaga ta ce saura kitso ko, Salma ta ce, "Eh zan je a fara wanke mani sai a yi mani kitson." Jinjina kai hajiya ta yi tare da mayar da idanunta akan tv, bayan wani lokaci ta kalli Deen ta ce, "Saboda kai aka kawo mawa shine kuma ido guba?" Ba tare da ya kalle ta ba ya yi ɗan murmushi tare da kai awaran da ya ɗebo baki, sosai Salma ta ji daɗin yadda ya saki jiki yana cin awaran bai ma yi amfani da fork ba hannu ya saka, jinjina kai hajiya ta yi ta ce ya ci awara lafiya in dai ita ce zata rama ne, sai lokacin ya ɗan ɗago ya kalle ta still da ɗan murmushi a fuskarsa ba tare da ya ce komai ba ya maida idon shi kan awaran yana ci, sosai Salma ta shagala tana ta kallon shi don komai na shi na musamman, hatta yadda yake cin abinci da burgewa, bata ankara ba kawai ta ga ya ɗago sun haɗa idanu, da sauri ta sadda kan ta ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa ganin ya kama ta tana kallonsa, still ya yi yana kallonta don ɗagowar da ya yi magana yake niyyar yi mata, rasa ta ya zai yi mata magana ya yi ganin ta sunnar da kai, after few seconds ta sake ɗagowa da niyyar kallonsa suka sake haɗa ido, tana niyyar kauda idonta ta ga ya yi mata alamar kira da kan sa, bin sa ta yi da kallo cikin alamun rashin tabbas ɗin idan gaske ne kiran nata ya yi, sai da ya sake yi mata alamar ta je sannan ta miƙe ta nufe shi walking slowly, tsayawa ta yi a gaban table ɗin ya ƙara ɗibar sauran awaran cikin kulan, bayan ya zuba sauce da coleslow ya ɗago ya kalli Salma ya ce mata ta ɗauki sauran ta kai ma hajiya, bayan ta yi kaman yadda ya ce hajiya na ɗan murmushi ta ce ai ta yi zaton ba zai batan ba, plate ta sa Salma ta ɗauko mata itama ta zuba mata sauran ta fara ci tana yaba daɗin awaran, bayan Deen ya gama cin awaran duba tissue ya yi a nan bai ganta ba ya tambayi hajiya, amsa ta bashi da ga ta can a dinning area ta kalli Salma ta ce ta je ta ɗauko masa, a saman table ɗin ta ɗaura tissue box ɗin bayan ta ɗauko ya yi mata godiya, ɗaukar kayan da ya yi amfani da su ta yi ta kai kitchen, sai da ta wanke su sannan ta dawo cikin falon ta koma ta zauna, after some minutes hajiya ta gama ta kalli Salma ta ce mata ta je ɗakin Balaraba ta kira ta ta zo ta wanke kayan, miƙewa Salma ta yi ta ce bari ta wanke hajiya na ɗan murmushi ta ce ta kawo masu abun daɗi kuma a barta da wanke-wanke, tana murmushi ta ɗauki kayan ta wuce kitchen, bada jimawa ba Salma ta dawo cikin falon bayan ta gama wanke kayan, hajiya ta yi mata sannu ta amsa da murmushi ta koma ta zauna, bayan ɗan lokaci hajiya ta miƙe ta ce zata ɗan shiga ciki, jin haka ya sa Salma miƙewa ta ce zata tafi, hajiya dake kallonta ta ce ba zata jira ta fito ba, tana ɗan murmushi ta ce ma hajiya ta ga dare ya yi ne, "Haka ne kuma, an gode sosai, itama maman taku ki yi mata godiya." Ta amsa da to, har zata juya ta tafi hajiya ta ce ina kayan da aka zubo awaran Salma ta ce suna a kitchen ta ce to ta je ta ɗauko ta tafi da su, wucewa ta yi zuwa kitchen ɗin hajiya kuma ta nufi hanyar shiga ciki, lokacin da ta fito Deen ne kawai a zaune idonsa na kan tv, ledan da aka sako kayan ta je ta ɗauka ta maida su ciki, kallon Deen ta yi daidai lokacin ya maido idonsa kanta, tsaye ta yi tana ƴan kifce kifcen idanu cike da ƙarfin hali ta yi ɗan murmushi a hankali ta ce masa, "Sai da safe..." Kai ya jinjina mata calmy ya ce, "Thank you, I appreciate it." Murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Mu ma mun gode Allah Ya saka da alkhairi ya ƙara ɗaukaka." Kai ya sake jinjina mata da ɗan murmushi, juyawa ta yi ta nufi hanyar barin falon hannunta rike da ledan kayan, tana zuwa daidai bakin ƙofa ta ɗan juyo ta saci kallonsa, daidai yana ƙoƙarin miƙewa ganin haka ya sa ta yi saurin ƙarasa ficewa har ta kusa yin tuntu6e....
*_ZEELALUH✍️_*
